GABA DA GABANTA

GABA DA GABANTA 11

by @ayshercool

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

P11


Zuba mata idanu ya yi, yana kallon yadda take gabatar da sana'ar ta ta cikin nutsuwa, ba hayaniya ko ƙazanta komai nata a nutse, amma mamaki ne ya biyo bayan tunanin da yake yi, me wannan budurwa take haka a titi? Yafi dacewa ace tana gidan Aure, ko kuma tana makaranta, amma kalleta a titi tana suya.

Yaron da ya aika ne ya kawo masa ruwan, ya barwa yaron sauran canjin, ya cigaba da kallon in da Hafsa take, sai dai yadda take gudanar da lamarin nata ne, da gani ka san za ta yi izza, saboda sai shan ƙamshi take, tare da haɗe rai dan kar ma wani ya kawo wargi. A hankali Khalil ya yi you tune, ya koma hannun da Hafsat ke zaune tana gudanar da sana'ar ta. Parking ya yi a gefenta, ya fito daga motar, ya ƙaraso in da take suyar awarar ya kalleta ya ce "Sannu dai" ba tare da ta ɗago ba ta amsa masa ƙasa ƙasa da 'Yawwa".

Ya miƙo mata dubu biyu ya ce "Zuba mini abin nan na 2k" wani irin kallo Hafsa ta yiwa Khalil, irin kallon ka raina mini hankali ma, ba ta ce masa uffan ba, ta cigaba da sallamar yaran da ke gabanta.

Khalil gani ya yi ba ta da niyyar sake ko ɗaga kai ta kalleshi, ya kuma matsawa ya ce "Magana fa nake yi, ki sa mini na 2k"

"Ka bari idan ka san sunan abin da nake sayarwa, sai ka dawo in sayar maka" ta bashi amsa.

Khalil ya ce "To, ikon Allah am serious ki karɓa ki bani".

"Malam nace ka bari ka san sunan abin da nake sayarwar sai ka siya".

Yaron da ke tsaye zai sayi awara ya ce wa Khalil, "Sunan abinda take sayarwa Awara".

Khalil ya ce "Ok na gode sosai, ki bani awara ta dubu biyu".

Ba tare da kalleshi ba ta ce "Ni awarata ba ta kai ta dubu biyu ba, ta ɗari biyar kawai za ka iya samu".

"To bani ta ɗari biyar ɗin, sai ki riƙe canjin"

Hafsat ta ɗago idanunta ta harari Khalil ta ce "Malam ba fa bara nake ba, sana'a nake yi".

"Ai nima bance bara kike ba, kyauta ce kawai na baki, ta ɗari biyar ɗin ki rabawa yara sadaka, sai ki riƙe canjin".

Ba ta kuma tankawa Khalil ba, ta cigaba da iza wutarta, ya tsaya ya zuba mata ido, ta gama soya awarar dake cikin mai, ta zuba masa a leda ta miƙa masa .

Khalil ya ce "Ai ba ni zaki bawa ba, sadaka zaki bayar".

Hafsa ta ce "Ai kai ma kana da hannu, zai fi kyau ace kai ka raba musu da kanka" Nan Khalil ya shiga jinjina halin yarinyar, ana mata abin Arziƙi amma ba ta gani, sai jin kai da tsabar taƙama.

Ya sa hannu ya karɓi ledar awarar, ya miƙa mata dubu biyun, ta kalli hannunsa da yake riƙe da dubu biyun, ta ɗauke kanta ta cigaba da sabgar gabanta.

"Ikon Allah, yau Allah ya haɗani da gamona, to ga dubu ɗaya tun da ba zaki karɓi dubu biyu ba".

Nan ma ɗauke kai ta yi, ta ƙi kallon in da Khalil ya ke.

"Idan ba zaki karɓa ba zan tafi da awarar ba tare da na biya ba".

"Ka daɗe baka tafi ba" ta furta a hankali.

Khalil ya durƙusa ya sa mata dubu ɗayan, a gefenta sannan ya juya ya fara tafiya.

Ko ɗago kanta ba tayi ba, balle ta dubeshi, fifita wutar ta kawai take yi.

Yayi gaba ya bawa wasu almajirai awarar, ya kuma waiwayawa yana kallon Hafsa, cike da mamakin wannan tsatstsauran ra'ayi nata.



Amina kuwa tana shiga gida, ta tarar da Baba ya dawo daga ƙauye, wurinsa ta nufa cikin fara'a, shima ya tareta da murmushi yana faɗin "Alhamdilillah".

"Baba an kai ni Makaranta, na zama 'yar Makaranta".

"Alhamdilillah, Allah yayi miki Albarka ya cika miki burinki 'ya ta".

Amina ta ce "Ameen, ka san wani abu Baba?".

"A'a sai kin faɗa uwata".

"Baba sufa wannan makarantar a aji biyar ake gamawa, babu aji shida, zuwa baɗi ta gaba insha Allah zan gama sakandare".

Baba ya ce "To Alhamdilillah, Allah ya baki miji na gari a birni kiyi Aure, wanda zai kula da cigaban karatunki" Jikin Amina yayi sanyi ta ɗan yi shiru tana nazari.

Baba ya ce "Ya kika yi shiru, ko kin fi son ki koma ƙauye ki auri Jarmai?" Da sauri ta ɗago ta kalli Baba ta ce "A'a Baba, nifa ko sunan Mutumin nan bana ƙaunar ji, ni ban tambayeka ya hanya bama, ya ka baro Inno?".

"Duk suna lafiya sunce a gaishe ki, Jarmai kuma ya sa su Yaya Bala a gaba a kan lallai su biya shi kayan Auren da ya kai, yazo ya sameni wai nima saina biya shi, ni kuwa nace masa sisinsa ban gani ba balle in ci, dan haka yaje can wurinsu ya karɓa, amma da ina da kuɗi da na rage masa wani abun".

Amina ta kalli Baba ta ce "Ka jika Baba, Mutanen da ba tare da kai suka ci kuɗin ba, akan ne za ka biya abinda ba kai ka ci ba, banda asarar da suka yi maka ma. Baba kalli litattafaina fa, wai duk wannan litattfan nawa ne" tayi maganar tana nuna masa cikin jakarta.

Baba ya buɗe baki, text books kawai sun kai goma sha shida, banda na rubutu, ga math set, da calculator komai akwai, shi kansa Baba ya san wannan kayan sun fi ƙarfin kuɗin aikin da Amina take yi musu.

Baba ya ce "Uwata mutanen nan sun mana karamci, duk na san kina da ƙwazo, amma ki ƙara sannan ki ƙara yi musu godiya, idan mai gidan ya dawo, ki kuma yi masa godiya".

"Insha Allahu Baba zan masa, idan na yi salla fa har Addu'a nake masa, Allah ya ƙara masa Arziƙi da lafiya, ba zan manta alkhairinsa ba"

"Yauwa uwata, har 'ya'yansa ma da matarsa da ahalinsa duk ki dinga saka su a Addu'a".

Amina ta ɗan tura baki ta ce "wannan 'ya'yan nasa da basu da kirki".

"A'a fa uwata, yanzu ba Makaranta ɗansa ya kai ki ba? Idan mutum ya miki ba daidai ba, ki bishi da alkhairi albarkacin addu'a da kike musu, sai Allah ya miki abin da ba ki zata ba"

"To Baba zan dinga yi musu insha Allah, bari in je in wanka nayi salla, ka ci Abinci kuwa?"

"Eh naci, Hajara ta kawo mini, maza kije ki yi salla"

Ta amsa da to Baba, ta miƙe ta shiga cikin gidan, cike da fara'a da jin daɗi.

Kallo ɗaya Mummy ta yi mata tare da kwaɓe baki, ganin yadda ta goyo uwar jakar Makaranta tana washe baki.

Amina tayi mata sannu da gida, amma da ƙyar ta iya amsa mata. Hajara ma tsokanar Amina ta dinga yi, tare da tayata murnar samun cigaba da zuwa makaranta.

Fadila ba ta dawo gida daga Asibiti ba, sai bayan biyar na yamma, ta dawo a gajiye matuƙa, kuma rai a ɓace saboda abin da Yazeed ya yi mata, kai tsaye sashenta ta wuce, ba tare da ta nemi ko in da Mummy take ba, dan ba abin da take son yi, banda ta yi wanka tai salla ta ci Abinci.

Duk da ranta a ɓace yake, amma abin da ta tarar a part ɗinta, yayi mata daɗi sosai. Tayi wanka tayi salla, ta fito ta nufi kitchen da kanta, a kitchen ta tarar da Hajar da Amina na ƙoƙarin ɗora girkin dare, sai bawa Hajara labarin makarantarsu Amina take yi.

"Wacece ta gyara mini ɗaki a cikin ku yau?".

Amina ta ce "Nice".

"Biyoni" ta yi maganar cikin bada umarni. Bayan Fadila Amina ta bi, tana fargabar kar abin Arziƙi ya zama na tsiya.

Da suka ƙarasa ɗakin Fadila, Fadila ta ƙare wa ɗakin kallo sannan ta ce "Naga aikin da ki ka yiwa ɗakin nan, kin canzan labulaye kin wanke waɗancan, kin ɗaga gado da wardrobe kin gyara kin canza musu fasali, na ji daɗin hakan, keep it up Ina son sauye sauyen Abubuwa lokaci zuwa lokaci".

Amina ta ce "To insha Allah"

Fadila ta ce "ɗan tsaya" ta ƙarasa ta ɗakko wata babbar ledar siyayya ta store, ta sakawa Amina turamen atamfa uku, da dogayen riguna, sai hoda da turare ta ce "Gashi nan kije kya saka" Amina ta karɓa cikin fara'a ta ce "Na gode Ubangiji Allah ya ƙara Arziƙi" ta amsa da Ameen.

Sai da Amina ta fara zuwa ta nunawa Baba kayan, sannan ta je tana nunawa Hajara, sai dai ran Hajara ya sosu, dan tun da take ba'a taɓa bata makancin wannan kyautar ba a gidan.

Amina ta ce "Yaya Hajaru, ki ɗau doguwar riga ɗaya, zan ɗinka atamfa biyu in ajiyewa Inno ɗaya".

A fuska Hajara ta ce "An gode madalla" amma a zuciyarta kuwa sam ba ta ji daɗin hakan ba.

Tun da Khalil ya baro wurin Hafsa yake tunanin mai ya fito da ita zaman titi da irin wannan sana'ar haka? Gashi ita ba gwanar fara'a ba, balle ya samu ya tambaye ta, to matar da ko fara'a ba ta yiwa kwastomominta, ga taƙamar tsiya ina zata saki jiki har kayi mata wasu tambayoyi?

Duk yadda ya so ya manta da batun Hafsa, ya cigaba da sabgarsa, amma ya kasa, duk in da ya motsa tunaninta kawai yake yi, har haskowa yake irin kyan da zata yi, idan har tayi dariya ko murmushi.

Bala'in Jarmai ya sanya su Bala a uku, dan duk in da ya tsuguna zaginsu yake a garin nan, kuma duk inda ya gansu ya dinga yi musu tijara kenan a kan kuɗin aurensa.

Haka suka ƙuƙuta, suka mayarwa da dillaliya kayan gadon da suka saiwa Amina, amma tayi musu sayen wulaƙanci, suka tattara dubu talatin da ƙyar suka kai masa, a wulaƙance Jarmai ya karɓa sannan ya kalli Kawu Bala ya ce "Amma dai ka san na baku kuɗi sun kai dubu tamanin ko?"

Bala ya ce "Haka ne"

"To banci nanin ba, nanin ba zata ci ni ba, ba ƙira ba abin da zai ci gawayi, ina ganin mutuncinku ne shi yasa ban kai ku ƙara birni ba, kuma wannan dubu talatin na karɓeta ne dan kar nayi biyu babu, amma daga nan zan fara wucewa wurin mai gari, in fara kai masa ƙarar".

Kawu Lawan ya ce "Haba Jarmai, dan Allah kar mu yi haka da kai mana, insha Allah zamu ciko maka sauran kuɗinka, kayi haƙuri".

Jarmai ya gyara wata daƙalƙalalliyar babbar rigarsa ya ce "Ai haƙuri shi ne kawai in ga uwar kuɗina a hannuna".

Kawu Bala ya ce "Insha Allah, zamu cigaba da lalubawa zamu baka sauran kuɗinka" da ƙyar suka lallaɓa Jarmai, ya haƙura bai kai su ƙara ba.

Washegari da Fadila ta koma Makaranta, Captain ya tambayeta ya mai jiki, ta sanar da shi tun a jiyan aka sallame shi ya tafi gida, 'yan aji suna son suyi tsurku su ji yadda abubuwa suka wakana, amma sanin halin Fadila ya sanya ba wanda ya tanka mata.

Ta dinga zuba ido, ta ga ta ina Yazeed zai shigo aji, amma babu Yazeed babu alamar sa, har aka yi lectures ɗin ranar aka gama.

Nan cikin Fadila ya sake ɗurar ruwa, ta san ba zai wuce ace jikin ne ya hana shi zuwa Makaranta ba, nan zuciyarta ta dinga saƙa mata abubuwa daban daban, ciki har da tunanin ko jikin ne ya tayar masa ya mutu? Nan da nan ta yi saurin kawar da wannan tunanin daga ranta.

Da aka tashi daga Makaranta ta samu Captain ta ce "Musa, kun yi waya da gayen nan ne?"

Captain ya ce "Wa kenan?".

"Wanda muka kai Asibiti jiya"

Murmushi ya yi ya ce "Hajiya Fadila ta mu, sunan nasa ne ma ba za a iya faɗa ba. Wallahi tun jiya nake kiran wayarsa, amma ba ta shiga, kuma ina kyautata zaton jikin ne ya hana shi zuwa yau" Fadila ta ce "Ok shikenan"

Daga haka ta wuce ta nufi motarta, tana cigaba da tunani.

A kwanakin nan kowa da abin da ya dame shi a jama'ar gidan, Khalil ya kasa sukuni saboda tunanin Hafsat, gashi ya kuma komawa amma bata nan bai sameta ba.

Fadila kuwa gaba ɗaya tunanin halin da Yazeed yake ciki ne ya dame ta, dan a rayuwarta bata taɓa aikata abin da ya dameta ba kamar abin da ta yiwa Yazeed ba, saboda ta tsorata da irin yanayin ciwonsa. Bata taɓa ganin mutum a mawuyacin yanayi na ciwo kamar Yazeed ba.

Tana zaune a aji, tana ƙoƙarin ɗauko littafi tayi rubutu, ta ga jotter Yazeed, ta ɗauko jotter ta fara bubbuɗewa, rubutunsa a tsare yake kamar musamman yake shirya rubutun, sai dai fahimtar abinda ya rubuta ɗin sai ƙwaro ko kuma shi kansa da ya rubuta abin sa.

Rubutu ne na turanci, jotting ɗin lectures ɗin da ake yi ne, sai yayi sentence ɗaya biyu ya gauraya su da rubutun larabci, ga wasu irin manyan Words na turanci, da bata taɓa jinsu ba.

To ya akai ya iya turanci a rubuce, amma bai iya a baki ba? 'Maybe yana da matsalar public speaking ne' ta bawa kanta amsa.

Bakomai ta iya ganewa a jotting ɗin nasa ba, saboda yadda yake rubutun larabci kamar rubutun yarensa na haihuwa.

Ɗan taɓe baki tayi, ta ajiye jotter, tana fatan Allah ya sa dai ba jikinsa ne ya hana shi zuwa Makaranta ba.

Khalil musamman sai ya shirya ya tafi unguwar su Abdul, yayi shawagi domin kawai ya ga Hafsat, cikin ikon Allah yau yayi sa'a ya tarar da ita a bakin kaskonta bayan magariba, tana ta harhaɗa kayanta ta tashi.

Parking ɗin motarsa ya yi, ya fito da sauri ya ƙarasa in da take. "Sannu dai"

Ɗagowa tayi ta kalleshi ta ce "Yawwa".

"Ba dai har kin tashi ba?"

"Me kaga ina yi?"

"Oh sorry haka ne, na gani haɗa kaya ki ke yi, yanzu ba zan samu ba?".

"Eh ta ƙare".

"Kwana biyu na zo ba na ganinki, meyasa ba kya fitowa?"

Hafsa ta ce "Eh da yake ai ba aikin gwamnati nake ba, kuma ba wani ne ya ɗauke ni aiki ba balle a tuhume ni"

Murmushi Khalil ya yi, yana jinjina hali irin na Mai awara, ya ɗan sosa kai ya ce "Haka ne, am sorry"

"Yawwa dama ina nemanka" tai maganar tana saka hannu a jakarta.

Khalil ya ce "Kina nemana kuma? Allah ya sa ba laifi na miki ba"

Ɗari biyar ta miƙo masa tana faɗin "Karɓi canjinka da ka tafi ka bar mini ranar"

"Ai ba bashi bane, kyauta na baki".

"Ai bance maka ina buƙata ba, ka karɓi canjinka".

Khalil ya ce "Ai kyauta na baki, kuma ba kyau mayar da kyauta".

"Meye tsakanina da kai, da haka kurum zaka bani kyautar kuɗi"

"Alkhairi ne tsakanina da ke. Naga kamar gida zaki tafi, ko zamuje in sauke ki?"

"Malam ka karɓi kuɗinka, zan tafi dare nayi"

"Da ban dawo ba ya zaki?".

Ƙoƙarin saƙala masa kuɗinsa take a hannunsa da harɗe a ƙirjinsa. Ja da baya yayi yana kallonta tare da sakin murmushi ya ce "ke dai kin fiye gaddama, dama zuwa na yi in ganki, kuma na sai awara, tun da ban samu awara ba na samu ganinki, shikenan, ki gaida gida" galala ta tsaya tana kallon Ikon Allah, Khalil kuma yayi gaba abin sa yana jin wani nishaɗi da ya rasa na menene.

Yana tafe a mota yana tuna yadda tai kicin-kincin da rai tana bashi kuɗinsa, sam bai gaji da ganinta ba, amma ya lura ba ta son takura, magana kuma na bata wahala, shiyasa ya tafi ya ƙyaleta.

Shiru yayi yana tunanin menene haka yake ji game da yarinyar nan? Wani irin baƙon al'amari yaji yana ratsa zuciyarsa, duk Hafsa daga gaban kaskon wuta ta tashi, ƙamshin turarenta ya haɗe da ƙaurin mai da na hayaƙi, amma a hancin Khalil ƙamshi ya bashi mai daɗin gaske.

Amina kuwa zuwa makaranta ya kankama, dan ta gane hanya, Baba ne yake bata kuɗin mota, ta hau abin hawa ta tafi, idan an tashi ma ta taho gida.

Kullum da kiran sallar farko, Amina idan ta tashi bata komawa, duk wani aiki da zata yi, sai ta tabattar ta yi shi, har karin kumallo sai ta dafa, ta gyara ko ina sannan take shiryawa ta tafi makaranta.

Sati ya shuɗe kusan kwanaki takwas, Yazeed bai dawo Makaranta ba, gaba ɗaya hankalin Fadila a tashe yake, dan ba wanda ya san gidan su Yazeed balle a samo information akan halin da yake ciki, gashi wayarsa ba ta shiga sam.

Fadila Addu'a take, da fatan Allah ya sa ba mutuwa yayi ba, dan da ƙyar in ta tambayi malamai ba a ce tayi azumi sittin ba, saboda abin da ta aikatawa Yazeed, dan da gayya ta balbale shi da hayaƙi da kuma ƙura, duk dan ta muzguna masa.

Yau Saturday, kuma suna gaf da fara exams, dan haka akwai lecturer da ya ce, lallai su shiga Saturday, dan bai yi covering course ɗinsa ba.

Jiki a sanyaye take tafiya dama gashi ta makara, dan ƙarfe goma ya ce aje, yanzu kuma sha ɗaya saura mintuna goma sha biyar, haka ta tunkari ajinsu tana fatan Allah ya sa malamin ya bari ta zauna, tuni har malamin ya fara lectures, Allah ya taimaketa bai koreta ba. Tun da ta shiga ajin ya ƙura mata ido, ɗaga idon da za tai suka yi ido huɗu da Yazeed. Gabanta ne ya faɗi ganin yadda yayi wata muguwar rama, sauke facemask ɗin sa yayi, tare da yi mata murmushi, gaba ɗaya ya rame sosai, sai dogon hancinsa da ya sake fitowa.

Tsuke fuska tayi, ta basar kamar ba ta ganshi ba, ta nemi wani wurin ta zauna, tare da ɗauke kanta da sashen da Yazeed yake.

Sai dai lokaci lokaci ta kan kalleshi, tare da sake tabattarwa da kanta yayi rashin lafiya sosai.

Haka aka gudanar da lectures ɗin aka gama, aka yi Attendance.

Da yawa ɗaliban zasu zauna ne a school, suyi karatu, saboda gabatowar exams, wanda ita ma Fadilan ta yanke shawarar ta zauna ta yi karatu, dan idan taje gida bacci zata yi, sai dai kafin nan akwai buƙatar ta ɗan samo abun motsa baki, da zai ɗebe mata kewa yayin karatu.

Bayan tafiyar malamin daga aji, akai ta yiwa Yazeed ya jiki.

Fadila tana ta hanzari ta tunkari motarta, ta saka key tana ƙoƙarin buɗewa ta ji an kira sunanta "Fadila" waiwayawa tayi, taga Yazeed a bayanta.

Cikin murmushinsa da ya zame masa ɗabi' ya ce "Kina lafiya?"

Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Lafiya ƙalau".

"Dama na ce bari in zo in sake yin godiya ne, game da taimakon da ki ka yi mini, na gode sosai Allah ya bar zumunci" Wata uwar harara ta watsa masa, ta buɗe ƙofar motar.

"Au ashe fa ni mai laifi ne, na manta a ranar na ɓata miki rai, kiyi haƙuri dan Allah, naga baki ji daɗin abin da nayi ba".

"Ashe kana sane kai min abin da kayi mini ko?" Tayi maganar tana hararasa.

"Ai nace kiyi haƙuri ban kyauta ba"

"Kaji da shi" tayi maganar tana ƙoƙarin shiga mota.

Cikin harshen larabci Yazeed ya ce

"هل يمكنني الحصول على jotter الخاص بي"

(*Can i have my jotter*)

Kallonsa ta yi saroro, ba tare da ta gane me yake faɗa ba.

Ya kuma maimaita mata abin da ya faɗa. Tsaki tayi ta ce "Malam speak what I can understand".

Wani irin ƙasaitaccen murmushi Yazeed ya yi ya ce "Ni kuma gashi ban iya turanci ba, amma dai ina roƙon ki bani jotter ta ne, zan ɗan kwafi lectures da na yi missing, ance mini suna wurinki"

Tura baki tayi, tana wani basarwa, ta fara duba jakarta, ta zaro jottersa da bironsa ta miƙa masa.

Sansana jotter ya yi ya ce

رائحته جميلة

(


*It smells nicely*)


Ƙaramin tsaki ta ja tana kuma ƙoƙarin shiga mota.

Riƙe ƙofar motar yayi ya ce "Malama kayana da saura" kamar ba shi yayi Maganar ba, ya wani basar, dan ba zaka taɓa cewa yana magana haka ba.

"Ban gane ba" ta faɗa tana kallonsa.

"Ina kuɗina?" Ya faɗa ransa a haɗe.

"Hamsin ɗin?" Ta faɗa a wulaƙance.

Yazeed ya ce "Eh ai tawa ce ko?"

Tsaki tayi ta saka hannu a jakarta ta ɗauko ɗari biyar ta ce "Ungo".

"Ni tawa nake so, amma dai shikenan na bar miki, ki zo muje muyi karatu tare, ki koya mini abin da aka yi bana nan, sannan baki mini ya jiki bama, kin kusa halaka ɗan marayan Allah, ni yakamata ma ki gaya mini laifin da na yi miki kika tsane ni haka".

"Dan Allah ka bani wuri in tafi, ka tsayar da ni kana ta mini surutan banza".

"Subhanallah, yi haƙuri na takura miki, shikenan ki gaida gida" ya matsa ya bata wuri, ta shige motar ta, ta sauke glashin ta ce "Ka matsa kar in tada ƙura ka kama sumewa mutane".

"Idan na suma ma in dai kina nan ai ba damuwa" hararsa tayi, ta bawa motarta wuta ta wuce ta bar wurin.

Shi kansa Yazeed bai san yadda aka yi ya tsinci kansa, da ƙoƙarin tsawaita hira da Fadila ba, dan a rayuwarsa kusan shi mutum ne mai tsoron duk wani abu da zai haɗa shi da mata.

Sake shanshana jotter yayi, sai ƙamashin turaren Fadila take, ya fara bubbuɗewa, kawai ya ci karo da rubutun da ba nasa ba, kusan duk lectures ɗin da aka yi baya nan, ta rubuta masa a ciki.

Zubawa Jotter ido yayi, a hankali ya ce "Allah ya sa ki fara jin abin da nake ji a kanki" can kuma ya ce "Subhanallah, ba ajina bace" shikaɗai yake wannan surutan, daga baya kuma ya ja jiki ya nufi masallaci.

Amina ta gama aikinta tsaf, ta zauna a falo tana karatu, Hajiya Zainab bata nan, Hajara kuma ta tafi yin sayayya.

Turo ƙofar falon aka yi, Amina ta waiwaya, taga baƙuwar fuskar da bata saba ganinta ba.

Yusra ta ce "Ina mutan gidan kuwa, naji kamar ba kowa?"


"Sun je Islamiyya a koya musu sallama, da yiwa wanda suka tarar sannu" Amina ta bata amsa.


"Ke, wacece ke kika gaya mini wannan maganar?"

"Ahh musulma mana Hajiya, ai a koyarwar addinin musulunci idan ka zo wuri da sallama kake farawa, kuma ka yiwa na zaune sallama, amma kawai kya shigo kanki tsaye ki hau Magana. Bisimillah shigo amma dai nan gaba ba a haka" saroro Yusra ta bi Amina da kallo, dan ba su taɓa haɗuwa ba sai yau.

Ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon Yusra take, amma Amina ta miƙe ta ce "Hajiya ba fa banɗaki zaki shiga ba, ya zaki shigo mana da takalmi falo, ciresu a nan wurin ki ƙaraso" Yusra cire takalman tayi tana kallon Ikon Allah wurin Amina, dan ba ta san matsayinta a gidan ba.

Yusra ta zauna, Amina kuma ta wuce kitchen, ta haɗowa Yusra ruwa da lemo, ta kawo gabanta ta ajiye mata ta ce "Ga ruwa ki sha, 'yan gidan basa nan, idan kuma zaki ci Abinci ne ki faɗi wanne zan dafa miki? Dan an cinye na rana, na ɗan gidan nan ne kawai ya yi ragowa"

Sai yanzu Yusra ta gane matsayin Amina, a ranta ta ce 'Ina Mummy ta samo wannan tantiryar mara mutuncin 'yar aiki? Ka rashin kunya ga karrama mutane'.

"Ba Abinci na zo ci ba, ai ban miki kama da mai jin yunwa ba"

Dariya Amina ta yi ta ce "Haba Yayata,. Idan a jiki ake gane yunwa ko rashinta, ai cewa za ai baki taɓa cin abinci ba ma" ai gaba ɗaya Amina ta kashewa Yusra bakin Magana.

Ƙamshin turaren da ya karaɗe falon ne, ya sanar musu da zuwan Khalil, sai dai tun kan ya shigo, Yusra ta rasa nutsuwarta.

Kansa tsaye ya shigo, da sallama iya wuyansa wadda shika ɗai yaji kayarsa, jiki na rawa Yusra ta risuna tana gaishe shi. Amma ya amsa ba yabo ba fallasa, haka ya shigo falon da takalmansa, sai da yaje dining ya ajiye takalman a kan step ɗin dining ɗin.

Amina kuwa ta ƙulu, saboda yadda ya biyo har ta kan carfet da takalmansa, a fusace ta miƙe taje ta kwaso takalman Khalil ta je ta watsa su waje tana mita cike da tsiwa "Ai ni ba baiwarku ba ce da zan dinga aiki kuna takawa, sai na sake!"

SHARE PLEASE

Domin samun update a kan lokaci, ko samun book ɗin daga farko

Follow me on

Watpad Ayshercool7724

Arewabooks Ayshercool 77724

What's app

***