KAICO CHAPTER 1
*🌸🌸 KAICO!*🌸🌸
MALLAKAR..
Kyauta Daga Allah
Da
Khadija salis Ibrahim
(Maman Amatullah)
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION.
YABO
DUKKAN YABO DA GODIYA SUNTABBATA GA ALLAH MA ƊAUKAKIN SARKI MAI KOWA MAI KO MAI TSIRA DA AMINCI ƘARAWA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) DA IYALAN GIDANSHI DA SAHABBANSA DA WA IN DA SUKABIYO BAYANSU DA KYAUTATAWA.
Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne
Bamuyi shi dan cin zarafin wani ko Wata ba , in ya yi dai-dai da halin ki ko naka , sai kayi haƙuri akasine.
Wannan littafin na kudi ne 300# kachal👌🏻 ki biya kafin ki karanta domin neman ƙarin bayani ku tun tuɓemu ta wa'innan lambobin *** ko ***
Shafi na 1️⃣
free page
Fatima!Fatima!! Ake kwaɗa mata kira cikin daga Murya , wacce ake kira na hango tana sanya safa a ƙafafunta , kallo ɗaya na mata naga fara ce tass usul Fulani , Mash Allah na furta ya yin da na ta mike daga durkushen da tayi wajen saka safa , ita ba za'a ce mata gajera ba kuma ba'a za saka jerin dogaye ba , tanada dogon fuska da tsinin hancin ta me kyau .
Zazzakar Muryan ta me daɗin sauraro naji tana faɗin "Na'am gani nan zuwa mama" , cikin hanzari takaraso gaban Mahaifiyar ta , cike da ladabi tace Mamy na gani na tsaya shiryawa ne , wacce aka kira da mamy jakar Makaranta tamiko mata cikin tsananin damuwa tace "Kinsan banason kiyi latti shiga Aji gashi bakici wani Abun kirkiba, ga awara nan nazuba miki a wannan karamin cooler ɗin , dan Allah dakin samu dama ki tsaya kici , kinji yar Amana" mamy ta ƙarasa maganar tana karyar da kai gefe alamar roƙo , murmushi kwance akan Fuskar Fatima tace " Na gode mamy na Allah yasaka miki da gidan Aljanna" ta ƙarasa maganar tana rataya jakar ta hannun ta ɗauke da coolern awara ahanzarce tabar gidan tana gudun yin latti.
Itakuwa mamy tana fita Adua ta soma cike da tausayawa tana Neman kariyar ubangiji akan wannan yarinyar ta da dukan ya'yan musulmi.
*Bayero university kano*
Mai gadin Makarantar cike da mamaki yake kallon Fatima hannun ta dauke da cooler zata shiga Makarantar , kallon takalmar kafafun ta yake yana yatsina fuska , cikin rainin wayau yace " wai Fati gidan Ku basuda Zuciyar nema ne ? ya yi maganar yana wani yatsina baki Wani kallon ta jefa masa tareda tsayawa cak tana kallon sa ranta yana mugun tsuya kamar zatayi magana kome ta tuna saita fasa , cigaba da tafiyar tata tayi tana karkada kai , cike da nazarin kalaman sa ta shiga Aji.
Shikuwa yana ganin tafiyar ta , dariya ya soma yace " Haba yarinya ga shegen kyau Amma ga shegen tsiya saikace talauci akan su yakare , horn din da akeyi da mota ne , yasa shi ahanzarce yabude gate din ganin prince ne yazo da kansa , bakin sa a washe yafara barka da zuwa Yallabai yau fa da wuri kashigo , prince Khalid daga masa hannu yayi yana wani babbasarwa tare da hura hanci, bata re da yace da shi ko mai ba ya danna hancin motar tashi cikin Makarantar har parking space.
Cike da izza da takama yafito daga cikin Motar shida abokan sa, inda ɗalibai dake kai kawo suka fara sai yarima suna daga hannu , murmushi ya sakar musu yana mai daga musu hannu shida magoya bayan nasu.
Lecturer dakyar yabar Fatima tashiga Ajin acewar sa tayi latti , tasha magiya kafun ya barta ta tafi .
Takun tafiyar prince yana kokarin shigowa Ajin yasa dukan ɗalibai suka dawo da kallon su akan sa Har malamin nasu , cike da izza da takama yake taku ko kallon inda Malam yake beyi ba , yasamu waje ya zauna shida abokan sa , lecturer da ke kallon su har suka zauna , cikin barin jiki yaje gaban sa yana fadin barka da zuwa yallabai naga ko kallona bakayi ba , prince cikin bacin rai yace " au nine ma Zan gaishe ka? Bakin malam na rawa yace " inakwana ranka yadade ya gajiyar hanya , hannu kawai ya daga masa be bashi amsa ba , abokan sa ma Saida ya gaishe su sannan yakoma bakin Allo , cikin zallan mamaki Fatima ke kallon Abunda ke Faruwa , tashi tayi tana kallon Malam tace " sir haba sir wannan ai ba Adalci kakeyi ba ,ya za'ai dakyar kabarni nashigo Ajin Amma wani yashigo kabar shi harda bin sa da gaisuwa gaskiya kaji tsoron Allah , wannan ba tarbiyya kake koyawa mana,ta kai ƙarshen maganar tana jifan prince da wani mugun kallo ,Prince aharzuke ya tashi daga zaunen da yake cikin tafasar zuciya da kunar rai yace " keeeee yar gidan uban waye ke? Fatima ahankali ta ƙara saka idonta cikin nasa tare da cewa "kar da kakuskura kafirta wani mummunan furuci akan iyayena dan kuwa suna da daraja, ta kai ƙarshen maganar tana jan dogon tsaki, Cikin tsawa lecturer yace " Fatima Auwal kin San dawa ki ke magana get out kije kizo da iyayenki" magana ta kesonyi ya ɗaga mata hannu tare da cewa I say get out" ya faɗa a tsawace tare da nuna mata hanyar fita, soma tattara kayan nata tayi tana ƙoƙarin fita taji wata Kawar ta , tana faɗin "haba Fatima nace miki in har prince zeyi Abu kiringa shiru , a harzuke Fatima tajuyo tana kallon ta , tace " Akan me zanyi shiru? sabi damu bamasu arzƙi bane shi yasa za aci zarafinmu wake bayarwa ? Hafsa tace " Allah , takara da fadin wake hanawa ? Nan ma Hafsat tace " Allah , ajiyar zuciya Fatima ta sauke tana ciza labban ta , tace " tunda Allah keyi komai yariga ya tsara mana bamu ne , muka tsarawa kanmu , saboda mu ya'yan talakawa ne shiyasa mu a banza ake daukar mu , meye na fada na rashin Da'a wani yashigo Aji an barshi batareda an masa fada ba , wai kawai suna takama da Arziki , nida nazo akan lokaci korata ya yi saboda nakara minti daya kacal , Saida nabashi hanƙuri sannan ya aminta , rayuwa bazataci gaba ahaka ba , an saba yimin wannan wulakanci sai inzo akan lokaci Amma kuma abuge da wulakantani gaban jama'a , Maganar kora kuma in Allah yace " zanyi karatu wallah shi be isa ya hana ba" bata ankaraba taji , saukar mari a kuncin ta ,wan da yasata yin shiru batare da tashiryaba juwowa tayi tana kallon wan ya yi marin cikin Mamaki take kallon prince yana huci sama _ sama , ƙoƙarin kara mata yake , cikin zafin nama ta rike Hannun sa, tare da kwaɗa masa wani lafiyayyen mari wan da ya yi sanadin ɗaukewar jinsa nawani lokaci idanun ta cike da kwalla tace" kai har ka isa kasaka hannu ka mareni to in barci ka keyi ka farka ba dai fatima Auwal ba? tana kaiwa nan ta gewayeshi ta wuce tabarshi nan tsaye riƙe da kunci tsabar mamaki kasa ko motsawa ya yi a gurin ban da tafasa babu abin da ziciyarsa keyi, kamarshi wata ƴar talakawa zata mara a bainar jama'a lallai ta kirawo ruwan da bazata iya tareshiba, ƴan ajin yabi da kallo wa in da suka zuba masa ido kowa da abin da yake saƙawa a ranshi wasu natajin daɗin abin da fateema tayi wasukuma naganin wautarta, tsawa ya daka musu tare da cewa "Meye kuka wani zubamin ido, kamar baku sanniba sabi da muna furci to karkuyi tunanin Zan kyaleta ne , wallahi saita biya bashi zatasan ni prince ba kanwar lasa bane , Malam dake mamakin Faruwar Al'amarin da kuma jin jinawa irin juriyar fateema haƙuri yasoma bawa prince Khalid ,yana faɗin "Ranka yadaɗe ka barta zamu ɗau doka a hannun mu , cikin tafasar zuciya yace" waye babanta ? Gabakidaya class ɗin kowa rarraba idanu suka soma , dawo da kallon sa ya yi akan Hafsat yace " ke nasan kin san ko waye uban nata , kije gidan nasu ayau ki sanar masa ana Neman sa a goben nan kuma yazo da yar tasa , yana kai karshen zancen yafice daga ajin cikin hanzari , haka magoya bayan nasa.
Hafsa hankalin ta yayi mummunar tashi jin Abunda prince ya sata .
Fatima koda tazo dai-dai fita cikin Makarantar, taji karo da director ɗin Makarantar , muryan sa na rawa yace " keee! Ina zakije? bayan ana karatu , shiru tayi tareda dukar da kanta Banda hawaye babu abunda ke kwaranya daga idanun ta , kara maimaita maganar nasa yayi hakan yasa ta faɗin , an koreni daga Makarantar ne ? What ya furta cikin tsananin Mamaki yace " a iya sanina bakya latti ko laifi waye da danyan aikin nan kuma laifin me kika Aikata ne ? Muryan prince yaji daga Sama yana fadin nine nasa aka koreta har sai tazo da iyayen ta uban nata nake nufi , director kallon sa yake yace " au daman kaima Malami ne a Makarantar nan? Prince cikin izza yace " ina bada Umarni daga kan malamai har dalibai , kuma karka sake faɗin komai director Abdullahi in bahakaba ze kawo raunin acikin aikin ka ,kallon Fatima yake cikin tafasar zuciya yace ke kuma ba dai kince dani za kiyi ba to muzuba mugani ƴar talakawa kawai " cikin ƙunar rai Fateema ta ke kallonshi tare da cewa "Daɗintama ba mu muka bawa kanmu ba kamar yan da kaima ba kaine kabawa ka ka arzikin ba" oh har yanzu kina da bakin magana zanyi maganinki ni Khaled" "Kadaɗe ba kayi ba" ta ƙarasa mahanar tana jan tsoki tare da barin gurin,
Shikuwa director be ƙara faɗin komaiba sai ma mamakin Fateema da ya rufesa , yana sake da baki har prince yashige motar sa , shida abokan , fuuuu sukaja motar tareda tada musu Kura daga shi har mai gadin.
Mai gadin kallon Director yayi yace " sai haƙuri ranka shi daɗe kasan Prince Khalid baya ganin darajar kowa a makarantar nan. cikin danne fishinsa
Director cyace " Karka damu zanyi iya kokarina inga na gana da Mahaifin nasa daga haka yafice cikin Makarantar.
Fatima , kamar daga Sama Mahaifiyar ta Halima taga tashigo cikin gidan kai tsaye Ɗakin kwananta ta nufa tareda rufe fuskar ta da pillow tana rera kuka ahankali , cikin tsananin damuwa mamy tashigo tareda hayewa gadon tace" haba Fatima meya dawo dake bayan baki daɗe da fita ba , kodai bakida lfy ne? ta ƙarasa maganar ta sigar tambaya ƙara sautin kukan nata Fatima tayi tace" wallahi tallahi nina gaji da zuwa jami'an nan kawai inyi zamana gida ina tayaki aiki zefi" mama cikin raunin Murya tace" haba ƴata me akayi miki ne ? Ki sanar mun mana kinsan banson Abunda ze dameki ga ƙanwarki da ke tasowa Zainab,inkika kiyin karatun dame kike son mu dogara Kinga dai mahaifin yanzu kayan Miya yake siyarwa , atamfofin ma ansan yanda aka masa sharri har aka kore shi daga wajen da yake dan rufa mana Asiri , dan Allah narokeki gayamin Abunda yake Faruwa" , cikin sheshekar kuka Fatima tashiga bawa mama labari tana kai karshen zancen tace " mama basai Abba yaje ba , muje tare dake muryan malam sa'adu Mahaifin Fatima sukaji yana faɗin duk abunda kuke faɗe Inajin Ku ,kuma maganar kije babu shi ,ni Zan kaita da kaina inji me ake son fadamun , mamy tace" kasan prince Khalid ne beda mutunci wlh , har kallon banza ya taba min a Makarantar yanzu inkaje wayasan me ze shuka kuma, Baba ya karɓe da cewa "ki rabu da shi ɗan zamani ne giyar kuɗi da milki ke jansa amman fa duk da haka be isa ya yi abin da Allah beyi ba dan haka ki kwantar da hankalinki babu abin da ze faru sai Alkairi dan mu da Allah muka dogara shi ne gatanmu" "Hakane malam to Allah ya zama gatanmu duk suka amsa da amin sai a lokacin Fateema taji zuciyarta fess gani ƙwarin guiwa da ya ƙara shigarta fuskarta ɗauke da murmushi tace Baba mamy na gode da ƙarfafamin guiwa da ku ke haƙiƙa kuɗin iyaye nagari ne Allah ya bani ikon sakamuku nima wataran" cike da jin daɗi suka amsa da Amin, Baba na cewa Haleema a kawo min abincina daga soro dan yafi iska" ya ƙarasa maganar yana juyawa, da to mamy ta amsa tana dariya.fitowa tayi ta nufi kicin Fateema na biye da ita a baya...
Momy na zuba abinci,Fateema tace "wai mamy ina Zainab ne naji gidan shiru" ta ƙarasa maganar tana kallon mamy murmushi tayi tare da cewa "Zainab na turata gidan husai tayi mata kitso yanzu za ki ganta" ta kai ƙarshen maganar tana miƙamata kwanikan abincin Baba karɓa fateema tayi tana wucewa soro...
Sai faman safa da marwa yake idonshi ya yi jajawur hannusa ya dunƙule ya kaiwa bango naushi tare da cewa "Nooooo kamarni kamarni prince Khaled wata banza ƴar talaka tasaka hannu ta mareni wacce ko a me aikin gidanmu bata isa tazoba wallahi sai na nuna mata asalin kalata sai tayi da nasanin marin da tayimin tabbas sai nasata na damar sanina ni prince Khaled a cikin rayuwarta" ya kai ƙarshen maganar yana saka kanshi a bango yana jin yan da zuciyarsa ke suya..
Ta baya yaji an dafashi cikin azama ya juyo cike da masifa ganin wacce ke tsayene yasashi haɗiye abin da ke ranshi,cikin aro jarumta ya ce "Au mom ashe kece" "Eh nice my son kana lafiya kuwa meke damunka waya taɓaka haka duk naganka wani iri? duk ta jero masa tambayoyin lokaci ɗaya tare da tsareshi da ido alamar tana so taji amsar da ze bata, sumar kanshi dake kwance luf-luf ya kai hannu ya shafa tare da cewa "Amakaranta ne aka ɓatamin rai amman kar ki damu mom zanyi maganin abin da kaina kinsani sam bana ɗaukan. Nonsense" ya ƙarasa maganar yana zama a bakin gadon, sosai mom ta ƙare masa kallo alamar tana nazartarshi ne kafin tace na "sani my son amman kullum ina faɗa maka ka dinga bin ko mai a sannu itafa rayuwar nan ko mai ɗan haƙuri ne banason wannan halin naka kai kasani ko? Cin wata iriyar murya wacce mai sauraro daga yajita yasan me ita yana cikin ɓacin rai prince yace "Nasani mom kuma ina ki ya yewa" ya faɗa tare da miƙewa ya nufi hanyar toilet ,kiran sunan sa mom tayi da "Khaled'' juyowa ya yi ahankali yana fuskantar ta sai a lokacin na ƙare masa kallo saurayi ne son kowa mai cikar haiba da zati ya haɗu ta ko ina burin kowacce mace farine fari mai kyau irin na larabawa gashi dogo mai doguwar fuska wacce take ɗauke da dara daran idanu ga sajensa da ya gewaye fuskarshi ya ƙara fito da zallan kyansa hancin sa dogo ne ga bakinsa ɗan ƙarami dai-dai da fuskarshi, a hankali ya tako ya dawo zuwa ga momy da fashi tayi tare da cewa "Haba ɗan gatan mom to kasaki ran mana kasan banason ganinka a haka ba wai dan bana sonka ba ne yasa nake yimaka faɗa ba Aa ina yimaka ne sabi da inaso rayuwarka tayi kyau wannan shine burin ko wacce uwa kaji my son" kai ya jin jina alaman "to" tare da sauke ajitar zuciya yana faɗaɗa murmushi nan naga zallan kyawunshi, "cike da jin daɗi mom tace yauwa ko kaifa Allah ya maka albarka" da amin ya amsa tare da shigewa ban ɗaki,....
**** ***** *****
A guje suka shigo gidan kai da ganin irin gudun da sukeyi wani ne ya biyosu,basu zame ko inaba sai cikin ƙarƙashin gado, wani ƙaton saurayine ya shigo gidan yana huci, "Bawan Allah lafiya kashigo mana gida babu ko sallama? wata dattijuwar mata ta tambaya cike da sanyin jiki, wani mugun kallo ya watsa mata tare da cewa "ina gidan yake ai ni banga gidanba balle har nayi sallama ina shegun yarannan marasa tarbiya ki fito min dasu ko kuma nayi rashin mutunci" "Haba bawan Allah ban tari numfashinka ba amman me suka aikata maka har ka ke sheganta mana yara? "Sata sukayi min kuma wannan ba shine na farko ba kullum haka ake zuwa a ɗaukar min biredi ban taɓa kamasuba sai yau dan haka wallahi ki fitomin dasu tin da ku bakusan ku bawa yaranku tarbiyaba haifarsu kawai kuka sani" "Haba bawan Allah kayi haƙuri yara ne kuma yinwace ta sakasu yin hakan tin jiya rabambu da abinci ɗana dan Allah kayi haƙuri" ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya wacce duk wani me imani in yaji sai yaji tabashi tausayi, "To naji amman wannan ya zama na ƙarshe dan muddin na sake kamasu sunyi min sata wallahi sai na ɗauki mummunan mataki a kai" "insha Allahu ma bazasu ƙaraba kayi haƙuri" ficewa wa ya yi ba tare da yabi ta kanta ba. Hannu ta tafa tare da cewa "Oh ni talatu yau nake ganin abin da yafi ƙarfina wai yaushe ne yaran gidannan zasu dena jawo mana bala'i ne" "Innar su Mabaruka lafiya naketajin hayaniya? wata dattijuwa dake ƙoƙarin fitowa daga ɗaki ta tambaya, "Inafa lafiya yarannan ne surajo da ado suka sato biredi a gurin me shayi shi ne ya ya biyosu yazo yana yimana tijara da ƙyar na bashi haƙuri ya tafi" Hannu itama ta tafa tana sallallami tare da cewa "ah dole kiyi ta zance ke ɗaya amman fa innar su mabaruka wallahi yinwace tasaka yarannan a gaba ni kaina daurewa kawai nake Allah dai isa da malam ze fita yabar mana wani abu? ta ƙarasa maganar ta sigar tambaya, "inafa yabar wani abu ne ra ɗari biyu ce kinganta ya bayar wai mu dama ko ko sannan muyi cefanen rana kidubafa ki gani rai kusan goma sha a ɗari biyu ko gasarar muka siyo ta ɗari biyu muka dama koko to ba lallai ya ishemu ba" "Haka ne innar su Mabaruka to yanzu ya zamiyi kenan? ya zamuyi kuwa Asabe haka zamu cancanata....
*Ku kasance da zafafan marubuta , Khadija Salisu (Maman Amatullah) da Ikilima Adam ( Kyauta daga Allah)*