ASMA’UL HUSNAH

Chapter 4

by @amjad2022

_~ASMA’UL HUSNAH _~


NA

_~HAFSATOUAMJAD _~


~FREE PAGE ~

04


ASMA’UL HUSNAH na kudi ne it’s just 400 call or chart *** . 


   

 Yana komawa gida part dinsa ya nufa ,direct toilet ya shiga bayan ya gama tube kayan dake jikin sa 

  Ya dan dauki lokaci yana wankan sannan ya fito sanya da babban towel brown colour daure a kugun shi se kuma medium one a hannun sa yana tsane ruwan jikin sa , zama yayi a gaban mirror ya fara shafa expensive lotion din sa seda ya gama ya tashi ya nufi closet wata milk din pyjamas ya saka me maiko da wani gashi gashi a jikin wuyan brown colour dayai matukar haska rigar da shi kanshi mammalakin rigan ,turarukan shi ya shafa kamar ko da yaushe sannan ya dauki wayoyin sa ya fito parlour ,aiki ya farayi a laptop dinsa dake jone ajikin charge kasancewar yau througout be fita aiki ba shiyasa aiyukan dayake yi ta laptop din suke da dan yawa .


   Mikewa yayi ya nufi dan karamin kitchen din dake parlour nashi be dauka lokaci ba ya fito hannun sa da Dan madaidaicin mug da yake tururi, zama yayi ya cigaba da aikin sa yana sipping cofee daya hado,


  Jin karar murda handle din kofar yasa shi dago fararen idon shi ya dorawa Arfat dake shigowa tana Dan Kumbura baki wanda yana da tabbacin Amma ce ta tilas ta mata zuwa . 

 Maida idon sa yayi kan laptop dinsa yana tabe baki , karasa shigowa tayi cikin parlour sannan tadan Rissina tace “Yaaaah sannu da dawowa “

  Girgiza kai kawai yayi batare daya mata magana ba ,itama kuma tasan baze kula ta ba 

  “Ammma ce tace na kiraka wai “

 Dago da kanshi yayi ya dora mata idanun shi masu matukar kyau a fuskanta sannan ya dage duka girashi guda biyun , kauda kai gefe tayi sannan tace “Nima fah ban San dalilin kiran ka ba “ Dan tasan tamabayr ta yake 

  “Okay”

Kawai ya amsa sannan ta juya ta fice tana kunkunin da ta saba 


Tattara aikin yayi gaba daya ya ajiye dan zuwa amsa kiran Amma Dan yana matukar girmama iyayen sa ,kuma yana ajiye komai a mazaunin da ya dace .


  Da sallama ciki ciki ya shiga kayataccen parlour Amma din ,tana zaune a daya daga cikin royal din dake parlour , amsa mishi tayi duk da bata ji ba amman tasan baya taba shiga wuri beyi sallama ba ,a kasan Carpet din yayi wa kanshi mazauni ,dabi’arsa ce haka baya iya zama muddin iyayenshi na zaune a kujeran sabida tsabar yanda yake girmamasu 

 “Sannu da gida Amma”

Murmushi Amma tayi me kayatarwa cike da kaunar shi tace “Yawwa Nooryn ,ya aikin “?

“Alhamdullilah “

Kawai ya furta yana kasa da kanshi 


Kallon shi Amma ta kumayi sannan tace “Yawwa na kiraka ne akan maganar Samha tun wancan lokacin da kace abaka time in ban manta ba mun doshi 5month kenan amman kayi shiru baka Kuma cewa komai ba “

 

  Dandanan yaji kanshi ya sara Dan shi baya son yaji Amma tana mishi maganar wata yarinya yafi so abarshi da kanshi ya zabi yarinya da ta mishi , 


“Amma a kara hakuri “

Abunda ya fada kenan yana dan dafe kanshi 



“Abbina ya kamata ka gane maganar aure ba abun wasa bace bafa ,taya zaayi ace daga bangaren Samha baa samu matsala ba seda ga bangaren ka Haba mana “


Jingina kanshi yayi da jikin kujerar Zuciyar shi har ta fara hautsinewa Amma tana son saka shi abunda baya so kuma shi baze iya budar baki ya fada mata bayason zabin shi na amman yasan tabbas baze iya wannan auren ba amman ta Ina ze fara nusar da ita hadin da take shirin yi baze yiwu ba .


 Ganin yaki responding ne yasa Ammah tace “Go and think “


Mikewa yayi akasalance ya fita daga parlour ,duk seyaji ranshi a Jagule baya son amishi wani auren dole sekace karamin yaro . 


 Koda ya koma kasa tabuka komai yayi dole ya rufe system din ya kashe sockets din sanna ya wuce bedroom , alwala yayi yanda ya saba kafin yayi tilawar alqurani ya kwanta , 


 Tana komawa ciki bata tarar da Mamy a parlour ba ,dakin ta ta wuce seda ta dake Gasa jikin ta sosai da ruwan zafi yanzu ko kadan bataji zafin ba , wanka tayi sannan ta fito sanye da towel a jikinta , doguwar riga ta saka na bacci me Dan kauri sannan ta saka hula akanta , da sauri ta karasa inda wayar ta yake jin ana kiran ta duk da batayi expecting kiran kowa ba .


Kayataccen Murmushi tayi ganin Yaah Fahad ne yake kiranta ,seda ta zauna a gefen bed sannan ta daga wayan ,Tana dagawa taji maganar su su duka atare ,saurin janye wayar tayi taga ashe conference call suka hada maida wayan kunnenta tayi tana jin tsantsar soyayayr su har cikin ranta ,tanajin In babu wani daga cikin su bazata iya rayuwa me dadi ba ,

   

 “Our little how is the body “?

“Favs”

Abunda ta furta kenan ashagwabe 

Dariya dukan su sukayi sannan Anwar yace “Little me kikeso , ko zakije Maldives “

 Sunsan favorite wurin da takeson zuwa a duniya kenan , 

Ihu ta fara tace “Yeess Favs please “

Fahad ne yace “Oya get well soon ,then we’re going to maldives “


Wani ihun ta Kumayi ta mike akan gadon ta tana “Yess Favs ,naji sauki ma “


Dariya suka kuma yi su duka sannan kamal yace “No more crying ,no more sadness “


“Promise “

“Good girl “

Anwar ya amsa cikeda farin cikin ganin Asma ta sake . 


“Favs amman Dady baya nan “,

“Eh zamuyi magana keep on preparing little “


“I love you mhuaaaah”

Ta fada da karfi tana jin wani farin ciki mara misaltuwa 


“Oya kisha magani yanzu ki kwanta ,and in munzo gobe muka ga kina zazzabi no more trip “

“Ahhh Favs na warke fah pleese “


“Jeki ki kwanta and make sure kinyi Dua “


“Insha Allah love you babes “

Kashe wayan tayi , ta rungumeta a chest dinta wani sanyi dadi taji yana ziyar tanta lastly zataje Maldives 


Wani kiran ne ya kuma shigowa wayan , dago wayan tayi daga chest dinta taga wanda ya Ke kira , mood din fuskan ta ne ya fara canzawa faraan da su ya fahhad suka sakata ya fara fading . “In law “shine sunan da yake yawo akan screen din Decline na wayar tayi sannan ta kasheta gaba daya bayan ta goge number Nasreen din gaba daya .


Jinjina tayi da jikin bed din cikeda damuwa me zata ce mata ? Ya kirane ta mata jajaen yayanta ya fasa auren ta ko yaya ?



 “Mommy kingani ko daman nace miki bazatayi picking ba ta kashe wayan ma gaba daya “


Kamota Momy tayi sannan tace “Calm down Nas daman ai anmata lefi nima banyi goyi bayan ta daga ba ,atleast abarta tayi healing kafin aje abata hakuri dan inada tabbacin yanzu inakaje babu wanda zata saurara ki yi shiru komai ze zama settle insha allah “


“Momy gobe zanje gidan su Dan allah ni banason tana fushi dani “


“Ki bari next week semuje tare ko “

Badan taso ba dole ta hakura Momy ta lallabata ta tafi dakin ta sannan itama ta kwanta .



 Around 4 ya tashi alwala yayi ya fita massalaci bayan an idar yana zaune yana lazimi har gari yayi haske bayan yayi azkar dinsa ya fito ,koda ya koma wanka ya shiga daya fito ya shafa mai yayi drying kwantaciyar sumarshi ya shafa musu maya mayen da yake shafa musu sannan ya nufi closet ,acikin blue black suit yayi dressing da blue neckties da sukayi matukar amsar shi agogonshi samfarin rolex ya Makala bayan ya shafe jikin sa da perfume dinsa me kamshi , takalmin shi ya saka na kamfanin Gucci full cover blue black Banda Kyalli babu abunda yakeyi , wayan shi ya tattara da briefcase dinsa yayi waje bayan ya ka she light din dakin .


Part din Ammah ya nufa ,har cikin bedroom ya shiga tana zaune a bakin gado tana waya da alamun da Dady takeyi ,seda ya jira ta gama sanannan yace “Barka da asuba Ammah “

Murmushi tayi tace “Barka Abbi har an fito “

Gyada kai kawai yayi yana dan duba agogo 

“Toh ka tsaya kayi breakfast please Ka dena fita bakaci abinci ba Dan nasan ko kaje Office din ba samun lokacin cin abincin kake ba “

“Toh “

Kawai yace dan shi a rayuwar shi be iya musu da babba ba ,musamman Ammah gashi dai sauri yake amman dole yaci ko kadan ne 


Mikewa yayi ya fito parlour ya zauna a hannun kujera , da kanta ta Hado mishi tea da chips se soyayan Kwai ta kawo mishi tea din yasha da yawa sannan yadan ci chips din ya mike bayan ya goge hannun shi da tissue , peck yayiwa Ammah a goshi ya fita da sauri .


Wurin 9 Mamy ta leka dakin Asma ganin bata tashi bane yasa ta fita ,

Wurin aiki takeson lekawa Hajara ta kira ta jaddadawa ta tabbatar Asma taci abinci kafin ta dawo ,da Toh kawai ta amsa ita kuma ta fita Hajar tana mata allah ya kiyaye . 


Itama Hajra din sau 3 tana lekawa dakin bata farka ba ,se wurin 11 ta farka ,sosai tayi mamakin baccin da tasha kuma suprisely taji ta normal babu abunda yake mata ciwo , saukko wa tayi daga kan gado ta zura Room slippers dinta taje jikin window zuge curtain din tayi ta leka ganin babu Motor Mamy ya tabbatar mata ta fita , bathroom ta wuce seda ta yi wanka sosai sannan tayi brush ta fito , Hajar ta gani tana share share “Ina kwana Anty Asma “

Murmushi Asma tayi tace “Lpia Hajar ,Mamy ta fita “?

“Eh ta fita tun safe ta shigo taga kina bacci , “?

Gyada kai tayi ta wuce gaban mirror “Ina chuchu na 2days ban ganin shi “

“Yana dakin ya Ammar “

Juyowa tayi tana zumbura baki tace “Yanzu wayace abarshi ya fita Oya jeki ki daukko min shi “


Fita Hajar tayi da sauri ta nufi bangaren ya Ammar , tun kafin ta karasa parlour ta hango chuchu yanata tsalle tsalle “Chuchu “

Ya kira sunan shi , tahowa yayi da sauri yana daga jelan shi ,daukar shi Hajar tayi ta fito dashi daga part din yanata makale mata ajiki.


  Da sallama Ta shiga dakin sannan ta sauke chuchu , da gudunshi ya karasa wurin Asma , bude hannunta tayi tayi hugging nashi tana shafa kwantaccen gashin jikin sa , “I miss you Chuchu “

 “Mamy tace wai kice abinci kuma kisha magani”

Hajar ta fada mata 

Dagowa tayi sannan tace “ki kawomin custard kawai “

Girgiza kai hajar tayi taci Gaba da aikin seda ta gama sannan ta fita.


Saukkowa kasa tayi chuchu ta na biye abayan ta, 

 Canza channel tayi tana Dan kwanciya a kujeran , karasowa Hajra tayi da bowl din Custard a hannun ta mikewa tayi ta amsa tace “thanks “

 Ahankali ta fara Shan custard din tanajin taste dinshi har cikin brain dinta “Hajar kawomin madara “

Ta fada da dan karfi 

“Little ta warke “


Da sauri ta juya tana dariya “Favs “

 Da gudunta ta karasa bakin kofan tace “Suprise “


Dariya su anty Marwa sukayi sannan suka karasa shigowa parlour , 

 Yaran ta fara hugging daya bayan daya tana kissing nasu cikeda kauna tace “Ur’e welcomes babes “

 Gaida su tayi gaba dayan su tana musu sannu da zuwa , kafin su fara hira yaushe gamo “Daman bakwa zuwa gidan nan se anyi mutuwa ko wani bashi da lafiya “


 Sosai maganar ta ta sakasu dariya Anty Hannah ce tace “Au shedar da kika mana kenan little “


Zumbura baki tayi tace “Toh ai gaskiya ne yaushe rabon da kuzo “

“Last 2weeks ma a gidan nan na wuni yarinya Ke da kina school ai baza ki san munzo ba ko bamu zo ba “

Anty Saudah ta fada 

“Ina Mamy ne “?

“Mamy ta je wurin aiki nima ban tashi na ganta ba “


Daga haka suka cigaba da hira , har wurin 2 Mamy bata dawo ba sallah sukayi sannan suka ci abincin bayan Hajar ta gama

Jerawa a dining , 

Hajar tasa ta damawa chuchu madara dashi akaci abinci a dinning kasancewar duk sunsan kaunar dake tsakanin Chuchu da Asma , tun daga england Dady ya siyo mata shi tana kaunar cat sosai shiyasa sukayi sabo dashi duk inda zata je dashi take zuwa , bayan sun gama ciii sama Asma ta koma ta dauka wayan ta ta Kunna tana gama Kunnawa kiran Mamy na shigowa “Kinyi abinci “

Tambayar da Mamy ta fara mata kenan “Mamy naci ,kin tafi har yanzu baki dawo ba “

“Se 5 zan dawo wani Dan aiki ne ya rikeni “

“Toh Mamy su Anty Marwa sunzo,Mamy kema kinci abincin “

“Eh naci Nima am on my way nasan se dare ai zasu tafi bye take care “

Katse wayan tayi ta jona acharge sanann ya saukko kasan .



Yau tunda yaje Office unfortunately ya kasa tabuka komai ,duk yanda yaso ya maida tunanin ta aranshi abun yaci tura , duk wani Motsi nashi yana tuna mishi da magaiyar da ta ringa mishi , yanajin sautin muryan ta acikin kunnen shi buga tabble din gaban shi yayi da karfi yace “Noooo”.