Chapter 2
by @ummubasheer
```CUTAR KAI....```馃拲
{ _Labari ne mai cike da nadama, yaudara, tausayi, tsantsar k'auna mai tab'a zuciya_ }
_Story And Written_
```By```
```UMMU BASHEER
&
MAIMOUNATH O.G```
*Wannan labarin k'irkira ne, bamu yarda a sace ko ayi mana copy and paste ba, duk wanda yayi kuma bamu yafe ba*
Page 02
Washegari da safe Nadrah da taje School bayan an tashi break take ba Yusrah labarin Saurayin da suka had'u a Sidi and Son's Super Market suka bugi juna, Nan take fad'a mata irin kyan saurayin, Yusrah tace"Wai ke daga haduwa da mutum sai kawai kiyi maganar shi sai wani kururuta kyan shi kike wai ke kyau an kai ki ne ma,Anya ma ba Aljani kika gani ba kuwa?"
Tsaki tayi"No that can't be...."
"Nifa gani nake da Aljani kika ci karo Allah kuwa Besty"ta k'are Cikin dariya.
Ganin yanda Yusrah ke mata dariya bata d'auka serious ba kawai ta watsar da tunanin ta maida hankali kan Karatun ta,bayan kwana biyu suka fara shirin Exams domin shiga SSS 3,haka sukayi ta Karatu,har suka Kamala,bayan sunyi hutu Daddy yace su shirya domin zuwa hutu Zaria,Sam Nadrah bata so ba,ita bata son shiga cikin mutane,haka dai ta shirya kayan ta tana ma Hisham mita wai duk hutu sai sunje Zaria ne,dariya kawai yake mata yasan halin ta da son zaman gida, washegari suka kama hanyar Zaria,Sosai kakan su taji dad'in zuwan su bayan kwana biyu suka zazaga y'an uwa suka gaishe su,Nadrah gidan Aunty Bilkisu (Autar Su Alhaji Sa'eed)taje wai sai tayi two days acan, Kasancewar suna shiri da Aunty Bilkisu ai kuwa kusan sati tayi kafin ta koma gidan su Hajja Kaka,Hisham kuwa ai ya samu yawo domin yana son zuwa,ana gobe zasu koma Ranar Friday, Daughter din Yayan baban su tazo gidan toh sa'ar Nadrah ce Inteesar shine da zata tafi ta raka ta har titi domin hawa napep,suna tsaye sai ga wata mota mai kyau tayi parking a gaban su Nadrah matsawa gefe tayi,Domin bata yi tunanin motar gurin su ya tsaya ba.
Saurayi ne Dogo bak'i ne mai d'auke da saje ba za'a kira shi mumuna ba haka kuma ba kyakyawa bane sanye yake Cikin Riga Dark green and black jeans, headphone ya d'an makale a wuya hannun shi rik'e da wayar shi da car keys, Cikin sanyin Murya yace"Assalamu Alaikum barkan ku y'an mata"
Inteesar ce ta amsa mai Cikin fara'a yayin da Nadrah ta kawar da kanta gefe cikin Murmushi yace"Ko zan iya rage muku hanya idan ba damuwa"
"No mun gode sosai"cewar Inteesar,Nadrah kuwa hararar ta take ganin ta tsaya kula wani zaiyi magana taja hannun Inteesar tana cewa"Mu matsa daga can mu samu ki tafi"
Da sauri yace"Dan Allah zan iya sanin sunan ku"
Inteesar tace" Malam fatan dai lafiya?"
" Alkhairi ne ya kawo ni gurin ku amma naga K'awar taki bata magana ne"ya tambaya ta.
" Oh Nadrah tana magana man kawai....."
Cikin haushi Nadrah tace" Wai meye haka kin tsaya sai zuba kike.."
Katseta tayi"haba Nadrah ai bai kamata mu wulakanta shi ba"
Murmushi yayi" yauwa K'awar mu dan Allah ki taya ni Campaign K'awar ki Nadrah nake so"
Da sauri Nadrah ta D'ago kai ta kalle shi suka had'a ido tayi Saurin sunkuyar da Kai, Inteesar Dariya tayi"Baka da matsala Sha kurumin ka..."
Cikin farin ciki yace" Dan Allah ki bani number ta naga kan titi muke kar in tsayar daku"
Cikin gajiya Nadrah tayi gaba saboda ta gaji da surutun Inteesar,haka tayi gaba kad'an ta tsaya, Inteesar kuwa ta bashi number Nadrah yayi godiya tare da zaro 5k ya Mik'a mata tak'i karb'a yayi godiya ya shiga mota, Daidai Nadrah ya tsaya ya zuge Glass"Hey Sai kinji kirana" ya d'aga mata hannu kawar da kai tayi gefe ya wuce a guje.
Inteesar ta k'arasa gurin ta Daidai nan ta tsayar mata da Napep tana cewa"Intee kin cika surutu da rawar kai wallahi,Allah yasa baki bashi number na ba"
Dariya tayi tana shiga Napep din" Wallahi gayen ya had'u ne, pls ki amshi soyayar shi sai munyi waya bye"
Tsaki kawai tayi mai Napep yaja suka wuce ita kuma ta juya zuwa gida,tana mai jin haushin rawar kai irin na Inteesar sai kace ba mace ba ta tsaya tana zubar da class dinta,Da daddare sai ga kira ganin bak'uwar number tayi mamaki domin ta manta da wanda suka had'u a titi,tana d'auka taji zazak'ar muryar shi,gaisawa su kayi tace wake magana yace"Yanzu baki gane niba Nadrah?har kin manta da wanda kuka had'u d'azun a kan titi"
Cikin basarwa tace" oh na tuna ya aiki"
" Alhamdulillah Nadrah suna mai dad'i, Kyakyawar sauraniya cikin mata,Zinariya cikin y'an mata"
Jin kirarin shi yasa tayi Murmushi,haka yayi ta jero mata kalaman yabo da fad'in irin kyan da take dashi,kunsan mata da son a yabe su nan fa Nadrah taji dad'i domin babu wanda ya tab'a fad'a mata irin kalaman nan,ai sai ta saki suka d'an fara hira,ya gabatar mata da kanshi ya fad'a mata sunan shi Sufyan shi d'an Kaduna ne bikin Abokin shine yazo Zaria shine suka had'u,haka suka danyi hira har sukayi sallama.
Tun daga ranar Shikenan Sufyan yake kiran Nadrah tun tana kula shi sama sama har ta fara kula shi sosai, domin shi irin mutanen nan ne masu saurin sabo,yana da ban dariya,ga iya kalamai,ga iya soyayya nan da nan Nadrah ta fad'a k'aunar shi, kullum makale take da waya,ko suna chats ko waya,Haka ya dinga tambayar ta yaushe zata koma Kaduna danshi tuni ya koma tace sai hutun su ya k'are,ai kuwa hutun su na karewa driver yazo ta d'auke su,suka koma Kaduna.
Sufyan Haidar Shine Asalin sunan shi,Shi kad'ai iyayen shi suka haifa baban shi nada kud'i,yayi Karatu har zuwa University inda yayi karatun acan k'asar Canada, Business Administration ya karanta,ya dawo Nigeria baban shi ya samar mishi aiki,Sufyan d'an gata ne iyayen shi sun shagwab'a shi kasancewar shi kad'ai suka haifa,Sam basa tsawatar mishi duk abinda yayi sai suce Lokacin shine ai, Tunda yaje K'asar waje ya had'u da turawa shikenan ya fara neman mata,baya shaye shaye amma fah ya iya tsara mace ya iya kalamai na soyayya da sace zuciyar mace,indai yaga mace tayi mai toh sai yasan yanda zaiyi ya same ta, Amma idan ya had'u da mace ko wata biyu basa yi tare suke rabuwa saboda ya hanga wata kullum cikin canza y'an mata yake kamar kaya haka ya d'auke su,Shi yana son ayi soyayar shan minti kawai a hole rayuwa,Yana kashe musu kud'i, iyayen shi sun san yana neman mata amma basu damu ba suna ganin yana yin aure ai zai daina,rana d'aya sai gashi ya had'u da Nadrah Wanda lokaci d'aya yaji k'aunar ta.
Tun bayan dawowar ta Kaduna yayi yayi su had'u tak'i saboda tana tsoron Daddy,kuma ita bata tab'a soyayya ba idan Daddy yasan tana soyayya ta tabatta sai ya kusa kashe ta domin kam Karatu yake so tayi,Ko gidan nasu tak'i yarda Sufyan yazo duk ranshi ya b'aci da yaso ya rabu da ita amma ya kasa kwana biyu baya Kiran ta kota kira baya d'auka, hankalin ta duk ya tashi sosai domin ba karamin son shi take ba,shima a nashi bangaren dauriya kawai yake amma shi kanshi ya tabbatar da cewa yana k'aunar ta sosai kuma son da yake mata so ne na aure ba wai da iskanci ba kamar Sauran matar,ya yaba da tarbiyya ta domin ko irin naked dinta yace ta turo bata turawa sai tace haramun ne,kenan shi d'an iska ne yake cewa ta tura mai jikin ta,ai nan ya fara mata dad'in baki wai so yake ya gwada ta yana son sanin tarbiyya ta ne,sai ya fara cewa ai y'an mata dayawa y'an iska ne amma ya tabbata ita kamilaliya ce,A haka da dad'in baki ya kawar mata da duk wani tunani. Nadrah kuwa ta fad'a mai ka'idar Daddyn su duk Lokacin da zata ba Mommy wayarta sai ta goge Chats dinsu da calls,kuma baya Kiran ta idan Lokacin ajiye wayar nasu yayi,akwai time din da suke waya da Chats, Mommy bata tab'a sani ba,tana yawan bincike wayar cikin dare Amma bata ganin komi,hakan yakan yasa hankalin ta ya kwanta, Hisham kuwa yasan Soyayar dake tsakanin Nadrah da Sufyan ta bashi labari amma tace kar ya Bari kowa ta sani,har Yusrah ta fad'a mata yanda suke matuk'ar k'aunar junan su.
Yana zaune duk abin duniya ya ishe shi,ba zai iya jure rashin jin Muryar ta ba D'aukar wayar shi yayi ya kirata, Lokacin tana tare da Mommy suna aiki a kitchen,Gaba d'aya ta kasa D'aukar wayar kusan sau uku yana kira bata d'auka ba,Can Mommy tace"Wai Daughter ba kiran ki ake a waya ba ki d'auka mana"
Cikin tsoro da rawar murya tace" Humm class mates nane tun d'azu ta ishe ni wai inyi mata snapping Questions na Assignment da aka bamu bata je ba jiya"
" Oya jeki mata snapping mana"ta fad'a tana juya miyar dake kan Electric Cooker
Da sauri Nadrah ta d'auki wayar tayi hanyar d'akin ta tana zuwa ta rufe k'ofa, hannun ta har rawa yake ta Danna kiran shi domin ita kanta tayi missing dinshi ba tayi tunanin zai kira ba,katse kiran yayi ya kira ta,tana d'auka kawai ta fashe mai da kuka,Sosai yaji zafin kukan nata"Meye ne na Kira kike min kuka"
Kuka ta cigaba bata ce Komi ba,can yace" In kashe ne sai kin gama kukan?"
Da sauri tace"No pls don't hang up,Mene nayi maka kwana biyu ka daina kirana kuma baka picking calls na,mene ne laifi na pls Tell me"ta k'ara fashewa da kuka.
Cikin rashin jin dad'in kukan nata yace"pls Nadrah tah ki bar kukan nan kinji,ina jin zafi a zuciya ta bana son kina zubar da hawaye"
Tsayawa tayi da kukan" Dan Allah ka fad'a min mene ne ya faru"
Karya ya kirk'iro yace" Sweet Nadrah Bani da lafiya ne shiyasa,bana iya D'aukar waya,a silent ma yake, anyi addmiting dina a hospital d'azun aka salame ni,...."
Cikin damuwa tace" Hassbunallah, Hope yanzu da sauki Wallahi ban sani bane I thought ka daina sona ne"
Da Sauri yace" Never Baby nida ke mutuwa ce kawai zata raba mu, matuk'ar ina raye bazan tab'a barin ki ba"
Ajiyar Zuciya ta sauke nan ya fara mata kalaman soyayya nan da nan ta manta da b'acin rai har ya dinga sata dariya, k'arshe dai sukayi sallama.
Haka suka Cigaba da soyayya,Gashi ko yaushe sai yace yana son ganin ta, tak'i bashi dama yazo gidan su, anan ne taje ta samu Mommy ta fad'a mata, Mommy tayi mamaki yaushe har Nadrah ta fara kula saurayi bata sani ba koda yake ta fad'a mata cewa a waya ne kawa basu tab'a haduwa ba, ita ma Mommy tana son Nadrah na gama secondary school tayi aure saboda bata son ta fara University ba tayi aure ba, gara ta aurar da ita da wuri duk da ta yarda da tarbiyyan data ba yarinyar nata, amma she's 18 yanzu ya kamata ace ta tsayar da Mijin aure shiyasa ta bata dama tace Sufyan yazo,ai kuwa da Nadrah ta fad'a mishi sai murna yake,shi kanshi yana Mamakin irin son da yake ma Nadrah Wanda bai tab'a ma kowacce mace irin shi ba,Gashi sun dad'e tare ba kamar Sauran y'an matan da yake rabubuwa dasu nan da Nan ba, shiryawa yayi cikin White Shaddah yasa blue Hula sai zuba k'amshi yake,sosai yayi kyau,ya nufa side din Maman shi yana zuwa ya gan ta kan Kujera a shagwab'e yaje ya rungume ta ta baya yana cewa"Sweetheart na,kin kusa zama granny"
Shafa kanshi tayi ya zagayo gaban ta,tace" Ban gane ba Son Granny kuma? Yimin bayani ince dai ba wata kayi ma Ciki ba?"ta fad'a tana tsare shi da ido
D'an b'ata rai yayi" Irin gani d'an iskan nan Koh?"
Dariya tayi tana cewa" No Son D'ana ba d'an iska bane, maganar naka ce ban fahimta ba?"
Shima dariyar yayi yana Kwantar da kanshi kan laps dinta" Ummu nah,Aure nake son yi na samu mata kinyi suruka"
Cikin farin ciki Marar missaltuwa tace" Alhamdulillah kai amma naji dad'i what a surprise,My Son dagaske nayi In law?,wanan shirin halan gurin ta za kaje?"
Dariya yayi ya Mik'e tsaye" Yeah Ummu,Mai zaki bani inkai mata"
Mike'wa tayi"wait for me"
Ta nufa d'akin ta can sai gata ta fito d'auke da warwaro na zinare guda biyu cikin d'an wani transperent karamin jaka,Ta damk'a mai a hannu"ina son kasa mata Wannan kace mata Ina farin ciki Sosai,Kuma Ina son ta"
Peck ya bata a hannu yace" you're the best Mother in the world, Ummu na ke ta daban ce"
Har ya juya zai fita ta kira shi" Son baka fad'a min sunan surukata ba"
Dariya yayi yace"Nadrah Sufyan shine sunan ta"
Dariya Ummu tayi tana jin dad'i a zuciyar ta bata tab'a ganin d'an nata yana son wata ba,tana fatan Allah yasa wacce ya samu zata zama sanadiyar shiryar dashi.
Yana mota ya saki kid'a sai bi yake cikin nishadi,dama already ta fad'a mai address din gidan nasu.
Marubuta biyu ke rubuta muku Wannan labarin wato
UMMU BASHEER
&
MAIMOUNATH O.G