JINNUL KAMIL(A TRUE LIFE STORY OF ALISHA)

5

by @milhaart

Bayan ya koma office kai tsaye office ɗin Ja'afar ya nufa,zaune yake yana ɗan rubuce-rubuce da sallam haɗe da tura kofan daddy yayi ya shiga wuri ya samu ya zauna a kujeran da ke kallon na Ja'afar ,wani irin nauyeyyen ajiyar zuciya ya sauke.



Tun shigowar sa Ja'afar ke aikin kallon sa,jin ya sauke ajiyar zuciya ya sauke biron da ke hannun ya ajiye haɗe da jingina bayan sa a jikin kujeran, nisawa yayi kana yace "Ya dai Hameed? Me kuma ya faru?"


Gyara zama daddy yayi kana yace "Mun koma gida da yaran nan"

Cike da rashin fahimta yace "Bangane kun koma gida ba? Wani gidan kuma da wasu yaran?"





      "Gidan mu muka koma kuma na akwai wasu yarane bayan su Alisha?"

A dan zabure yace "gidan ku ko gidan ka?"

Fuzar da iska yayi cike da hasala yace "Wai dan Allah da wani yare kake so na maka magana ne? Nace maka gidan mu,gidan iyaye na" ya karisa maganar yana dirza goshin sa da yatsunsa.






   "Ikon Allah ,to ita kuma Haleema fa?"

"Mun bar mata gidan" yace a takaice.

Riks hab'a Jafar yayi kana yace "yau naga ikon Allah kace min yaji kayi ko ince yaji kukayi....?" daddy ko kallon sa beyi ba bare ya bashi amsa ganin baida niyar amsa mishi yace "Amma me dalilin ka nayin hakan?"

"Dalilina shine inaso ni da yara na mu samu kwanciyar hankali"

"Kana nufin baza ku koma ba kenan?"

"Kamarya baza mu koma ba?zamu koma man,kawai dai sati ɗaya zamuyi zuwa biyu"





"Hmmm Hameed,kana gudun matsalar ka to wa zai gyara maka su? Shawaran da zan baka shine ka zauna ku fahimci juna da matarka shine bayani,kuma how sure are you that baza ta zo gidan ba itama?"





     "Baza ta zo ba sabida kwanaki ma babu yabda banyi da itaba akan taje ta gaida mama taki,in baka manta ba tayi wa Hajiya ta rashin kunya tun daga nan bata sake zuwa gidan ba yanzu kusan shekaru biyu kenan fa"




    Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "Ni wallahi haleema na bani mamaki ta kasance mace ta gari mai alkunya amma tashj ɗaya ta canza tamkar ba ita ba"

"Kaima kenan ni kuma ince me? Wallahi Allah jafar aure zan kara sai dai ta mutu"


Dariya sosai jafar yayi kana ya dai daita kansa yace "Aure dai wai kai ɗin ne zakayi aure?"

"Wallahi da gaske nake maka aure zanyi ko ba yanzu ba" ganin irin dariyar da jafar yake yi yasa shi tashi cikin fushi ya nufi kofar fita, sai da ya kai bakin kofa ya rike handle ɗin kofar ya waigo ya kalli jafar yace "Gara ma ka fara shiri,don wallahi aure kaine gaba a kan auren da zanyi ko ka bani goyon baya ko kayi na dole,in kuma kaki sai nayi" yana kai nan bai tsaya jiran abinda zaice b aya sa kai ya fita ya rufe da ɗan karfi har saida jafar ya ɗan razana baki a buɗe yake kallon kofar kamar jafar ɗinne a gun, ya daɗe yana kallon kofar kana ya girgiza kai haɗe da fuzar da iska tace "Lallai hameed Allah ya kyauta" ya gyara zama ya cigaba da duba aikin da yake gaban sa.





Daddy na shiga office ɗinsa ya jaa dogon tsaki haɗe da jan kujera ya zauna ,ya shiga dirza goshin sa a hankali ,ya lula duniyar tunani idanun sa a rufe kamar mai bacci ya ɗauki kusan mintuna goma a haka kana ya numfasa ya ware idanun sa ganin yana 'batawa kan sa lokaci ga aiyukan nan birjik a gaban sa ya yi tsaki ya dukufa ya fara duba files ɗinda ke jere a kan tebur ɗinsa.





    Alisha bayan sun tashi daga school Granpa da kanshi ya kuma dawowa ga ɗauke su,basu wuce gida ba kai tsaye,wani shopping mall ya kai su zo kuga murna a gunsu, a baya suna fita da mummy da daddy amma yanzu sai dai asa driver ya sayo musu abubuwan da suke so.hatta fa'eez uban tsiwa sai da fuskar sa ya nuna tsananin farin cikin da yake ciki, Granpa yace su ɗauki duk abinda suke so haka kuwa akayi ,bayan sun gama ɗaukan abinda suke suke so suka wuce gun biya ya biya suka kama hanyar gida.






      Suna shiga gida Granny na ganin su ta fara oyoyo oyoyo kamar ta daɗe bata gansu ba,sabida tayi kewar su ita kaɗaice a gidan tun ɗazu da daddh ya fita sai yan aikin ta,ganin sun tayi da kaya niki niki ta rike hab'a tace "Iye wato shine kuka je shopping banda ni,shiyasa mana naga kun daɗe to ni me aka sayo min?" Granpa da Alisha a tare suka ce "Na ɗauko miki........" kallon junan su sukayi kana suka shiga dariya,girgiza kai granny tayi tace "Maza a je a cire uniform azo a ci abinci ko?" da to suka amsa duk suka watse.






   Alisha wanka ta fara yi tayi sallah,sabida yau bata samu damar yi a school ba,bayan ta idar da sallah ta ɗauki doguwar rigar atamfa ta sanya a jikinta an mata fited gown kalan Maroon da ratsi ratsin fari yayi matukar ɗaukan jikinta, ta kama yakwataccen gashin kanta da ribbon ta ɗauki ɗankwalin kayan ta yane akanta ta fitbadaga ɗakin.






   Tun daga nesa take jin karan cokula ,tsayawa tayi tana kallon su ta turo dan mitsitsin bakin ta tace "Shine kuka fara cin abincin bani?" Ta karasa maganar cikin shagwaba.




Granny tace "Da man zaman jiran ki kike so muyi ko? kinje kin zauna abinki a ɗaki"

"Toh ba sallah nayi bane" 

Fa'eez yace "Kin daiyi wanka,granny Kema kin santa da wanka ai kamar a gwagwa"

Hararan wasa tamasa ya fashe da dariya haɗe da faɗin "Nayi shiru" 

Nawal kam sai aikin cikinsu kawai suke.





Granpa yace "Amaryata kyau kenan? Ina fatan dai wannan kwalliyar ni akayiwa ko?" ya karasa maganar cike da zolaya

Tabe baki tayi ita ala dole sai an bata hakuri,grannpa da ya fahimci inda ta dosa yace "Zonan Amaryata kiyi hakuri kinji? Zo ki zauna a kusa dani ni da kaina zanyi feeding ɗinki" murmushi tayi harda ƴar tsallane ta ,ta zago ta zauna a kusa dashi,nan ya shiga feeding ita kuma tana karba kamar wata karamar yarinya.





  Granny tace "Yau naga ikon Allah,yarinya wuyan ki yayi kauri,ki shigo min har cikin gidana kiyi kokari kwace min miji?"

Alisha sau da ta tsiyayi ruwa a glass cup kana ta kwankwaɗe tas tayi ajiyar zuciya ta kalle ta tace "gidan ki ko gidana?na kwace miki miji kika ce? Taya za'ayi na kwace abinda dama nawane? Da ma kawai aron shi na baki"





Granny da tunda ta fara magana yake danne dariyar sa sabida yanda alisha ke magaana tana yauki haɗe da kashe murya yace "Yauwa Gaya mata daai" girgiza kai granny tayi zatayi magana fa'eez yace "Granny me na tada hankalin ki? Bayan gani nan,saurayi mai sabon jini me zakiyi da wani tsoho kawai kyale su"




Dariya sukayi granny tace "Hakane mijina,nayi shiru" nan suka cigaba da cin abincin su ciki farin ciki da kwanciyar hankali.





*BAYAN KWANA BIYU*

Mummy na hango a zaune da wata mata,mummy kafarta ta ɗaura ɗ'aya akan ɗaga tana lasar waya haɗe da cin chewn gum,karewa shagon kallo na shiga yi har saida yawun bakina ya bushe nace Ahhh lallai mummy ta yi yadda ta ga dama irin wuri haka kamar ba a nigeria ba? A nigerian ma cikin garin gombe? Komai na shagon abun kallo ne kayane jibge kala da iri babu abinda babu in dai na suturane ,kama daga kan Atamfofi,laces,abaya's,materials,jakakkuna da takalmi masu ubansun kyau masu tsada.





  Mutane sai shiga da fita suke amma Mata sun fi yawa,duk wacce ka gani a gun fa to takaine sabida wurin na masu hannu da shuni ne, komai na shagon a tsare yake masu karban kuɗi a gefe guda haka masu rakiyar idan mutum ya shigo daban sannan masu fita da kaya su kai mota ma daban,idan na tsaya kwatan ta muku haɗuwar shagon mummy sai mu daɗe bamu gama ba,ku kiyasta ku hango kyau iya kyau haɗuwa iya haɗuwa ku hango mana shi.





   Mikewa Mummy tayi ta kalli matar dake zaune a gefen ta mikewa tayi tace "Qawata zo mu shiga daga ciki muyi magana a chan nan gun bazaiyu ba" tayi gama ,matar nan da ta kira da kawarta ba tace komai ba ta rufa mata baya. Ina ganin hakan nayi sauri na bi bayan su, wani kofa naga sun nufa daga gefe mummy ta buɗe ta shiga da Alama office ɗinta kenan ,itama qawarta ta shige,nima nayi saurin bin su na kusa kaina a ciki.






  Masha Allah shine abinda na iya furtawa kenan ,ban an kara ba biro na ya faɗi sabida na shagala wurin kallon kyawu da tsaruwar gun kiris ya rage takardata ta faɗi nayi saurin riko wa.komai na office ɗin baki da fari ne kama daga kan Kujerun,curtins da pentin duk mix akayi da baki da fari,daga chan gefe na hango wasu hutuna a manne a jikin bango ya ja hankali na ,nayi gun da sauri don bawa idanuna abinci, cike da mamaki nake kallon hotunan ,family picture ɗin family Abdul-hameed sunyi matukar kyau ga murmushi a fuskar su kamar ba su ba,ɗayan hoton kuma Mummy ne da Daddy suna dariya aka ɗauki hoton, ɗayan kuma Alishane da kannen ta ,sannan sauran ko wanne su ne shi kaɗai, ina cikin kallon hoton ne na tsinkayo muryar matar nan tace "Haleema kinyi shiru? Kefa kika ce nazo muyi magana kuma kin tsaya kina kallo na"

Ajiye wayar mummy tayi haɗe da gyara zama tace "Aisha,ina cikin tashin hankali,damuwa da rashin sanin madafa kaina ya kulle na rasa me zanyi na ji daɗi"

"Toooh me kuma ga faru na kasa fahimtar ki? Kimin magana dallah dallah yanda zan fahimta,ko dai haryanzu maganar hajiyar Hameed ne don nasan kusan itace kaɗai take baki matsala?"





"Mtswww wa yake ta wata hajiyar sa wannan karon Hameed ɗin ne da kansa ,hameed ha canza totally wallahi kamar an canza min shi"

"Me ya miki?" ta faɗa haɗe da gyara zama.






"Yau kwanaki ɗaya ɗaya har biyar kenan ban sanyi shi a ido na ,hatta yaran ma ya rabani da su"

Waro ido tayi tace "Meeeee? Sakin ki yayi?"

"Mtsww matsalata dake kanki baya kawo haske wallahi,saki kuma? Kawai dai ya koma gidan sune sabida fitina ta a faɗin bakin sa"







   dariya Aisha ta shiga yi harda rike ciki,yarfa hannu ta shiga yi tana faɗin "Inna lilllahi kice min yaji yayi, ah lallai kin tabo hameed mutum me hakuri haka?"




  "Dallah malama shawara zaki bani me abunyi na rasa yanda zanyi kin sani ina son mijina da ƴaƴana ya zanyi?"

  



"Ai kawai ki share su kawai dole zasu dawo"

"Anya kuwa nifa tun abin baya damina yanzu har bacci ma kasawa nake sai dai ya sace ni"


"To me kike ganin yadace kiyi in ba hakan ba? Sai ga raina ki na gaya miki ba a yiwa na miji haka,ki share shi kawai zai dawo don kansa"

Numfasawa mummy tayi kana tace "Nagode kawata shiyasa kika fiye min ko wacce qawa ba kamar Rabi ba, sai tayi tamin wa'azi ko yaushe ta zama malama oho"

Dariya kawai tayi amma a zuciyar ta tace "Hmm baza ki gane mai son ki ba sai ranar da na cika ƙudirin a kanki amma kamin nan lokaci ya kure miki"




Maganar mummy ne ya kaseta daga duniyar tunanin da ta lula, tace "Bari na kawo miki abinsha,sai yanzu hankalina yadawo jikina" ta nufi yar madaidaicin fridge ɗin dake gun ta ɗauko mata Maltina da ruwan faro ta dire mata a gaban ta ,ta koma ta ɗauko glass cup fa ijiye mata,Aisha kallon mummy take mai ɗauke da ma'anoni wanda ita kaɗai tasan dalilin yin hakan,nan suka cigaba da hirar su.



(Tooh fa Readers yanzu aka fara labari me kuke ganin Aisha take shirin aikatawa mummy? Ku kasance dani domin samun amsar tambayar nan,kar ku manta littafin na kuɗi naira 300 kachal,zaku iya turo kati kuma,sannan akwia garabasa idan kika biya 500 zaki samu labari biyu a cikin Taurari bakwai, domin karin bayani , a min magana ta wannan number ***.)

Zaku ga errors ban samu damar editing bane amin afuwa.

________________________

Milhaat ce 

Yar Terawa 

Please comment and share.