Maryam
by @azizat
*Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*
Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat
*Free page*
*5-Maryam*
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ba abu ne mai sauƙi ba amma kuma zai yi komi domin ta samu farin ciki. Fasa tafiyar sa ya zo da kace-nace a cikin gida sai dai kuma bai damu ba tunda ya tabbatar buƙata za ta biya. Kwana takwas ya ƙara kafin ya koma chan Obowo, cikin kwanaki takwas ya nemawa Nkiru aiki a wata primary school na gwamnati, ba a dai ɗauketa officially ba saboda ba ta da takardar shaidar karatu amma ance da zaran ta samu takardun ta za a aika ministry a ɗauketa aiki. Kafin nan kuma za ta dinga aiki ne ana ba ta ƙaramin allowance duk ƙarshen wata. Takardunta ba za su samu ba saboda ta baro su a gidan su da ke Owerri, wanda ya rage ma ta mafita ɗaya wato sai dai a sake turo mata takardun daga chan makarantar su, gashi da primary school da high school ɗin duk a England ta yi. Graduation ɗin su ma ko wata biyu bai yi ba su ka dawo Nigeria.
Ranan da T J ya tafi ta sha kuka sosai dan ji ta ke kamar idan ya tafi ba zai dawo da wuri ba. Ba ta san T J ya shiga ranta har haka ba sai ranan da ya tafi, ji ta yi tamkar ya tafi da zuciyar ta ya bar gangan jikin a Ringim.
*"Ba na son ki rinƙa yin dare a waje, ban yadda ki keɓe ke kaɗai da Okafor ba. Banda zuwa church da dare.."*haka yai ta jero ma ta sharuɗɗa safiyar ranan da zai wuce.
Wasa-wasa sai gashi an shafe sati ɗaya da tafiyar sa tun tana kuka har ta dena ta maida hankali ga koyarwan da ta ke yi. Okafor bai dena bibiyarta ba dan ko ta je church haka zai liƙe ma ta, ga pastor ma ya nace akan sai ta bar gidan su T J. Ita yanzu banda kitso ba abinda ke kai ta gidan su Okafor, the more ya ke son kusanci da ita the more ta ke ƙara ja baya da shi.
A gida kuwa ba a sati ɗaya ko biyu Muntari bai zo ba, tun Iya ba ta gane saboda Nkiru ya ke zuwa ba har ta gane ta dinga faɗa tana zage-zage shi kuwa ya kwantar ma ta da hankali akan yana hakan ne saboda yana so Nkiru ta musulunta, idan Nkiru ta musulunta ta dalilinsa ai sunan gidan su zai ƙara daraja ƙila shima a fara kiran sa da Modibbo Muntari. Da wannan ya samu ta sauko amma duk da haka sai da ta ce ya rage shiga harkanta.
A wajen Nkiru kuwa ganin Muntari ta ke a matsayin mutum mai barkwanci shiyasa ba ta taɓa damuwa da zuwansa wajenta ba ko kuma yawan tsaraba da ya ke kawo ma ta idan ya zo.
Shi kam Muntari sai da ya je wajen malamai ɗai-ɗai har uku aka tabbatar ma sa zai iya auren Nkiru dan haka ya zage damtse yana ta buga-buga, burin shi nan da shekara ɗaya zai siyi gida a Kano ya auri Nkiru su dawo Kano tare, ko ta musulunta ko ba ta musulunta ba ba ruwansa ba ne wannan, shi dai ya ga Nkiru kuma yana son ta ko a yaya ta ke.
A hankali Nkiru ta fara sabawa da rashin T J ta kuma zage tana koyon Hausa da Fulatanci. So ta ke ta impressing T J idan ya dawo, malamai 'yan uwanta musamman Mr Kabir da Malam Abdullahi su su ke taimaka ma ta take koyo dan har littafi ta ke da shi na darasi.
A gida kuwa tun ana magana akan zaman Nkiru a gidan har aka zo aka saba aka ma dena maganar, har idan ba a ji ɗuriyar ta ba za a fara faɗin 'Boɗɗiyon Hamma na nan kuwa?'
Idan tana maimaita kalmomin da ta koya na fulatanci kuwa Goggo da Yadikko su na shan dariya, wani lokaci su gyara ma ta ta fahimta ko da ba Pendo ko Yakubu wani shima da ya ke ɗan jin turanci a gidan da zai ƙara ma ta bayani da turanci.
A zamanta kuwa ta lura akwai wata mata wacce kamannin Muntari ta ke da shi shiyasa ta ɗauka mahaifiyar sa ce, matar ba ta son ta ko kaɗan da ta ganta za ta fara tsuke fiska tana yare. Idan ta gaidata da Fulatanci ko Hausa kuwa sai ta kama masifa hakan ya sa ta dena gaisheta. Kwatsam ranan su na hira da Pendo ta ke cewa Maman T J wato Goggo kenan ta fi Maman Muntari kirki. Pendo ta kwashe da dariya ta ce ai T J da Muntari mamansu ɗaya ne kawai dai T J ya girma a hannun Goggo ne. Abun ya ba wa Nkiru mamaki...
***
Lokacin da T J ya tafi wata uku da sati uku ya rage T J ya gama bautar ƙasar sa amma haka ya dinga ganin kwanakin nan kamar ba sa tafiya. Ba ranan Allah da za ta fito da ba zai wuni da Nkiru a ransa ba. Tun da ya ba wa Eze labari kuwa Eze ya samu abun tsokanar shi yana cewa ya faɗa soyayya. Shi dai bai gaskata hakan ba ya dai san yana jin tausayinta.
A wani weekend me ya sa Eze ya rakashi ƙauyen su Nkiru inda su ka bibiyi labarin Uncle Udodiri. Da ke Eze ma igbo ne ba su sha wahalar samun information ba. Augustus Udodiri ya koma Owerri da zama bayan ya yiwa Yayan sa da matar sa burial na gani na faɗa a ƙauyen. Har shanu biyu aka kashe a wajen burial ɗin abinda ba a taɓa yi ba a ƙauyen na su. Da su ka tambayi maganar 'yar Patrick da Caroline cewa aka yi ta gudu saboda kunyan kashe iyayenta da ta yi. Wasu kuwa sun ce ma ta mutu ne.
Haka dai su ka bar ƙauyen cike da jimamin wannan Al'amari, sun so haɗuwa da Elizabeth amma kuma ance ta tafi wani church program a Enugu...
Tunda su ka ci wata biyu T J ya fara lissafin kwanaki. Kwanakin na matsowa yana ƙara fargaban abinda zai tarar idan ya je gida. Tsoron sa kar Nkiru ta koma mu'amala da Okafor duk da ya hanata, kai koma ba Okafor ba wani ɗan uwanta christain ɗin. Idan ya tuna haka duk sai ya ji ran sa ya jagule. A haka dai kwanakin su ka cigaba da tafiya.
***
Yau ma kamar kullum kitso ta zo gidan su Okafor, su na da shago nan dukkan su ke zama har da Mama Okafor sai dai ranan sunday ba sa zuwa. Ita kuwa Mama Okafor dama tana dawowa da wuri irin 4-5pm ɗin nan. Ko da ta je gidan babu kowa sai Okafor, shima fita zai yi lokacin da ta zo. Sai ya ma ta ƙarya akan ta shiga ciki Maman sa ta je maƙota ne za ta dawo yanzu, ba ta kawo komai a ranta ba ta shige ciki, shi kuwa yana shiga ya kulle ƙofa da key. Bayan ta zauna ne ya fara tambayarta akan dalilin da ya sa ta ke gudunsa ta ce ma sa ba komai. Ya ce ƙarya ne ya lura ko gida ya je ya aika a kirata sai ta sa a ce ma sa ba ta nan.
"Kina tunanin T J yana son ki ne? Ko kuma kina tunanin su za su fi mu son ki?. Barin gaya miki abu ɗaya ki ji, T J da ki ke gani ba zai taɓa son ki ba..."
"Zan je gida, idan Mama ta dawo ka gaisheta" ta faɗa tana miƙewa tsaye saboda yadda maganar sa ta fara karya ma ta zuciya.
Shima miƙewa tsaye ya yi ya matso kusa da ita ya dafa kafaɗarta ya ce "Nkiruka ki tsaya tukunna. Give me a chance, ina son ki, zan kula da ke sosai, idan ki ka amince da ni za ki ji daɗi. Ba zan taɓa goranta miki ba infact duk lokacin da mu ka tashi zuwa ƙauyen mu a Enugu zan raka ki mu je na ku ƙauyen"
Tureshi ta yi ta yi hanyar fita ya jawota da ƙarfi.
"Okafor ka bar ni, ba na son ka, na ce ba na..."
Danneta yai da ƙarfi akan kujera yana shirin ɗaga mata skirt ta fara kuka tana roƙon sa amma bai saurareta ba sai ma rufe ma ta baki da yai yana ƙoƙarin kunce belt ɗin sa.
Mama Okafor ta sa key ta buɗe ƙofa dan dama ba ta ran za ta samu kowa a gidan ba. Sauran su na shago shi kuwa Okafor da ya zo gida wanka ta tabbata ya riga ya tafi dan ya jima da barin shagon.
"Okafor!" Ta faɗa da ƙarfi lokacin da ta ga abinda ɗan ta ke shirin aikatawa.
Da sauri ya miƙe jikinsa na rawa ya fara ƙoƙarin zuge zip ɗin wandon sa amma ya ka sa. Mama Okafor ta ƙaraso ta ɗauke shi da mari.
"Shame on you Okafor"
Ta faɗa ta koma kan Nkiru da ke ta kuka. Rarrashin ta ta farayi tana ba ta haƙuri, sai da ta tabbatar ta nitsu sannan ta ɗauko ma ta zani ta ɗaura saboda skirt ɗin ta ya yage. Ba dan ta zo da wuri ba da mai afkuwa ta afku. Ta so Nkiru ta zauna har Papa Okafor ya dawo amma ta ce gida za ta je dan haka dole da kanta ta raka Nkirun har gidan su T J, a hanya ta cigaba da ba ta haƙuri tana cewa ta gafartawa Okafor ba ta san a ina ya ɗauko banzan halin nan ba.
Da ta je gida kuwa zazzaɓi ya rufeta, kewan T J ya ƙara shigarta, ashe gaskiyar T J da ya ce ta yi hankali da Okafor ta dena keɓewa da shi. Yau ba dan Mama ta zo ba da shikenan, ita ko first kiss ba ta taɓa yi ba balle wani abun daban...
Tun daga wannan lokaci ta ɗaukewa gidan su Okafor ƙafa, magana ta je gaban Pastor aka kira ta aka ba ta haƙuri amma ita ta ƙi yarda ta koma gidan, wasa-wasa ma ta fara ja baya da zuwa church ɗin. Kuɗin da su ke ba ta duk wata kuwa ta ce ba ta so saboda kuɗin da ta ke samu a wajen aiki ya isheta. Haka dai ta fara nisanta kan ta da su. Daga makaranta sai gida. Ko kitso za ta yi sai dai ta je gidan su wata student ɗin ta Folake wacce mamanta ke kitso.
Wasa-wasa sai ga shi watanni uku sun shige ana irga kwanakin dawowan T J a lokacin ne kuwa aka fara Azumin Ramadan. A nan Nkiru ta ga abubuwan mamaki, domin tana mamakin yadda dukkan gidan su ke ɗaukan Azumi har ɗokin Azumin ake yi kafin zuwan sa. Ba abinda ke ƙara burgeta irin lokacin sallar Taraweeh, daga ɗaki tana jin yadda su ke daɗewa su na sallah ga karatun da ke burgeta. Abokanan ta Malamai kam sun sha tambayoyi akan Azumi saboda ko ta tambayi Pendo ba ta iya ba ta amsa saboda ƙarancin ilimi da ta ke da shi. Ranan Azumi na goma sha ɗaya ta ce bari ta gwada Azumi tunda har 'yar Pendo ma na yi, ta ƙi cin abinci tun safe har yamma da ta gayawa Pendo tana Azumi sai ta ringa ma ta dariya ta ce gara ta ci abinci dan ba ta da lada. Ita kuwa ta ƙi haka ta kai Azumin da ƙyar.
Haka ta cigaba da ɗaukan Azumin, Pendo da Yadikko su yi ta ma ta dariya, Goggo kuwa ta ce idan tana da rabon musulunci za ta karɓa a barta ta yi Azumin tunda da kan ta ta ji tana son yi.
A ranan Azumi na sha bakwai T J ya dira a gidan. Zo ka ga murna a wajen 'yan gidan, amma duk ciki babu wanda ya kai Nkiru murnan dawowan sa. Lokacin da ya shigo gaida Goggo haka ta tsura ma sa ido tana ji kamar ta je ta rungumeshi. Shi kam bayan ya kalleta sau ɗaya bai sake waiwayarta ba, ba wai dan baya son kallonta ba ne sai dan saboda an cika ɗakin Goggon kar a ma sa sa'ido. Bayan ya fita haka Nkiru ta rakashi da ido tana ganin ya rame ma ta ko dan Azumi da ake yi ne oho.
"I miss you" ta furta a hankali.
Wannan karan ko dan saboda Azumi ne T J ba ya ba ta lokaci kamar da, kwana uku yai ya koma masallaci Ittikafi saboda goman ƙarshe da aka shiga. Hakan ya sa Nkiru ta dena ganin sa, sau ɗaya su ka zauna su ka yi hira wanda shima sama-sama ne.
Ana washegari sallah aka kawo ma ta kaya kala huɗu, ɗaya Baffan su T J ne ya siya ma ta sauran kuma T J ne ya siya. Ta ji daɗin karramata da aka yi duk da kuwa ba ta san matsayin sallar da za ayi goben ba hakanan ba ta san ya ake yi ba. Ranan sallah kuwa ya banbanta da kowacce rana da ta zauna a gidan, babu wanda bai yi shiga mai kyau ba a gidan. Ga abinci da aka yi da nama dumu-dumu a ciki. Safiyar sallah ta ga T J wanda shima ya sha ado cikin shadda light blue, ba ƙaramin kyau ya yi ba. Da yammacin sallah kuwa T J ya ɗauketa su ka fita yawo a nan ne take gaya ma sa itama ta yi Azumi har goma shabiyu.
"Ya ki ka ji da ki ka yi Azumin?" Abinda ya tambaya kenan
"I feel good" ta amsa tana murmushi...
Washe gari sai ga Muntari wai ya zo ɗaukan Nkiru wai za su tafi Kano ta ga hawan daushe. Ta ce ya tambayi T J shikuwa ya ce ba zai tambaya ba T J bai da hurumin hanata tafiya inda ta yi niyya. Ita kuwa ta ce ba inda za ta, yayi-yayi ta ce ba za ta je ba, haka yai fushi ya fita yana jin haushin T J a ran sa.
Shima T J ya so su je Kano ɗin kawai wa su lissafi yai ya ga bai dace ba a wannan lokaci...
***
"Barkindo kana da niyyar aure kuwa?"
T J ya sunkuyar da kai yana jin tsananin kunyar mahaifin sa.
"Karatu daga wannan sai wannan, shi karatun ai ba zai hana aure ba. Duk sa'anninka fa suna da mata da 'ya'ya"
"Baffa wannan karan karatun ba zai yi tsawo ba, shekara ɗaya ne zan yi na gama"
"Wallahi ana min surutu Shehu, ko dai ba ka da lafiya ne?"
T J yai saurin girgiza kai
"To dan Allah ka haƙura da batun karatun nan tukunna, ka yi aure. Idan da hali sai ka cigaba da karatun, a hakan ma ai kana cikin 'yan tsirarun da su ka kai matakin karatun ka a nan garin"
Bai san ya zai yi da ran sa ba idan ya amince da aure yanzu, bai shirya aure ba, baya tunanin zai iya zama da wata mace yanzu ko da ya zauna ba za ta samu kan sa ba.
Ya ɗan tausasa murya ya ce " Baffa idan da hali a ɗan ɗaga min ƙafa zuwa shekara ɗayan nan, Insha Allahu ina gama karatun nan zan yi aure"
"Ka yi alƙawarin bayan shekara ɗaya idan ba ka yi aure ba ni na maka?"
Ya ɗago ido da sauri ya kalli mahaifin na sa wanda ko kaɗan ba alamar wasa a tattare da shi.
"Na amince" ya furta a hankali...
Cikin watanni huɗu da T J yai kafin ya fara masters na shi ya jawo wata muguwar shaƙuwa tsakanin sa da Nkiru fiye da da. A ɓangaren Muntari ma duk wani dama da ya samu ƙoƙarin gwadawa Nkiru kulawa ya ke yi. Shi a yadda ya fara ji ma yana ga zai wa Baffa magana a aura ma sa Nkiru kawai tunda Malamai sun ce zai iya aurenta ko da ba ta musulunta ba. Hakan ya sa watarana da ya zo gida ya samu Baffa da maganar. Baffa da ya ji maganar sai da ya ƙware da ruwan da ya ke sha.
"Baffa ina son ta, ka ga idan na aure ko shekara ba za ayi ba na tabbata za ta musulunta ka ga na yi jihadi kenan"
"Tashi ka bani waje"
"Baffa.."
"Tashi na ce" haka Muntari ya tashi simi-simi ya fita yana ƙunƙuni.
Ganin bai samu kan Baffa ba ne ya sa shi komawa kan Goggo akan ta taimaka ta yiwa Baffa magana.
Haka dai Goggo ta ji maganganun sa banbaraƙwai. Amma ta san halin Muntarin na taurin kai dan haka ta ce "yo kai Muntari yarinyar nan fa ba wanda ya isa ya ma ta auren dole a gidan nan ko da kuwa musulunta ta yi. Ka cigaba da jawota zuwa musulunci ƙila idan da rabo sai ta amsa ka ga sai a zo ayi maganar aure amma yanzu kam na san ba wanda zai yarda ma ka, kuma ina tabbatar ma ka da idan Iya ta ji maganar nan sai kashin Mary ya bushe a gidan nan"
Da wannan ya sa ya chanja tunani ya ajiye maganar. Ya cigaba da kyautatawa Nkiru shi a ganin sa hakan zai sa ta ji son musulunci.
Duk abunda ake yi T J bai sani ba dan ko da ya dawo ba wanda ya ma sa maganar abinda Muntari ya faɗa. Duk sati biyu ya ke zuwa Ringim ba dan komai ba kuwa sai dan Nkiru. Shi kam yanzu ya amince da maganar Eze, ko da kuwa a da yana son ƙaryata hakan to yanzu kam duk jikinsa ya amsa da soyayyar Nkiru. Kullum addu'ar shi Allah ya kawo ma sa mafita kafin ya ƙare masters ɗin sa Baffah ya tuntuɓeshi da maganar aure. Baya ganin zai iya juran auren wata mace idan ba Nkiru ba duk da kuwa ya san hakan ba mai yiwuwa ba ne...
A haka dai lokaci yai ta tafiya har ta kai watan Nkiru goma a garin Ringim. Ba tareda wani ya tursasata ba, ita da kan ta ta ji son wannan addini, tun lokacin Azumi addinin ya fara burgeta. Yadda Goggo ke tashi tana sallar dare a goman ƙarshe abun ya tsaya ma ta a rai, gashi bauta ta ke yi amma ba hayaniya ba tashin hankali. Ta kan tambayi T J ko su Malam Abdullahi akan addinin musulunci kuma a hankali ta fara ganin girman wannan addini. Akwai abubuwa da su ka shige ma ta duhu shiyasa tun da jimawa ba ta gama amincewa da addinin ba amma a hankali komai ya fara warwarewa. Kullum tana addu'an idan addinin T J ne gaskiya Allah ya sa ta ji tana son addinin. Kuma yadda T J ke fassara ma ta wa su ayoyi hakan ya ƙara sa ma ta sha'awar wannan addini.
Wata ranan Jummu'ah ta samu Goggo da ta idar da sallar la'asar ta ce tana so ta koya ma ta sallah. Goggo ba ta gama fahimtar maganarta ba dan haka ta sa aka kira ma ta Pendo dan ta ma ta bayani da kyau.
Da Pendo ta zo ta sake maimaita zancenta. Pendo ta yiwa Goggo bayani Goggo ta ɗau Kabbara tana faɗin "ki tambayeta tana son musulunta ne? Tana son yin addini kamar na mu?"
Duk tambayar da aka ma ta sai ta ce eh.
Goggo ta sa aka nemo ma ta Baffah inda Nkiru ta sake maimaita sha'awarta na son karɓan musulunci. A yammacin ranan aka kai ta gaban malami inda ta karɓi kalmar shahada.
Zo ka ga murna a wajen 'yan gidan su T J, wanda ke ƙyamatarta a da yanzu su ne su ke ta jan ta a jiki suna ta rungumarta.
Daren ranan kuwa Muntari ya dira a gidan, a bakin Iya ya ke jin wai Boɗɗiyon Tijjani ta musulunta. Ita har da ƙarawa da cewa " ni ban yarda musulunta ta yi ba, yaudara ce kawai irin ta Arna"
Shi kam Muntari jin maganar Iya ya sa wani sanyi ya shigeshi lokaci guda, bai san ma sanda ya tashi ya bar ɗakin ba ya nufi ɗakin Goggo. Sai dai da Goggon da Nkirun ba sa ɗaki ya tambayi Asma'u ta ce ba ta san inda su ka je ba. Ɗakin Baffah ya wuce dan ya samu abunda ya jima yana muradi, maganar Goggo ta tabbata, yanzu da Nkiru ta musulunta babu mai aibanta auran su.
Yana zuwa kuwa ya ci sa'a Baffan na ɗaki " Baffa maganar kwanakin baya ne na zo da ita"
"Wacce magana kenan?"
"Auren Mary"
"Maryam" Baffah ya gyara ma sa
"Yawwa auren Maryam"...