JINNUL KAMIL(A TRUE LIFE STORY OF ALISHA)
6
by @milhaart
Hiran su suke hankali kwance,chan naji Mummy tace "Yauwa Rabi fa tace min zata zo amma haryanzu shiru"
Ta'be baki Aisha Tayi kana tace "Kin santa ai sarauniyar jiji da kai,ta nuna ta fi kowa sanin komai"
Gigiza kai mummy tayi tace "wallahi ina mamaki yanda akayi baki son Rabi kwata kwata tunfa muna school fa ko dai ta kwace miki saurayine ban sani ba?" ta karasa maganar cikin tsigar zolaya.
"Eh mana ,kin manta ne nifa nace ina son jafar amma yarinyar nan taje suna soyayya abun har ya kai ga ta aure shi,gashi har yau Allah bai basu haihuwa ba" ni ko nace wato Rabi da ake magana akai tun ɗ'azu matar jafar ce? Abokin daddy muje zuwa.
Mummy Tace "Matar mutum kabarinsa fa akace miki,inda mijinkine wallahi da sai ya aure ki kuma haihuwar da kike magana akai ɗin ai Allah ke bayarwa ba mutum ba,ba a yiwa mutum gorin aure da haihuwa sabaida kamar yarda baki san ranar mutuwar ki ba haka suke"
"Idan na fahimce ki so kike ki gaya min magana sabida kunyi aure ni banyi aure ba?"
Kama baki mummy tayi haɗe da faɗin "Niii rufa min asiri yaushe nace miki haka? And by the way rashin auren ki kece kika jawa kanki kintsaga rawar ido,ke sai me kaza sai me kaza ga irin ta nan ai"
Cike da takaici Aisha tace "Hmm yanzu fa kika gama faɗin cewar lokacine ba a yiwa mutum gori amma kuma kike min?"
"Ni ba gori na miki ba gaskiya ce kawai bakyaso,ohh ashe ba daɗi"
"Ba laifin ki bane laifi nane da na ɗauki ƙafata na zo inda kike" tana kai nan ta mike ta ɗauki jakar ta,miƙewa mummy tayi ta sauri ta rike ta "Haba qawata me yayi zafi kiyi hakuri dan Allah ni wallahi ba da wata manufa na faɗi hakan ba,yi hakuri ki zauna dan Allah"
Ba ta ce mata komai ba ta ajiye jakar ta zauna,Wani irin kallo take yiwa mummy wanda ita mummy hankalin ta na kan wayar ta, ciza leben ta Aisha tayi tace "Zanyi maganin kine"
Sun ɗauki tsawon lokaci ko wacce na latsa wayar ta,babu abinda kake ji a ɗakin sai karan saukan AC da chewn da Mummy ke taunawa,turo kofar da akayine ya sa mummg ɗago kanta yayin da Aisha kuma ta ɗan waiga kasantuwar ta bawa mashigar office ɗin baya,Ganin Wacce ta shigo duk suka sakewa juna murmushi.
Aisha ce tayi saurin faɗin "Oyoyo friend" cike da mamaki baki a buɗe mummy ke kallon ta a ranta tace "Kamar ba itace take zagin ta yanzu ba ,Aisha halin ta sai ita" ganin kallon da take mata yayi yawane ta harereta haɗi da faɗin "Wannan kallon fa?"
Girgiza kai tayi tace "Allah ya kyauta" nan suka shiga gaishe gaishe, Rabi tace "Hope lafiya ko amina kike neme ni?"
Kan mummy ta bata amsa charab aisha tace "Ina fa lafiya Hameed yayu yaji"
Cike da rashin fahimta tace "Bangane yayi yaji ba?"
"To ya bar mata gidan ko ince sun bar mata gidan........"
Nan dai ta zayyana mata abinda mummy ta faɗa mata,Rabi tace "kinga abinda nake gaya miki ko Haleema? Ki guji fushin me hakuri yanzu hakan ya gaji da abubuwan da kike masa ne ya bar miki gidan, na tabbata yanzu hankalin ki ba a kwance yake ba ,shi kansa nasan babu yanda zayyi ne sabida mijin ki na kaunar ki yana son ki kawia dai halayyar da kika canza ne baya so,amma kiyi wa kanki faɗa before ia too late,ki bishi ki bashi hakuri sannan na daɗe ina bin ki akan kije ki bawa hajiyar sa hakuri tunda dukkan mu mub san laifin kine ,yanzu da ace baki mata rashin kunya ba ai da kin bisu gidan kema kinga daganan dole ya sauko"
Mummy tace "Nifa na gaya miki tun ba yau ba wallahi bazan bawa kowa hakuri ba wallahi,kar ta hakuran mana ita ta sani,kima br maganar bana so"
Aisha tace "Ai Mrs Jafar haka take, sai dai tayi tawa mutum wa'azi kamar wata malamar islamiya"
Girgiza kai tayi in da sabo da saba da irin maganganun su ba halin tayi magana sai suce mata tana musu wa'azi ,idan taci sa'a su fahimce ta wataran kuma suyi chaaa akanta sai tayi shiru ta kyale su ta zuba musu na mujiya.
Mummy ta shiga tunani shin shawarar wa zaya ɗauka acikin shawarin kawayen nata? Zuciyar ta ta amince mata da Maganar Rabi amma kuma Aisha gaskiya ta faɗa hameed zai raina ta,a haka ta yanke shawarar baza ta sake neman shi ba har sai ya gaji don kansa ya neme ta.
Daddy,Granpa da Granny da sauran yaran ne a zaune a parlor suna kallo,Granny ce ta gyara murya tace
"Alhaji nifa na kasa gane abinda yaron nan yake nufi, kusan sati biyu suke gidan nan idan na masa magana sai ya lauyance ko ya nemi hanyar da bar wajen,in akwai wata matsala ne tsakanin shi da matar sa ai sai yayi magana ko a san matakin da za'a ɗauka amma yana miji yayi yaji ai mata aka sani da hakan nan ma yanzu an waye ba kamar da ba"
Grandpa kallon su Alisha yayi yace "Ku koma ɗaki na kuyi kallon ku a chan" sum sum suka mike suka haura ɗakin sa kana Yace "Hameed wai hakane? Yaji kayi ka bar mata gidan?"
Kai a kasa daddy ya fara inda inda sabida bai sna me zaice ba ,duk sanda Granny ta ɗauko Maganar sai yasan yanda yayi ya kawar dashi yau kam baisan me zaice ba.
Granny tace "Ai gashi nasan dama akwai wata matsala tunda gashi ya kasa magana"
Granpa yace "Ya isa haka hajiya bari muji ta bakin sa......" ya maida kallon sa ga hameed yace "Ina sauraron ka me ke faruwa?"
Shiru ya kasa ɗago kansa bare ya bashi amsa zancen zuci kawai yake "A gaskiya bazan iya jurewa inji ana kushe min mata ba,idan na sanar dasu abubuwan da take yi zasu daina ganin kimar ta"
Granny yace "Shirun ka na nufin baka da gaskiya kenan to gobe goben nan ka tattara yaran ka ku bar min gida" yana kai nan ya mike ya haura ɗakin suna kallo da yaran.
Granny tace "Ka dai ji abinda mahaifin ka yace,ni kuma ka saurareni da kyau hameed na sani haleemah na baka matsala nasan kana hakuri da ita ka kara hakuri akan wanda kaje sannan zaka barmin Nawal anan tana ɗebe min kewa."
Kai a ƙasa ya amsa da "toh hajiya" mikewa tayi ta shige ɗakin ta,suka barshi shi kaɗai sai karan TV kake ji bai so haka va yaso ya hora ta sosai ta gane muhimmancin su a gidan,kashe kayan kallon yayi ya koma ɗakin sa shima.
*WASHE GARI*
Daddy ne ya ajiye su school kana ya wuce gun aikinsa bayan an tashi kuma Grandpa ne ya ɗauko su, Sai da akayi sallar isha Daddy ya shigo kasantuwar akwai meeting ɗin da sukayi a ranar,shigowar sa gidan kenan ya ci karo da kayayyakin su a tsakiyar parlor duk yaran sunyi zugum suna kallon sa,jiki a sanyaye ya karasa shiga cikin parlor zama Jiki a mace ya zauna bayan ya gaisa da iyayen naaa ya mike ya zai shiga ɗaki ya tsinkayo muryar granny na cewa "bafa zama zakayi ba as you can see yaran nan jiran ka suke ,kayi sauri ka fito ku tafi dare na yi"
Girgiza kai yayi yama rasa me zaice,yana shiga ya watsa ruwa ya ɗauki duk wani abuda yasan nashine kma zeyi amfani dasu ya kwasa ya nufi parlor,kallon yaran yayi yace "Ku tashi mu tafi" mikewa duk sukayi Alisha kuwa ji take kamar ta sa hannu a kai ta rushe da kuka, ta nufi waje ba tare da takalli kowa dake gun ba.
Daddy ma ya bi bayan ta haɗe da faɗin "sai da safen ku"
Mummy da duk tausayin ɗan nata take ji ta kasa ce masa komai,Granny ne dai yayi karfin halin amsa masa,Nawal kuwa har kuka sai da tayi, sai da ta rakasu har jikin mota daga fitan su kana ta dawo cikin gida.
Horn ɗin da mummy ta ji ya sa ta mikewa ta window ta leka don ganin ko waye da dare haka don a lokacin kusan karfe tare ne, shima mai gadi lekawa yayi yaga uban gidan sane da sauri ya wangale musu gate ɗin yana ɗaga musu hannu, Mummy kuwa ji tayi bugawar gudun zuciyar ta ya karu, ta wani bangare taji daɗin ganin su amma da ta tuna mantawa da ita sukayi sai taji ba ba daɗi,tsaki tayi ta sake labulen ta koma ta zauna ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya tana girgiza ƙafa.
Da sallama tayi suka shigo ko kallon inda suke ba tayi ba bare su sa ran zata amsa musu sallamar,cike da girmamawa suka karisa inda take suka gaishe ta bata amsa ba sai wani irin mugun kallo da tayi musu,Alisha jiki a sanyaye ta mike ta shige ɗakinta,Fa'eez kuwa wani uban tsaki ya jaa ya wuce nasu ɗakin Hisham ya mara mishi baya, daddy girgiza kai yayi ya wuce nasa ɗakin, muryar ta yaji tana faɗin "Ai ni ɗuwawune....." ta fashe da wata shaiɗaniyar dariya.
Tace "Gaskiya aisha tayi a rayuwa bara ma na kirata dole taji labarin nan"
Wayar ta ta ɗauka da shiga kiran layin ta,daga chan bangaren Aisha tana ganin Mummy ce ke kiran ta ta buga uban tsaki haɗe da faɗin jarababiya kawai tayi wa wayar dakuwa tamkar mummy na ganin ta,har wayar ya kusa tsinkewa ta ɗaga haɗe da faɗin "Hello qawata" haɗe da ƙirkirerren murmushi.
"Qawalliya albishir" faɗin mummy, turo baki aisha tayi kana tace "Goro bani insha"
"Yanzun nan Hameed ya dawo da yarannan nace dole na kira ki kiji,gaskiya ke qawar arziki ce"
Duk sai taji ranta ya dakule dajin Hameed ya dawo, Mummy tace "Ya dai ina magana kinyi shiru"
"Ai na gaya maka miki cewar zai dawo,kin tsaya kina biyewa wannan shashashar"
"hmm Aisha kenan,to sai da safe kamun ki fara zagin Rabi bana jin daɗi wallahi"
"Ai dole kice haka,mtswww" ta katse wayar.
*Washe gari*
Alisha bayan ta idar da sallar asuba bata yi ƙasa a gwiwa ba ta fito ta fara gyara gidan sabida sanin halin mummy,yana daga cikin karamin aikinta ta shige ɗakin ta taci mata mutunci,ai kuwa tana cikin aikin ta hango mummy durkusawa tayi tace "Mummy ina kwana?"
"Mtswww da ban kwana ba zaki ganni wallahi kinyi sa'a da kika tashi, da idan na shiga ɗakin na same ki wallahi duk haushin da nake ji a kan ki zan sauke"
"Am sorry mummy"
"Sorry for yourself"
Daddy ne ya shigo dashi da Hisham da Fa'eez dawowar su kenan daga Masallaci tsayawa yayi yana kallon ta ɗago kai tana ganin daddy ne tsaye sai da ta girgiza da irin kallon da yake mata, jikinta ne ya hau rawa bata san sanda tace "Ina kwana" tsaki yayi ya wuce ɗ'akin sa.
Yaran ma duk suka koma ɗakin su,Alisha kuwa ta cigaba aikin ta,ɗago kai tayi ta hango mummy har yanzu tana tsaye suna haɗa ido ta harareta tace "Idan kika bari na zo na same ki a wurin na wallahi sai na saba miki" da sauri ta juyawa ta bar wajen.
Haka rayuwa ta kasance a gidan Hameed yau zuma gobe maɗaci daddy ya ɗauke mata wuta ko kallon baiyi bare ya kula ta ,abun ba karamin damin ta yake ba wasa wasa har sun kai wata biyu da dawowa gidan amma ko ci kanka baya haɗasu tana kuma amfani da huɗubar da Aisha take mata, Rabi kuwa kullum faɗa take mata akan ta jaa mijin ta a jiki amma tayi burus da shawararta.
*After 5 months*
Alisha tayi WAEC and NECO ɗinta kuma Alhamdulillah yayi kyau hakan yasa daddy beyi kasa a gwiwa ba ya mata register na jamb shima kuma taci ta kuma sami admission a University of Bauchi,ana ta shirye shiryen tafiyar ta, a wannan lokacin mummy tayi kokorin haɗa mata abubuwa da dama duk da cewar daddy ya mata itama ta kara mata sannan tayi mata fatan Allah ya tsare,alisha taji daɗi sosai a tunanin ta Mummy ta fara gane gaskiya ne.
Depertment of computer science shine abinda aka rubuta a jikin bangon da manyan harufa, ajiyar zuciya ta sauke kana ta fara takawa a hankali har ta shiga ciki Lecture Theater (LT) ta samu wuri ta gefe ta zauna tana latsa wayarta.
Wata yar budurwa na gani wacce baza ta wuce sa'an Alishan ba ,tsayawa tayi ta na duba inda zata zauna tana hango Alisha ta nufi inda take ta mika mata hannu haɗe da faɗin "Assalam zan iya zama anan?" tana murmushi
Alisha ma murmushin ta maida mata kana tace "Eh bismillah man" ta mika mata hannu itama,zama tayi a gefenta tace "Suna na jamila ke fa?"
"Alisha!"
"Wow nice name,kema a hostel kike ko day?"
A hostel nake na ta faɗa nata hostel ɗin da take da room da take cike da mamaki Jamila tace "Ashe dai ɗakin mu ɗaya kai amma naji daɗi wallahi,department ɗaya ɗ'aki ɗaya,Alisha murmushi tayi kana tace "Nima naji,Allah yasa mu fara a sa'a"
Ta amsa da amiin,shirun da suka jine ya tabbatar musu da cewar malami yashigo,ba bata lokaci ya shiga gabatar da darasi
_______________________
Milhaat ce
Yar Terawa
Please comment and share