IDAN BA KE

Page 15

by @nimcyluv

Saif ya ce "Aure kuma? waya ɗaura, dawa kuma?" Sheikh gyara tsaiwa ya yi zufa na yanko masa ta cikin naman jikinsa,kalmar auren ta gigita masa tunani dama lissafi baki ɗaya. Labo ya kalli Saif-wazir ya ce "Aradu aure aka ɗaura musu, babu wanda ya isa ya warware shi sai ikon Rabbi.. kai Giɗaɗo maza jawo mana su cikin Rugar Bello" cikin gargaɗi Saif-wazir ya nuna Labo da hannu ya ce "Saurara fillo kake kowa, an faɗa maka aure wasan yara ne? Kuma wanda kake cewa zaka aura masa ita already yana da aure wajan matar shi ma zamu, don haka babu wani aure idan ma kunyi sai ku warware auren yanzu nan" Labo ya ɗaga sanda sama gaba ɗaya sauran Fulanin suka ɗaga sanda sama tare da zagaye su Sheikh "ƙarya kake Aradu ina shemeka na sheme banza Alqur'anin Allah, aure kuma dole ne hukuncin duk wanda ya yi fyaɗe ko ya nemi lalata ƴar mutane ke nan, ku shige muje Rugar Bello" Saif-wazir zai magana Sheikh yaja numfashi da ƙyar yana girgiza masa kai domin sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi musamman da yake ɓangaren Fulanin suka shigo tsaf za su yi musu gayya. And he doesn't want that to happen. "But Sheikh....," Sheikh ya ware idanu wanda suke ɗaukan hankali kamar ba zai ce wani abu ba sai kuma ya yi ƙasa da murya kamar wanda aka ɗauke wa In-inar ya ce. "Saif-wazir" kallon Sheikh kawai Saif-wazir yake cikin mamaki.

Suna ƙoƙarin tsallake ta su shige Labo ya yi saurin faɗin "Waye zai ɗaukar maka matar ka? yadda ka kawo ta nan haka zaka ɗauke ta mu ƙara sa Rugar Bello" a fili Saif-wazir ya ce "Tab..." Domin yasan that's the first thing da Sheikh can't do it ba zai taɓa ɗaukan ta ba. A hankali Saif-wazir ya sunkuya zuwa inda take kwance zuciyarsa ta buga da ƙarfi lokacin da idanun shi ya sauka akanta. A ruɗe ya juya ya kalli Sheikh Aliyu haydar Aliyu wanda ya tattare Alkyabbar jikinsa idanun shi rufe lokaci guda jijiyoyin kansa suka fito hakan kuma tabbaci ne na zuciyar shi na kusa, tashin hankalin da Saif-wazir ya shiga lokacin da idanun shi ya sauka akan fuskar Halisa Danejo Rome yafi ƙarfin tashin hankalin da Sheikh Aliyu haydar Aliyu yaji akan batun auren nashi da suke ƙoƙarin ƙaƙaba mishi. Saif-wazir ya daidaita nutsuwarsa wani kuzari na zuwar masa mmkin abin da idanun shi ke nuna masa ya cika masa zuciya. Ɗaukan ta ya yi daidai lokacin da Sheikh ya runtse idanunsa yana juya baya da ɗan sauri bakinsa ɗauke da sunan Allah. Saif-wazir na gaba ɗauke da Danejo Sheikh Aliyu haydar Aliyu na binsa cikin nutsuwa da daddako haɗi da kamala yanayin yadda ya kame kansa yake tafiya zaka ɗauka sarki ko Hakimi ne. Gaba ɗaya ƴan Fulanin suka mara musu baya har zuwa Rugar Bello lokacin tuni saƙo ya isa wajan Arɗo gaba ɗaya sun fito tare da yin shimfiɗa a gaban wata bukka wacce ta cika da yalwar inuwa, tun daga nesa Arɗo ke kallon Sheikh Aliyu har cikin ransa bai na'am cewa zai aikata abin da Giɗaɗo ya faɗa ba, amma ya kasa fahimtar mene ya sanya yaji auren shi ne mafita a gare shi dama su baki ɗaya?. Saif-wazir na zuwa ya kwantar da Danejo wacce har lokacin bata farka daga suman da take ba, jini kuma bai daina zuba daga goshinta ba. Arɗo ya kalli Sheikh cikin mutumtaka ya ce "Ka zauna mana?" Ko inda yake Sheikh bai kalla ba balle ya ama shi, sai ma tsaiwa daya gyara yana ɗan duba time fuskar shi tai jajir. Arɗo ya jinjina kai yana ƙara samun ƙarfin gwiwar abin da zuciyar shi ke ayyana mishi. Cikin nutsuwa ya ce "Sannunku, an kawo ƙarar an kama wancan yana ƙoƙarin aikata abin da Rugar Bello ta hana, wasu sunce ya aikata ga yarinyar nan kwance, bisa doka duk wanda ya yi hakan muna ɗaura masa aure da ɗiyar wannan ya sanya zamu aura masa yarinyar nan a yanzu ba tare da ɓata lokaci ba" Sheikh dai jin abin yake kamar ta tsuniyar yara ko damuwa bai ba, auren Zahrah ba bai taɓa damunsa ba balle na wannan ƴar tayin yarinyar. Saif-wazir ya ce "Amma wannan kuskure ne, idan mutum baya so ba, kuma ai ba haka ake ɗaukan doka ba, shigowarmu garin kenan fa suka fara ihun ya yi me ne kamar wasu marasa ilimi?" Giɗaɗo ya ɗaga sanda zai makawa Saif-wazir Arɗo ya yi saurin cewa "A'a Giɗaɗo, ko ma dai yaya ne kuyi haƙuri aure babu fashi" Modibbo da tun ɗazo bai magana ba ya ce "Sai a karɓi sadaki wajansa ai babu lokaci" Labo ya ce "Ga wannan a wajansa muka amsa" ya miƙawa Modibbo zoben gold ɗin da suka amsa wajan Sheikh. Sai a lokacin Saif-wazir ya ƙara cewa "Ga kuɗi a bada zoben, yana da tsada sosai kuma yana da muhimmanci ga mai shi" Modibbo ya yi murmushin jin daɗi ya ce "Daman abu mai daraja muke buƙata ai" abu kamar wasa akan idanun Saif-wazir da kunan Sheikh aka ɗaurawa Sheikh Aliyu haydar Aliyu aure da Halisa Danejo Rome akan sadakin zoben gold. Modibbo ya zama waliyin Danejo Arɗo ya zama waliyin Sheikh. Mutane kusan ashirin suka shaida daga ciki harda Saif-wazir.


Shiru wajan ya ɗauka Saif-wazir ya rasa ta ya ya zai kalli idanun Sheikh ya ce da gaske Danejo matarsa ce? Zai amince da auren ne ko ya ya? Kamar gilmawar walƙiya haka Sheikh ya juya yana gyara Alkyabbar jikinsa kai tsaye baki n titi kuma ya nufa,ganin haka ya sanya Saif-wazir miƙewa da sauri Arɗo ya ce "Ina zaka baka ɗauki yarinyar ba?" Saif ya juya ya kalleta rauni ya bayyana a fuskar shi har baya son kallon yarinyar gani yake kamar idanunsa ke masa gizau da abin da yake gani ɗin. Da sauri ya ɗauke ta ya marawa Sheikh baya yana zuwa titi ya samu Sheikh zaune acikin mota ya dafe kansa da hannu bibbiyu hayaniyar duk ta sauya masa lissafi baki ɗaya, Saif na shirin saka Danejo cikin motar Sheikh ya ce "N...n.. No!!!!" Ya faɗa cikin tsawa da faɗa idanunsa na fitowa waje sosai da kyau, a tsorace ya ce "Jini na zuba a jikinta kada ta samu ƙarewar jini kuma ba zamu je da ita gida haka ba sai mun fara zuwa asibiti" kallon da Sheikh ya yi masa ya sanya Saif yin shiru yana ƙasa da ƙansa. "Please Yaa Lee Matarka...." Kafin Saif ya ƙarasa Sheikh ya yi wa motar key cikin wani irin azababban gudu ya juya kan motar tare da cillata titi ya nufi hanyar da zata mayar da shi Kano ba tare daya ƙarawa wajan Zahrah ba..

Baki Saif ya saka cike da mmkin zafin zuciya irin ta Sheikh Aliyu da alama za a sha fama kafin Sheikh ɗin ya amince da batun auren Danejo ɗin. Mota ya tsayar ya ce masa asibiti mafi kusa don Allah. Kai tsaye aka kai shi Specialist Yola dake Jimeta. Yana shiga reception yaci karo da wata cikin sauri ya ce "Oh sorry it was a mistake.." Tsaki ta ja ta ce "mistake ko rashin hankali Malam? Kana tafiya kai a sama" kallonta kawai ya yi shi bashi da lokacin ta ma, Saurayina ta ce "Banza kawai" Zahrah da hankalinta ya yi gida sbd zuwan wanda yake shirin zama mijinta ta ce "Wai Surayyerh har lokacin cacar baki gareki ne? Tunda muka zo asibitin nan ki ke neman faɗa" Surayyerh ta ɗaga hannu ta ce "Saurara Zahrah ke tunda kika samu cikin nan kike ji da masifa, daidai nake da ko wanne ɗan iska Wallahi" Saif-wazir ya kalli Zahrah da kyau kaya ne wanda suka kama jikinta sosai hannunta duk farce taci gashin doki, juyawa ya yi ya kalli Surayyerh ba tare ce komai ba ya juya zuwa cikin emergency. Kai tsaye aka bawa Danejo gado Dr ya kalli Saif-wazir ya ce "Suna?" Saif ya shafa kansa sbd sam bai sani ba sai kawai ya wayance da faɗin "Dr ka fara yi mata taimakon gaggawa, sai mu yi magana" Dr ya ce "Dole a buɗe mata file ai" "I knw, amma kulawa da ita ba zai hana buɗe file ba, a duba ta first buɗe file second" Dr ya miƙe tsaye tare da nufar ɗakin da suka kwantar da Danejo abun mamaki ba ita ba alamarta, cikin hanzari ya fito sukaci karo da Saif-wazir ya ce "Yarinyar nan ta gudu bata cikin room ɗin?" Saif ya ce "What?" Da sauri ya juya zuwa waje amma neman duniya babu Halisa Danejo Rome babu ko inuwarta "Innalillahi yau na shiga uku ko dai aljana ce yarinyar nan? Amma babban asibitin irin wannan ina zata?" Ganin bashi da wata mafita ya nemi abin hawa wanda zai dawo da shi Kano domin ba zai iya komawa Rugar Bello ba yace bai ga yarinyar ba, haka kurum su kashe sa a banza.


Ɓangaren Halisa ana kwantar da ita a saman gado A.c ta fara ratsa ta, ta farka da sauri tana dabe kanta, tsoro ya kamata tana mamakin yaushe tazo. Ita dai ta fito tallan Kindirmo ta ce bari ta biya ta Rugar Bello a hanya yunwa da jiri suka yarda ita, kanta ya daki wani dutse bata ƙara sanin inda take ba. Miƙewa tsaye tayi jikinta na rawa ta ce "Hande en boni gidan cire kai aka kawo ni wayyo Allah Dadata na lalashe, lalashewa ta sameni" kuka take sosai har da majina fuskarta tai jaa. Leƙewa tayi ta window taga ashe bayan asibitin ne, da sauri ta kama tagar ta dira baya duk da zafin da kanta ke mata amma haka ta dinga gudu kamar barewa a haka ta isa Rugar Rome. Shiri sosai Zahrah tayi ta tarbar Sheikh amma har dare babu labarinsa baƙin cikin duniya duk ya kamata ga ƙawayenta duk ta tara zata nuna musu haɗaɗɗan mijin da zata aura amma ya kwafsa mata.


Misalin 10:23 Abba Hakimi na zaune a Main parlour dashi da Momi kamar daga sama su kaga Sheikh ya shigo hannunsa guda ɗaya dafe da kansa, Momi zatai magana Abba Hakimi ya Girgiza mata kai alamar tai shiru,babu wanda ya kula ya shige part ɗinsa dake gidan, kai tsaye bathroom ya nufa bayan ya zame kayan jikinsa abin da bai taɓa yi ba shi ne, amfani da ruwan sanyi ya tsaya a shower na sauka akansa sanyi na ratsa masa tsakiyar kansa, sai numfashi yake fitarwa dan kansa ya kashe shower ɗin ya naɗe jikinsa a cikin wata bathroom mai ɗan kauri, idanunsa na rufewa sbd azababban ciwon kai a haka ya kwanta saman gado ya daɗe kafin barci ya ɗauke sa.


"Lafiyar Sheikh ɗaya kuwa?" Abba Hakimi ya ce "Kinga alamar bai da lafiya ne?" Momi ta ce "A'a, kawai yadda na shigo gidan ne" Apple ɗin hannunta da take miƙa masa ya amsa ya ce "Kada ki damu, duk sanda ya yi haka alheri ne ke bibiyarsa" tattaunawa sukai akan gobe za a kai kayan lefen na Sheikh ita ma zata a hankali ya ce "Allah ya kaimu" sai kusan 12 na dare Sannan Saif-wazir ya shigo ganin dare ya yi kai tsaye ya nufi part ɗinsa, motar Sheikh da ya gani ya bashi tabbacin ya dawo gida. Da batun Auren Sheikh ya kwana yana tunanin ya faɗawa Abba Hakimi ko ya yi shiru? Har barci ya ɗauke shi ba samu mafita ba.


Washegari da yamma wajan 5. Dr A'isha ta zabga tagumi Yaya Halima ta ce "Dr wai lafiya tun da muka dawo kike wata kala?" Dr A'isha ta ce "Wallahi Yaya tausayin Sheikh nake, ina zai kai wannan uwar matar? Na girgiza ban san rashin tarbiyyar ta ya kai haka ba, kalli da ita aka amshi kayan lefen fa?" Yaya Halima ta kalli Dr A'isha tana mmkin rashin control na bakinta da bata iya riƙe zance. "Kowa da tsarinsa fa Dr Allah dai ya sanya albarka" daga bakin ƙofa akace "Ba Amin ba, mugun ji da mugun gani ruɓaɓɓan baki ya kau daga kan Gadanga, yau ko ni ko uban Gadanga ya zaɓa" gaba ɗaya suka kalli bakin ƙofa, tana tsaye taci lace ɗauri har gaban goshi ta lafta uban Glasses a fuska wanda ya cinye rabin fuska. Cikin farin ciki Mother ta miƙe tsaye tana faɗin "Jadda" haɗe fuska tayi ta nemi waje ta zauna, Uncle Haroon ya shigo hannunsa riƙe da torelly ɗin Jadda ya zauna kusa da ita. Cikin farin ciki Mother ta ƙara cewa "Sannu da hanya Jadda ashe kina tafe" Jadda ta ɗauke kai sai da Mother tabar wajan, ta juya ta kalli Uncle Haroon murya can ƙasa ta ce. "Munafuka Algunguma duk masifa da yaƙin da ake a gidan fa bata sanar dani ba, shi ya sa na haɗe mata fuska na kame kai na, ba kaga jikinta ya yi sanyi ba, ai wlh yau sai sun bala'i ya sauka" murmushi kawai Uncle Haroon ya yi ta haɗe rai tana ƙanƙantar da idanu ta ce "Kaji masifa ko? Ba murmushi za kai ba cewa zakai nayi daidai" ya ƙara murmushi ya ce "Jadda duk abin da ki kai ai daidai ne" cikin ƙaramin lokaci Mother ta cika gaban Jadda da kaya kala-kala, Yaya Halima da Dr A'isha suka gaidata ta amsa a ciki. "Kinga ba kwaɗayi ya kawo ni ba, maza kira mini mijin naki" Mother ta haura sama yana zaune yana duba Invitation ɗin bikin Sheikh dana Zahrah Mother ta shiga a hankali ya ce "Barrister ya dai?" Kai tsaye ta ce "Jadda na kira" tana faɗin hakan ta juya, yabi bayanta da kallo da sauri kuma ya miƙe shima. A hankali yake sakkowa daga benen yana sakin fuska bayan ya zauna ya ce "Sannu da zuwa Jadda" banza Jadda tayi masa, ta zare Glasses ɗin idanunta ta miƙawa Uncle Haroon, ta cire mayafi shima ta miƙawa Uncle Haroon, fuskar Father cike da tsoro ya ce "Jadda lafiya me kike shirin yi haka?" Bata kula shi ba, ta buɗe rigarta tana nunawa father ta ce "mene wannan?" Kansa a ƙasa ya kasa cewa komai ta ce "Idan ba zaka iya ba, ai Ubangiji ya tsaga mini bakin magana nonon dana shayar da kai ne, kasan Allah tun nonon yana kwance ka lalata batun auren Gadanga da wannan gantalalliyar yarinyar, idan ba haka ba zan ɗaga maka nonon sama ka lalace kaje duk inda zaka...