A love marriage
by @azizat
*Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*
Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat
*Free page*
*6-A love marriage*
Bismillahir Rahmanir Rahim
"Yanzu dan Allah Muntari daga ta musulunta yau sai a fara ma ta zancen aure?. Ni ban goyi bayan haka ba, sannan duk yadda ka ke son auren yarinyar nan ba fa auren dole za a ma ta ba. Idan ta amince za ta aureka fani'ima amma idan ta nuna ɗan uwanka ko wani daban ta ke so to ka ga dole ka haƙura"
Kaman an buga ma sa guduma a tsakiyar ka haka ya ji kalaman Baffah na ƙarshe a ƙwaƙwalwarsa.
"Baffa ban gane ɗan uwana ba. Ba dai Hamma Tijjani ka ke nufi ba?"
Baffa yai shiru dan tambayar ta yi kama da renin hankali.
"Baffa idan za a min adalci, tun kan yarinyar nan ta musulunta na ce ina son aurenta ku ka hanani, yanzu da ta musulunta sai ku ce wai idan ta zaɓi Hamma Tijjani sai dai na yi haƙuri. Wannan son kai ne Baffah. Kuma ba zan taɓa yarda da ba. Ina son auren Maryam kuma Wallahi babu wanda ya isa ya hanani aurenta."
"Muntari ni ka ke faɗawa haka? Wannan yarinya tun kafin ta musulunta na ɗauketa amana a gareni, yanzu da ta shigo musulunci kuwa nauyi ya ƙara ƙaruwa mani, marainiya ce kuma na ɗauki amanar kula da ita kamar 'ya'yan da na haifa. Babu wanda zai ma ta auren dole. Tashi ka bani waje"
"Tabbas Biri yayi kama da mutum, na gane manufarku Baffah. Hamma shi ne Shalele ɗan Boko shiyasa za a bashi ita ko?, to wallahi ba zai yiwu ba. Maryam ni ta ke so kuma ni za ta aura"
Daga haka ya buga ƙafa ya fita.
Baffah ya sauke ajiyar zuciya, wani irin daƙiƙanci ke kan Muntari. Yanzu shi aka ce ya auri Maryam sai ya aura, bayan ga wanda ya kawota. Ko Tijjani bai faɗa ba sun san akwai soyayya a ƙasan ran sa gameda Maryam. Balle ko da ace wani daban ne ya kawo Maryam gidan, sau dubu Tijjani zai zaɓa ma ta saboda shi ne zai iya riƙeta amana ya kuma nutsar da ita bisa tarbiyan musulunci. Shi Muntari da Boko da Arabin duk yayi fatali da su ya shiga gari shi dole yana son yin zaman Birni, yana son yin kuɗi ba ta hanyar noma da kiwo ba.
Baffah ya kawar da zancen zucin da ya ke, ya sawa ransa yarinta ke damun Muntari da sannu zai haƙura da Maryam.
Washe gari da safe sai ga ɗan aika wai Baffa ya je gidan Alhaji Isa yana neman sa. Baffah ya shirya ya wuce gidan ƙanin mahaifin na sa. Daga zuwa sai ga Muntari zaune gaban Alhajin yana ta rarraba idanu.
Baffa ya zauna ya gaida Alhaji amma Muntari yai ƙyam ya ƙi yiwa Baffah magana.
"Shaƙiyancinka ya kai ba za ka gaida Uban ka ba Muntari?"
Muntari ya haɗe rai ya gaida Baffah sama-sama.
Alhaji ya ce " Habubakar ga ɗan ka ya kawo ƙara, wai yana son yarinya kai kuma ka ce a Shehu za ka ba wa. Miye gaskiyar magana?"
Takaici ya kama Baffah amma ya daure ya ce " Alhaji yarinyar da ake magana yarinyar da Shehu ya kawo ne kusan shekara ɗaya kenan yanzu, sai jiya Allah ya sa ta amshi musulunci. A nan wajen jiya ka min faɗa akan nauyi da ya ƙaru min na haƙƙin yarinyar da ya hau kai na, saboda ko ba komai Maryam ta zama 'ya ta. Ni ban ce zan ba wa Shehu yarinya ba, na dai ce bai dace daga ta musulunta jiya sai a fara ma ta batun aure ba. Haka nan na jaddada mi shi ba zan ma ta auren dole ba, idan Maryam ba ta son shi dole ya haƙura da ita. Iya abinda mu ka yi da shi jiya kenan"
Alhaji ya kalli Muntari ya ce " kai kuma wuyan ka yayi ƙauri har kana yiwa mahaifinka sharri ko?. Za ka zo gaba na ka yi min ƙarya"
"Alhaji ni ba ƙarya na yi ba. Baffah baya so na yayi maganar nan ne saboda ba Hamma ba ne. Yasin da Hamma ne ya ce zai auri yarinyar nan da a jiya an ɗaura mu su aure"
"Yi min shiru!"
Muntari ya haɗiye sauran maganar yana ƙyafƙyafta ido.
"Magana ta mutu a nan Muntari. Idan lokaci yayi da za ayiwa Maryam aure za'a nemeka"
Muntari ya miƙe fuu ya bar ƙofan gidan. Da Baffah da Alhaji su ka bi bayansa da kallo.
Yana zuwa ya kira Nkiru wai ta zo Alhaji Isa na nemanta. Goggo ba ta san miya ke faruwa ba ta ce lafiya? Ya ce ba ruwanta dan itama haushinta ya ke ji, ya san duk yadda aka yi harda sa hannunta a maganar da Baffah yai jiya, dama dole ta goyi bayan Hamma Tijjani tunda ita ta rene shi, tun yana shekara uku ya koma hannunta.
Nkiru ta ɗau mayafin da Goggo ta ba ta jiya ta yafa ta bi bayan Muntari. A hanya sai da ya sake tambayarta ko tana son shi ta ce ta yi dariya ta ce tana son shi.
Tambaya ne da ya ke ma ta a mafiya yawan lokuta wanda ita kuwa ta ɗauka duk cikin barkwancinsa ne, musamman saboda yanayin turancin da ya ke amfani da shi wajen tambayar.
Alhaji da Baffa suna tattaunawa sai ga Muntari ya dawo tareda Maryam.
"Kai kuma lafiyan ka?" Baffah ya tambaya tun kafin Alhaji yai magana.
Kafin ya amsa Alhaji ya ce " barshi mu ji wani rashin kunyar zai kuma yi"
Muntari ya nuna Maryam ya ce " na kawota ne ta faɗa mu ku da bakinta cewa ni ta ke so. Kunga sai a mana aure tunda ba ita da bakinta ta ce tana sona"
Baffah dai kunya ya kamashi ya sunkuyar da kai kawai yana yiwa Muntari addu'ar shiriya.
"Lallai kam, yanzu dai zamani ya kawo mu ɗan kunyan nan da ake ji ta iyaye ba ajinta yanzu. Allah ya huci ranka Muntari, bari mu ji daga bakin yarinya"
Ita dai Maryam na gefe tana ɗan cancankan maganganun su amma ba ta gane inda maganar ta dosa ba dan haryanzu ba wai yaren ya zauna a bakinta ba ne har gara ma Hausa a kan Fulatanci.
Alhaji ya ƙwalawa wa su yara da ke wasa a ƙofar gida kira ya ce su shiga gida su kira ma sa Hamza. Hamza ɗan Alhaji Isa ne kuma shima kaman T J yana da son karatu, dan yanzu haka ya ƙare Sakandare School yana son wucewa Jami'a.
Ba a jima ba sai ga Hamzan ya fito. Ya rusuna ya gaida Baffah tareda Muntari.
Alhaji ya ma sa bayani kan abinda ke faruwa a taƙaice ya ce ya tambayi Maryam ko ita ta ce tana son Muntari da aure.
Muntari ya ce " ai ba sai ya fassara mu ku ba nima nan ina jin turancin"
Alhaji ya ce " ban sa ka ba"
Hamza ya iya turanci ba kaman Muntari da ya ke turancin kame-kame ba.
Tunda ya fara bayani Maryam ta fara girgiza kai, sai da ya ma ta tambayar da Alhajin yai ne ta zaro ido ta ce "No" da ɗan ƙarfi
Muntari ya ce " No kuma?. Me i say i love you, you you say you love me. For everyday i can ask you, you say you love me harda dariya wallahi"
Maryam ta dafa ƙirji dan sai yanzu ta fahimci inda maganar ta dosa.
Ta kalli Muntari sannan ta maida duban ta ga Hamza ta ce " i never said i love him. I just said i like him. I like him because his funny"
"Banten Uba. Mary kalle ni nan. Ki ji tsoron Allah, afraid of God Maryam. We for come here i say i love you you say you like me. Miye maraban dambe da faɗa?"
Alhaji ya ce "Hamza mi ya ke faruwa ne?"
Hamza ya fara bayani cewa Maryam cewa ta yi Muntari na burgeta amma ba wai tana son sa ba ne shi kuma ya doge wai cewa ta yi tana son sa.
"Muntari ka ji abinda ta ce dan haka tashi ka bamu waje, daga yanzu na kashe maganar" Alhaji yai maganar yana kallon Muntari
"Wallahi ba zai yiwu ba. Da like da love duk ɗaya ne, ni na san Goggo ce ta kitsa wannan munafurcin, ita ta hana Maryam ta faɗi abinda ke ranta"
Baffah dai ya ka sa magana Alhaji kuma sai ya kama dariya dan buruntsun Muntarin dariya ya bashi.
Muntari har da taɓa kafaɗar Maryam ya ce " i love you, you love me we marry. Dont afraid of Goggo ko wasu 'yan baƙin ciki. We marry for love"
Idon Maryam har cikowa da hawaye yai saboda yadda Muntari ke maganar yana zare ma ta ido.
Ta ce "I'm sorry Muntari but i dont love you, i only like you as a friend"
"Friend ɗin uwarki, na ce auren ki zan yi. Marriage" ya ƙarisa maganar yana kamo hannunta.
Alhaji ya daka ma sa tsawa akan ya sake ma ta hannu. Sannan ya kalli Hamza ya ce ya cewa Maryam ta koma gida.
Har Maryam ta tashi Muntari bai bar masifa ba, har ta fara tafiya Hamza ya sake kiranta. Ta dawo jiki a sanyaye. Ba ta san miyasa Muntari ya misunderstanding maganar ta ba, ko dan baya jin turanci sosai ne?
"Tambaya min ita ko tana son auren Shehu Tijjani?" Alhaji ya faɗa fiskar sa ɗaure.
"Do you love Tijjani?"
Murmushi ne ya suɓuce ma ta, ta yi saurin sa hannu ta tare bakinta, she cant believe she actually blushed a gaban waɗannan manyan mutane.
"Do you want to Marry him?"
Wannan karan gyalenta ta jawo ta rufa fiskarta da shi tana murmushi zuciyarta na bugawa da ƙarfi ƙarfi.
Wannan kaɗai ya isa ya nuna mu su tana son T J amma sai da Alhaji ya sake cewa Hamza ya sake ma ta tambayar dan su na son gane wani abu ne.
Ya sake maimaita tambayar wannan karan ta cikin gyalenta ta ɗan leƙo ta ce "Yes"
Gaban Muntari ya buga kaman tashin nakiya.
Alhaji ya ce "Ka dai ji Shehu Tijjani ta ke so. Dan haka daga nan, daga yanzu magana ta wuce. Idan ba kai butulu ba ne ba Tijjani ba ne ya kawota garin nan?"
Muryar sa a raunane ya ce " Allah ya isa, dukkan kun nan kun ci amanata. Kuma fin ƙarfi kuka min amma Maryam ni ta ke so ba Hamma ba. Kuma..."
Yadda Alhaji Isa ya haushi da faɗa ne ya sa yai shiru sai ga hawaye na zubo ma sa. An cuce shi, an cuce shi abinda ya sani kenan...
Maryam da ta koma gida gaba ɗaya wani shauƙi da kewar T J ta ke yi gashi saura sati ɗaya ya dawo.
Da Baffa ya dawo ne ya sanar da Goggo duk abinda ake ciki ita kuma ta ce yai wa Iya magana dan Muntari yana jin maganar Iyan.
Sanda Baffah ya samu Iya da maganar ita kuwa ta ƙeƙasa ƙasa ta ce sharri ne ƙila ma Maryam ce ta shanye shi amma ba abinda zai sa Muntari ya ce zai auri Maryam.
Abu dai sai gashi gaba ɗaya gida an ɗauki zancen.
Shi kuwa Muntari daga ƙofar gidan Alhaji Isa sai gidan Sarki. Ba kunya ba tsoron Allah ya faɗi ƙarya da gaskiya akan abinda ya faru yana kuma so a bi ma sa hakkin sa.
Iyalen Modibbo ba bare ba ne a Fada dan haka Sarki ya aika sammaci.
Alhaji Isa, Baffah da Baffah Umar da Baffah Jibrillah su suka je amsa kiran Sarki. Ƙara ce dai Muntari ya kawo, nan Sarki ya ji ta bakin Alhaji Isa gameda duk abunda ya ke faruwa.
Sarki ya fara yiwa Muntari nasiha akan rashin kunya da yai wa iyayen sa amma Muntari ya ɓare baki ya ce indai a fada ma ba za a masa adalci ba zai kai kotu. Wani dogari ne ya doki bakinsa da dorina sai da gefen bakinsa ya fashe ya sake zuba ma sa a baya. Sarki ya ce ya tsaya haka.
Alhaji Isa ya ce idan dai Sarki ya yarda yana so a ɗaura auren Maryam da Tijjani a gaban Muntari saboda a rufe maganar.
Fadawa su ka yi na'am da maganar.
Nan ta ke Alhaji ya ba da sadaki aka ɗaura auren *Tijjani Abubakar Modibbo Djibo* da kuma Amaryarsa *Maryam Nkiru Uzodinma*
Wanda Maimartaba Sarkin Ringim ya zama Waliyyin Amarya shi kuma Alhaji Isa Wakilin Ango.
Har aka gama ɗaura auren Muntari bai bar hawaye ba. Shikenan ya rasa Maryam, yarinyar da tunda ya fara ganinta kullum sai yayi mafarkinta, shikenan ya rasa masoyiyar sa.
***
Duk bayanin da ake ma ta ba wani ganewa ta ke ba, maganar farko ita ta mamaye ilahirin jikinta wai an ɗaura aurenta da Teejay. Wani farinciki ta ke ji wanda ke ratsa duk wani kafa na jikinta, rabonta da irin farinciki haka tun iyayenta na raye. Auren ya ma ta banbaraƙwai tunda ita ko T J ba sa wajen aka ɗaura auren, sai kuma ta tuna irin auren su kenan ba kaman wanda ta sani da ake yi a church ko kotu ba...
Kwanakin da su ka shige ana nutsar da ita gameda addini tareda gyarata da Goggo ta farayi a matsayinta na Amarya. Wasu abubuwan kam tun tana mamakin su har ta dena. Kowa yayi na'am da auren banda Iya wacce ke ganin kamar wata ƙungurman Arniya Bamagujiya aka aurawa Tijjani. Ba ma wannan ba tun da aka yi wannan rikicin da Muntari ya tafi ba a ji ɗuriyar sa ba, ko sallama bai wa Iya ba ya tafi. Baffa kuwa ya ce kar wanda ya ƙara tada zancen abun da ya faru, idan Muntari yayi hankali zai dawo ya nemi gafaran iyayensa bisa wannan tonon asiri da ya mu su.
Sati ɗaya ake tunanin T J ya rage ya dawo gida kamar yadda ya sabayi amma bai zo a satin ba. Sai su ka ɗauka sai ƙarshen wata zai zo. Rashin zuwan sa ya sa Amarya Maryam ta ƙara jin wani matsanancin kewar sa daga ƙarshe kuma ta fara fushi da shi.
Labarin musuluntar Nkiru ya sa su Okafor da ma church members ɗin su suka shiga alhini, sun je har gida suna neman ta ba su dama su zauna da ita a tattauna amma ta ƙi ba su dama dole haka su ka tafi, gashi ana hutu balle su je su ritsata a makaranta. Yadda dai su ke tsoro tun farko sai da hakan ya faru. Pastor dai gaba ɗaya ya ɗaurawa Okafor laifi dan gani ya ke da bai yi yunƙurin yiwa Nkiru fyaɗe ba da ba za ta guje shi ba ƙarshe har ta zo ta dena zuwa church...
Ranan ashirin da tara ga watan october 1986 T J ya dawo gida, tunda ya fara masters program na shi wannan ne karo na farko da yai wata ɗaya ba tareda ya zo gida ba. Hakan ya faru kuwa saboda wani gasan Maths na sakandare schools da ake yi a garin Kaduna wanda aka sa shi cikin Alkalai hakan ya sa gaba ɗaya bai samu ya zo ba.
As usual ɗakinsa ya shiga ya ajiye jaka sannan ya wuce ɗakin Goggo, mutum biyu ya gani suna sallah a ɗakin bai tsaya gane waye ba ne saboda babu wuta fitila aka kunna a ɗakin, kai tsaye ya wuce ɗakin Yadikko wacce itama ke sallar Isha'i dan haka ya wuce ɗakin Iya. Ɗan amsa gaisuwar na sa da ta ke yi da yau bai samu ba, ya fi sau goma yana gaisheta ta yi banza da shi ƙarshe ta ce ya bar ma ta ɗaki. Ya fice daga ɗakin sumu-sumu, yana tunanin me kuma ya faru.
Ya yi sallah a hanya dan haka ya koma ɗaki ya cire kayan sa ya saka jallabiya ya fito ƙofar gida. A nan 'yan uwansa da su ka dawo daga masallaci ke ma sa barka da dawowa wasu kuma su na tsokalar sa Ango- Ango. Gaba ɗaya sai ya rikice, ba dai Baffah ya ma sa auren ba, ai shekara ɗayan da ya nema ba ta cika ba. Ganin Baffan na dawowa ne ya sa shi zare jiki ya je wajen sa yana gaisheshi. Tare su ka shiga gida inda su ka yi masauki a ɗakin Baffan.
Zuciyar sa harbawa ta ke da sauri-sauri saboda abunda ya ji a ƙofar gida.
Baffah na sane da yadda Tijjani ya ke a zabure amma ya dake yai ta jansa da hira sai daga baya ya fara ma sa bayani.
"Shehu kafin zuwan ka akwai wasu abubuwa da su ka faru, ba na so na yi tone-tone saboda ba abinda hakan zai haifar sai fitina. Na san duk hukuncin da na yanke kai mai karɓan shi hannu bibbiyu ne shiyasa ni da iyayen ka muka yanke wannan hukunci. An riga an gyara mu ku ɗakin da za ku zauna, ba a dai gama saka ma ta kaya a ciki ba amma a hankali za a sa komai tunda abune da ya zo a gaggauce. Sai ka yi haƙuri da ɗaurin auren da hidiman duk anyi babu kai"
Da Baffah zai kalli T J da kyau da zai ga yadda jikinsa ke rawa, ga gumi na tsatstsafo ma sa duk da kuwa akwai sanyi a garin.
"Maryam 'ya ta ce, ina fata za ka riƙemin ita Amana duk da na san kana ƙoƙarin hakan tunma kafin a aura ma ka ita. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a ɗayyiba. Zan yiwa Goggon ka magana a buɗe mu ku ɗakin dan babu amfanin wani jinkiri tunda kai ba mai zama ba ne"
"Insha Allahu Baffah" abinda T J ya iya faɗa kenan ya miƙe ya fita baya ma gani da kyau. Yana zuwa ɗakinsa ya kwanta yijif sai ga hawaye a idanun sa. Duk wani ɗokin ganin Nkiru da ya ke yi yanzu danasanin dawowa gida ma yake yi. Ta ina zai fara rayuwa da wata Maryam? Ta ina zai fara zaman aure da wata wanda ko sanin ita wacece bai yi ba, he has always challenged irin auren da ake mu su, auren haɗin gida duk da ma yanzu ana ɗan bari a saba kaɗan kafin ayi auren amma shi duk cikin cousins ɗinsa babu wacce zai iya cewa tana burgeshi balle har yai tunanin zaman aure da ita. Wani zazzaɓi ne ya rufe shi lokaci guda...
Tunda Baffah ya sanar da Goggo cewa a tura Maryam ɗakin mijinta ba ya son wani hayaniya ta sa Maryam ta je ta yi wanka. Da ta dawo cikin sababbin kayan da aka ɗinka ma ta ta zaɓa ma ta ɗaya ta saka aka feshe ta da turare, aka yafa mata gyale aka rufe fiskarta Goggo, Yadikko, Pendo da Inna Zulai su ka raka Maryam ɗakin ta ana tafiya Inna Zulai da Yadikko na ta guɗa.
Ɗakin dama a gyare ya ke, addu'a kawai su ka ma ta su ka fito dan ba sa jin turanci balle su ma ta nasiha.
Shiru-shiru Tijjani zai zo bai zo ba har ƙarfe goma. Tun Maryam na gyangyaɗi har ta kwanta sosai akan gado ta fara bacci garin da sanyi saboda iskar damina da ke kaɗawa hadari ne ma ya taso a garin.
T J na kwance a ɗakin yana rawan ɗari ƙaninsa wanda su ke 'ya'yan Baffanu ya shigo ɗakin. Shi ma farkon shekaran da za a shiga za a ma sa aure. Tsakanin sa da T J shekara ɗaya ne.
Ganin yadda T J ya ke rawan ɗari hakan ya sa shi ƙarasowa ɗakin da gudu.
"Lafiya, mi ya faru?"
T J ya ce "ka ce Yusha'u ya zo ya min allura Dan Allah"
"Hamma ko dai tsoron haɗuwa da Amarya ne? Ni na ɗauka ko ciwo ka ke yi aka ce an ɗaura ma ka aure da Maryam a take za ka warke"
"Dan Allah ka je, idan ba za ka je ba ko su Ƙasimu ka aike su"
"Ba Yusha'un da za a kira, ga kaza nan na siyo maka kaje Amarya ta maka maganin zazzaɓi"
"Ba za ka gane bane Suleman, Dan Allah ko magani ne ka siyo min"
"Ikon Allah. Na ɗauka za a raba dare ana soyayya ashe duk shirme ne. Gaskiya abin Babba ne. Barin je na kira Yusha'un"
Har zai fita sai T J ya ce " wai dan Allah Suleman wace Maryam ɗin aka aura min?"
Sai lokacin Suleman ya gane abinda ke damun T J ashe bai san wa aka aura ma sa ba.
Ya dawo gefensa yana cewa kafin ya gaya ma sa sai ya bashi tukwici.
T J yai tsaki yana dafa kan sa da ke wani irin sarawa.
"Hamma kar ka kashe kan ka fa. Boɗɗiyonka aka aura ma ka"
T J ya ɗaga rinannun idanun sa ya kalleshi ya ce " ba na son shirme"
"Aradun Allah Boɗɗiyo ce, ai musulunta ta yi shine su Baffah su ka aura ma ka ita"
Kafin ya ƙare maganar tuni T J ya miƙe tsaye. Suleman ya sa dariya
"Dan Allah ban da wasa kar zuciyata ta buga, ka faɗamin gaskiya" yana magana yana jin wani jiri-jiri.
"Na rantse da Allah Hamma"
Tijjani ya sa kai zai fita Suleman ya riƙeshi ya ce "ga gudummawa" ya miƙa ma sa ledar gasashshiyar kaza.
A hankali ya buɗe ƙofar ɗakin yana tantamar maganar da Suleman ya faɗa. Ankawo wuta dan haka ɗakin tarr ya ke da haske. A hankali ya ƙarisa bakin gadon ya ƙurawa yarinyar da ke kwance kan gadon ido bai san lokacin da dariya ya ƙubuce ma sa ba yanayi yana hawaye. Ya ranƙwafo ya kwanta gefenta ya sa hannu ya shafa kumatunta.
"Inkiru" ya kira a hankali yana cigaba da shafa fiskarta.
A karo na uku ne da ya kira sunan ta buɗe ido. Ta lumshe ido ta sake buɗewa tana kallonsa sai ga hawaye ya zubo kan kumatunta.
"I'm i dreaming?" Ya furta murya a shaƙe.
Ta girgiza ma sa kai.
Ya tallafo kan ta a hankali ya haɗe bakin su. Kissing ɗinta ya shiga yi passionately yana yi yana gurnani. Sun jima a haka kafin ya sake ta yana maida numfashi.
"I love you Maryam-Inkiru"
Rufe idonta ta yi tana murmushi. Abu ne da ta ke son ji daga gareshi tun da jimawa. Ya jawota jikinsa ya rungume yana cigaba da furta ma ta kalmar I love you. Ruwan da aka fara ne ya sa shi ankara, da sauri ya miƙe ya fita, ɗakinsa na zaure ya je ya ɗauko sallaya tareda buta ya dawo ɗakin. A barandar ɗakin dukkan su biyu su ka yi alwala yana sa ido yaga babu kuskure a alwalan na ta. Ya shimfiɗa sallaya ya ja su sallah raka'a biyu na godiya. Bayan sun idar ne ya gaya ma ta ma'anar sallan. Ya jawo mu su kazar da Suleman ya kawo, kaɗan su ka ci saboda ita Maryam ta riga ta ci abinci kuma dare yayi sosai ba ta son sake cika cikinta. Shi kuwa T J duk ɗoki ya ke ji. Wani zazzaɓi da rashin kuzari da ya ke ji ɗazu duk sun tafi hutu.
Ruwan sama aka fara tsalawa wanda ya ƙara sawa ɗakin na su yai sanyi hakan ya sa ɗumin jikinsu ya zame mu su garkuwa. Soyayya ce da ta ke zuciyoyinsu tun da jimawa wacce ba ta samu daman fitowa ba sai yanzu. Soyayya ce da ɗaya ba zai iya cewa ga lokacin da soyayyar ta shige shi ba. Soyayya ce da addini, yare, da banbancin gari ya mu su shubuha a da, amma musulunci da igiyar aure ya zo ya haɗe komai ya ba su damar bayyanawa junan su irin tsananin son da su ke wa junan su.
Nkiru dama ba baya ba wajen sakalci dan haka ya sha yare kala-kala a wannan dare, har yaren mahaifiyarta Efik da ba ji ta ke sosai ba sai da ta mi shi. Ita kuwa ta sha lallashi da yaren fillanci. Da ita da shi ɗin duk zazzaɓine ya rufe su a wannan dare mai cike da tarihi. Daren daya zamo ɗaya daga cikin dararen da ba za su iya mantawa ba a tarihin rayuwar su...