Chapter 5
by @amjad2022
~_ASMA’UL HUSNAH _~
NA
~_HAFSATOUAMJAD_~
~_FREE PAGE _~
05
ASMA’UL HUSNAH na kudi ne it’s just 400.
Rai abace ya fita a office din yana fita Motor shi ya shiga yajaa da sauri yabar company gaba daya .
Ringing din wayar shi ne ya tsayar da shi daga maganar da yake “Excuse me “
Ya fada yana mikewa Dan fita daga conference hall din .
Kara wayar yayi akunnenshi bayan yayi picking , daga can bangaren Hammad yace “Yaaaaaah”
Dan taqaitaccen murmushi Noor yayi yana shafe kwantacciyar sumar shi yace “Hammad”
“Yaaaaah yaushe zaka zo am missing you “
“Maadd am on my way kaji ,very soon zanzo na ganka ya jikin ka “?
“Yaaaah sunce dai na kusa samun sauki “
Murmushi Noor yayi yace “Get well soon dear “
“Thank you yaaah “
“Baka tambaya su Ammah da Dady ba “
Hade rai Hammad yayi kamar yana gaban Noor yace “Ni ban sansu ba “
“Maadd stop acting like this please Ammah is ur mother and she really loves you please “
Girgiza kai Hammad yayi hawaye na cika mishi ido yace “Ni Anty juwairriya ce Mama na kai kuma Dady na “
Yana gama fada ya katse wayar
Kallon screen din wayar Noor yayi yana jin babu Dadi aranshi yanda Ammah da Dady suke treating Hammad kamar basu suka haifeshi ba ,kwata kwata basa sakashi ma alissafin ‘yaya su , shiyasa yaron ya taso da Kadaici da damuwa kuma ga rashin lafiyar dake damun shi , yanada chycatric problem baya normal activities dinsa yanda well-being people sukeyi ,and baya iya thinking so long ,akoda yaushe tunanin shi takaitacce ne akan komai ,ze iya aikata komai either good or bad ,shysa Noor ya fitar dashi malaysia saboda Amishi aikin kuma aikin se ya dauki 6years ana mishi treatment kafin a mishi aikin .
Tunda aka kai shi Tsakanin Dady da Ammah babu wanda ya taba kai mishi ziyara ko kiran waya aji lafiyan sa ,shysa Noor ya maye mishi gurbin iyayen da ya rasa , yasan yau baze wuni cikin walwala ba Anty juwairiya tana matukar kokari wajen kula dashi itada mijin ta .
Jiki asanyaye Noor ya koma cikin conference hall din da suke gudanar da meeting .
Zamewa Hammad yayi a kasan yana sakin wani kuka me taba zuciyar meji kukan Kadaici yakeyi ,da rashin gatan iyaye da sauri Anty juwairiyya ta karaso inda take hankalin ta atashe ta rukoshi tace “What’s wrong Hammad “?
Dagowa yayi yana kara rike hannun Anty juwairiyya da ita yake kallo a matsayin uwa yace “Nanny mesa ni iyayena basa kaunata ko dan ni handicapped ne “?
Toshe mishi baki Anty juwairiyya tayi itama hawaye na taruwa a idonta tana girgiza mishi kai ,saboda sharadin doctor na kar abarshi cikin bakin ciki ko damuwa
“Ammi da Dady suna sonka Madddd ,kayi hakuri kar ka saka kanka a damuwa please “
Ganin yakiyin shiru yasa Anty juwairiyya ta tafi dakin ta da sauri ta dauki Wayan ta tayi dialing number Noor .
Dafe kai Noor yayi ganin kiran Anty juwairiyya ya shigo baze iya ignoring kiran ba ,Dan haka ya tashi ya fito daga hall din bayan yayi picking
“Noor Hammad yakiyin shiru bansan me ya sameshi ba “
Dafe kanshi yayi dayaji yanason yadauki charge yace
“Bashi wayan .”
Mikawa Hammad wayan tayi dayake kuka sosai idonsa har yayi jaa yanajin zuciyan shi babu dadi , kuma yanajin bayason ganin Ammah da Dady .
Make kafada yayi ya juyar dakai
“Yaaaah ne fah “
Dagowa yayi da sauri jin abunda Anty juwairiyya ta fada ,hannun shi na rawa ya karbi wayan ya kara a kunnen shi ,
Sauke ajiyan zuciya Noor yayi sannan a hankali yace “Hammad kanason na kasa aiki a office ne “?
Girgiza kai Hammad yayi da sauri hawaye na zubo mishi
“Oya wipe the tears and take a promise bazaka kuma kuka ba “
Goge hawayen yayi sannan yace”I promisee yaaah”
“Good boy then me kakeso na kawo maka In zan taho “
Dariya yayi me kayatarwa da ta fito da tsantsar kamanninshi da Noor
Sannan yace “Anything sweet “
Gyada kai Noor yayi yace “Toh kar ka sake kuka if not Anty juwairiyya zata fadamin In kayi kuka kuma na fasa zuwa “
“Na dena “
“Oya bawa Anty juwairiyya hakuri kace Ka dena “
“Nanny kiyi hakuri na dena “,
Ya fada yana dan marairaicewa
Share hawaye Anty juwairiyya tayi tace
“It’s okay Maddd “
“Go and rest “
Noor ya fada yana datse kiran ,zama yayi a kujerun dake waiting area yana jin kanshi na daukan zafi kwata kwata bayason doguwar magana ,Amman in yana tare da Hammad dole se yayi saboda yanda yake kaunar shi .
Samha dake tsaye a jikin window ,ganin tahowar Noor daga part dinsa yasa ta saukko da sauri ta tsaya a bakin kofar .
Yana murda handle din Kofar ya shigo ta tafi da gudu zatayi hugging nashi ,saurin matsawa Noor yayi yana Binta da wani wulaqantaccen kallo ,accidentilly ta bugi kofar ta dawo da baya ta fadi , saurin sakin ihu tayi Dan jin yanda forehead dinta ke barazanar tsagewa Dan ba kadan ba ta bugu ,
Da sauri Ammah ta fito daga kitchen Arfat na bayan ta jin yanda samha take ihu , ko kula da Noor dake zaune a parlour batayi ba ta karsa wurin samha tana mata sannu sannan ta dagota daga kwancen da take ,Arfat kuwa ko karasawa batayi ba ta tsaya daga kitchen din tanajin dadin abunda ya samu samha Dan ita ko kadan yarinyar bata mata ba dukda families ne amman ita rawar kan ta yayi yawa,kuma gashi ana kokari a kakabawa yaaah auren ta,ta gama yawon rashin mutuncin nata babu miji, dayake an rainasu zaace yaaah ya aureta.
Tana nan tana kallon yanda auren ballagaza da Kamillalle ze kasance
Tabe baki tayi taci Gaba da kallon drama tasu itada Ammah
“Kinga danki ze lantani ko “?
Kallonta Ammah tayi suprisely sannan tace
“Noor kuma meya hadaki dashi a ina kika ganshi ma “
“Waifa saboda naga ya dawo na taho zanyi hugging nashi shine ya bugani da kofa “. Da gudu Arfat ta koma kitchen tana kyalkyala dariya , Dan daman tasan Yaah baze lamunci wannan haukan ba .
Kamo hannunta Ammah tayi asigar lallashi tace “Haba mana samha Noor fah mijin kine,keda zakibi hanyar da zaki bi ki saye zuciyarshi kuma kya zauna kina shirme In kikayi wasa wata ta aure shi ke kina zaune , shi kinsan besan duk wadandan abubuwan yafison mace Kamila kiyi kokarin zama kamilar mace indai kinason auren Noor
Dan shi kamili ne, duba fah kiga shigar jikin ki “
Zumbura baki Samha tayi tana jin haushin maganar da Ammah ta fada ,tayi kokari ta zamaa kamilar mace Dan shi kamili ne ita a gidan karuwai take kenan ,
Batayi mgn ba ta haye stairs da sauri hills dinta a hannunta
Binta da kallo Ammah tayi kafin ta girgiza kai ta dawo cikin parlour se a lokacin ta lura da Noor Dan Duk a tunaninta daya buga mata kan komawa yayi ,
Zama Ammah tayi sannan shikuma ya saukko kasa yana mata barka da gida
Ganin gaba daya kamar baya cikin Mood dinshi yasa Ammah tace “Lafiya dai Noor “?
Dagowa yayi ahankali ya kalli cikin idon Ammah , abunda ta gani ba karamin daga mata hankali yayi ba
Kamar fararen idonsa suna kokarin tara kwalla amman kwallan mene?
Ahankali yace “Hammad “
Sauke ajiyar zuciya Ammah tayi tana hade rai sannana tace mishi
“Kaje ka huta “
Batare da yayi magana ba ya mike da sauri yabar Parlour yana kokarin Danne abunda zuciyar shi Take Aiyana mishi .
Sosai Mood din Ammah ya canza Dan ita gaba daya mantawa takeyi tanada wani Dan , Dan ita bata daukeshi a mutum ba tunda mutumin da bazeyi normal function na mutane ba ,alokacin da tayi noticing cutar har addua take Allah ya dauki ranshi saboda yanda take wahala dashi ga kudin dayake ci musu , ganin abun yaki karewa yasa Ammah ta tattara shi ta ajiye agefe ta barwa masu aiki alhakin kula dashi Dan lokacin Noor baya nan ya tafi karatu , daga ita har Dady basu damu ba , saboda kowa aikin gaban shi yafi mutuntuwa shysa tunda Hammad ya tashi ,ya taso ne cikin kunci da rashin Kulawar iyaye harda soyayyar su ma babu wanda yake zuwa ko part dinshi, bashi da wanda ze fadawa damuwar shi ahaka har ciwon zuciya ya kamashi babu wanda ya sani ,suna ganin kamar wata wahala ce Allah ya daura musu akan shi,
Lokacin da Noor ya dawo ya fahimci halin da ake ciki beyi kasa a gwiwa ba ya dauki damarar kula da Hammad harda wanka da komai shi yake mishi sabuda zuwa lokacin ya girma har yakai 20years ,sosai Noor yake iya kokarin shi akanshi yayi spending Duk wani lokacin sa dashi ,saboda shi yaki fara aiki da wuri , ganin abun babu cigaba yasa yayi magana da wani likita abokinsa wanda yake malaysia ya mishi bayanin cutar Hammad din ,kuma likitan ya tabbatr mishi ze warke amman se yayi undergoing treatment na 6years kafin a mishi aikin saboda hadarin aikin , dole Noor ya amince ya fara musu shirye shiryen tafiya batare da kowa ya sani ba ,
Da Anty juwairiyya dake can itada mijin ta da yayansu yayi magana ta tabbatar Mishi babu matsala ,zata kula dashi Anty juwairiyya Kanwa ce ga Ammah itace autar su .
Har suka bar kasar babu wanda ya sani , bayan ya kai shi ya kwashi akalla 2 weeks yana kula dashi a asibitin sannan yabar ragamar komai a hannun Anty juwairiyya ya dawo nigeria , saboda kiran da Dady yaketa mishi akan Ina ya tafi be sanarwa kowa ba .
Koda Noor ya dawo be fada musu yakai Hammad wani wuri ba , seda yayi shekara uku suka gane baya gidan ,basu damuba amman Ammah ta tambayi Noor masaniya kuma ya fada mata.
Gyada kai kawai tayi tana ganin kamar aikin banza kawai noor yakeyi Dan bawai ze warke bane ,ta manta Allah yana raya wanda yakeso kuma ya kashe wanda yakeso alokacin dayaga dama bighairi hissab.
Wannan kenan .
Kiran Arfat Ammah tayi tace “Jeki hada abinci ki kaiwa Noor part dinsa “
Samha dake saukkowa cikin shigar riga straight data matseta kanta babu dankwali tace “Ah Amma ki bari na kai mishi “
Wani disguess kallo Arfat tayiwa Samha dake kokarin karban tray din hannunta .