ZAYTOONAH

I'm not leaving

by @azizat


*Chronicles of*

*...... ...... .......ZAYTOONAH*

Rubutawa.....Azizat

Wattpad@Azi_zat

     

*Free page*

*4-i'm not leaving*

Anyi biki lafiya ankai yara ɗakunan su. A sashen Baffa Abubakar kam duk yaran sa mata ya aurar. Dama Murjanatu kaɗai ta rage kuma anyi tareda wasu 'yan uwanta biyu, yanzu saura auren Tijjani da Muntari. Har gara Muntari da alamu yana da niyyar yi nan kusa amma T J kam tunda ya fara Jami'a baya so a ma sa maganar aure. Ba wai ya girma sosai ba ne dan shekarun sa ashirin da uku amma kasancewar yawancin samarin familyn na su daga shatakwas, ishirin zuwa ishirin da ɗaya za ka ga sun yi aure. Mata kuma a ta girma dayawa agida shine shekara shashida.

Yau ta ke Christmas, duk da mabiya addinin Christianity ba su da yawa a garin hakan bai hana anƙi yin hidima ba. Iyalai da su ke celebrating wannan rana tun da dare ake ta murna ana ta shirye-shirye.

A jiya da daren ne T J ya kawowa Nkiru kyautar ta ya ce ka da ta buɗe sai safiyar christmas. With full excitement ta kwana tana tararradin mi T J ya siya ma ta. Da safe kuwa tana tashi gift ɗin ta buɗe da mamakin ta sai ga Bible sai kuma ɗan ƙaramin box wanda ke ɗauke da ɗan kunne da sarƙa. Ta fara shafa sarƙan tana murmushi lokaci guda kuma ta tuna da iyayenta. Ta tuna yadda su ka celebrating christmas ɗin su last year, ta tuna yadda su ka decorating christmas tree ɗin su. Ta goge hawaye tana fata Daddy and Mommy su na heaven su na kula da ita shiyasa su ka turo ma ta mutumin kirki ya taimaka ma ta.

Bayan ta yi wanka ta shirya cikin atamfar da T J ya siya ma ta wanda jiya aka karɓo ma ta ɗinkin. Ta sa kayan riga da skirt amma ta ka sa ɗaura ɗankwalin duk yadda ta ɗaura sai ta ga bai ma ta ba. Tana ganin Pendo na ɗaurawa amma ba ta ɗauka da wuya haka na. Ta san balbalin su Pendo amma ba ta son zuwa saboda Innar Pendo ba ta son ganinta, da sun zo da Pendo za ta fara yare tana tofe tofen yawu kamar ƙyamar Nkirun ta ke.

Tana haka sai ga T J ya shigo ɗakin da sallama. Goggo ba ta ɗakin Asma'u kuma ta je wanka. Tsayawa yai yana kallonta yadda ta yi kyau cikin kayan Hausawa.

"Thank you Teejay, i like the gift"

Ta faɗa bayan sun gaisa.

Tambayarta yai ko ta shirya ta ce ta shirya amma ta kasa ɗaura ɗankwali ko ta barshi a gida ne. Ya ce a'a bari ya kira ma ta Pendo. Ya fita da sauri.

Shi da Pendo su ka dawo yana tsaye har Pendo ta ɗaura ma ta ɗankwali sai gashi ta dawo Bahaushiya sak, kayan sun sake fidda kyan ta.

Ta ɗau Bibble ɗin da ya ba ta su ka fita. Wannan ne karonta na farko da ta fita daga gidan har anguwar ma, suna tafiya T J na ma ta bayanin yanayin zamantakewar 'yan garin.

Gidan su abokin sa Okafor su ka je, sun ma shirya dama shi su ke jira. Bayan ya gaisa da Papa da Mama Okafor sannan ya damƙawa Okafor amanar Nkiru yana jan kunnen sa akan ka da ya bari wani abu ya sameta. Okafor yai dariya ya ce ai Nkiru ƙanwar sa ce ba zai bari wani abu ya sameta ba. Yana tsaye su ka wuce church dan gudanar da bauta a safiyar ranar christmas. Sai da ya ga sun ƙule ma sa kafin ya bar wajen yana jin kamar ya bi su church ɗin.

Shiru-shiru yana ta tsumayin dawowar Nkiru amma shiru har yamma lis babu alamun ta hakan ya sa ƙarfe shida na yi ya wuce gidan su Okafor. Yana zuwa ya samu Iyayen Okafor da ƙannen sa amma babu Okafor da Nkiru. Wai ba su dawo daga church ba, hankalinsa ya tashi wani irin church ne tun safe har dare. Ya bar gidan ransa a ɓace ba tareda ya mu su sallama ba. Ya san church ɗin ai, zai je koma miye ne ya ga ni. Sai dai ko da ya je an tashi, church ɗin ma a kulle ya ke. Kan sa wani juyawa yai ya fara jin wani jiri-jiri. Ba abunda ya hango irin hoton Okafor da Nkiru tsaye ana ɗaura mu su aure gashi har Okafor ya sa ma ta zobe. Bai san ya aka yi ya bar church ɗin ba ya dawo gida, da ƙyar ya je yai sallar Magariba, da ya dawo ya sake leƙa ɗakin Goggo amma su ka ce ba ta dawo ba. Ya fito ƙofar gida yana dakon dawowanta lokaci zuwa lokaci yana duba agogo.

Bayan ya dawo daga sallar Isha ne da ya leƙa ɗakin ya ganta zaune tana naɗe kayan da ta cire.

Tsabar yadda zuciyarsa ke tafarfasa ya rasa ma mi zai ce ma ta. Ga shi fiskarta ko alamun ta damu da daɗewar da ta yi bai ba.

"Nan gaba ki dinga dawowa da wuri" ya faɗa yana danne ɓacin ran sa. Ta fara ma sa bayanin dalilin da ya sa ba ta dawo da wuri ba. Pastor ne ya buƙaci ganinta shine Okafor ya kaita gidan sa bayan an tashi daga church to shine bayan sun ci abinci ya tambayi labarinta ta gaya ma sa shine yai ma ta addu'a tareda cewa ta dawo gidan sa da zama ko kuma gidan su Okafor saboda za ta fi samun nitsuwar yin Bauta.

Tunda ta fara bayani ya ke kallon ta yana jin wani fargaba na taso ma sa musamman ma da ya tuna hasashen da yai ɗazu.

Bai ce komai ba ya tashi ya fita ba tareda ya ji ƙarashen bayanin ba.

Ta ɗauka abu zai je ya yi ya dawo amma har ta yi bacci bai dawo ba. Washegari da ya zo ya gaishe da Goggo ba ta tashi ba saboda gajiya sai kusan ƙarfe takwas ta tashi. Wasa-wasa har rana ba ta ga ko ƙeyar T J ba. Muntari ne ya shigo ya ma ta sallama akan zai wuce Kano, sai da ta sha dariya sosai saboda turancin sa. Shi kuwa ganin tana dariya sai ya dage yana ta zuba labari. Da zai tafi har da ma ta alƙawarin zai dinga zuwa duk sati yana dubata, shi da ya ke tafiya yai wata ɗaya biyu bai leƙo gida ba amma yanzu wai zai dinga zuwa duk sati.

Yammacin ranan Okafor ya zo gida ya aiko aka kirata. Gidan pastor su ka je, wannan karan ma ƙoƙarin convincing ɗin ta su ke akan ta bar gidan su T J amma ta ƙi cewa ta yi idan ta bar gidan su T J ba ta mu su adalci ba.

Su kuwa su Pastor sanin gidan ne ya sa su ke tsoron zamanta a gidan musamman saboda sashin Modibbo da ta ke zaune. Zamanin Modibbo anyi babban malami, 'yan uwansa kaf ɗin su kiwo da noma su ka ba wa muhimmanci amma shi karatun addini yai mai zurfi shiyasa ma ake kiransa da Modibbon saboda malami ne masani sosai akan addini. A zamanin sa ya yi sanadiyar musuluntar da mutum tara. Tsoron su kar zaman Nkiru a gidan ya sa ta musulunta duk da kuwa yanzu babu Modibbo a gidan.

Ita dai duk yadda su ka yi da ita ta ƙi, ƙarshe su ka fito ma ta da wani salo akan ta dinga zuwa tana yini da su saboda su san juna sosai. Ba tareda ta kawo komai ba ta amince da hakan. Da za su tafi Pastor ya ja Okafor gefe ya ƙara jaddada ma sa akan maganar su ta jiya.

Ƙarfe tara ya wuce lokacin da su ka iso ƙofar gidan. Hamma Tijjani na cikin wasu abokanan sa ana hira amma shi hankalinsa na kan hanya yana baza ido ya ga dawowar Nkiru, ya ga fitan su ɗazu da ya ke dawowa daga masallaci.

Hango su da yai ya sa shi tashi ya shige gida. Baccin kirki bai iyayi ba, yana so yai baccin ko dan ya samu sauƙin abinda ke damunsa amma ya ka sa. Yana son mata magana amma bai san mi zai ce ba, duk yadda ya juya abun shine bai da gaskiya Nkiru na da daman komawa gidan su Okafor saboda ɗan uwanta christain ne kuma yaren su ɗaya duk da sun zo daga gari mabanbanta. Amma kuma bai yarda da Okafor ba, to miye na shi a ciki tunda ita ta zaɓe shi sama da shi. Haka dai yai ta tunani kala-kala har daga baya bacci ya sace shi.

Washe gari da ya shigo gaishe da Goggo ne Nkiru ta tambayeshi ina ya je jiya bai leƙo ta ba. Wani kallo ya watsa ma ta sannan ya tashi ya fita. Jikinta yai sanyi ta lura kwana biyun nan baya kulata amma ta rasa dalili. Ƙarshe ta fara zargin ko ya fara gajiya da ɗawainiyar da ya ke ma ta ne, sai kuma ta yi saurin kauda zancen da cewa Teejay ba zai yi ma ta haka ba.

Da rana ya dawo daga sallar Azahar ya shigo ɗakin Goggo ta ce ma sa Pendo da Nkiru sun fita za ta raka Nkirun kitso. Ba su gama zancen ba sai ga Pendo ta shigo ɗakin. Ganin ita ɗaya ne ba Nkiru ya sa T J tambayarta ina ta bar Nkirun. Pendo ta ce ma sa sun je gidan kitson ne matar ta ce ba za ta yiwa Arniya kitso ba, wai ance idan ka yiwa Arniya kitso kana da zunubi. T J girgiza kai da jin jahilcin mutanen na sa. Ya ce "sai ki ka bar ta a ina?"

"Mun kusa isowa gida ne mu ka haɗu da abokin ka shine ta bishi"

"Okafor?" Ya faɗa a fusace

Ta gyaɗa ma sa kai. Da sauri ya fice ɗakin Goggo da Pendo su ka bi shi da ido. Sai da yai tafiya mai nisa kafin ya tsaya. Zuciyar sa ce ta faɗa ma sa babu amfanin zuwa gidan su Okafor, Nkiru da kan ta ta bishi miye na shi a ciki, idan ma gaba ɗaya za ta koma chan kaman yadda Pastor ɗin su ya buƙata ai ba matsala ba ne. Haka ya juya ya koma gida zuciyar sa na tafarfasa. Ranan ma dai bai sake kulata ba, sai dai duk da haka hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ga ta dawo gida kusan ƙarfe biyar na yamma.

Da safe da ya shigo ma tana gaishe shi haka ya amsa ko kallon ta bai yi ba. Goggo tana lura da shi kwana biyun nan  yadda ya ke share Nkiru. Ba ta dai ma sa magana ba ne amma yau kam ta kasa yin shiru.

"Barkindo yarinyar nan ta ma ka laifi ne?"

Duk da ya san wa ta ke magana akai amma ya dake ya ce "wa ce yarinya kenan?"

"Ungo na ka Barkindo"

Yai dariya ya ce "Goggoji na cewa ki ka yi yarinya, zai iya zama Asma'u, Pendo, Kulu, Hadiza... kai yara mata a gidan nan ai dayawa"

Ganin ya raina ma ta hankali ya sa ta ce "koma wacece dai abu ɗaya zan gaya ma ka. Ka ga kai ka kawota garin nan kuma a duk faɗin garin nan babu wanda ta yarda da shi sama da kai. Idan har za ka dinga nuna ma ta fushi ba tareda ka sanar da ita laifin da ta yi ba za ka sa yarinyar ta tsaneka. Kwana biyun nan kullum sai ta yi kuka ko mi ya ke damunta na san ya na da alaƙa da kai. Idan laifi ta yi ka gaya ma ta sai ta gyara amma sai ka shigo min ɗaki kana ta kumbure-kumbure, ba abinda hakan zai haifar"

"Ni ba na fushi da kowa"

"Tashi ka bani waje, Ja'iri"

T J ya fita yana dariya.

Tana ganin ya fita ta fara matsa ƙwallan da ya taru ma ta. Miyasa ita kaɗai ne ya ke ɗaurewa fuska? Rabon da ya ma ta murmushi tun ranan christmas...

***

"Asma'u tashi ki kai wa Hamma ki ce ya zo ya tambayi boɗɗiyon sa ko za ta sha furan na ga sai kallona ta ke lokacin da na ke damawa"

Yarinyar ta tashi tana ɗan kumburi dan ba a fara bata na ta ba sai na Hamma Tijjani ta ɗau ƙwaryan ta fice da sauri. Ba ta jima ba ta dawo da ƙwaryan wai ba ya ɗaki.

Asma'u ta ɗau na ta ta fara sha. Goggo ta miƙawa Nkiru nono da fura wanda tunda ta fara damawa ta zuba ido tana kallon duk wani motsinta.

Suna sha Goggo ta tsinkayi muryan T J yana yiwa kakar sa Yawuro tsiya. Maganar aure ta ke masa shi kuwa ya dage ita zai aura.

"Maza tashi ki kai ma sa ya dawo"

"Assalamu Alaikum, ga ni nan a bani rabona"

Ta ce an duba shi ɗazu baya ɗaki.

"Asma'u tashi ki kai ma sa"

"Batta tasha a hankali, Nkiru za ta kawo min"

Yai wa Nkiru magana akan ta ɗauka ma sa kindirmon. Ta tashi da sauri ta ɗauka ta bi bayan sa.

Tana ajiye ƙwaryan ya kira sunan ta a hankali "Inkiru" ta ɗaga jajayen idonta ta kalle shi.

"Will you like to taste it?"

Ta gyaɗa ma sa kai da sauri

Ya buɗe ƙwaryan ya ɗau ludayin da aka ɗaura a kai ya ɗebo kaɗan ya kai saitin bakinta. Ganin ta tsaya tana kallon sa ne ya sa shi gyaɗa ma ta kai hakan ya sa ta buɗe bakinta ta ɗan kurɓi furan.

"You like it?"

"Its sugary" ta faɗa tana murmushi

"Bafulatanin kenan" ya faɗa yana murmushi shima

Sauran na ludayin ya kai bakinsa ya shanye, ya sake ɗebo wani wannan karan sai da ya sha ya rage sannan ya miƙa ma ta ta sha. A haka a haka har su ka shanye furan ba tareda wani ya yi magana ba. Ta ji daɗin furan duk da ma sugar ɗin ciki ya yi yawa.

Gefen bakinta akwai sauran furan dan haka ya sa babbar yatsar sa ya share ma ta. Shi kan sa bai san ya aka yi ya yi hakan ba. Its like tunda ya haɗu da yarinyar nan akwai wasu notinan kansa da su ka kunce. Ranan da ya fara ganin ta tana rawa a daren ranan sai da yai mafarkin ta, abun ya bashi mamaki sosai. Tunda ya ke bai taɓa sa wata mace a rai har ya yi mafarkinta ba. Lokacin yana undergraduate akwai wata Helen 'yar Auchi, haka ta nace ma sa wai tana son shi, bai taɓa jin wani abu gameda ita makamancin wanda ya ke ji yanzu ba, ya zo ajin ƙarshe ma ya taimakawa wata yarinya Hamdiyya 'yar Bauchi itama ta zo ta fara liƙe ma sa wai su yi soyayya. Shi tun da ma da yanzu mata ba sa gaban sa amma Nkiru is different. Ya rasa ko tausayinta da ya ke ne ya jawo ya ke jin abinda ya ke ji gameda ita oho.

Itakam tunda ta ji yatsar sa a daidai bakinta ta sandare a wajen. Tunaninta kissing ɗin ta zai yi, there's something in his eyes that's so inviting.

"Saura kwana goma na koma Obowo, fatan kin shirya" ya katse shirun na su

"Mmm" kawai ta ce

"Ko kin fasa tafiya ne? za ki koma wajen Okafor, probably ki raising family da shi?"

"No" ta faɗa da ƙarfi tana zaro ido

"Then why Inkiru? Miyasa ki ke zuwa gun sa kullum ki daɗe, kin san yadda na ke ji kuwa idan na zo na samu kin fita?"

Ta girgiza kai

"Ina tsoro kar wani abu ya sameki Inkiru, ba zan taɓa yafewa kai na ba. Ban ce kar ki je gidan su Okafor ba ko kar ki je wajen Pastor amma..." ganin hawaye a idonta ya sa shi kasa ƙarisa maganar.

Sai yanzu ta gane miyasa ya ke fushi da ita ashe saboda fitan da ta ke yi ne.

"I'm sorry" ta faɗa in between tears.

"Ba na son kuka kin ji" ta gyaɗa kai tana share hawayen...

Daga ranan su ka shirya kamar da, sai dai kuma daga ranan Nkiru ta shiga wani hali na fargaba. Ba komai ba ne face tafiyar su da ta ke matsowa kusa, daga ta tafi shikenan ba za ta sake ganin T J ba. Maimakon fitan da su ke da Okafor yanzu da shi su ke fita yai ta nuna ma ta wajaje musamman gonakin su. Har gidan gonan Alhaji Isa sai da ya kaita a nan ta ga yadda ake matsar madaran shanu itama ta gwada matsawa. Ranan sunday kuwa shi ya raka ta har bakin church bayan awa uku ya dawo daidai an fara fitowa kenan, suna fitowa kuwa ta hangoshi, ko sauraron Okafor ba ta yi ba ta je ta sameshi su ka wuce gida.

Da yamma sai ga Muntari ya dira a gidan abun mamaki ko ɗakin Iya bai shiga ba ya wuce ɗakin Goggo. Yana zuwa kuwa jiki har rawa ya ke sanda ya ke kunce jakar sa. Tsarabar Gurasa, kilishi da dabino yai wa Nkiru wacce tun randa ya bar garin ta ke ran sa.

Goggo ta ce "ikon Allah" ganin yadda Muntarin ke ta rawan jiki a gaban Nkiru.

Ba ta ida mamaki ba sai da ta ga ya yagi kilishi yana ƙoƙarin turawa Nkiru a baki yana cewa ta ci ita kuwa tana girgiza kai.

"Muntari ba na tunanin ka yi sallar la'asar, ka wuce masallaci ko raka'a ɗaya ka samu"

Ya miƙe yana cewa "kar wanda ya taɓa kayan nan na Mary ne, ita kaɗai na yiwa tsaraba"

Goggo ta ce ta ji.

Bayan fitar sa Goggo ta sauke ajiyar zuciya tana fatan abinda ta ke tunani ba gaskiya ba ne...

Daga masallaci kuwa ya dawo zai shiga ɗakin Goggo, Iya ta ƙwala ma sa kira. Bai sake samun sarari ba sai chan dare. Yana shigowa ya ga T J a ɗakin, ya yi narai narai da fiska yana tambayar Nkiru ko ta ci abinda ya kawo ma ta ta ce ta ci. Ba ta ma ci ba sai da T J ya zo ta nuna ma sa ya ɗau kusan fiye da rabi ya ba wa Goggo ya ce a rabawa 'yan gida. Nkiru kam dabino kaɗai ta ci ba ta ci kilishi da gurasan ba. Shi kuwa T J haka ya haɗa gurasa da kilishi yai ta ci yana addu'ar Allah ya saka wa Muntari, wannan karan yayi abun kai.

"Hamma ina son magana da ita"

T J ya juya ya kalli kan gado Asma'u ta riga ta yi bacci Goggo kuwa ta wuce turakar miji saboda ita ke da girki.

"Ban gane ba"

"Ina son magana da Mary"

Abun ya bashi dariya amma ya dake ya ce "ga ta nan faɗi maganar ka"

"Hamma waje za ka bamu, maganar ta mu biyu ne"

T J ya ce " lallai kana da aiki"

Ya cigaba da koyawa Nkiru gaisuwar Fulatanci.

Ganin an maidashi wani shashasha ya sa shi barin ɗakin kamar zai fashe. T J bai kawo komai a ransa ba dan ya ɗauka irin shiriritan ƙanin na sa ne da ya saba. Sai kusan goma ya bar ɗakin...

Washe gari aka yiwa su T J rasuwa dan haka ranan kam gaba ɗaya Nkiru ba ta gan shi ba. Duk da ba a na su sashen ba ne amma kusan kaf 'yan gidan sun fita gaisuwa aka bar Nkiru a gida. Ba abinda ke zuciyarta irin tunanin yadda za ta yi ta cigaba da zama a nan ko da dai ba wai kowa ke son ta ba amma T J yana son ta haka Goggo ma na son ta. Idan ta tafi Calabar ta kasa samun kakannin ta fa?. Ko kuma ta je sun mutu ya za ta yi kenan? Wannan tunanin shi ya ɗauke ma ta hankali wunin ranan...

***

Jaka ce madaidaiciya ya kawo ma ta ya ce ta shirya kayanta ciki saboda tafiyar su ta jibi. "Ki tabbatar kin shirya komai saboda mantuwa"

"I'm not leaving" ta faɗa a hankali. Da sauri ya juyo saboda dama fita zai yi

"What?"

"I'm not leaving" ta sake maimaitawa wannan karan da ɗan ƙarfi. Dawowa yai gabanta ya tsugunna. Zaune ta ke a shimfiɗar ta da ta ke kwana.

Ta girgiza kai ta kasa magana.

"Na san kin fara sabawa da nan amma dole ne mu tafi, na yi alkawarin zan maida ke na kai ki har Calabar..."

"Idan ba mu same su ba fa? Ina zan je? Chief James Asibong ba shi ɗaya ba ne a Calabar, tukunna which part of Calabar za mu fara zuwa?"

Tanada gaskiya amma kuma...

"Tunda mu ka haɗu ka ke mun ɗawainiya, kuma ko da mun koma ɗawainiya za ka yi ta yi da ni. Ba na son ka shiga ƙunci saboda ni, ka bari na zauna a nan na nemi aiki idan na tara kuɗi sai na tafi ka ga ko da ban same su ba zan fara sana'a ko kasuwanci da abin da na tara"

"Inkiru..."

"Shekara ɗaya, biyu, uku, i dont care, indai za ka amince zan zauna a nan. Zan yi kowani irin aiki ne, kowani iri"

Shiru yai ya rasa mi zai ce.

Ta sa hannunta ɗaya a kan hannun sa da ke kan cinyarsa ta ce "please Barkindo"

Ya kalleta cike da mamaki. Ta gyaɗa ma sa kai ta ce Pendo ce ta gaya ma ta Kakansa ne ya ke kiran sa da Barkindo shiyasa wani lokaci ta ke ji Goggo na kiran sa da sunan.

Shiru ne ya ratsa ɗakin, ba kuma dan ya rasa abin faɗa ba ne sai dan wani lissafi ya ke yi a ƙwaƙwalwarsa. Mi zai faru idan Nkiru ta cigaba da zama da su?

*ba a fara komai a chronicles of Zaytoonah ba*