CUTAR KAI

Chapter 1

by @ummubasheer

``CUTAR KAI....```๐Ÿ’



{ _Labari ne mai cike da nadama, yaudara, tausayi, tsantsar k'auna mai tab'a zuciya_ }


_Story And Written_

        ```By```

```UMMU BASHEER

   &

MAIMOUNATH O.G```


*Wannan labarin k'irkira ne, bamu yarda a sace ko ayi mana copy and paste ba, duk wanda yayi kuma bamu yafe ba*


*Page 1*




Kaduna State


Nigerian Turkish 


Tsaye take a bakin gate Sanye Cikin School Uniform, Kyakyawa ce Yarinya wacce ba zata wuce Shekaru goma sha bakwai ba, Fara ce doguwa, Kyakyawa Tana da manyan White eyes, Ga dogon hancin ta sai d'an karamin lips dinta wanda take ta cicijewa tana yi tana duba Wristwatch dinta, Sai tsaki take ja,Can sai ga wani d'an saurayi d'an 15yrs ya k'araso kusa da ita yana cewa"Aunty Nadrah har yanzu Bala driver bai iso ba"


  "Hisham Kwana nan sam baya zuwa D'aukar mu da wuri I don't know why"ta fad'a tana tare hannun ta kan fuskar ta saboda yanda rana ke kashe mata fuska.


D'an tsaki yayi shima Cikin gajiya,bayan 5 minutes suna tsaye sai ga Motar gidan su ta iso,Nadrah a gajiye ta shige motar ta zauna a back seat,da k'yar ta gaishe da Bala driver,Shi kuma Hisham ya shiga front seat suka gaisa da Bala ya jasu,suna tafe yana musu surutu dama Hisham ne mai kula shi,Nadrah dake baya duk surutun shi ya ishe ta,wani had'adden gida mai kyau dake Unguwar Malali Cikin G.R.A Bala yayi horn mai gadi ya bud'e gate din,yana yin parking Nadrah ta fice tare da shigewa Cikin gidan wanda ya had'u sosai,Da sallama ta shiga Parlour, Mommy ta gani nan tace"Mommy barka da gida"


Cikin fara'a Kyakyawar matar ta amsa" Yauwa Daughter you're welcome, ya Karatun?"


Zama tayi kan Kujeran tana cewa" Alhamdulillah Mommy I'm just tired sai yanzu fah Bala ya d'auko mu"


Hisham da shigowar shi kenan ya fara wurgi da school bag ya gaishe da Mommy, Nadrah cikin haushi tace"wai kai waye zai d'auke ma school ba, kana dawowa sai ka hau jifa da kaya mtsss"taja tsaki


Tab'e baki yayi" Nidai ba wanann ba Allah yasa Inna ta gama abinci"


Tsaki Nadrah tayi tare da D'aukar jakar ta tayi hanyar d'akin ta tana cewa"Mutum ba abinda ya iya sai ci"


Mommy ko Murmushi tayi tace" Hisham pick up your things sai kaje ga abinci nan a Dining kaci kaji Babana ita wancan ai abinci bai dame ta ba"


Dariya yayi" Shiyasa wlh na fita girma da tsawo ko a school mommy cewa ake nine yayan ta,kawai dan ta fini class ne"


Dariya Mommy tayi ya kwashi kayan shi daya watsar ya nufa bedroom dinshi.


Nadrah tana zuwa bedroom dinta ta cire kaya tayi wanka tasa doguwar riga na atamfa ta d'aura d'an kwalin ta fito,Hisham ta gani kan dining yana cin abinci ta k'arasa ta bud'e warmers din Dan bata fuska tayi ganin Miya wanda yaji kifi sam bata son kifi a rayuwar ta,juyawa tayi ta kalla Mommy"Mommy miyar kifi akayi nikam yau ya zanyi"


Murmushi Mommy tayi" Kwantar da hankalin ki naki miyar yana kitchen babu kifi"


Murmushi tayi Cikin murna taje kitchen ta d'auko miyar ta zuba abinci, kad'an taci ta tashi, Around 4pm sukayi shirin zuwa Islamiyya sai mita take ma Hisham wai zai sa su makara, Cikin Maroon Colour Hijab take ta rataye jakar Islamiyya ta,A kaf'a suka tafi kasancewar babu nisa anan Unguwar ne,Bayan an tashi suka dawo gida,da Daddare suka duba litafan su na school dana Islamiyya, around 8:30pm Daddyn su ya dawo,Bayan ya shigo duk sukayi mai Sannu da zuwa,Ya tambaye su ya Karatun su,kira ne ya shigo wayar shi Nan ya nufa Parlour shi yana mai amsa wayar,Domin Aminin shine ya kira shi, d'aukar wayar yayi suna gaisawa cikin farin ciki,suka d'an tab'a hira Sannan suka yi sallama.


Suna gama Assignment dinsu kowanen su ya nufa d'aki domin da wuri suke bacci, Mommy ce ta kira ta tana cewa Daddyn su na kiran su, Lokacin da taje Hisham har ya isa Parlour Daddyn,Wata leda Daddy ya d'auko tare da ciro kwalin waya guda biyu yana Mik'a ma kowanen su domin yayi musu alk'awarin zai siya musu waya,"Ga Alk'awarin ku nan na cika muku" Daddy ya fad'a cikin murmushi, cikin murna suka karb'a suna godiya suka ciro a kwali babbar waya ce masu tsada da kyau wato Samsung Galaxy S10,iri d'aya,nan Daddy yace akwai Sim yayi musu Register yasa musu Numbers dinsu,Sosai suke murna suna godiya,Nan Daddy yace idan za suje school ko Islamiyya su dinga ajiye wayar a gida, Sannan da Daddare k'arfe 9 su kawo mai wayar ya ajiye domin baya son chats din dare,haka su kayi godiya sosai.


Washegari a School Nadrah ta had'u da K'awar ta Yusrah nan ta fara fad'a mata Daddyn su ya siya mata waya sosai Yusrah ta taya ta murna tace zasu dinga chatting yanzu tunda dama ita Yusrah tana da waya,yau ma da aka tashi Bala bai zo da wuri ba sai d'aure Fuska take suna komawa gida tayi wanka ta shirya as usual ta fito parlour cin abinci, Hisham ta gani sai Abinci yake ci hararar shi tayi"Sarki ci,acici kawai"


 Spoon din abinci ya kai bakin shi" Aunty Nadrah baki ga shiyasa na fiki girma ma shiyasa nine ke amsa sunan Yaya a ko'ina bake ba..."


 Cikin haushi tace" Mommy kin ganshi ko, wallahi yaron nan ya raina ni"


Mommy Murmushi tayi" Nadrah da gaskiyar shi ya kamata ki dage da cin abinci ace mutum kullum shikenan baya son Abinci"


Turo baki tayi" Mommy kawai kina goyon bayan shine"


Gwalo yayi mata" Shiyasa ga ki nan kamar taliya y'ar murji na hausa"


Ai kuwa jin abinda yace tayi kanshi zata dake shi da gudu yaje bayan Mommy yana b'oyewa ita kuma tana kokarin kama shi wai sai ta dake shi.


Mommy tace"Yau halan karya ni kuke son yi kai Hisham wuce ka ci Abincin ka, k'yale shi ke kuma"


Jawo wuyan rigar shi tayi" Mommy Allah sai na dake shi ya raina ni" rank'washi tayi mai akai" ashh wayyo kaina, Mommy ta fasa min kai"


Mommy ta saba da rigimar su kasancewar su sak'o, Sosai suka fara fad'a kamar za suyi dambe rai a b'ace Mommy ta daka musu tsawa, nan suka shiga taitayin su sai hararar juna suke,jawo drower dake jikin Center table tayi ta ciro nailscutter ta Mik'a ma kowanen su tace su zauna,zama sukayi domin sun san punishment dinsu,Hakuri suka fara bata ta daka musu tsawa"Kuna hauka ne, ban hana ku fad'a ba ke kina mace za kiyi dambe da namiji ne oya start" rik'e k'afar Hisham tayi tana cire mai k'umba da nailscutter duk yi d'aya sai tace"I'm sorry Brother" shima haka yake mata sai yace" Sorry Sister"koda kuwa basu da nails haka Mommy ke sa suyi tun suna jin haushi har su huce su shirya sannan tace kowanen su ya tashi, Lokacin Islamiyya haka suka shirya suka kama hanya suna hira kamar ba sune masu fad'a d'azun ba.



**************************



Alhaji Sa'eed Shine mahaifin su Nadrah Asalin shi D'an Zaria ne,anan iyayen shi suke Unguwar Liman,Su Hudu iyayen su suka haifa,Sani,Aisha,sai Sa'eed sai kuma Bilkisu Autar su,Suna da rufin asiri,Yayi Primary and Secondary school inda ya samu Admission a ABU samaru Zaria,ya karanci Building and Engineering,Sa'eed Yana da wani aboki ko ince Aminin shi tare sukayi Secondary school tare suka samu Admission a ABU course d'aya suka karanta.


Kabeer shima d'an Zaria ne shima iyayen shi suna da hali Lokacin da suka gama ABU suka yi Services a Lokacin ne iyayen Kabeer suka rasu,Sosai yayi rashin iyaye y'an uwa ma ba'a damu dashi ba kasancewar shi kad'ai iyayen shi suka haifa,akwai wani Kanin baban shi wanda yake son shi yana zaune a kaduna,shine ya sama mai aiki a kaduna, Sa'eed shima ya samu aiki a kano,akwai shak'uwa mai karfi a Tsakanin su,basa dadewa basu had'u da juna ba, Sa'eed a Kano ya had'u da wata budurwa kyakyawa mai suna Layla,Suka fara soyayya mai karf'i har magana ya Kai gurin manya aka sa rana.


Layla kyakyawa ce sosai Asalin ta y'ar k'asar Mali ce,Buzuwa ce gaba da bayan ta,Suna da y'an uwa anan Nigeria Kano,ta kawo ma K'anwar Mahaifiyar ta ziyara ne a Kano nan take aure,a Lokacin ne suka had'u da Sa'eed, soyayya mai karf'i Ya shiga tsakanin su,aka yi auren su anan Kano suka fara zama,Bayan shekara d'aya ta haifa Baby girl aka samata Nadrah,bayan shekaru biyu ta sake haifar Baby Boy aka sa mai Hisham.


Bayan shekaru biyar Alhaji Sa'eed ya koma Kaduna da aiki,Kuma tunda kan Hisham Hajiya Layla bata sake haihuwa ba, Alhaji Kabeer bai yi aure ba, saboda shi cewa yake har yanzu bai ga macen da yake so ba,sam shi mata basa gaban shi,domin miskili ne na k'arshe,aikin shi kawai ya sa a gaba ba'a dad'e ba ya koma Lagos domin business yake yi sosai,Sai dai ya kawo ziyara Kaduna.




A Yanzu Shekarar Nadrah 17,yayin da Hisham yake 15yrs,Akwai shak'uwa tsakanin su,tana son kanin nata shima haka suyi fad'a ne su shirya tare suke zuwa makaranta su dawo,Nadrah kyakyawa ce sosai domin Kam ta biyo maman ta, Mutane dayawa sukance ita ba y'ar k'asar nan bane sai dai tayi Murmushi, Mommy Bata wani musu yaren Tamashek(Buzanci),sai dai suna son koya toh da girman su shine take d'an musu kad'an saboda idan taje dasu Kano sai su fita daban cikin y'an uwa yo basu iya yare ba,haka y'an uwan Mommy ke mata fad'a wai bata koya musu ba shine yanzu take Dan musu,sau d'aya ta tab'a zuwa dasu Mali suka ga yan'uwa ,Nadrah iyayen su sun basu tarbiyya,babu inda suke zuwa daga school sai Islamiyya,Sai dai idan wani gurin ma za suje driver ke kai su, Alhaji Sa'eed yana da kudi,kuma Sosai yake kashe ma iyalan shi, Nadrah Sunyi Primary and Secondary school dinsu anan Nigerian Turkish dake cikin Kaduna State,yanzu haka tana S.S2,shi kuma Hisham yana S.S1, Islamiyya ma suna kokari sosai yanzu izifin su 40,a gida akwai malamin dake zuwa yin musu lesson, na school dana Islamiyya,Sai weekend amma,Nadrah tana da K'awa wato Yusrah halin su yazo d'aya suna shiri Sosai school dinsu d'aya,ita Yusrah tana Unguwar Dosa ne,baban ta shima yana da kudi,su biyar iyayen su suka haifa Yusrah itace auta.



A yanzu Alhaji Kabeer shekarar shi kusan Hudu kenan rabon shi da Kaduna,sai dai sun tab'a haduwa sau kusan Hudu da abokin nashi sai dai Yawanci ba'a kaduna ba,Ko Yaushe sai Alhaji Sa'eed yace yaushe zai zo,sai yace ya kusa zuwa,gashi har zuwa yanzu baiyi aure ba,domin shi business dinshi kawai yasa a gaba,kanin baban shi yayi fad'an har ya gaji,duk da cewan suna nesa da juna Amma kusan kullum suke waya,har yanzu akwai shak'uwa a Tsakanin su day so irin ta aminan juna,shima Alhaji Sa'eed din yasha mai maganar aure har ya gaji ya k'yale shi.



************************




Nadrah ce gaban dressing Sanye take Cikin navy blue abaya tayi rolling veil din akanta,abayan anyi mai addo da stones black, yawanci bata damu da make up ba saboda Daddy baya so idan tayi fad'a yakeyi, powder kawai sai kwali ta shafa ta d'auki lipgloss ta d'an shafa a pink lips dinta,turare ta fesa kusan kala biyu tasa flat shoe black ta d'auki y'ar karamar wizzy jakarta ta rataye, Fitowa tayi ta nufa bedroom din Hisham tsaki tayi ganin shi yana tace kai"Wai kai meyasa ka shiga shiririta ne always idan zamu fita sai ka b'ata min lokaci"



  " Sorry my sweet sis<na gama let's go" ya fad'a tare da nufo ta


 Tsaki taja ta nufa parlor Mommy ce ta d'auki kud'i tare da Mik'a ma Nadrah ta bata wani takardar na list tace"Idan kunje Shopping din naku ku biyo min da wa'inan" Karb'a tayi"Okay Mommy inshaallah sai mun dawo"



" A dawo lafiya,kuma w kula da kyau Allah ya tsare"


Ameen sukace tare da nufar waje,suna zuwa Bala driver ya tada mota suka shiga,SIDI AND SON'S SUPER MARKET suka nufa,Haka suka d'an zazaga suka d'auki abubuwan da suke da Bukata sannan tayi ma Mommy nata siyayar wayar tace tayi ringing d'auka tayi"Hello Besty ya kike"


 Yusrah tace"Besty ki kuna datar ki na turo miki sak'o"


 Okay kawai tace tare da kunna datar nan suka fara chats Yusrah ce ta turo mata pic din saurayin ta wanda take bata labari d'an uwan tane yana karatu a k'asar waje,Sai chats suke ta biya kud'in Hisham har yayi gaba da kayan ita kuwa sai chatting take tazo daidai zata fito daga Cikin shopping Mall din shima ya taho rik'e da waya yana d'an sauri ba tare da sun ankara ba kawai sukayi karo da juna,Wayar shi ce ta fad'i ya d'auka har screen ya fashe a fusace ya juyo ita ma Juyawa tayi jin ta buge mutum idanun sune ya had'u Dana juna,Gaban su a tare ya buga,Gaba d'aya ji yayi ya kasa mata magana kallon ta kawai yake Yayin da heart dinshi yake beating very fast,Da k'yar ta iya bud'e baki tace"Kayi hakuri Dan Allah" 


Muryar ta mai dad'i ne ya sauka a kunnen shi,Bai ce Komi ba ya juya ita ma juyawa tayi,amma sai ta k'ara juyawa zuciyar ta na bugawa yayin da k'amshin turaren shi duk ya cika mata hanci,yana tafe yana waigen ta zuciyar shi na beating ita ma waigen shi take tana cewa a ranta masha Allah kai wannan Saurayin Allah yayi mai kyau kamar Aljani ko dai ba mutum bane irin Wannan kyau haka,suna tafe suna waigen juna har suka b'ace, Nadrah cikin sanyin jiki ta shiga mota,Hisham ya lura da yanayin ta yayi ta tambayar ta lafiya tayi banza dashi,haka suka k'arasa gida, jikin ta a sanyaye,Yayin da zuciyar ta bai daina beating ba,Koda ta cire kayan ta still k'amshin Saurayin d'azun take ji,a Daren haka ta kwana tunanin saurayin nan.













Marubuta biyu ke rubuta muku Wannan labarin wato....



UMMU BASHEER

     &

MAIMOUNATH O.G