CUTAR KAI

Chapter 5

by @ummubasheer

```CUTAR KAI....```๐Ÿ’



{ _Labari ne mai cike da nadama, yaudara, tausayi, tsantsar k'auna mai tab'a zuciya_ }



_Story And Written_

        ```By```

```UMMU BASHEER

   &

MAIMOUNATH O.G```


*Wannan labarin k'irkira ne, bamu yarda a sace ko ayi mana copy and paste ba, duk wanda yayi kuma bamu yafe ba*



*Page 05*



Nadrah ce zaune tayi nisa cikin tunani sai ga Hisham zama yayi kusa da ita"Aunty Nadrah dan Allah ki cire damuwa a ranki"


Wasu hawaye ne suka zubo mata" Hisham ba zaka gane abinda nake ji bane, Baba Kabeer fah za'a aura min, ya za'ayi in aura tsoho kuma ma Abokin Daddy" ta fashe da kuka.


Sosai yake jin tausayin Yayar tashi"Nima bana son ki auri abokin Daddy amma kuma kinsan Daddy akwai kafiya abinda yace shi za'ayi, kuma Ya Sufyan babu ruwan shi bansan meyasa Daddy baya son shi ba"


Da Sauri tace" yauwa d'an kani nah Pls ara min wayar ka"


D'an Zaro ido yayi" Kar fa Mommy ta gani tace nine ke baki waya"


"No bazan bari ta gani ba" ta fad'a tare da Mike'wa tsaye, Mik'a Mata wayar yayi ta shige d'aki, tana zuwa tasa key a k'ofa tasa number Sufyan wanda dama ta haddace shi, ai kuwa ringing d'aya ya d'auka dama yana da number Hisham,"Hello Nadrah tah, hope kina lafiya, an karb'a wayar ki ko shiyasa bana samun ki, yanzu meke faruwa Nadrah ina son ki sosai wlh bazan iya rabuwa dake ba"ya jero mata tambayoyi cike da tashin hankali.


Kuka ta fashe dashi"Nima bazan iya rabuwa da kai ba, Wallahi Sufyan ina matuk'ar k'aunar ka, Daddy wai aure zaiyi min kuma da Abokin shi! "


" What? Aure? "Ya fad'a cikin d'aga murya mai nuna tashin hankali.


"Eh wai aure zaiyi min kuma Wallahi ni kai nake so, dan Allah Sufyan take serious action, if not Daddy zai aura min abokin shi, kuma Daddy yana da kafiya akan maganar shi"


" No Nadrah babu wanda zaki aura ke din tawa ce, Babu wani tsoho da zai k'wace min ke, ki bani nan da zuwa gobe,zan kira ki anjima muyi magana I love you"


" Tohm shikenan Luv you too" 


Suna gama wayar da ita ya nufa Parlour Mommy shi,nan ya fad'a mata Halin da ake ciki amma bai fad'a mata Cewa Daddy yayi ma Nadrah miji ba, ita kuma tace kar ya damu tunda baban shi ya dawo k'asar anjima za tayi mai magana, da Daddare ta samu Baban Sufyan da maganar Nema ma Sufyan aure, amma bata cemai ga wani matsala ba kawai tace ya samu mata yana son aje a nema mai auren ta, Baban yaji dad'i Sosai, Sufyan ma yazo ya sake mai bayani da Unguwar su Nadrah, nan yace mai kar ya damu zaije ya nema mai auren Nadrah,kafin Baban nashi yaje sai da yayi bincike ya gano y'ar gidan mutunci ne yaji dad'i sosai yayi ma yayan shi magana da kuma Aminin shi,suka shirya ranar wata Friday da la'asar, Sufyan ya kira Nadrah a wayar Hisham ya fad'a mata magabatan shi zasu zo nema mai auren ta,yasan yanzu Daddy zai san dagaske auren ta yake son yi Ranar Nadrah sai farin ciki take,bata fad'a ma kowa ba gudun matsala gara kawai magaban nashi su zo,Sunyi sa'ar samun Daddy kuwa,ganin manyan mutane yayi Mamaki sosai anan ya bud'e musu kofar Parlour shi suka shiga,Ya shiga ciki yace ma Mommy a kawo ma bak'i Drinks da ruwa nan yake ce mata bai san su waye ba,tace yaje yaji Allah yasa dai lafiya,ita kuma Inna mai aiki ta kai musu drinks da ruwa.


Sunji dad'in yanda Daddy ya zauna suka gaisa cikin fara'a suka d'an sha drinks sanan Da Mamaki Daddy yace"Sai dai ban gane daga ina kuke ba, dafataan dai lafiya?" Ya fad'a cikin sakin fuska.


 Da Mamaki suka kalle shi, abokin Baban Sufyan yace"Abin mamaki ba'a sanar maka da zuwan mu ba?"


 "Aa wlh bana expecting bak'i,amma ina bukatar Karin bayani dan Allah" ya fad'a Cikin murmushi.


 Anan suke fad'a mai meke tafe dasu ranshi ya b'aci sosai amma ya danne bai nuna musu ba,sai dai yace bashi da masaniyar zuwan su kuma sanann ya riga yayi ma Nadrah Miji,ya k'ara da basu hak'uri,haka suka tafi cikin sanyin jiki da b'acin rai ya za'ayi Sufyan yasa su zo neman aure ashe ma yarinyar anyi mata Miji,Baban Sufyan bayan ya koma gida yayi ma Ummu bayani ita ma ta shiga tashin hankali domin tasan irin son da Sufyan yake ma Nadrah sai dai bata taba sanin cewa anyi ma Nadrah Miji ba,yanzu sai dai su bashi hakuri.





Daddy kuwa suna tafiya ya nufa Parlour inda Mommy da Nadrah suke zaune sai Hisham da yayi Shirin zuwa Ball, Amma Nadrah gaban ta faduwa kawai yak tana tunanin mai zai faru idan magabatan Sufyan suka zo,Daddy ranshi a b'ace yace"ashe ke yarinyar nan kina da taurin kai ban ja miki kunne akan ki rabu da shegen yaron nan ba?"


 Mommy ta Mik'e" meke faruwa Alhaji kar dai wani abin ta kuma yi?"


 Rai a b'ace ya fad'a mata tare da cewa"Nadrah Matuk'ar nine mahaifin ki ya zama Dole ki auri Alhaji Kabeer,aure kamar an d'aura shine"


 Kuka ta fashe dashi,shi kuma ya bar gurin, Mommy ta zauna gaba d'aya zuciyar ta ba dad'i bata son Nadrah ta auri Alhaji Kabeer amma kuma tana jin haushin yanda yarinyar ke biye ma Sufyan yanda take son shi tunda shi ba nagari bane, Sosai Nadrah ke kuka Tana cewa"Mommy dan Allah ki taimake ni kar Daddy ya aura min Baba Kabeer wallahi bana son shi,zan iya hak'ura da Sufyan din amma bazan iya auren baba Kabeer ba"


 Mommy tace" Nadrah a matsayina na mahaifiyar ki ina baki Shawara kiyi ma mahaifinki biyayya,sanann daga yau ina son ki rabu da Sufyan"


 Cikin kuka take kallon Mommy" Mommy kema kina son in auri tsoho, Abokin Daddy ne fah"


 Mommy jin tausayin y'ar nata yasa ta tashi ta bar gurin,Hisham dake gefe idon shi yayi ja sosai,gaba d'aya ya kasa magana sai yanzu da k'yar yace"Aunty Nadrah kiyi hakuri nasan ba'a kyauta miki ba amma a Islamiyya ance muyi ma iyayen mu biyayya tabas ba zasu Cutar damu ba,Idan kika yi musu biyayya zaki ga alkhairi a rayuwar ki,ko dan saboda Mommy baki ga alamun ita ma bata so ba,yanzu ki bita d'aki I'm sure kuka take,kawai ita ma biyayya take ma Daddy meyesa ke ba zakiyi mai biyayyar ba?"


Duk da he's just 16yrs amma maganar shi ta manya ne kuma tasan gaskiya ya fad'a mata, cikin Sanyin jiki ta tashi ta nufa d'akin Mommy,tana yin sallama taga Mommy ta fara share fuskar ta, gaskiyar Hisham ne, k'arasa tayi ta rungume ta,tana sakin kuka sosai, mommy danne zuciyar ta tayi ta share hawayen ta tare da D'ago Nadrah tace"A matsayina na mahaifiyar ki Nadrah ina baki Shawara ki yi biyayya ta hanyar amincewa da auren nan,nasan Daddy ki akwai abinda yake hango miki,nasan ko kin Amince ko baki Amince ba sai anyi auren amma ina son kiyi hakuri ki bar ma Allah komi muyi ta Addu'a, sannan kuma ki hak'ura da Sufyan domin bai dace dake ba"


 Cikin kuka tace" Mommy Meyasa kuke cewa Sufyan bashi da hali meyasa kuke cewa bai dace dani ba?"


 Anan mommy ta fad'a mata video da aka turo ma Daddy tabbas Nadrah ta girgiza tasan iyayen ta ba za suyi mata karya ba, Sannan kuma Mommy ta k'ara da cewa"Nadrah duk namijin da zai dinga rik'e hannun ki ko yana shafa ki,ko yana yaba surar Jikin ki,ko yana miki zancen batsa,toh ki sani wanann ba auren ki zaiyi ba ba sonki yake ba,wanann din bashi da hali,yanzu kin fahimce ni"


Hawaye ta Share cikin gamsuwa da maganar Mommy domin kuwa sau dayawa Sufyan yakan rik'e mata hannu ko ya rungume ta ya dinga fad'a Mata cewa ita kyakyawa ce da dai Sauran su.


Mommy ta k'ara rik'e hannun Nadrah tace"ina son daga yau ki rabu da Sufyan,idan har kina son farin Cikin mu,ki rabu dashi Nadrah,ki sani a rayuwa ba zamu tab'a CUTAR dake ba"


 Cikin hawaye zuciyar ta na zafi kuma har Cikin Zuciyar ta take jin zata rabu da Sufyan kodan iyayen ta wanda suka haife ta suka raine ta suka kula da cinta da shanta suka tufarta da ita suka raine ta suka bata tarbiyya,ba zata iya bijire musu ba,tasan Allah ma sai yayi fushi da ita dama idan iyayen ka na fushi da kai Allah ma zaiyi fushi da kai,dan haka tace"Mommy inshaallah bazan k'ara kula Sufyan ba,kuyi hak'uri kuma inshaallah zanyi hakuri in auri Baba Kabeer Matuk'ar hakan shine farin Cikin ku zanyi muku biyayya"


 Rungume ta mommy tayi cikin farin ciki Sosai,tace kuma taje anjima ta ba Daddy hak'uri,tace Inshaallah,daga nan ta koma d'akin ta,koda taje tayi kuka Sosai,Bayan magrib Hisham yazo d'akin ta bai ce mata Komi ba ya Mik'a mata wayar shi, karb'a tayi ganin Sufyan,tana son tayi mai sallama k'arshe,Hisham fita yayi ya bata guri, Cikin tashin hankali yake sosai tana d'auka tace"Nasan iyayena ba zasu k'i ka haka kawai ba,sai da dalili,Sufyan akwai wanda ya turo ma Daddy na Video kai da wata kuna aikata Zina!"


"What"ya fad'a da karf'i


 "Wannan ne dalilin da yasa sukace bazan aure ka ba,sanan kuma a yanzu ina son mu rabu,ina son zanyi ma iyayena biyayya,dan Allah Sufyan kayi hak'uri...." Kuka ne yaci karf'in ta ta kasa magana.


Wani irin zafi yake ji a zuciyar shi bai ankara ba kawai sai hawaye bai tab'a zubar ma da mace hawaye ba sai gashi yau yana ma Nadrah hawaye, Cikin rawar murya yace"Yanzu kin daina sona?"


Cikin Kuka tace"Sufyan ina matuk'ar k'aunar ka,ba wai na daina son ka bane domin abinda kake aikata Aa iyayena nake so inyi ma biyayya,kuma ina son kaji tsoron Allah ka daina neman mata,dan Allah daga yau kar ka sake kira,na hak'ura da kai Domin yin masu Daddy biyayya"


Zaiyi magana ta katse wayar,kuka take sosai,ya kira yafi sau goma bata d'aga ba,daga k'arshe ma hannun ta na rawa tayi blocking dinshi tare da deleting number shi,Ta dad'e tana kuka tayi Addu'a sosai Sannan taji wani sanyi a ranta,taje ta wanke fuskar ta tare da nufar Parlour, Hisham na zaune Mommy kuma na tare da Daddy a Parlour,Ta Mik'a mai wayar ta wuce Parlour Daddyn su,yana ganin ta ta d'aure fuska sai taji ba dad'i a hankali ta zauna a gefe Muryar ta na rawa ta fara bashi hak'uri,Yayi mamaki yanda ta sauko haka har ta Amince da auren Baba Kabeer,yaji dad'i sosai,Dama d'azun ya gama waya da Alhaji Kabeer din akan maganar Nadrah din amma abin mamaki sai Alhaji Kabeer yace mai shifa wasa yake,wai dama shi Dagaske ya d'auka toh wlh shi wasa yake ya za'ayi ma ya auri y'ar Abokin shi,Shi kuma Daddy yace wallahi har Cikin Zuciyar shi ya bashi Nadrah ai ba haramun bane,kawai idan ya amince yazo ya ganta suyi magana,sai gashi yanzu tazo tana bashi hakuri,yaji dad'i gaskiya,yasa mata albarka yace taje inshaallah ba za tayi Dana sani ba, Mommy ma taji dad'in yanda y'ar nata taji maganar ta,duk da bata son auren.



Nadrah wannan daren ta kasa bacci sai juyi take rabuwa da massoyi akwai zafi,amma dole tayi ma iyayen ta biyayya matuk'ar tana son taga Haske a rayuwar ta.



Sufyan ma daren ya kasa bacci yayi kuka tamkar mace ya tsine ma wacce ta tura video nan ba iyaka,gashi y'an matan dayawa bai san wace ce tayi mai hakan ba, washegari kawai yaje yayi visa domin barin k'asar zaiyi gaba d'aya yaji ya tsani Nigeria,gaba d'aya zuciyar shi tafasa take gara yayi nesa da Nadrah domin yasan iyayen ta ba zasu tab'a bashi ita ba, sannan ita ma yanzu ta hak'ura dashi Domin yin ma iyayen ta biyayya.



Jamy budurwan Sufyan itace ta had'a mai wannan tarkon dama akwai video su data d'auka wai incase koda wata rana za tayi mai barazana akan wani abu da video za tayi amfani,sai gashi kuma yace su rabu ita kuma tayi bincike ta gano yana soyayya da wata zaiyi aure sai da tasan yanda za tayi ta tura ma Daddy video nan,sai gashi kuwa ta tarwatsa komi.taji dad'in hakan kuma tana ganin maganin irin su Sufyan kenan masu D'aukar mata kamar kayan canzawar su.



Bangaren Alhaji Kabeer kuwa har ga Allah da wasa yayi maganar nan amma kuma yanzu Aminin nashi yace dagaske yake kuma ya bashi Nadrah,dan haka kawai bayan two days ya shirya yaje Kaduna domin haduwa da Nadrah.




Girki su kayi saboda Daddy ya sanar dasu zuwan Alhaji Kabeer din hakan yasa ake shirya mai Dinner anan Parlour Daddyn su Nadrah ta shirya Abincin, Nadrah sam zuciyar ta ba dad'i hak'uri kawai take,gashi data fad'a ma Bestyn ta Yusrah ita ma shawara ta bata mai kyau Akan tayi ma iyayen nata biyayya tare da Kwantar mata da hankali,Haka Nadrah ta shirya cikin doguwar riga na lace dinkin buba yayi mata kyau Purple color tayi dauri amma ko make up ba tayi ba perfumes kawai ta fesa ko powder tak'i shafawa,haka Hisham yace Taje Parlour Daddyn su,ta fita sai turo baki take ita bata ma wani san fuskar shi sosai ba,koda ta shiga kanta a k'asa ta samu guri ta zauna, kallon ta yake tunda ta shigo, Cikin sanyin Murya ta Gaishe shi,ya amsa cikin jin dad'i, Muryar ta mai akwai zak'i kam.


Katse shirun yayi ta hanyar cewa"Nadrah nasan Daddyn ki yayi miki bayanin komi,ina fatan zan samu karbuwa?"


 Shiru tayi tana jin haushin shi a zuciyar ta,Bai damu ba ya k'ara cewa"Ko akwai wanda kike so ne?"

Dam gaban ta ya fad'i tasan idan har tace akwai kashin ta ya bushi gurin Daddy kawai sai tayi shiru,haka dai ya dinga d'an janta da hira duk da magana bata dame shiba,sama sama take amsa mai a haka dai yace ta bashi number ta tace Wayar na gurin Daddy sai yace zai sa ya bata sai su dinga waya,daga k'arshe dai sukayi sallama, Nadrah na koma d'aki taja tsaki wallahi sak bata son shi,amma ya za tayi dole tayi hak'uri.



Washegari sai ga sabuwar waya Hisham ya kawo mata Wai Baba Kabeer ya siya mata harda Sim da komi,har number shi yasa mata,ba ta wani yi murna da wayar ba haka dai koda ya Kira sama sama suka gaisa,tun daga wanan Lokacin Baba Kabeer na Kiran ta suna gaisawa domin ba maganar soyayya,Sai dai shi Baba Kabeer yana son ta sosai Yarinyar ta shiga zuciyar shi,bai tab'a son wata mace ba,sai Nadrah,time to time yakan zo gidan a haka aka sa ranar aure wata biyu.



Nadrah tasha kuka sosai amma tana dannewa bata bari a gane amma Mommy duk tana lura da ita,kuma Mommy ta dage sosai gurin gyara y'ar tata,haka aka fara shirye shiryen biki,Alhaji Kabeer ya gina gida Mai Shegen kyau ta gurin SMS Queters, Baban gida ne na bene akwai parlour mai kyau sai da kitchen dining room sai wani bedroom guda d'aya na bak'i,sai upstairs kuma parlour ne babba da balcony sai wani corridor idan aka shiga kuma two bedroom ne nata da nashi,duk akwai toilets manya a ciki,an zuba dukiya sosai a gidan nan ta baya akwai boy's Queters,gida dai yayi kyau haka aka zuba furnitures masu Shegen kyau da tsada, Nadrah kuwa gaba d'aya hankalin ta yana kan Karatun ta ne bata ta wani bikin,ana Saura two weeks biki aka kawo lefe nan ma Alhaji Kabeer ya zuba dukiya sosai, Event's kuwa Nadrah tace ita bata so, toh Amma da yake shi yana son irin events haka nan aka shirya yin Mother's Day,Dinner da kuma Arebian night, K'anwar Daddy Aunty Bilkisu tun ana saura one week biki tazo gidan,ita ma tana tausaya ma Nadrah auren babban mutum,ko ita da ba zata iya auren babba ba bare kuma Nadrah yarinya,haka dai aka dinga gyara amarya Nan ta fito tayi kyau ranar Tuesday Yusrah tazo da ita aka dinga shirin bikin duk da tana yi tana lalab'a Nadrah dinne, K'awar ta na school wato Khairat ita ma tazo, Khairat matar aure ce yaran ta biyu maza,suna d'an shiri da Nadrah ba tayi wani gayya ba,dan ma Yawanci Yusrah itace ta gayyaci wasu na school dinsu,ita ma kuma Khairat haka itace ta sanar da y'an class dinsu,ranar Thursday akayi Mother's Day, Friday kuma around 8 akayi Arebian nights,Ranar Saturday Nadrah tun safe take kuka karshe ma ta shige toilet ne tak'i fitowa ta shirya sai da Aunty Bilkisu da wata K'anwar Mommy Hajja Itran suka zo suka sata a gaba aka shirya ta,Gashi tayi mugun kyau abin ba'a magana, K'awaye sai D'aukar pic's ake, Nadrah kuwa gaban ta fad'i kawai yake,idan ta tuna wai yau zata auri abokin Baban ta ba Wanda take so ba sai taji hawaye.














#UMMU BASHEER

#MAIMOUNATH O.G