JINNUL KAMIL(A TRUE LIFE STORY OF ALISHA)

1

by @milhaart


Wani Kataferen ɗaki ne da sai idon ka ya gane maka, domin ɗakin yayi matuƙar ƙayatuwa. Komai na wannan d'akin kalarsa ta kasancs pink color ne,Mai d'aukeh da wani ƙayataccen Royal bed, A kwance take baccin ta cikin nitsuwa da kwanciyar hankali. Tamkar wata sarauniya..




Kwankwasa kofar da akayi ne yasa ta bud' lumsassun idanta ,muryar mummy taji tana fad'in "Alisha bazaki tashi daga wannan baccin asarar da kike yi ba? kinajin gari yawaye Amma kin kasa tashi ko?"


Mikewa tayi had'e da fad'in "Gani Nan zuwa Mummy."

Bathroom ta fad'a ta watsa ruwa, tun da Asuba Daddy ya tada ta tayi sallah tana idar da sallar ta koma bacci.


Fitowar ta Kenan daga bathroom tana kokarin saka kaya bata an Kare ba sai taji saukan duka a bayan ta, wani yar karamar Kara ta saki a tsorace ,cikin kuka take fad'in "Mummy am Sorry yanzu zan fita."

"Don ubanki Ni sa'ar kice, ko Ni baiwar kice da ina Chan ina aiki a kitchen kina Nan kina shirme?"


Taji zafin bugun da ta kaima ta hakan yasa hawaye ya tsiyayo mata har kuncin ta,mummy na ganin hawayen ta kama hab'ar ta Tace "jimin ja'irar yarinya me na miki kike kuka?"

Cikin muryar kuka tace "Mummy ba kuka nake ba."


Wani gigitacciyar mari ta mata had'e da fad'in "Yanzun Ubanki kikeyi ne, Wallahi Alisha ki kiyaye ni,bana son munafurci,yanzu me na miki da kike kuka?"


"Kiyi hakuri Mummy, Wallahi bazan sake ba"

"Ya dai fi miki,dama kiyi sauri ki tashi ki sa kaya ina jiran ki a kitchen"

Ciki ciki ta amsa da "Toh."


Ban 'daki ta koma, ta wanko fuskar ta, ta zauna a gaban mirror tana kukan zuci a gaggauce ta shafa mai, ta nemi Riga da wando jeans ta saka sannan ta d'auki karamin baby Hijab ta sa , tayi sauri ta fita ta nufi kitchen, a hanyarta ta zuwa kitchen ta hango daddy a parlor yana zaune.



Ta nufi inda yake, cikin girmawa ta durkusa har kasa ta gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska, Murmushi yayi yace "Mamana kin tashi lafiya?"

"Lafiya Lau daddy, kana zaune kana hutawa"

"Eh kin San weekend, sai da haka."


"hakane a huta lafiya, Bari na Shiga kitchen"

Murmushi yayi yace "Alisha ina jinki da mummyn ku, me Kika yi mata ne da sanyin safiyar Nan"

 


Kai a kasa Tace "Babu komai daddy"

"Na sani dama baza ki fad'a ba, maganar da na saba fad'a miki shi Zan sake fad'a miki, ki cigaba da hakuri da mummyn ku, sannan nasan ko baki fad'a ba kina kokonto akan ba itace ta haife ku ba ko?"


Kai ta d'aga alamun eh, yace "To ba haka bane, Haleema itace mahaifiyar ku, ke da kannen ki, abinda nake so dake shine ki cigaba da hakuri akan Wanda kikeyi, Kinga ke mace ce, a ko ina ana son mace Mai hakuri, kin...... "


"Alisha!!! Alisha!!! Suka tsinkayo murya mummy cike da masifa take Kiran sunan Alisha.

Girgiza Kai yayi yace "Tashi kije, ina ga tana so ki taya ta wani aikin ne"

 Mikewa tayi tace "Toh Daddy." Da sauri ta Mike da niyar Shiga kitchen d'in.


Juyawar da tayi ta hango Mummy ta nufo su, Saida ta ji zuciyarta ta fara bugawa uku uku, ga mamakin ta sai taga mummy na Murmushi tun Kan ta karaso inda suke tace "Daddy and Daughter,Kuna Nan Kuna abinda aka saba,nasan gulmata kuke."



Yar karamar dariya yayi yace "A'a mu ba gulmar ki muke ba, gaisawa mukeyi Kuma kin San yanzu sun kusa rubuta WAEC d'insu, ranar Monday nake so nayi mata registration" 


"Hakane Allah ya kaimu,ya basu sa'a"

Ya amsa da "Ameen" a tsawace Tace "Alisha kin San Allah ki kiyaye ni,ki wuce Kitchen kije ki daga min sakwara, sannan idan kin gama kije ki ta da Fa'eez da Hisham, baccin ya Isa Haka"


Ta Masa da to had'e da barin gun, tana Shiga kitchen ta Fara aikin da ta sata, bayan ta gama kirb'a sakwarar ta sa a leda ta jera a food flasks, bata fita a kitchen d'in ba sai da ta gyara shi tsaf sannan ta wanke kwanukan.



'dakin kannen ta, ta nufa ta tarar dasu suna kallo a TV Baki ta Kama Tace "Laaah Ashe dama Kun tashi, Kuma baku fito ba?"


Fa'eez dake shine babba yace "Aunty Alisha kin San, halin mummy Sarai, yanzun Nan kana fita ta fara surutai ta Shiga Nan ta fita Chan,inda take Shiga ba Nan take fita ba mtsww"


A tsawace Tace "Fa'eez ban hanaka fad'an mumunanan kalamai wa mummy ko a bayan idon ta ne? Meyasa baka jine,ko so kake Hisham da Nawal su koya? Ko so kake ka koya musu yanda zasu Raina mummy?"


"idan sunyi hakan ma ai ba laifi bane ba, ke kina ganin abinda take yi dai dai ne? Mummy fa ta fifita business d'inta fiye da komai a duniya, hatta daddy Bata d'auke shi a matsayin Miji ba" 


"Nasan da hakan addu'a kawaii Zamuyi mata, Kuma ko ba komai ta haife mu ko da kuwa a Kan bola take,Sam bana Jin dad'in hakan da kakeyi fushinta bala'ine akan mu, Dan Allah ka daina fad'an irin maganganun Nan kaji?"

"Insha Allah na daina sis" had'e da sosa keya alamun maganar tata ta shiga Jikin sa.

"Nagode da jin maganata da take, ku tashi muje, Kai Hisham kana ji ana magana Amma kaki kula mutane ko?"


"Sorry sis naga maganar taku ce shiysa, yauwa nace yaushe za a dawo da Nawal ne, Nifa ina kewar ta"



Yar karamar dariya Alisha tayi tace "Anya kuwa kewarta kake? Ko Kuma ka kosa ta dawo ka rika cin zalinta?"


Fa'eez yace "Ai kuwa daii."

Suna Hira suka fita suka nufi dinning Table, mummy na ganin su wani irin harara ta wurga musu had'e da fad'in "Na d'auka jirana kuke na Kai mu ku abincin a d'aki."



Girgiza Kai Fa'eez yayi ya ja kujera ya zauna, yace "Good Morning Dad" 

Ya amsa da "Morning son" Shima Hisham d'in ya gaida Daddy da Mummy,duk suka amsa fuska a sake.

Fa'eez kuma abincin sa ya fara ci, mummy ajiye spoon d'in dake hannun ta tayi tace cike da mamaki da masifa tace "Kai don ubanka Ni Kuma ban Kai ka gaisheni bane ko me? Ubanka kad'ai ka gani anan?"


Burus yayi kamar baiji ta ba tace "Fa'eez ba da Kai nake ba"

'dago Kai yayi yayin da dai dai ya Kai spoon bakin sa, fasa ci yayi ya ajiye yace "Mummy Wai ke Dan Allah yaushe Zaki daina irin wannan halin naki ne? Ke kullum bakya gajiya da surutu ke da kowa ma sai kinyi mtssw" Yana Kai Nan ya tashi ya fice daga gidan ma gabaki d'aya.



Sai huci take tana balbalin masifa Babu Wanda ya tanka Mata,ta fad'i Wannan ta Fad'i wanchan ta inda take shiga ba tanan take fita ba tace "Yanzu Kai Abdulhameed kana ganin rashin kunyar da yaran nan suke min Amma baza ka sa baki ba?"


Daddy cin abincin sa kawai yake, ba tare da ya kalle ta ba yace "To me kike so ince Miki Haleemah? Kullum maganar da nake gaya miki Kenan ki daina takurawa yaran Nan Amma kinki ji Baki San yawan takura na sanya yaro ya tsane ki ba ? Musamman ma na yaro, Fa'eez Yana cikin tashen balagan sa shi komai zai iya fad'a miki Kuma ya ga kamar dai dai ne,kefa uwace Kama ta ai ki ja yaran ki a jiki,ki nuna musu soyyayar ki da kulawar ki ba ki Rika tsangwamar su ba"


Nisawa yayi kana ya kalle ta yace "ki duba kiga yanzu abinda Kika ja wa kanki yaron Nan Fa'eez kwata kwata a nawa yake yaro d'an shekara Sha biyar ya tsaya Yana gaya miki magana, Kuma d'an da Kika Haifa da cikin ki, Haleema ya kamata ki canza hali"



"Dama na sani Kai kake goya musu baya suke abinda suke so a gidan nan, har ya kai ga suna Raina ni, Banga laifin ka ba yaran Nan da ace bani na haife su ba ai da na Shiga uku...... " Alisha ganin hakan da mummy take da d'auki plate d'in abincin ta , ta koma d'akinta Hisham da yaga hakan Shima ya tashi ya fice daga gidan.



Daddy yace "Kinga ni ko Haleema kin gani ko? Dan Allah me amfanin hakan? Yara suna cin abinci kin tada musu hankali sun kasa ci, Haka kikayi jiya duk Kika Hana mu cin abinci muka kwana da yunwa"



Mikewa yayi yace "Tunda Haka kike so gaki ga abincin kisan yanda zakiyi dashi" duk maganar Nan da Daddy yake acikin ruwan sanyi yake maganar sabida shi ba mutum bane Mai son hayaniya ba. Magana ma yake ba zaka tab'a gane ko fushi yake ba.


Mummy kuwa duk da ya tafi ya barta a gun ita kad'ai,bata daina surfa masifa ba, sai ma abinda ya karu sai da tayi ta gaji ta Shiga d'akinta ta shirya ta d'auki makullin motarta ta wuce shagonta.


Alisha tunda ta shiga d'akin a gaban mirror ta zauna sannan ta ajiye plate d'in abincin nata daga gefe kallon fuskan ta tayi a madubi girgiza kai tayi sannan tayi Murmushi tace "Allah ka iya Mana" Zama tayi taci abincin nata,dake dama yunwa take ji rabon ta da abinci tun jiya da ta dawo daga school, sun Fara cin abincin Kenan Mummy ta fara halin nata,a dole suka hakura da cin abincin,sai da ta cinye tass ta ajiye plate d'in.



Karar motar da taji ne yasa tayi saurin mikewa ta nufi window lekawa tayi ta hango motar mummy na fita Murmushi tayi Tace "Alhamdulillah."



'daukan plate d'in tayi ta nufi hanyar Kitchen,tun daga nesa ta hango Kan dinning d'in kacha kacha Murmushi tayi ta girgiza kai ta nufi Kan dinning d'in ta tattara ta gyara gun tsaf,kana ta d'auki sauran chips d'in ta kai wa Mai gadin su, ya karb'a yayi ta mata godiya yana washe baki kamar Mai tallen toothpaste, Murmushi kawaii tayi ta koma d'akin ta. Killing yaumin idan sukayi girki basu Isa suci ba sabida mummy duk yadda zatayi sai ta nemi abinda zatayi masifa akai.



Ta na kwance taji an turo kofar d'akin ta had'e da sallama, tana ganin Wanda ya Shigo ta kauda kanta Murmushi yayi yace "Haba Aunty Alisha, Sallama fa nake Kuma baki amsa ba."



"Wa alaikassalam" kawai tace ba tare da ta kalle shi ba.

zama yayi Akan karamar gujeran da ke gefen gadon ta yace "Hmmm bacci kike ne?"

"A'a" kawai tace Masa a takaice.

"Ya na ga kamar ranki a 'bace ne?"


Tashi tayi zauna tace "ba Dole Raina ya 'baci ba, Kai kullum Fa'eez sai ka jawowa mutane magana,kasan Halin mummy fa sarai, sannan 'dazun Nan na maka magana Akan yanda kake mayar mata da magana Amma sai da ka sake, sabida Ni ban Isa na fad'a maka magana kayi amfani dashi ba."



Gyara Zama yayi yace "look s is bai kamata kina tada hankalin ki Akan minor(karamin abu) abubuwan nan ba"

"Minor? Mene ne minor d'in kana jin dad'i idan kaga suna sa'insa da Daddy,kana jin daddyn hakan ko?"

"No kin San babu yanda za a yi naji dad'in hakan,Mummyn ne duk hakurin ka Sai ta shakar da kai"


" Idan kayi shiru mutuwa zakayi, sannan wani daliline yasa kaki gaishe ta d'azu?"

"Nothing(babu)"

"Nothing Fa'eez? Nothing fa kace?"

"Eh nothing kawai banji Zan iya gaida ta bane,sabida ba Sona take ba,nima bana son ta" yana Kai nan ya mike ya fice, Alisha kuwa binsa tayi da kallo har ya fice,ta dad'e a haka kana Tace "Inna lillahi wa Inna ilaihirraji'un."



Komawa tayi ta kwanta,ta rufe idonta, ta dad'e a haka kana bacci Mai dad'i ya d'auke ta.



Bata farka ba,har Saida taji horn na mota a razane ta farka, tana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,agogon 'dakinta ta duba taga karfe uku na yamma tsalle tayi ta dirka daga kan gado ta nufi window ta leka,ganin Mummy da tayi ne yasa ta dafe kirjinta tace "Innalillahi na Shiga uku."

__________________________

Please comment and share

Milhat ce 

Yar Terawa✍🏻