FreeArewaPen original
KAICO
- 1views
- 17chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · KAICO CHAPTER 1
*🌸🌸 KAICO!*🌸🌸MALLAKAR..Kyauta Daga Allah DaKhadija salis Ibrahim(Maman Amatullah)JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION.YABODUKKAN YABO DA GODIYA SUNTABBATA GA ALLAH MA ƊAUKAKIN SARKI MAI KOWA MAI KO MAI TSIRA DA AMINCI ƘARAWA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) DA IYALAN GIDANSHI DA SAHABBANSA DA WA IN DA SUKABIYO BAYANSU DA KYAUTATAWA.Wannan labarin ƙirƙirarren labari neBamuyi shi dan cin zarafin wani ko Wata ba , in ya yi dai-dai da halin ki ko naka , sai kayi haƙuri akasine.Wannan littafin na kudi ne 300# kachal👌🏻 ki biya kafin ki karanta domin neman ƙarin bayani ku tun tuɓemu ta wa'innan lambobin *** ko ***Shafi na 1️⃣ free page Fatima!Fatima!! Ake kwaɗa mata kira cikin daga Murya , wacce ake kira na hango tana sanya safa a ƙafafunta , kallo ɗaya na mata naga fara ce tass usul Fulani , Mash Allah na furta ya yin da na ta mike daga durkushen da tayi wajen saka safa , ita ba za'a ce mata gajera ba kuma ba'a za saka jerin dogaye ba , tanada dogon fuska da tsinin hancin ta me kyau .Zazzakar Muryan ta me daɗin sauraro naji tana faɗin "Na'am gani nan zuwa mama" , cikin hanzari takaraso gaban Mahaifiyar ta , cike da ladabi tace Mamy na gani na tsaya shiryawa ne , wacce aka kira da mamy jakar Makaranta tamiko mata cikin tsananin damuwa tace "Kinsan banason kiyi latti shiga Aji gashi bakici wani Abun kirkiba, ga awara nan nazuba miki a wannan karamin cooler ɗin , dan Allah dakin samu dama ki tsaya kici , kinji yar Amana" mamy ta ƙarasa maganar tana karyar da kai gefe alamar roƙo , murmushi kwance akan Fuskar Fatima tace " Na gode mamy na Allah yasaka miki da gidan Aljanna" ta ƙarasa maganar tana rataya jakar ta hannun ta ɗauke da coolern awara ahanzarce tabar gidan tana gudun yin latti.Itakuwa mamy tana fita Adua ta soma cike da tausayawa tana Neman kariyar ubangiji akan wannan yarinyar ta da dukan ya'yan musulmi.*Bayero university kano*Mai gadin Makarantar cike da mamaki yake kallon Fatima hannun ta dauke da cooler zata shiga Makarantar , kallon takalmar kafafun ta yake yana yatsina fuska , cikin rainin wayau yace " wai Fati gidan Ku basuda Zuciyar nema ne ? ya yi maganar yana wani yatsina baki Wani kallon ta jefa masa tareda tsayawa cak tana kallon sa ranta yana mugun tsuya kamar zatayi magana kome ta tuna saita fasa , cigaba da tafiyar tata tayi tana karkada kai , cike da nazarin kalaman sa ta shiga Aji.Shikuwa yana ganin tafiyar ta , dariya ya soma yace " Haba yarinya ga shegen kyau Amma ga shegen tsiya saikace talauci akan su yakare , horn din da akeyi da mota ne , yasa shi ahanzarce yabude gate din ganin prince ne yazo da kansa , bakin sa a washe yafara barka da zuwa Yallabai yau fa da wuri kashigo , prince Khalid daga masa hannu yayi yana wani babbasarwa t...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.