KAICO CHAPTER 11
🌸🌸KAICO!🌸🌸
🌸🌸
🌸
MALLAKAR...
KYAUTA DAGA ALLAH
DA
MAMAN AMATULLAH.
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION💪🏻📚
Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne bamuyi bamuyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba in ya yi dai-dai da halin ki/ka to akasi ne sai ayi ƙoƙarin gyarawa.
Wannan littafin na kuɗi ne kobiya #300 kacal👌🏻 kafin ki karanta domin neman ƙarin bayani a tun tuɓemu ta wa innan lambobin *** ko ***.
Shafi na1️⃣1️⃣
Free page
"Kidnapping innalillahi sannu Baba ina wuni? tafaɗa cikin rawar murya, tsawa ya daka mata wacce tasa ta ƙara furgicewa,cikin ɗaga murya ya ce ƴar ku tana hannunmu muna neman kuɗin fansarta ko kuma mu aiko muku da gawarta" cikin rawar murya da kaɗuwa mamy tace "kuyiwa Allah da Manzonsa karku kashemin yarinya bamu da kuɗin baku mu talakawa ne kuyi haƙuri dan Allah ku tausayama" "Ke rufemin baki an faɗa miki mumunsan tausayi ne to idan kuka sake wa'adin da zan baku ya cika baku kawoba to kufara shirin karɓar gaisuwa dan kuwa a mace zamu dawo muku da ƴarku kunji na faɗa muku mun baku awa arba'in da takwas (48) kwana biyu kenan duk in da kuɗi suke ku nemo miliyan biyu (2m) ku kawo" "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yanzu ina zamu samu wa'innan maƙudan kuɗin dan Allah kuyi mana rai wallahi bamu da hanyar samunsu kuyi mana ragi dan Allah" "ke kinga banason doguwar magana wannan kuɗin su zaku kawo sannan idan kuka sake hukuma ta sani to ku tabbata ran ƴarku ze salwanta kunji na faɗa muku" yana kaiwa nan ya kashe wayar ji ka ke kitttt..
Cikin kuka mamy taketa faman hello!hello, Malam sa'ad dake tsaye duk yana jin abin da suka faɗa ya rasa ma me zeyi ji yayi juwa tana ɗibansa guri ya samu ya zauna ji ka ke daɓas! ƙara fashewa da kuka mamy tayi tana mai maita innalillahi basuyi aune ba sai ganin ta sukayi ta sulale ƙasa sumammiya...
***** ****** *****
Zaune take ta zabga uban tagumi abin duniya duk ya isheta ga ɓatan ƙawarta Fatema ga kuma matsalar da take ciki gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi tarasa mekeyimata daɗi wayanta dake gefe ke tafaman ƙara amman sam batajiba sabi da ta lula duniyar tinani,sai da aka kira kusan sau uku kafin a na huɗun ne ta ankara sai da gabanta ya faɗo Rassss dan ganin sunan dake yawo a fuskan wayan hannu na rawa ta ɗauka cikin sanyin jiki dana murya tace "Hello" daga ɗayan ɓangaran a kace "Ƙanwata ina ki ka shiga ne inata faman kira baki amsaba? cikin rawar murya tace "Yaya kayi haƙuri ban gani ba ne sai yanzu" "ok karki damu babu matsala kizo ɗakina ki kawo min coffe yamzu" da to ta masa tare da kaɗa kai kamar ƙadan garuwa, miƙewa tayi jiki a matuƙar sanyaye hijabi ta zura tare da ficewa daga ɗakin nata, kai tsaye kitcin ta shiga, ummanta ta tarar a kicin ɗin,duban ta umman tayi tare da cewa "Ke kuma fa lafiya ki ke? tayi tambayar tana tsareta da ido, cikin sanyin jiki tace "lafya ƙalau kawai ina ta tinanin Fatema ne ko a wanne hali take ciki yanzu abin duk ya dameni" "Au wai kina nufin haryamzu ba'a samu labarin in da ƙawarki takeba? "Wallahi kuwa umma haryanzu shiru" "To Allah ya bayyanar da ita cikin ƙoshin lafiya" da Amin Hafsa ta amsa tana haɗawa yayansu coffe tana gama haɗawa ta fita tare da cewa "Umma zan kaiwa yaya Marwan coffe" kai ta jinjina mata ba tare da tace ko mai ba ,itama kai tasa ta fice ba tare da ta ƙara furta ko mai ba..
Bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar ɗakin Marwan ta shiga,amsa mata ya yi yana binta da wani shu'umin kallo mai wahalar fassara mai cike da tarin ma'anoni wan da shi ya barwa kanshi sani. kanta a ƙasa ta gaishesa amsawa ya yi yana binta da ido, kofin ta miƙa masa tare da cewa "Yaya gashi" karɓa ya yi yana faɗin "Nagode" Juyawa tayi da nufun barin ɗakin cikin cool vaice ɗinsa yace "Hafsat" tsayawa tayi cakkk ba tare da ta juyoba,ganin tatsaya amman batace momaiba yasashi cigaba da faɗin "Dawo ki zauna zamuyi magana" dawo watayi ta zauna ɗan nesa dashi, murmushi ya yi tare da faɗin "Yau kuma ni ki ke gudu Hafsat yayanki nefa Marwan" ita dai batace ko mai ba sai wasa da takeyi da yatsun hannunta ,ƙureta ya yi da ido tare da faɗin "Shikenan manta kawai ya maganarmu naji ki shiru har yanzu bakice ko mai ba ki temaka ki amsa min ko na samu sanyi a cikin zuciyata ki tausayawa yayanki mana" ya ƙarasa maganar cikin sanyin murya.
Kanta ta ƙara sunkuyarwa tana wasa da tatsun hannunta tace "Haba yaya kaima kasan abin da kazo dashi baze yiwuba nifa ƙanwarka ce to tayama za kazomin da irin wannan maganar gaskiya Aa ka sake tinani amman ba dani ba" Taƙarasa maganar cikin rawar murya hawaye nabin fuskarta.
Kofin hannunsa ya ajiye tare da miƙewa ya matso kusa da ita ya na faɗin "Subahanallahi! to meye abin kuka kuma" ya ƙarasa maganar yana saka hannu yana goge mata hawayen, da sauri ta kwace fuskarta tare da miƙewa cikin sauri tana ja da baya cin zafin nama ya fizgota tare da rungumeta tsam jikinsa yana sauke a jiyar zuciya cikin kasalalliyar murya tace "Haba Hafsa wai me yasa ki ke haka ne gudunafa ki keyi kamar ba yaya marwan ɗinki ba me laifina meyasa za kimin haka kin san yan da ki ke da matsayinki a raina da kin sani tabbas da bakiyi abin da ki keba amman zan ƙara miki lokaci kije kiyi tinani a kai" ya ƙarasa maganar yana shafa mata baya..
Hawaye kaɗai kebin fuskarta cikin zuciyarta kuwa ita kaɗai tasan me takeji gawani baƙon lamari dake fusgarta cikin zafin nama ta turesa daga jikinta tare da ficewa daga ɗakin da gudu, bayanta yabi ta kallo tare da wani shu'umin murmushi, saman gadonsa ya faɗa tare da lumshe ido yanajin wani daɗi na ratsa dukkan ilahirin jikinsa..
Ummanta na zaune a falo taga tazo ta wuce da gudu tana kuka kira ta kwada mata amman ina sam batajiba ta wuce ɗakinta, kai umma ta girgiza,ta cigaba da sabgarta,.
Tana shiga ɗakin ta faɗa saman gadonta wani kuka mai tsuma zuciya ta saki, tana tsaka da kukan taji muryan ummanta tana faɗin "ke kumafa me akayi miki kike kuma? tana daga kwancen tace "umma yaya Marwan ne wai yace...tsaki umma taja tare da tarar numfashinta tace "Wai dama tsakaninki da marwan ne wallahi bakwa rabo da shirrita na ɗauka ma wani abu ne" tana kaiwa nan ta fice abinta.
Wani saban kuka Hafsat ta saka tare da faɗin 'wannan wace iriyar uwa take da ita,wacce sam bata damu ta tsaya taji damuwar ƴaƴanta ne hannu tasa ta goge hawayenta tare da yiwa kanta Alƙawarin daga yanzu ta dena yinƙurin faɗawa ummanta damuwarta tin da ko tafaɗa ma ba sauraronta zatayiba tanaganin gara ta hutar da kanta ta dena ƙoƙarin faɗa....
****** ******* ******
"Wai ke me yasa ki ke damun kanki a kan batun yaron nan ne iyiii me nene a ciki dan ya yi auren sirri ni banga wani matsala a cikiba ke ko da wani abu ze je ya dawo ni ina da arziƙin da zan magancesa ƴarfa mara gatace balle galihu to mema zeje ya dawo babu ko da kuwa fyaɗe ya yi mata balle daraja ya ƙara mata ya aureta har kuma ya haɗa jiki da ita duk da matsayinta be kai ba dan haka ke ki ke wahalar da kanki a banza da damuwa amman ni duk abin da yarona keso zan bashi in dai a faɗin wannan duniyar ne dan kuwa farin cikinaa shine nawa"....
Ita dai mom jinsa kawai take tana mamakin yan da idonsu yarufe da uban da ɗan sam basa hangen matsalar da kaje ka dawo ita dai tanaji a jikinta sun tafka babban kuskuren da zesaka su kuka dan ba a ko ina dukiya take da amfaniba,..
Nisawa tayi hmmm tare da cewa "Alhaji kenan walahi ina jiye muku ran da zakuzo kuna kuka akan wannan bin kuna ma damar da burin dama baya ta dawo ku gyara kuskurenku alokacin zaku gane abin da nake nuna muku sai dai kash! lokacin kun makara guri ya ƙure muku, tabbas ina mai jieye muku wannan ranar" ta ƙai ƙarashen maganar tana barin gurin...Da kallo ya bita yana juya kalamanta baki ya taɓe tare da faɗin " Mata sam bason farin cikin ɗanta ɗan guda ɗaya tilo to idan bamu gatantashiba waza muyiwa dole na bashi duk farinci tin da dukiyadai a kwaita Allah ya hore har ƴaƴa da jikoki".....
****** ****** ******
Ɗaki ta shiga ta dinga safa da marwa tanajin zuciyarta na yimata suya tabbas da tasan haka abin ze ƙare da batayi maganaba yanzu gashi shi da kansa ta tafi kaisu wannan ai rashin sa'a ne Sa'a ta faɗa a ranta.
Tin da suka ɗauki Hanyar ƙauye babu wan da yace ƙala shiru ka keji ko wa da abin da yake saƙawa a ransa, da haka har suka isa guri ya samu ya yi fakin bakin wani gida wan da kallo ɗaya za kayi masa kasan cewa ko a ƙauyen su masu rufin asirine, yana gama dai-daita tsayuwarsa duk suka firfito zuciyoyinsu cike da farinci, da sauri suka nufi cikin gidan suna kwana sallama..
Salamatu na ƙoƙarin shigewa malam Tanko ya dakatar da ita tare da faɗin "Sati ɗaya kacal na baku sannan zan dawo da kaina na ɗaukeku in kinshiga ki gai da mutan gidan yana kaiwa nan ya juya baki tabuɗe tare da cewa.....
Kukasance da zafafa biyu Maman Amatullah D Kyauta daga Allah....