ZAYTOONAH

Tijjani

by @azizat

*Chronicles of*

*...... ...... .......ZAYTOONAH*



Rubutawa.....Azizat

Wattpad@Azi_zat



*Free page*

*3-Tijjani Abubakar Djibo*





Modibbo Muhammadu Djibo Kakan T J kenan, Bafulatanin usul ne gaba da baya, kakannin sa daga garin Djibo su ka fito da ke ƙasar Mali sai dai kasancewar su makiyaya ya sa ba sa zama waje ɗaya. A lokacin da kiyo ta kawo su har garin Ringim shine babban su ya fara rashin lafiya. Jinya sosai har kusan shekara, su da ba sa yin shekara a waje sai gashi har shekara na biyu ta same su a garin, kusan shekaru uku kafin Usmanu Djibo ya warke sosai. Karamci da kuma yanayin garin ya sa dukkan su suka haɗa baki su ka tsaida magana akan za su cigaba da zama a garin. Daga nan auratayya ta shiga tsakanin su da fulani 'yan asalin garin, sai aka haɗu aka zama guda.


Kakan T J wato Modibbo Muhammad yana da mata ɗaya Rumaysa'u wacce ake kira Daadawuro, 'ya'yan su biyar Allah ya ma ta rasuwa wannan ya sa aka aura ma sa ƙanwarta Fatima da su ke kira da Yadikko.  

Fatima, Khadija, Aisha, Umar da Usman sune 'ya'yan Daada ita kuma Yadikko ɗa ɗaya Allah ya ba ta wato Abubakar.

A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda aka aurar da yara mata yara mazan ma su ka yi aure ban da Abubakar Auta. 

Usman ya auri Maryama su na zaune lafiya shekara huɗu kafin Allah ya bata haihuwa ta samu mace aka sa ma ta Rumaysa'u amma Ruma su ke kiranta. Yarinyar ba ta cika shekara ba Allah yai wa Usman rasuwa. Maryama ta shiga cikin tashin hankali, kusan gaba ɗaya iddar ta ta yi shi cikin jinya ne. Hakan ya sa ko bayan ta gama idda ta cigaba da zama a gidan dama kuma ta haɗa jini da Usman dan auren haɗin gida aka mu su. Shekaru biyu bayan rasuwan Usman Maryama ta samu nitsuwa da kwanciyar hankali, dama har da ƙuruciya da ke daminta shiyasa mutuwar ta girgizata sosai dan tana shekaru sha bakwai Usman ya rasu.


Mahaifin maryama wanda kusan ƙani ya ke ga Modibbo Muhammadu ya samu Modibbo akan ya kamata Maryama ta sake wani aure tunda dai har yanzu da ƙuruciyarta, shima dai yayi tunanin hakan, ganin Maryaman ba ta kwantar da hankalinta ba ne ya sa bai tada maganar ba. 

Wasa-wasa duk wanda aka turo ya nemi Maryama sai ta ce ba ta so. Abun ya ishi mahaifinta ya zo har gida ya ma ta faɗa ya ce daga yanzu duk wanda ya fito amincewa zai yi tunda alamu sun nuna ba auren ta ke so ba.

Yadikko ta samu Modibbo akan ko za a haɗa Maryama da Yayan mijinta wato Umar. Abin yai wa Malam daɗi sai dai wani hanzari ba gudu ba halin Umar da Usman ba ɗaya ba ne. Yayinda shi marigayi Usman ke da sauƙin kai shi Umar yana da zafi, matan sa biyu amma kullum cikin shari'a ake yi baya mu su adalci kwata-kwata.


"Ni kam ba dan kar ka ce na so kai na dayawa ba da sai na ce a haɗa Maryama da yaron wajena"


Modibbo ya kalli Yadikko yana tunanin hikimarta.

Daga nan aka tsaida magana akan za a haɗa Abubakar da Maryama wanda tsakanin su kwata-kwata ko shekara bai kai ba. Sa'anni ne dan a shekara ɗaya aka haifesu, sun ma yi wasa tare.

Mahaifin maryama yai na'am da maganar ya kuma karɓi sadaki. Amma da aka sanar da Maryama maganar ta ce ba ta san zance ba bazata iya auren ƙanin mijin ta ba. Abu dai aka ja aka ja ƙarshe dai dole ta haƙura aka yi auren.


Da ke ba son auren ta ke ba ba ƙaramin wahala ta bawa Abubakar ba, shi kuwa sarkin haƙuri bai taɓa nuna ma ta damuwa ko ya tsawatar ba. Shekara ta zo ta wuce, auren Maryama da Abubakar a suna ne amma a aikace ba wani abu da ke shiga tsakanin su. Daga ƙarshe dai tausayin Abubakar ya kamata tareda tuna nauyin da ke kanta wanda kullum Yadikko ke zaunar da ita tana ma ta nasiha, daga ƙarshe ta ajiye makaman yaƙi ta rungumi mijinta su ka cigaba da rayuwa cikin farin ciki, bayan wata shabiyar da aure suna zaman kurame.


Aishatu Indo itama 'yar cikin gida ce kuma tun tasowarta ta ke son Abubakar, lokacin auren Abubakar da Maryama tana shekara shauku a duniya. Shekara ta zago aka fara maganar aurar da ita, ta ƙeƙasa ƙasa ta ce Abubakar ta ke so ba Iliyasu da ake son haɗa su ba. Ƙarshe dai dole aka amince tunda auren Abubakar na fari bazawara ya aura. Ba a jima ba aka ɗaura auren Abubakar da Aishatu wacce ta ke ji da tashen balaga da gigin budurci. Kafin auren su, Abubakar da Maryama ba ƙaramin shaƙuwa su ka yi ba saboda halin su ya zo ɗaya kuma tun suna yara dama sun yi wasa tare, dama dai kunyar ƙanin miji ya sa Maryama cewa ba za ta iya auren sa ba.


Aishatu da falli ta shigo gidan tana son nuna ita ce aka aureta budurwa, amma ba wannan ba ne a gaban Abubakar. Maimakon ta kwantar da hankalinta ta samu soyayyar miji sai ya zama kullum cikin shiri ta ke yadda za ta muzgunawa Maryama, ko ba matsayin kishiya ba Maryama ta girmi Aishatu amma ba ta ganin wannan haka za ta rufe ido ta yi ta zuba ma ta rashin mutunci. Maryama ba ta kulata dan ta san yarinta ke damunta.


A haka dai aka yi zaman har Aishatu ta haifi ɗa namiji aka sa mi shi suna Usman amma su na kiran shi da Manga. Wannan ya ƙara sawa Aishatu girman kai da tinƙaho ganin har lokacin Maryama ba ta haihu ba. Shekaran Usman biyu ta sake samun ciki wannan karan itama Maryama Allah ya ba ta cikin sai ga shi Aishatu na haihuwa da sati biyu Itama Maryama ta haihu dukkan su kuma maza.

Ɗan Aishatu ya ci sunan Babban Yayan Aishatun wanda ya rasu a ranan da ta haihu, wato Shehu Tijjani, shi kuma ɗan Maryama ya ci su nan Kakan sa wato Muhammad su na kiransa da Gidaɗo.


Bayan Tijjani Aishatu ta haifi Zainab sannan Mukhtar da su ke kira Muntari. Ita dama Maryama irin matan nan ne da ba sa haihuwa da wuri dan sai da Aishatu ta yaye Muntari kafin ta haifi autar ta Fatima Zahra wato takwarar Yadikko. 

Ita kuma Aisha bayan Muntari ta sake haifan Halimatus Sadiya da kuma autar ta Murjanatu.


Zaman Goggo Maryama da Iya Aishatu abin dai har aka tara 'ya'ya bai ƙare ba. Ba abinda ya ƙara kunna wutar rashin jituwar su irin yadda Abubakar ya ɗauki Tijjani ya damƙawa Maryama saboda wani faɗa da su ka taɓa yi akan Tijjanin.


Kasancewar Tijjani da Gidaɗo kan su ɗaya sai ya zamana kullum suna maƙale tare kaman 'yan biyu abinci ma tare su ke ci, ko Aishatu ta zubawa Tijjani nashi haka zai ɗauka ya je ɗakin Maryama ya zauna su ci tareda Gidaɗo. Watarana suna cin abinci tare sai Aishatu ta zo ta raba su ta ja kunnen Tijjani ta ce kul ba ta yarda ya sake cin abinci da Gidaɗo ba har da cewa ta sake kama shi sai ta ma sa shegen duka. Ashe kaf abin ya faru a idon Yadikko ne, ba ta ma ta magana ba sai da Abubakar ya dawo ta ce ya je ya kwaso kayan Tijjani ya kawo wajen Maryama bai tambayi dalili ba yai kamar yadda mahaifiyar sa ta umurta.

Aikuwa Aishatu ta yi faufau ba za a bawa Maryama ɗan ta ba, ta biyo Abubakar har tsakar gida tana ta masifa.


Yadikko ta daka ma ta tsawa ta ce idan hukuncin da ta yanke bai ma ta ba ta wuce gidan su, ba za ta zo ta haɗa gaba tsakanin jikokin ta ba.

Aishatu ta yi shiru tana huci. Daga lokacin da Tijjani ya koma wajen Maryama Aishatu ta ƙi shi, ko ya zo kusa da ita sai ta dinga hantarar sa kamar ba ɗan cikinta ba. A da duk cikin 'ya'yan ta tafi son shi saboda tsananin kamannin sa da Mahaifinsa, Abubakar da Tijjani yadda ka san an tsaga kara, amma yanzu gaba ɗaya ta ƙi shi. Shi ma bai damu ba saboda yarinta ya koma ɗakin Maryama hankali kwance. Har wa yau Goggo Maryama ya ke gani a matsayin Uwa ita Iya haihuwar sa kawai ta yi amma duk wani tarbiya da ya samu daga wajen Goggo ne.


Gidaɗo Allah bai yi shi lafiyayye ba ashe ciwon sugar ya ke da shi ba a sani ba. Idan ciwo ya tashi ayita ɗura ma sa maganin gargajiya wani lokaci abin yai sauƙi wani lokaci kuma kamar ba zai yi rai ba. Yana shekara goma shahuɗu aka ma sa aure bisa shawaran manya akan ƙila aure zai sa ya samu lafiya. Wata cikin 'yar uwarsa aka aura ma sa 'yar shekara shauku. Shekaran farko kam da Gidaɗo da Hannatu an tafka kwaɓa da shirme kafin a hankali su ka samu kan zaren. Gidaɗo na shekara shashida ya rasu nan ma ciwon sa ne ya tashi ana ta bashi maganin gida sai kumburi ya ke yi ƙarshe aka kai shi Asibiti a Kano a nan likitoci su ka gano ainihin mi ke damun shi amma its too late dan ko sati bai yi ba da aka fara treating na shi ya cika.

Da rabon Asma'u za ta zo duniya ya sa aka ma sa aure da wuri dan bayan rasuwar sa aka gano Hannatu na da cikin wata biyu.


Tundaga primary school Tijjani ke da ƙwazo hakan ya sa lokacin da ya ci makarantar kwana Yadikko ke ƙorafin zai yi nisa da gida kuma Bokon ma yawanci daga primary 'yan gidan su ke tsayawa, akwai wani ɗan Kawun su Tijjanin da ya fara Sakandare ya watsar ya dawo ya cigaba da noma ya ce a ma sa aure. Ta ce ita ba ta so Tijjani yai nisa da gida.


Modibbo ya ce Tijjani ɗan Baiwa ne idan aka bashi dama zai yi ilimi sosai.

Dole dai haka ta haƙura Tijjani ya tafi boarding school. A cikin jikokin na ta ba ƙaramin son Tijjani ta ke ba har ba ta iya ɓoyewa.

Daga gama secondary school ya samu sakamako mai kyau ya kuma samu gurbin karatu a ABU Zaria inda ya ke karantar Maths and Statistics. A shekarar sa ta biyu ne Allah yai wa Modibbo rasuwa. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har ta kawo yanzu da Tijjani ya gama makaranta har ya kusa kammala bautar ƙasa.

Wannan kenan...


***


Cincirindo aka yi a ƙofar ɗakin Goggo ana son kallon Arniyar da Tijjani ya kawo gida. Daga balbali-balbali matan yayye, ƙanne da ma 'ya'yan gida haka ake ta shiga ana dubata. Babu wanda Goggo ta tankawa cikin su dan ta san neman magana su ke yi. Wa su da sun shigo sai su cewa Goggo ɗakinta ya zama najasa tunda akwai Arniya a ciki, wasu su ce indai ta yi sallah a ɗakin sallarta ba zai karɓu ba. Wasu kuma su ce mala'iku sun tsine ma ta tunda ta ba wa Arniya mafaka. Jahilci dai kala-kala.


Nkiru kam tunda aka fara shigowa ana kallon ta ana yare ta duƙunƙuna kanta jikin bango tana hawaye. Yadda su ke ma ta kaman wata alien ce a ɗakin, ko da ba ta jin Fulatanci ta san zaginta su ke yi.

Yadikko ta yi masifar amma ba wanda ya kulata sai shigowa ake yi ana turereniya...


T J kam da sassafe da ya shigo ya gaishe da Iya ta sashi a gaba da faɗa wai taji ya kawo mu su karuwa gida to maza maza ya fitar da ita. Yanada masaniya akan Baffa ya sanar da ita komai amma kuma ta rufe ido tana kiran Nkiru da karuwa. Har da cewa dan ya yi Boko ne ya tafi kudu bariki.


"Hamma idan aure ka ke so, ga mata nan birjik a garin ku sai ka je wata duniya ka ɗauko Arniya. Tarbiyan da Maryama ta ɗaura ka kenan? Allah ya kyauta amma sakayyar da ta min Allah ya isa"


Duk yadda T J ya so ya ma ta bayani ta ƙi fahimta ƙarshe ta ce idan har Nkiru ba ta bar gidan ba kar ya ƙara shigowa ɗakin ta. T J ya fita jiki a sanyaye.

Duk da gajiyar da ke tattare da shi haka ya fita daga gidan.


Zuwan Alhaji Isa gidan ne ya sa kowa ya fara ƙoƙarin guduwa. Faɗa ya farayi yana zagin su kan aikin jahilcin da su ke yi kaman ba Ahalin Modibbo ba. Idan ba su manta ba mutane nawa su ka musulunta a dalilin kyawawan halayen Modibbo. Mutane nawa ne ba musulmai ba ba kuma Fulani ba Modibbo ya bawa mafaka a gidan sa sai a kan wannan za a ringa yayaɗa magana kamar wani sabon abu ne a gidan.


"Wallahi duk wacce ta muzgunawa yarinyar nan sai na bata kashinta a hannu" daga haka ya juya ya fice, ana bashi haƙuri amma bai saurari kowa ba.


Alhaji Isa ƙanin Modibbo ne. Duk cikin su kuwa shine Allah ya bawa arziƙi, yafi kowa yawan shanu da gonakai. Yayinda Modibbo ya ke babban malami shi babban ɗan kasuwa ya zama. Shima dai gidan sa kusa ya ke da gidan Modibbo dan gaba ɗaya inda kakannin su suka zauna a nan suma suka yi ginin su. Sai dai ko ba a faɗa maka ba kana zuwa anguwar za ka san Alhaji Isa wani ne domin gidan sa ya fi na kowa girma da tsaruwa a anguwar...


Tafiyar Alhaji Isa ya sa kowa ya watse ana ta ƙananun maganganu. Sai lokacin Nkiru ta samu nitsuwa.

Kusan ƙarfe goma shaɗaya na safe sai ga T J ya dawo ɗauke da ledoji guda uku. Ɗaya kayan tea ne a ciki ɗayan kuma kayan sawa ne. Doguwar riga ne irin ta turawa guda biyu sai riga da skirt guda biyu, sai takalmi guda biyu. Ɗaya ledan kuma zannuwa ne guda uku ya bawa Goggo akan ta sa Asma'u ta raka Nkiru wajen Tela a ɗinka ma ta.


Cewa yai ta gwada kayan dan hasashen jikinta yai ya siyi kayan. Tsayawa ta yi tana kallon shi, shima sai ya ƙura mata ido.


"Barkindo da alama dai a gabanka za ta sa kayan" Goggo ta faɗa. Ya fara sosa kai ya fice daga ɗakin.


Ƙuryar gado Nkiru ta shiga ta fara gwada kayan. Duka sun mata sai doguwar riga guda ɗaya da bai shigeta ba. Takalman ma sun yi daidai.


Kusan minti Ishirin sai ga T J ya dawo ya tsaya a bakin ƙofa yana tambayar Goggo ko ya shigo ta ce Bismillah.


Nkiru ta ma sa bayanin kayan tareda godiya, ya karɓi wanda bai shigeta ba ya ce zai mayar a chanja ma ta. Ya ce akwai bread ta haɗa shayi tunda ba lallai ta iya cin ɗumame ba. Ta yi dariya lokacin da ta ji kalmar 'ɗumame'...


Haka dai kwana biyu su ka shige gida ya fara cika ana ta shirye-shiryen biki. Nkiru kam banda T J da wata Pendo wacce ke ɗan jin turanci kaɗan-kaɗan saboda ta ƙare primary ba ta magana da kowa. Pendo cousin ɗin T J ne shekaranta shauku. Tsakanin ta da Goggo da Asma'u kuwa sai maganan kurame. Asma'un ma ta fara makaranta tana primary one amma ba ta jin turanci.


A hankali ta ke karantar 'yan gida da yanayin su, abinci kam da safe, rana da dare T J ke kawo ma ta. Idan ba za ta je banɗaki ba ba ta fita tana zaune a ɗaki. Ranan da Pendo ta ce su fito ta ga yadda ake nakiya da Alkhakin biki haka matan ke ta tsura ma ta ido suna nunata da hannu. Itakan abun da su ke ya burgeta dan haka ba ta damu da yadda su ke kallon ta ba ta zuba mu su idanu tana kallon abun da su ke yi.


"Ni tausayi Boɗɗiyon Tijjani ke bani. Ashe ga mace har mace amma ba addini ba miji"

Wata daga cikin matan ta faɗi. Boɗɗiyon Tijjani ko Boɗɗiyon Hamma sunan da su ka laƙawa Nkiru kenan.


Pendo ta ce " sunan ta fa Mary"


"Ungo na ki Pendo" matar ta ma ta daƙuwa.


Pendo ta ja baki ta yi shiru...


Da yammacin ranan Muntari ya dawo daga Kano ya zo biki ƙannen sa. Ankaishi makaranta yana aji biyu ya gudo ya ce ba zai iya ba Kwanyar sa da ta Tijjani ba ɗaya ba ne. Buga-buga ya ke yi a Kanon ba wai ya zauna waje ɗaya ba ne ko yana da takamaimai abu ɗaya da ya ke yi. Ya ƙi ma ya zauna a Ringim yai noma, kaman yawancin 'yan uwansa. Ɗan Bokon da yai da kuma shiga Birnin Kano da ya ke yi ya jawo Muntari ya koma wani shaƙiyi. Shekarun sa shatara amma abinda ya ke yi da burukan da ya ɗaurawa ransa ko ɗan shekara talatin iya kaci.


Tunda ya shigo Iya ke ta masifa. Ta je za ta shiga banɗaki ne ta haɗu da Nkiru ta fito daga banɗakin shine ta fasa shiga ta shiga ɗayan.


"Wai ni kam wacece wannan ne da ta sa Iya ta cikin damuwa haka?"


"Karuwar da Hamma ya kawo mana, ni inaga mayya ce ma dan tun randa ta zo na ke fama da ciwon kai" 


Muntari yai dariya ya ce "ikon Allah Hamma Tijjani ne ya kawo karuwa har gida"


Iya ta shiga bashi labarin ƙarya da gaskiya gameda Nkiru, gaba ɗaya sai ya matsu da ya ga wannan yarinyar da ake ta magana.


"Barin je na gaida Goggo" ya faɗa tareda miƙewa tun kafin Iya ta cigaba da ƙorafi...


Wanka ta yi ta saka kaya amma ta kasa motsawa jini ne ya zo mata ta rasa ya zata yi, ba kowa a ɗakin gashi ƙila T J sai dare zai dawo. Tana zaune a ƙasa inda ta shimfiɗa wani zani kar jinin ya ɓata ƙasan duk da ta san zai jima kafin ya ratsa doguwar rigan da ta sa tunda da kaɗan-kaɗan ya ke zuwa ranan farko.


"Salamma Alaikum, Goggojiya ina baƙin na ku" ya faɗi yana kutsa kai cikin ɗakin


"Goggo i..." maganar ya maƙale lokacin da ya hango ta zauna tana yamutsa fiska. Ya buɗe ido baki hanci duk yana kallonta. Fara ce sosai dan zai iya cewa ta fishi fari nesa ba kusa ba. Kai Murjanatu da Talatun Inna Adama ake ganin farin su har yayi yawa amma wannan ta ninka su. Shi ba dan ance ma sa Inyamura ba ce da Baturiya zai kirata. Ga ta ɗan 'yar duma-duma irin matan da ya ke so ba kamar matan su na nan da su ke a bushe ba. Kitson da aka ma ta lokacin da za su yi festival a ƙauye shine a kanta, ya fara tsufa amma bai hanashi ƙasa haskaka fiskan ba. Beads ɗin da aka yi kitson da shi har lokacin suna kan ta.


"Hallo Bentiful woman. Am Muntari, small brother of Tijjani" ya faɗa tareda tsugunnawa a gabanta.


Murmushi ta yi saboda jin turancin sa, accent ɗin bahaushe ne ke bakin T J nan ma ba sosai ba amma ya iya turanci, suna full conversation ba wani gargada. Amma wannan kam ba vocabulary ba grammar ba komai, kuma yadda ya dage yana maƙe murya ka ce turanci mai kyau ya ke faɗi.


Murmushin da ta yi ya ƙara fito da dimple ɗin ta wanda hakan ya sake birkita Muntari.


"What is ya name?"


"Mary" ta amsa a taƙaice tunda T J ya ce sunan ta Mary ne Nkiru zai mu su wuyar faɗi. Shi kaɗai ke kiranta da Inkiru.


"Bentiful, me i come for Kano. Small Sister is to marriage tomorrow"


Ta gyaɗa ma sa kai tana murmushi, ya sa hannu ya shafa fiskarta yana danna wajen dimple ɗin

"Kan bala'i! wannan taushi haka"


"Muntari!" Ya ji an daka ma sa tsawa.

Ita kanta Nkiru sai da ta tsorata.

A fusace ya ƙariso yana huci kamar mayunwacin zaki.


"A wani dalilin za ka taɓa ma ta fiska"


"Hamma kawai"


"Ka shiga taitayinka Mukhtari. Dan ba ta sallah ba shine zai sa ka dinga taɓata yadda ka ke so ba, ba muharramanka ba ce ka kiyaye" ya faɗa kaman zai make Muntari


"Mi ya ke faruwa?" Goggo da ta shigo ta ke tambaya. 


"Ba fa abinda na yi Goggo, na ga baƙuwa a ɗakin ne na ke gaisawa da ita"


"Fita a ɗakin nan" ya faɗa da ƙarfi. Muntari ya fice yana tsaki.


Ganin ba shi da niyyar magana ne ya sa Goggo cewa "Allah ya baku haƙuri"


Daga tsaye ya fara yiwa Nkiru faɗa akan ka da ta yarda ta bari wani namiji ya taɓata babu wani ƙwaƙwƙwaran dalili ko da kuwa shi ne. Bai jira mi za ta ce ba ya fice a ɗakin.

Yana shiga ɗakin sa ya kasa zaune ya kasa tsaye, hannun Muntari kawai ya ke gani a fiskar Nkiru. Zuciyarsa tana wani ƙuna. Yarinyar kam akwai ta da wauta ko dan saboda ita ce 'yar fari, amma bai ɗauka wautan ta ya kai har ta tsaya Muntari ya dinga shafa ma ta fiska ba tare da ta buge hannun ba. Wata zuciyar ta ce ma sa " ka ma ta uzuri, addinin ku ba ɗaya ba haka yaren ku ba ɗaya ba ne" sai dai duk da ya tuna da hakan zuciyar sa ba ta yi sanyi ba. Buga ƙofar sa da ake yi ne ya sa shi dai na sintirin da ya ke a ɗakin.


Asma'u ce ta gaya ma sa saƙon Goggo nan da nan ya fice da sauri...


Kuka sosai ta ke yi lokacin da ya shigo.

Tsugunnawa yai a gabanta yana jin wani abu na zungurar shi a zuciya.


"I'm sorry Inkiru" ya faɗi da tausashashshiyar murya. Shi kan sa bai san dalilin yi ma ta wannan faɗan ba.

Rarrashinta yai ta yi har ta yi shiru. Ganin ta dena kuka ne ya sa shi tashi zai tafi sai ya ji ta kira shi a hankali "Teejay" 

Ya kalli idonta wanda ke birkitashi tun haɗuwar su.


"I'm i'm" sai ta rasa bakin magana, yadda ya tsareta da ido ya sa ta ji kunyar gaya ma sa abinda ta yi niyya.


"What?" Ya ɗaga ma ta gira


"My p p period" ta faɗa tareda rufe fiskarta da tafukan hannun ta.


Murmushi yai ya ce bari ya kawo ma ta takarda sai ta rubuta ma sa abinda ta ke buƙata.. 



*har yanzu fa sharan fage ake a labarin*


*Ga Hamma Tijjani ga kuma Muntari duk idon su ya ƙyasa da Mary-Nkiru*