JINNUL KAMIL(A TRUE LIFE STORY OF ALISHA)
4
by @milhaart
Ciza leb'en tayi tana huci cikin tsananin 'bacin Rai Tace "Wai ni yau Hameed yake wa tsawa? Ba laifin kowa bane illa na Alisha , yau sai Naga gatan ki a gidan Nan" mikewa tayi ta shige d'akin tana kananun suratai ita kad'ai.
Bangaren su Alisha kuwa bayan sun gama cin abinci suka zauna suna Kallo, Alisha ta Mike Tace "Granny Wallahi wanka nake son yi gashi Kuma babu kayan da Zan canza inna yi"
"A a akwai kayan Balki(Balki Yar Cousin din Hameed ne) inaga ai kayan ta zai miki tunda Jikin ku kusan d'ayane"
" Eh zeyi duk da ma ta d'an fini cika"
Mikewa granny tayi Alisha Kuma a biye da ita suka shige cikin d'akin Granny, wardrobe d'inta ta nufa ta d'auka Kaya sun Kai kala biyar Tace "Duk nata ne tunda tazo ta manta su anan Kuma ta kasa zuwa ta d'auki tsummakaran ta"
Yar karamar dariya Alisha tayi Tace "Kai Granny ki dubi kayakin Nan fa sabbi ne Amma kike cewa tsummakarai......wani atamfa ta hango tasa hannu ta d'auka Tace "kiga wannan fa sabo ne kamar ma bata saka ba"
Tab'e baki granny tayi Tace "Ku kuka sani Baku da aiki sai d'inke d'inken banza da na wafi Kuna cinye min kud'in Yara"
"kaai Granny ki duba kiga wardrobe d'inki fa acike makali ni Wallahi kayana Basu Kai naki ba Amma Kuma mune muke cinye miki kud'in yarana?"
"mtsww..... Alisha bakya magana Amma idan surutun ki ya tashi manta jiki kike Shiga kiyi wankan bari na koma parlor" tana Kai Nan tayi ficewar ta, girgiza Kai Alisha tayi ta shige ban d'aki.
Ta ɗauki kusan mintuna goma kana ta fito daga wankan,Jin and fara Kiran sallar la'asar tayi saurin komawa ban ɗakin tayi alwala bayan ta gama ta fito,Man Granny da ta gani agaban Mirror ta ɗauka ta shafa kana ta ɗauki powder ta shafa sama sama, Waldrope ta nufa ta zaro hijab ta saka,kana shimfiɗa prayer Matt ta fara sallah,tana idar da sallah ta zauna don yin azkar, ta idar Kenan Granny da Nawal suka shigo,Suma alwalan sukayi,suka tada sallah,Bayan sun idar da sallan ne duk suka koma parlor,zaman su ke da wuya Fa'eez da Hisham suka shigo gidan da sallama. Nan suka cigaba da hirar su hankalin su kwance Amma Banda Alisha ta rasa dalilin da yasa take Jin Fad'uwar gaba,lokaci zuwa lokaci takan hango irin masifar da zata Sha agun mummy idan sun koma gida.
Tun da magrib daddy ya shigo unguwar su Amma ganin an fara Kiran sallah sai ya ratse masallaci Bayan an idar da sallan ne ya shigo gidan, kusan tare Papi, Fa'eez da Hisham suka shigo gidan.
Papi na ganin Murmushi ɗauke a fuskan sa, Yana faɗin "kaga manyan mutane" Hisham da gudu yayi tsalle Jikin sa yana "oyoyo papi"
Fa'eez ma da gudun sa yayi tsalle a Jikin papi har Saida ya kusa faɗiwa Fa'eez ɗin yayi saurin rike shi , Daddy tun Kan ya karaso inda suke cikin ɗaga murya Yana faɗin "Kai!! Kaai!! So kuke ku hallaka min shi?"
Murmushi papi yayi yace "ina mamakin Fa'eez Wallahi shikam baya girma , jibi fa Kato dashi yazo Yana so ya karya Ni"
Fa'eez tamke fuska yayi yace "Nikam dama ai bana gwanin ta" Hannayen sa yasa a aljihun wandon sa ya shige cikin gida, ya tarar babu kowa a parlor, Kallo ya cigaba da yi har suka shigo.
Daddy yace "Kai Fa'eez Kai baka Isa a maka magana Bako sai ka nuna kafi kowa zuciya , ka kiyayi kanka da wannan mugun halin"
Papi ne yayi saurin fad'in "A'a bar shi kaji ai na mijine da zuciya a ka sanshi"
Muryar granny suka tsinkayo tana faɗin "au ma a Haka zai nuna mazantakar tasa? Yaje filin daga Mana ai maza suna Chan a sambisa forest" dariya Papi yayi yace "Baki da dama hajiya"
Tace "to ai gaskiya ne,sannu da dawo wa"
Ya amsa da "Yauwa sannu"
Hannu tasa ta karb'i jakar dake hannun sa ,da niyar kai ɗaki Alisha ta karb'a ta ce "Bari na Sami ladar angona"
Yar ƙaramar dariya papi yayi yace "Ashe harda ke aka Zo"
Ta amsa da "Eh" ta nufi ɗakin tana ajiyewa ta dawo.
Yace "House Full"
Fa'eez yace "sunan wani film" babu wanda ya kulashi hakan ba karamin kara bata masa rai yayi ba.
Nawal na hango daddyn ta da gudu ta nufi inda yake tana "Oyoyo Daddy" rungume juna sukayi Shima daddy dariya yake yi Yana matukar son yaran sa , Amma Haleemah tana kokarin ruguza masa gida da dukkanin farin cikin dake cikin gidan sa.
Granny Tace "Ya Naga duk kun tsatsya? Ku zauna Mana"
Papi yace "No Zama bata kamani ba, wanka nake bukata a yanzu gaskiya, hope an gama girki?"
"Eh an gama gashi Chan ma a dining area"
" Yauwa na kwaso yunwa sosai bari naje na fito" ya haura ɗakin sa, Daddy yace "Gaskiya Hajiya Nima wankan nake bukata"
"Jimin ja'iri ka bari sai ka koma gidan ka sai kayi wankan mana"
"A'a ai anan zamu kwana"
Ɗan zaro Ido tayi Tace " kwana Wai anan gidan? Ai baka Isa ba ita Kuma Haleemah ku barta da waye?"
Sosa ƙeya yayi yana tunanin abinda zaice mata, ƙwatsam tsintar kansa yayi da faɗin "Ai bata gidan tayi tafiya, taje Kano saro kaya, shiyasa zamu zauna a nan har sai ta dawo"
"ban gane tayi tafiya ba? Bayan ɗazu ta Aiko a ɗauki Nawal?"
"Uhmn to dake d'azu tafiyar ta tashi, ta Kirani ina office ta sanar dani"
" Ikon Allah, Amma inace a Dubai take saro kaya yaushe ta Fara a kano Kuma?"
" Ban sani ba Hajiya" Yana Kai Nan yayi saurin barin gun don ya lura so take ta kure shi.
Ɗakin da dama nasa ne tun Kan yayi aure anan yayi samartakan sa, ya nufa ɗakin fes-fes dashi kamar da Mai zama a cikin sa, Murmushi yayi ya tuna rayuwar da yayi anan ya girgiza kai a bayyane yace "Kamar ba'a yi ba" ban ɗaki ya faɗa ya watso Ruwa gaggauce sabida yasan suna Chan suna jiran sa, yana gama wakan yayi alwala ya fito ɗaure da towel a kunkumin sa, a bayyane yace "Tirkashi!!! To wani kaya Zan sa?" don sbi bazai iya maimaita kaya ba musamman ma da yayi wanka.
Wardrobe ɗin ɗakin ya nufa ya buɗe wasu kaya ya gani a ciki a wanke a goge, yana mamakin kayan Nan fa , Yana cikin dubawane ya tuna wani zuwan su da sukayi da Ja'afar gidan da wasu abokan su, ana Shirin bikin wani abokin su sai suka Zo nan sukayi Hira Kuma a lokacin yayi sabbin ɗinki,sai wani jjallabiya baka Mai mugun kyau,ya nemi kayan bai gansu ba Amma shi Sam tunanin sai bai bashi anan ya manta su ba, kawar da tunanin da yake yi ne a kwakwalwar sa ya zura jallabiyar ya fice daga ɗakin ya tarar duk suna zazazzaune suna cin abinci Shima Zama yayi , Alisha ce tayi saurin mikewa ta Shiga zuba Masa abincin, cikin girmawa mawa ta Mika masa Murmushi yayi yace "Daughter ya school? Bamu gaisa ba"
"Alhamdulillah Daddy, ai daddy idan Kuna tare da granny bajin magana kake ba,na gaisheka yafi a irga Amma baka ji ba"
"am sorry kin San ance uwa da ɗa sai Allah,ina son uwata"
Murmushi tayi a zuciyar ta Tace "Uhmn Banda irin tamu uwar" Amma a bayyane cewa tayi "Hakane daddy."
Komawa tayi ta zauna ta cigaba da cin abincin ta , sai Karan cokali kake ji kwas-kwas sunayi suna Hira cike da farin ciki da kwanciyar hankali.
Bayan sun gama mazan suka fita masallaci don yin sallar Isha, Matan Kuma suka haura ɗakin Granny, Bayan sun idar suka dawo parlor suna Kallo suna Hira a haka har su Daddy suka dawo daga masallaci,suka zauna Suma ana kallon dasu.
'Bangaren Mummy kuwa sai kallon time take, haɗe da lekawa ta taga ko zata ga shigowar su gashi yanzu karfe tara saura ,a bayyane Tace "Duk yanda ake ciki suna hanya yanzu Kam" ta cigaba da latsar wayar ta tanayi tana kallon wani series a Zeeworld Mai suna *I Do*,shiru shiru har karfe 10:30,layin Daddy ta fara Kira har sau uku ba'a ɗaga ba,ta bada kusan mintuna goma Amma shiru ba a a ɗaga ba gashi tana shakkan kiran layin granny sabida rashin kunyar da taba yi Mata,duk tsiya dai baza ta Kira ta ba ta faɗawa kanta hakan.
Daddy kuwa suna Chan suna ta Hira Basu ma San lokaci ya tafi har haka ba, granny ce ta kai dubanta ga agogon bangon dake ɗakin tace "La la la" suka juya suna kallon ta Tace "Karfe 11 saura maza maza ku tashi gobe akwai school Zaku makara" ba don sun so ba suka Mike Hisham ɗakin papi yayi, Fa'eez Kuma ɗakin daddy a yayin da Alisha da Nawal suka nufi ɗakin Granny.
Daddy ne ya kashe TV yayiwa iyayen na sa Saida safe,ya shige ɗakin Yana Shiga yaji karar wayar sa, Hisham yace "Daddy tun shigowa ta fa ake ta Kiran ka"
Wayan yasa hannu ya ɗauka ba tare da yace uffan ba,wayar ya Shiga latsa wa ,31 missed calls ya gani zaro Ido yayi yace "Kai 31 missed calls waye haka?" yana Shiga call log yaga sunan *wifey* ne ya bayyana akan fuskar wayar,Yar karamar tsaki yaja zaman da yayi da iyayen sa 'ya'yan sa yasa ya manta da wata mai suna haleema,ji yayi bayi da sauran matsala a duniya, sako ya tura mata kamar Haka.
*"Muna cikin koshin lafiya, baza mu dawo gida ba sai mun huta na sati,and Kar ki damu da inda muke"*
Yana tura sakon ya kashe wayar a take.
Mummy na gani ta Fara hura hanci tana Jin wani mugun haushin Daddy,wayar shi ta fara Kira taji a kashe ,Rai a 'bace Tace "Ashe dai matsoraci ne mtsww" ta kwanta da niyar bacci,baccin yaki ɗaukan ta sai juye juye take tana tsaki,ji tayi ta fara kewar su. (Niko nace me ma akayi tukunna? Ai yanzu wasan ya fara).
Daddy Kuwa baccin sa yasha harda minshari, Haka ma yaran.
*Washe gari*
Bayan sunje sallah asuba sun dawo suka koma bacci, kusan a tare suka fito parlor, daddy sanye yake da Shirin zuwa office, yaran kuma sanye suke cikin uniform, Papi kuwa jallabiyar da ya je massallaci dashine a Jikin sa , Granny Tace "Yallab'ai ya na ganka haka? Aikin fa?"
"Kawai hutu nake bukata, Ina Jin gajiya sosai, Hameed zai kula da komai" yana maganar yana Kallon Hameed ɗin.
Hameed yace "Abba ai sai da nace maka ka bar aikin hakan Nan Ni zan kula da komai Amma kaki"
"ah to idan na zauna a gidan me zanyi? Gara dai na Rika zuwa ina rage lokaci"
Shiru kawai Hameed yayi sabida yasan halin mahaifin nasa ko kwana zasuyi yana ce Masa Kar yaje to sai ya nemi amsar da zai koreshi.
Gaishe gaishe suka hau yi suka dunguma suka nufi dinning domin karyawa,suna gamawa karyawa suka fice motar daddy suka nufa , papi yace "A'a Ni zan Kai ku da kaina, Hameed yi tafiyar ka" yana kallon daddyn, to daddy yace ya shige motar sa ya fice daga gidan, suka nufi motar Granny, hakan kuwa shi ya kaisu school kuma shi zai dawo ya ɗauke su.
Misalin karfe 10 na safe daddy ya Kira mai gadin gidan sa yana tambayar sa ko mummy na gida, yake shaida Masa cewar yanzun Nan ta fita bata Kai mintuna biyar da fita ba okay yace masa haɗe da katse wayar makullin motar sa ya ɗauka ya fice daga office ɗin a hanya suka Haɗu da Ja'afar.
Ja'afar yace "Ahh abokina ina zuwa Kuma? Office ɗinka fa zani"
"Zan ɗan fita ne yanzun Nan Zan dawo"
" Me sirrin ne naga yau kana cikin farin ciki?"
Murmushi yayi kana yace " Zan baka labari idan na dawo"
"Ok sai ka dawo"
Bai ce masa komai ba ya yi tafiyar sa.
Yana fita motar sa ya faɗa yayi hanyar gida, yana Isa gate ɗin yayi horn mai gadi ya wangale Masa gate ɗin ya shige cikin , a tsakiyar gidan ya faka motar ya fita cikin sauri, ɗakin sa ya nufa ya ɗauki duk wani abu da zai bukata, ya shige ɗakin Alisha da sauran yaran yasa musu, Trolley uku ya ɗauka ɗaya nasa, ɗaya na Alisha sai Kuma Fa'eez da Hisham ya haɗa musu nasu a ɗaya,a cikin duk ya ɗauka musu uniform kala uku uku, gidan su ya nufa Amma daga bakin gate ya tsaya ya umurci Mai gadin da ya Shigar da kayan ciki, Yana ajiye Masa ya ja motar sa ya koma office.
_________________________
Milhaat ce✍🏻
Yar Terawa
Please comment and share