ZAYTOONAH

Igbo girl

by @azizat


*Chronicles of*

*...... ...... ......ZAYTOONAH*


Rubutawa.....Azizat

Wattpad@Azi_zat

*Free page*

*2- Igbo girl (Inyamura)*

Bismillahir Rahmanir Rahim

A inda ta ke zaune ta fara gyangyaɗi sai dai buɗe ƙofar ɗakin da aka yi ya fargar da ita ta buɗe ido tana kallon ƙofa cike da tsoro. Wata mata ce ta shigo ɗauke da lantern irin na da wanda ake sawa kerosene. Sai da ta matso kusa da ita kafin Nkiru ta gane waye. Anty Nonye ce wacce ta maida sunan ta Elizabeth, ƙanwar Patrick. Tunda mijinta ya mutu shekaru uku bayan auren su ta dawo gida da zama, kusan shekaru sha shida kenan ba ta sake wani auren ba. Ta maida kan ta wata ƙaramar pastor dan ta maida rayuwarta kwacokam wajen yiwa church ɗin su hidima.

Elizabeth ta sa hannu a bakinta tareda faɗin "shshshsh"

Kunce ma ta ɗaurin da aka yi ta yi sannan ta ce a hankali "ki biyoni a hankali"

Siɗak-siɗak su ka fito daga ɗakin Elizabeth na riƙe da hannunta su ka fice daga gidan, kasancewar ɗakin yana chan ta baya ne sannan kuma tsakar dare ne kowa yayi bacci dan ana maganar ƙarfe uku na dare.

Sosai su ka yi tafiya kafin su ka kai bakin church ɗin ƙauyen inda wani mutumi ke tsaye a bakin keke yana jiran su.

Elizabeth ta kama hannun Nkiru guda biyu tana faɗin " kin ga iyayen ki da su ka mutu ina da yaƙinin Uncle ɗin ki Udodiri ne ya kashe su kuma ke ma sharri ya miki dan a kashe ki. Dukiyar mahaifin ki ya ke son ƙwacewa, ki bi Antony zai kai ki garin Obowo akwai gidan wani elder na church ɗin mu sai ki zauna a chan idan kin huta zai sa ki a mota ki wuce Calabar, ban san gidan Kakannin ki na chan ba amma na san tunda Patrick ya ce iyayen Caroline ma su kuɗi ne ba za su yi wuyar samu ba. Sai ki tambayi gidan Chief James Asibong" Nkiru ta gyaɗa kai tana hawaye. Ko ba ta faɗa ma ta ba ta san sunan Kakan na ta, tunda maiden name ɗin Mommy shine Caroline Asibong. Ta kuma san Mommy ce 'yar fari a wajen mahaifinta kuma tana da ƙanne biyu maza 'yan biyu.

Elizabeth sai da ta ga sunyi nisa kafin ta bar bakin church ɗin tana addu'an Jesus ya sa Nkiru da Anthony su isa garin Obowo lafiya...

Sun fita daga ƙauyen lafiya amma ba su yi wani nisa ba keken Anthony ta yi faci dan haka a ƙafa su ka ci gaba da tafiya Anthony na tura keken ita kuma Nkiru na binshi a gefe. Nkiru tana tafiya ne tana hawaye, yunwa da ishirwa sun ma ta kamun talala amma ba wannan ne damuwarta ba damuwarta shine abinda Uncle Udodiri ya yi.

Kafin su iso garin gaba ɗaya ta jigata amma a haka ta dage tana tafiya ba tareda ta nuna gajiyawarta ba.

Ko da su ka je gidan Elder ɗin safiya ta yi sosai sai dai rashin sa'a matar sa ta ce mu su baya gari. Antony ya gayawa matar saƙon Elizabeth akan Nkiru za ta zauna da su na wani lokaci dan haka duk da Elder baya nan zai bar Nkiru a wajenta idan ya dawo sai ta sanar da shi. Matar Elder ta washe baki ta ce ma sa ba komai.

Anthony ya fita dan ya je yai facin tayar keken sa sannan ya wuce ƙauyen su.

Bai fi minti takwas da tafiyar Antony ba matar ta kalli Nkiru da ke zaune tana zazzare idanu ta ce da yaren Igbo " ba zan amince da zaman ki a gidan nan ba saboda na san halin mijina, the last time da aka kawo mace gidan nan ban ji da daɗi ba dan haka ki tashi ki kama gaban ki, idan dai Calabar za ki je ga hanya daga nan ba nisa zuwa park za ki samu mota"

Nkiru da ta ɗauko kofin silver na ruwa da matar ta kawo mu su za ta kai baki sai ta kafe a wajen hannunta ya fara rawa.

"Ba ki ji abinda na faɗa ba ne" ta faɗa da ƙarfi wanda yai sanadiyar da kofin hannun Nkiru ya suɓuce ya faɗi ƙasa.

"Please help me, ban san ko'ina ba a garin nan kuma ba ni da kuɗi. Ki bari..."

"Will you shut up! Irin ku ne mijina ke so, sweet sixteen. Ba zan yarda ba, ki tashi ki tafi kafin rai na ya ɓaci"

Nkiru ta fashe da kuka saboda ba ta san inda za ta je ba daga nan. Ina ta sani a Nigeria. Gidan su da ke Owerri ko sunan anguwan ba ta sani ba, balle ko ta sani ma ba halin zuwa dan Uncle Udodiri zai iya zuwa ya kamata a wajen.

Yadda matar ta harzuƙa ne ya sa Nkiru ta fice daga gidan da gudu tana gudu tana tunanin ko za ta dace da haɗuwa da Antony. Sai da ta yi nisa sosai da gidan ta haƙura da gudun ta soma tafiya...

Chochi shine mafita gareta za ta samu mutanen ƙwarai da za su taimaka ma ta a wajen. Tana tafiya tana baza ido ko za ta ga alaman church. Ba a jimaba kuwa ta hango wani madaidaicin church sai dai a kulle ya ke ta yi tsaki ta cigaba da tafiya. Sanyin December na shigarta amma ba ta damu da sanyin ba ta cigaba da tafiya a hankali tanayi tana zubda hawaye. Mafiya yawancin ma su wucewa kallon mahaukaciya su ke ma ta, pink pyjamas ne ajikinta mai gajeran hannu gashi ƙafarta ba takalmi. Slippers ɗin da Elizabeth ta ba ta ya tsinke lokacin da su ke tahowa garin Obowo a ƙafa, yanayin tafiyarta kaɗai ya isa ya gamsar da mutum cewa ba ƙalau ta ke ba.

Yadda ta hango wasu treloli da bus bus a ɗan nesa da ita ya sa ta ɗan tsaya. A ranta ta ke tunanin ƙila za ta iya samun motan Calabar a nan, sai dai matsalar ba ta da kuɗin mota amma ba ri ta gwada roƙon su ko za su taimaka ma ta. Ta shafa cikinta da ke ta ƙugi yana neman abinci, rabon da ta ci abinci tun shayin da ta sha daren da aka kashe iyayenta. Sakwara da miyar egusi aka kawo mu su daren ranan wanda ya ji naman Akuya nasha-nasha sai dai ita ba ta cin naman Akuya kuma ba ta son cin abinci mai nauyi da dare, shiyasa kawai ta haɗawa kan ta tea ta sha yayinda iyayen ta su ka ci sakwaran, ashe da rabon za ta rayu ne shiyasa ba ta ci ba...

"Kai ɗan Fillo akwai ka da abin dariya"

Ɗaya daga cikin ma su lodin jarkunan manja cikin trailer ya faɗa yana kallon T J da ke cigaba da ba su labarin yadda aka kusa kasheshi a wani ƙauye.

"Ka san na sadaƙar da rai na, ina ta tunanin ina ma albarkacin sunan Shehu Tijjani da na ci nima Allah zai ba ni karama kawai na ɓace na ganni a gaban Baffa na. Amma inaaa, ita mutumin sai wuwulwuwul ta ke da wuƙa tana faɗin Osibatata osibututu osiburebure..."

Gaba ɗaya 'yan wajen su ka fara dariya, wani da ya ɗau jarka sai ga shi da jarkan a ƙasa ya riƙe ciki yana dariya.

T J ya dage yana maimaita mu su siddabarun da mutumin ke faɗi yana cikin haka ya ji an dafa ƙafaɗar sa.

Ya juyo a hankali yana dariya, buɗe baki yai yana kallon wacce ta dafa shi, ya ɗan rufe ido ya buɗe ko dai yarinyar ce ta ke ma sa gizo.

"Please help me, i'm going to Calabar but i dont have money". Nkiru ta faɗa kamar za ta yi kuka. Tunda ta shigo wajen ta ke rarraba ido tana neman wanda za ta yiwa magana, yadda ake kallonta ya sa jikinta yai sanyi tana tunanin anya akwai wanda zai taimaka ma ta, ganin wani saurayi sanye da kayan NYSC ya sa ta tunkare shi, ko a Owerri ta ga ma su irin kayan watarana da su ka fita shaƙatawa inda Baban ta ya ma ta bayanin ko su waye ma su saka irin kayan.

"Please" ta sake maimaitawa ganin ya ƙi yin magana.

Daɗin muryanta tareda British accent ɗin ta ya dawo da shi daga duniyar tunani da ya tafi na 'yan sakanni.

"Sorry, you said Kalaba?"

Ta gyaɗa ma sa kai

Ya kalli ɗaya daga cikin ma su lodin manja ya tambayeshi ko ana samun motar Calabar a wajen, mutumin ya ce ma sa sai dai ta je General Park.

T J ya juyo ya gaya ma ta da turanci.

Yadda ta sauke ajiyar zuciya ya sa T J ya san ba lafiya ba. Ɗago idon da za ta yi sai ya ga hawaye a idonta mamaki ya kamashi.

So ta ke ta gaya ma sa ba ta da kuɗi kuma ba ta san inda General Park ɗin ya ke ba amma ya ma ta kwarjini ba ta sani ba ko kallon mahaukaciya zai ma ta. Ta juya a hankali ba tare da ta ce ma sa komai ba ta fara tafiya, wannan karan church za ta je ko da a rufe ya ke za ta zauna a bakin church ɗin, ba ta da mafaka da ya wuce House of the Lord, ko da mutuwa za ta yi gara ta mutu a church.

"Hey wait" muryan T J ya tsaidata. Ta dai tsaya amma ba ta juyo ba.

Tambayarta yai ko ita ce ta yi rawa a wani festival da aka yi a ƙauye kwana uku da su ka wuce. Ta gyaɗa ma sa kai.

"What happened to you?"

Hajijiya ta fara ji dan haka ta tsugunna tana dafa kanta.

"Are you Ok?" Ya tambaya cike da damuwa. Kallon ƙafarta yai ya ga ashe ko takalmi babu ga ƙafar har ya faffashe.

"This is serious. Where are your parents? Why are you like this?"

Ba ta iya ba shi amsa ba sai hawaye.

"Ɗan Fillo yarinyar nan fa yunwa ta ke ji, tana cin abinci za ta warware" wani a wajen ya faɗi.

Wani kuma ya ce " Ku ga idon ɗan Fillo dan Allah, ya ga yarinya 'yar dumaduma ya ruɗe"

Aka kwashe da dariya

Wani kuma ya ce "Ɗan Fillo da rabon dai yau za a yanke ma ka wuya"

Nan su ka hau maimaita Osibatata Osibututu su na dariya.

Taimaka ma ta yai ta miƙe tsaye sannan ya ce ta biyo shi. Wajen mai shayin da ke tashar su ka je, duk garin shi kaɗai ke sana'ar shayi, da farko Hausawa 'yan uwan sa kaɗai ke siya daga baya kuma ya fara samun ɗaiɗaikun mutane da ba hausawa ba wanda su ke aiki a tashar su ma suna siya.

"Malam Idi zubo min shayi dan Allah"

Malam Idi ya ce "to Shehi" Da ke ya saba da 'yan tashar , su na haɗuwa wajen Sallah, sannan duk wata ya kan zo tashan ya ba da saƙo a kai ma sa Kano daga nan har garin su.

Yadda ya ke haɗa ma sa shayi ya ji sugar sosai haka ya haɗo ya miƙa ma sa. T J ya karɓa ya miƙawa Nkiru da ke zaune a kan benchi. Ta amshi kofin shayin ta kai baki, yadda hannunta ke rawa ya sa T J ya ƙara jin tausayinta tabbas akwai yunwa a tattare da ita.

Ko zaƙin tea ɗin ba ta damu da shi ba haka ta fara kurɓan tea ɗin nan ba kakkautawa, kafin ka ce me ta shanye shi tas. Ta miƙa wa T J kofin tana faɗin "Thank you"

Ya miƙawa Malam Idi kofin ya karɓi wani shayin tareda bredi ya miƙa ma ta. Ta wafce bredin da sauri ta fara ci da sauri-sauri. Saboda yadda ta cika bakinta da bredi da ƙyar ta ke taunawa. Ganin haka ya sa T J da ke kallon ikon Allah ya miƙa ma ta kofin shayi ta kuwa amsa ta kurɓa, hakan ya sa bredin da ke bakinta yai laushi har ta samu ta haɗiyeshi haka ta cigaba da ci har ta cinye.

Shi ma mai shayin ya lura da yadda Nkiru ke cin bredin ya san ba ƙaramin yunwa ta ke ji ba.

"Shehi ko za ka ƙarɓo ma ta shinkafa a wajen Maman Chukwudi"

T J ya amsa da to. Ya kalli Nkiru ya ce "wait here, i'm coming"

Da sauri sauri T J ya wuce shagon Mama Chukwudi da ke sai da abinci a tashar ya karɓo shinkafa da wake da miya har tiriri ta ke saboda ba a jima ma da sauke ta ba, haka ya karɓo yana sauri kamar zai tashi sama. Har a lokacin zuciyarsa na son sanin mi ya samu yarinyar nan cikin 'yan kwanaki uku kacal ta lalace haka.

Wannan karan rabin shinkafar Nkiru ta ci ta tura gefe ta ce ta ƙoshi.

Ganin ta fara dawowa hayyacinta ya sa T J ya tambayeta sunan ta.

"Nkiruka-Mary"

"Kiruka?"

Nkiru ta girgiza kai ta sake maimaitawa, wannan karan tana stressing N ɗin

"NNNkiruka or Nkiru"

T J ya ce "Inkiru"

Still ba dai dai ba ne amma ta bar shi haka.

Ganin ta na kallon sa ya sa shi cewa " My name is Tijjani but people call me T J"

Itama ta maimaita T J ɗin da ba za ta iya kiran Tijjani ba.

Tambaya na gaba shine miya kawota nan sannan miyasa ta ke son zuwa Calabar.

Ba ta san miyasa ta ke jin za ta iya yarda da shi ba, its like there's something in his eyes that is telling her he's honest trust him. A taƙaice ta bashi labarin yadda aka kashe ma ta iyayenta da kuma yadda wata ƙanwar mahaifin ta ta taimaka ma ta ta gudu.

Ya tambayeta ko ta taɓa zuwa Calabar ta ce ma sa a'a. A zuciyar sa yana faɗin lallai akwai matsala.

"Kin san gidan ku na Owerri?" Nan ma ta amsa da a'a, kusan komai ya tambaya sai ta ce a'a.

Ya ce "tirƙashi ashe kai kifin rijiya ne"

" what?"

"I mean what are you going to do?"

"I dont know, i want to look for my maternal grandparents but i dont know how"

Kafin yai magana ya ji ana ƙwalla ma sa kira.

"Ɗan Fillo mota za ta tashi ka matso kusa"

Ya amsa da to. Ya kalli Nkiru ya ce mata zai tafi, nan da nan idon ta su ka ciko da hawaye. Ya fito da kuɗi a aljihunsa ya miƙa ma ta ya ce ta je tasha ta nemi motan Calabar kuma ta sayi takalmi.

"Take me with you" ta faɗa ba tareda ta san dalilin da ya sa ta faɗi hakan ba.

A hankali ya fara ma ta bayanin cewa shi ba ɗan nan ba ne kuma garin su akwai nisa.

"Ɗan Fillo" aka sake kira

Ya miƙe tsaye yana jin zuciyar sa na ma sa nauyi.

"Nice meeting you Inkiru-Mary, and goodluck" ya faɗa a hankali sannan ya juya ga Malam Idi ya ce "Malam Idi zan wuce, idan ba damuwa ka yiwa yarinyar nan kwatancen inda za ta samu motar Kalaba"

Malam Idi ya ce to tareda ma sa addu'ar Allah ya tsare.

A hankali ya ke tafiya saboda tsananin tausayin Nkiru da ya ke ji ya kashe ma sa jiki, fatan sa Allah ya sa ta samu kakannin ta idan ta je Calabar. Wani zuciya na raya ma sa ya fasa tafiya ya raka Nkiru zuwa Calabar, to amma idan bai tafi yau ba sai wani sati domin ba koyaushe ake samun motar Kano ba. sannan idan bai tafin ba zai rasa bikin ƙannen sa da za ayi ranan Jummu'a ya kama saura kwana huɗu kenan. Da Eze bai riga ya tafi na su ƙauyen ba a chan Nsukka da ya haɗata da Eze ya rakata. Haka dai yaita tunani har ya kai wajen trailer ɗin, har dreban ma ya tada motar. Ya buɗe gidan gaba zai shiga sai ya juya ya hango Nkiru tana tahowa wajen da sauri. Murmushi yai ya ɗaga ma ta hannu ɗaya, yana ganin sanda hawaye ya zuba a idonta ta sa hannu ta fara sharewa. Yai saurin shigewa cikin motar dan kada shima ya fara hawayen.

Yana shiga mota ta tashi, Dreba da yaron motan sa guda ɗaya su ka fara tsokanan T J. Su uku ne a gaba yayinda bayan aka cikata da jarakunan manja ciki harda jarka guda biyu na T J wanda ya rubuta sunan sa saboda shaidah. Jakar Ghana-must-go guda biyu ya ɗauka wanda ɗaya kayan sa ne aciki da littattafai sai ɗaya Jakar ta tsaraba ce.

Ko kalma ɗaya bai faɗi ba, idanun sa na kan side mirror yana hango Nkiru tsaye tana kuka, bayan sun ma ta nisa ya dena hangota ya sunkuyar da kansa yana lissafin abubuwa a ransa. Ƙarshe dai answer ɗaya ya samowa kansa ita ce kawai mafita, ita ce kawai zai yi ya ji hankalin sa ya kwanta. Duk da wannan mafitar za ta zo da ƙalubale amma a hakan gara ya san ya taimakawa wannan yarinya da ya barta ba tareda ya san halin da za ta shiga ba.

"Dreba ki tsaya" ya faɗa lokacin da ya ɗago kan sa. Har yau dai a mafiya yawancin lokuta idan zai yi Hausa yana maida mace namiji ya maida namiji mace. Shi idan ba karatun da yai a Zaria ba da ba zai ji Hausa har haka ba. A gidan su jefi-jefi ake Hausa amma Fulatanci kawai su ka sani, shi kuma ya bi harshen su.

"Zamu tafi da wancan yarinyar" ya faɗa lokacin da ya ga Dreban bai da niyyar tsayawa.

Da Dreban da Yaronsa suka sa T J a gaba da faɗa suna gaya ma sa illar abinda yake da niyyar yi. T J ya nuna koya nene zai tafi da Nkiru idan ya so idan ya dawo dan ya ƙarisa watanni huɗu da ya rage ma sa a garin sai ya raka Nkiru zuwa Calabar ya sa da ta da 'yan uwan Mahaifiyarta.

Da Dreba da Yaronsa dukkan su Hausawa ne sai su ke ganin wautar T J ɗan Fulani. Ƙarshe da su ka ga ya dage sai su ka barshi amma da sharaɗin T J zai biya ma ta kuɗin mota duk da kuwa shi T J ɗin alfarma aka ɗauke shi. T J ya ce ya amince.

Yana saukowa daga trela ɗin gudu ya fara yana fata ba ta bar tashar ba. A wajen da ya barta tsaye lokacin da zai shiga motar a nan ya ganta tsaye tana hawaye yayinda wata mata ke tsaye kusa da ita tana ma ta magana. Tunda ya ganta kuwa yai Hamdala a ransa ya ƙara gudu. Ɗago idon da za ta yi ta hangoshi yana gudu nan ta kama murmushi. Har T J ya iso ba ta dena murmushi ba, matar ganin tana murmushi ita ɗaya ya sa ta ja tsaki ta wuce dan acewarta Nkiru mahaukaciya ce.

Yana haki yana tambayarta ko za ta bishi garin su idan ya so sai su dawo tare ya rakata har Calabar. Ta gyaɗa kai.

Ya duƙa ya fara cire takalmin sa tareda socks ɗin. Da ya gama cirewa ya ce ta sa, ta kalli cikin idon sa cike da mamaki, ya gyaɗa ma ta kai yana murmushi. Jiki na rawa ta fara saka socks ɗin wanda sai alokacin ta ga yadda ƙafarta ya ɓaci, ta gama ta sa takalmin wanda ba dan socks da kuma ɗaurewa da ta yi tamtam ba da haka ƙafar za ta yi ta lilo a ciki, T J dogo ne sosai gashi siriri ita kuma duk da ta ɗan fishi faɗin ƙafa amma ba ta kai shi tsayin ƙafa ba.

Jacket ɗin sa ya ba ta ta sa sannan ya ce su tafi. Da gudu-gudu sauri-sauri su ka kai wajen da motar ta ke, ya taimaka ma ta ta hau sannan shima ya shiga.

Dreba da yaronsa Ibrahim ba fahimtar turancin ta su ke ba lokacin da ta ke gaishesu. Su pidgin su ke ji ita kuma turanci kamar Sarauniyar Ingila. Ban da gaisuwa kuma ba abinda su ke ji a yaren Igbo.

Haka su ka kama doguwar tafiya. Tun ba a kai awa ɗaya da kama hanya ba Nkiru ta sa kan ta a kafaɗar T J ta fara bacci. Dreba ya ce T J ya ma ta magana ta koma kan doguwar kujera da ke bayan su wanda su ka maidata gado. Nkiru ta koma baya ta miƙe jiki sai bacci.

Lokaci zuwa lokaci T J yana leƙata ko ta tashi amma ba ta tashi ba. A ƙalla ta kai awa biyar tana bacci kafin ta farka. Haka dai tafiyar ta kasance jefi-jefi T J yana ma ta tambayoyi wanda ta ke amsa ma sa bisa gaskiyarta...

Tafiyar ta su ta ƙara daɗewa saboda ɓaci da motar ta yi a hanya, sai da su ka yi kusan awa huɗu su na jira kafin aka gama gyarata. Ba su suka iso Kano ba sai

Ƙarfe takwas na safiyan washegari.

Kafin T J ya samu ya haɗa kan kayan sa ma sai da su ka kai wajen ƙarfe shaɗaya. Daga nan ya nema mu su Bus da za ta kai su garin su wato Ringim wacce lokacin ke haɗe da Kano saboda ba a raba Jigawa da Kano ba...

Abu uku ya gaya ma ta wanda ya ce ta riƙe su da kyau, idan ta yi haka har su dawo ba za ta samu damuwa ba.

"Gidan mu musulmai ne kuma Fulani ke kuma Christian ce 'yar ƙabilar Igbo. Ba kowa ne mai sauƙin kai kamar ni ba dan haka duk abinda za a miki na nuna ƙyama ko wariya ka da ki bari ya ɗaga miki hankali. Na biyu kuma iyayena da mafiya yawanci 'yan uwana ba su yi Boko ba dan haka ba sa jin turanci, kusan maganar kurame za a dinga yi idan ba na kusa da zan fassara miki ko kuma wanda su ke ji ɗin ba sa kusa. Na uku kuma za ki yi haƙuri da yanayin gidan mu, gidan mu gidan yawa ne kuma ba gida ne irin wanda ki ka taso ba, ina fata yadda kika lallaɓa da zaman ƙauyen mahaifin ki za ki lallaɓa da zaman gidan mu"

"Thank you. You are truly a good man" abinda ta faɗa ma sa kenan lokacin da ya gama ma ta bayani...

***

Bayan Isha su ka isa daidai ƙofar gidan su T J, mai mota ya fitar mu su da kaya sannan ya ƙara gaba. Tun da yaran da ke ƙofar gida su ka ƙyalla ido su ka gan shi su ka fara ihu suna kiran "Hamma Tijjani wartoyi, Hamma wartoyi" su ka yo kan shi da gudu, ya ɗauki ƙaramin cikin su yana cillashi yaron na ta dariya.

Cikin gidan su ka shiga nan ma dai ihun murna ake yi, tunda ya tafi bautar ƙasa wannan ne karon farko da ya zo gida.

Nkiru dai bin bayan sa kawai ta ke yi tana mamakin yaran, ita tun a hanya ta ke mamakin ƙasar Hausa.

Magana yai da wata mace da Fulatanci sannan ya juyo ya kalli Nkiru ya ce ta bi ƙamwarsa za ta kai ta ɗaki.

Yarinyar da ba za ta wuce shekara bakwai zuwa takwas ba ta jagoranceta har wani ɗaki, ganin yarinyar ta cire takalmi ya sa Nkiru ma ta cire takalmin T J ta shigo ɗakin wanda ke wadace da hasken lantarki saboda akwai wuta a lokacin. Tun kafin ta shigo yarinyar ta soma yiwa tsohuwar da ke zaune akan sallaya bayanin abinda T J ya ce ma ta.

"Maraba da zuwa" tsohuwar ta faɗa tana kallon Nkiru.

"Goggo ba ta jin Hausa fa"

Goggo ta ce "tooo"

Ta yiwa Nkiru nuni da ta zauna a kan kujeran da ke ɗakin. Nkiru ta zauna tana sauke ajiyar zuciya akai akai...

Bayan ya rabu da yaran ne ya shiga wajen mahaifiyar sa Iya ya gaisheta sannan ya wuce ɗakin kakar sa ita ma ya gaisheta kafin ya dawo ɗakin Goggo wacce har lokacin tana lazimi. A gabanta ya duƙa ya gaisheta ta amsa cike da farin ciki. T J ya tambayeta ko Baffa na ɗaki ta ce da alama bai dawo ba tunda ya tafi sallah. Cikin yaren fillanci ya fara ma ta bayani akan Nkiru da kuma dalilin kawota nan. Ya sani ko da sauran 'yan uwan sa ba za su fahimceshi ba to Baffa da Goggo za su fahimce shi.

Bayan ya gama bayani Goggo ta ɗaga ido ta kalli inda Nkiru ke zaune ashe ta yi bacci. Ta kalli T J ta ce "ba ni da matsala da zamanta a nan gidan amma ka san ko za ta zauna sai da yardar Baffan ku sannan za ka sha magana a wajen Iya sai dai ka yi haƙuri"

T J ya ce "na sani kuma zan amince da duk hukuncin da Baffa zai yanke, idan ma bai amince ba zan yiwa abokina Okafor magana ta zauna a gidan su"

Goggo ta ce " Allah ya taimaka, ka duba ɗakin na sa ko ya dawo"

T J ya amsa da amin tareda miƙewa tsaye yana stretching hannayensa da su ka yi tsami.

"Zan sa a sa muku ruwan zafi da za ku yi wanka saboda jiki ya warware"

T J ya ma ta godiya sannan ya fita, kai tsaye ɗakin Baffan sa ya nufa ya kuwa ci sa'a ya dawo. Ya ma buɗe kwanon tuwo kenan zai fara ci T J yai sallama.

Ba ƙaramin farinciki Baffa Habubakar ya ji ba ganin ɗan na sa wanda tun da ya tunkaro gidan yara su ka tareshi a hanya su na gaya ma sa Hamma Tijjani ya dawo. Dan haka da farin ciki ya shiga gidan.

Suna gaisawa ya ce T J ya wanke hannu su ci abinci ba mu su T J ya wanke hannu duk da ba yunwa ya ke ji ba dan ya siya musu Gurasa da nama sun ci a hanya.

Tare su ka cinye abinci sannan aka shiga hira yaushe rabo, daga baya T J ya bayyanawa Baffansa duk abinda ake ciki, ba abinda ya rage ma sa gameda labarin da Nkiru ta gaya ma sa.

Shiru Baffa yai bayan ya gama bayanin yana tunani kusan minti biyar yana nazari kafin yace " Ba zan ce ka kyauta ba ba zan kuma ce ba ka kyauta ba amma abu ɗaya na sani shine duk abinda ka yi ka yi shi ne da kyakykyawar niyya. Kasancewar ta kafira ba zai sa mu ƙyamaceta ba, dan haka za ta zauna har zuwa lokacin da za ka koma ɗin. Allah ya shige mana gaba amma..."

Bayan T J ya baro ɗakin Baffa ɗakin Goggo ya wuce, Goggo da Asma'u sun rasa yadda za su yiwa Nkiru bayani ta je ta yi wanka sai indiya indiya su ke, ita kuma ta baza ido tana son gane abinda su ke nufi. Da ta ga Asma'u na cuccuɗa jiki sai ta gane wanka su ke nufi, ta fara faɗa mu su idan ta yi wanka ba ta da wani kayan da za ta sa amma ba su gane ba.

Da T J ya shigo sai ya zauna ya zama interpreter tsakanin su. Bayan ya ji bayanin Nkiru ne ya sanar da Goggo akan zai fita ya siyo ma ta kaya kafin ta yi wankan.

"Haba Shehu, daga zuwa sai fita dan kayan da za ta sa yanzu kam ai akwai shi"

Ta je ta ɗauko ma sa riga da zani cikin kayan da ta yi sallar Azumi da shi sau ɗaya ta saka ba ta kuma sa shi ba.

T J ya karɓa ya miƙawa Nkiru ya ma ta bayani ta amsa tareda godiya. Ta bi bayan Asma'u su ka fita.

Wanka ta yi da sabulu zalla ta cuɗa jikinta sosai, ita kan ta ta san ba ƙaramin datti ta yi ba. Ta so wanke gashinta amma tana ganin babu shampoo sannan ruwan ba zai isa ba. Ruwan kuwa da zafi sosai dan haka ta ji daɗin yadda ya ratsa jikinta sosai.

Da ke Goggo ba ta da jiki rigan Goggo da ƙyar ya shigi Nkiru dan ma wai ɗinkin zamanin da ne wanda ake yinsa da ɗan faɗi ba kamar na zamanin yanzu da ake yin fitted ba. Ta ɗaura zani ta fito bayan ta naɗe pyjamas ɗin da ke jikinta da.

Har lokacin T J na ɗaki su na hira da Goggo haka ta shigo tana ɗari-ɗari ta so manta ɗakin ma albarkacin takalmin T J da ta gani ne ya sa ta gane ɗakin.

Sun riga sun yi magana da Baffa akan za ta zauna ɗakin Goggo dan nan ne ba za ta samu takura ba. T J yai wa Nkiru bayanin za ta dinga kwana a ɗakin Goggo ya kuma jaddada ma ta Goggo ba ta da matsala ba za ta samu damuwa ba, ya kuma nuna ma ta inda Goggo ke sallah ya ce ma ta private space ɗin Goggo ne inda ta ke Ibadah dan haka kar ta je ta wajen. Nkiru ta gyaɗa ma sa kai.

Sai da zai tafi ya tambayeta ko tana jin yunwa ta ce a'a. Bayan ya tabbatar ba ta da matsala sannan ya fita.

A ƙasa aka ma ta shumfuɗi ta kwanta, a nan Asma'u ke kwana amma Asma'un za ta kwanta a kan gado tareda Goggo. Allah Sarki Nkiru na kwantawa ko minti goma bai kai ba ta fara bacci har da minshari. Da ke ba Goggo ke da girki ba bayan ta gama abubuwanta ta rufe ɗaki ta kwanta kusa da Asma'u da itama tuni ta yi bacci. Addu'an ta Allah ya sa kar zaman Nkiru ya jawo matsala a gidan.

Zuwa washegari duk girman gidan ya ɗauka da zancen Hamma Tijjani ya dawo da wata Arniya kuma Inyamura...