Happy couple
by @azizat
*Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*
Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat
*Free page*
*7-Happy couple*
Bismillahir Rahmanir Rahim
Washegari kiran sallar Asuba ne ya farkar da T J daga bacci. Lokacin daya buɗe ido ya ɗauka abunda ya faru jiya mafarki ne sai daya ga Maryam gefensa tana bacci, yai murmushi yana hamdala a ransa. Ya ma ta ligt kiss a bakinta kafin ya tashi, baya jin wani ƙarfi sosai amma a haka ya saka jallabiyar sa ya fita. Ruwan zafi ya kamata ya nemo amma ya san ba a kunna wuta ba, sai yanzu ya ji haushin tafiya da heater ɗin sa Zaria. A haka dai ya daure ya je yai wanka ya ɗauro Alwala ya dawo ɗakin har lokacin Maryam na bacci. Ya gyara ma ta kwanciya sannan ya fita, a bakin ɗakin Goggo ya ga Goggon riƙe da buta za ta fita, yai saurin ƙarisawa wajenta yana sosa kai yana wani sunsun da kai ya ce ma ta idan ba damuwa yana son ruwan zafi idan ya dawo daga masallaci. Goggo ta yi murmushi ta wuce ba tareda ta amsa ma sa ba.
Lokacin da ya dawo daga sallah Maryam ta farka amma ba ta tashi akan gadon ba, tausayinta ya ji dan jiya bai ma ta da sauƙi ba.
Ta ce ma sa tana son yin wanka ya ce ta bari a sama mu su ruwan zafi tukunna. Ya jawota jikinsa yana cigaba da ba ta haƙuri tareda jaddada ma ta soyayyar shi gareta. Su na haka sai Asma'u ta yi sallama wai Goggo na kiran sa. Ya fito bayan ya mannawa Amaryarsa kiss a kumatu.
Da ya je Goggo ta ma sa bayanin yadda Maryam za ta gasa jikinta da ruwan da aka kai ma ta banɗaki. Sai sosa ƙeya ya ke yana jin kunyar Goggon ta sa.
Da ya koma yai wa Maryam bayani komai, ya so tallafa ma ta zuwa banɗakin amma ya san magana kawai zai ja wa kan sa idan aka gan shi. Har ta fita daga ɗakin sannu ya ke ma ta yana ƙara jin soyayyarta na mamaye ilahirin jikin sa...
Kwana takwas T J ya kwashe yana cin Amarci kafin ya koma Zaria tareda alƙawarin ƙarshen sati zai zo. Kafin ya tafi wani soyayya mai tsabta su ke gudanar wa junan su. Ba dan cikin babban gida su ke ba da ya nuna wa Maryam gata fiye da tunaninta. A waɗannan kwanakin ne ya ji labarin yadda akayi ta musulunta da yadda aka yi har su Baffah su ka mu su aure. Ta gaya mi shi komai amma banda abinda Muntari yayi. Kwana biyu bayan an ɗaura aurenta da TJ Baffah ya sa aka kira ma sa ita, Yakubu ne ya fassara ma ta abinda Baffan ya ce.
*"Ina neman alfarma a wajenki Maryam, ba na so ki sanar da Tijjani abinda ya faru tsakanin ki da Muntari. Ba na son zumunci ya yanke, da Tijjani da Muntari duka suna da zuciya, amma ina tsoron abinda zai biyo baya idan Tijjani ya san abubuwan da Muntari ya aikata kafin auren ku. Ina fata idan Allah ya sa Muntari ya huce da kanshi zai nememu ya nemi gafaran mu, zuwa lokacin gara a rufe maganar"*
Itama ta gamsu da bayanin Baffan domin dama ba abinda maganar zai haifar wa T J sai haushin ɗan uwansa. Ba za ta so a kanta 'yan uwan juna su samu matsala ba.
Idan ka ɗauke Iya kowa yayi na'am da kasancewar Maryam matar Tijjani. Ita kam ƙiri-ƙiri ta ke nuna ma ta tsana hakan ya sa Maryam ke kaffa-kaffa da ita. Tunda ta ke ba ta taɓa amsa gaisuwarta ba. Ba dan kashedin Baffah ba da abinda Iyan za ta yiwa Maryam sai ya fi haka...
Muntari kam tunda ya tafi bai sake waiwayan gida ba wata uku kenan, haka ya kuma ɗaga hankalin Iya ta kuma tsanar Maryam dan gani ta ke ita ce silar komai.
A ɓangaren T J duk sati sai ya zo gida idan bai zo ba to wani abun ne ya tsaida shi, daya fara thesis na shi ne ma ya ke ɗan jimawa wani lokaci bai zo ba.
A yau Maryam ta dawo daga makaranta, fitsari ne ya dameta ta yi hanyar banɗaki da gudu ba ta ankara ta ɗan buge Iya wacce itama daga banɗakin ta ke.
"I'm sorry" ta faɗa ta wuce da sauri.
Tundaga banɗaki Maryam ke jin ihu da kururuwan Iya. Da ta fito kuwa har anfara taruwa a wajen Iya ta tsaya tana kukan munafurci wai Maryam ta bangajeta kuma ko sannu ba ta ce ma ta ba.
Ganin yadda Iyan ke kuka ya sa dayawa daga cikin matan su ka yadda da abinda ta ke faɗa, harda cewa dama ƙabilu ai ba su da kunya.
Ita kuwa Maryam ba ta fahimci maganar su ba andai tsareta anata magana wannan yai wannan yai. Ganin Iya na ta kuka ya sa ta fahimci buge Iyan da ta yi ɗazu ne ya sa take kuka. Har ga Allah ba ta ma san Iya ta buge ba, sannan ba wani bugewan da za a nuna damuwa ba ne.
Hayaniyar 'yan gidan ya tada Yadikko daga bacci. Ta fito ta tarwatsa taron ta ce ba ta yarda Maryam za ta buge Iya ba sharrinta ne kawai dan ba ta ƙaunar Maryam ɗin.
Tunda Maryam ta shiga ɗaki ta fara kuka, ya za ta yi da mahaifiyar T J ne? Mi za ta ma ta matar ta dena tsanarta?
Ƙarshe ciwon kai ne ya sa ta baccin dole.
A satin da T J ya zo kamar kullum ɗakin iyayen sa ya fara shiga dan ya gaishe su kafin ya wuce wajen Amaryarsa. Ɗakin Iya daya shiga ne ya sameta tana saka lalle a ƙafarta.
Kamar kullum ya gaisheta ya tashi zai tafi dan ya san ba kulashi za ta yi ba. Sai kuma ta ce ya tsaya, ya zauna fiskarsa shimfiɗe da farin ciki.
"Takarda na ke so ka rubutawa Inyamuran matar da ka ke kira da mata"
Daam ya ji ƙirjinsa ya buga. Ya ɗago ido ya kalli Iya da itama ta ƙura ma sa ido.
"Iya Dan Allah ki yi haƙuri, duk abinda Maryam ta miki ki yafe ma ta, zan ma ta faɗa za ta gyara"
"Tsaya ka ji Shehu, na zuba maka ido ne kawai saboda ba yadda zan iya. Amma wallahi yanzu kam ba zai yiwu matarka ta dake ni kuma ta cigaba da zama da kai ba. Duk yadda ka maƙalewa Maryama dai ni ce nan na haifeka kuma wallahi ko ka saketa ko na ɗaga maka nono"
Da sauri ya zaro ido yana girgiza kai.
"Kiyi haƙuri dan Allah, wallahi ba zan iya rabuwa da Maryam ba, ki taimaka min"
Ta yi kaman ba ta ji shi ba ta cigaba da saka lallen da ta ke yi. Kawai ya fashe ma ta da kuka yana yi yana roƙonta.
Ganin ya isheta da kukan ne ya sa ta ɗago ta kalleshi ta ce"Ko ka saketa ko wallahi na tsinemaka"
"Bismillah, ki tsine mi shi"
Su ka tsinkayi muryan Baffah.
Wucewa zai yi ya je masallaci ya ji kukan TJ daga ɗakin Iya shine ya shigo.
"Aishatu na ce ki tsine ma sa, ɗan ki ne ai ki tsine ma sa ya bi duniya"
Jikin Iya ya fara rawa, yadda Baffah ke magana da ƙarfi ya sa ta kuma tsorata.
Ya kalli T J ya ce " kalleni Shehu"
T J ya ɗago rinannun idanun sa ya kalleshi.
"Wallahil Azim duk ranan da ka saki Maryam to a bakin auren mahaifiyar ka"
T J ya rikice da jin wannan magana. Itama Iya ba ƙaramin kaɗuwa ta yi ba da jin abinda Baffah ya ce.
"Kinga Aishatu duk ranan da ki ka sa Shehu Tijjani ya saki matar sa kaman na sake ki ne, kuma Allah ko bayan rai na kika sa shi rabuwa da ita ba zan taɓa yafe miki ba. Haba, haba Aishatu. Ke kina ƙara girma kina ƙara rashin hankali ne, yaron nan kullum hantarar sa ki ke yi ba dama ya so abu sai ki dinga kushewa. Wai shin ma kyautar da Allah ya mi shi ki ke so ya yar? Wani jahilci ke damunki da za ki dinga irin wannan furucin"
Ya kalli T J ya ce "tashi ka tafi wajen matarka"
"Baffah ka yi haƙuri" ya faɗa murya a raunane
"Tashi ka tafi"
Haka ya tashi simi-simi ya bar ɗakin. Baffah ya cigaba da yiwa Iya masifa duk wani abu da ya ke shanyewa tun da sai da ya amayar ma ta da shi. Ta fara kuka wiwi har da majina. Rabon da Baffah ya ma ta irin faɗa haka tun tana Amarya, watarana da ta je ɗakin Maryama ta kwarara ma ta ruwa bokiti biyu a cikin ɗakinta. Ranan sai da Modibbo ya shiga tsakani dan duk yadda ya ke da haƙuri sai da ya mareta a ranan.
Yana shigowa ɗaki kai tsaye gado ya hau ya jawo Maryam jikinsa ƙyam yana sauke ajiyar zuciya. Tana bacci ta ji an rungumeta hakan ya sa ta buɗe ido, jin yadda jikinsa ke ɓari ya sa ta yi saurin juyowa ta kalleshi.
"Miya faru?" Ya girgiza ma ta kai ya kuma jawota jikinsa yana faɗin "I love you Maryam, ba zan iya rabuwa da ke ba, I love you. Idan aka rabani da ke zan shiga tashin hankali, without you I cant have a happy life"
"I love you too" ta faɗa tana shafa gashinsa tana hura ma sa iska a kunne...
Washegari Baffah ya kirashi ya kuma jaddada masa maganar sa ta jiya tareda cewa ya shirya ya tafi da Maryam Zaria. Idan ba shi da wajen da zai ajiye ta ne to zai bashi kuɗi ya kama mu su haya a chan. Ya haɗa da cewa Maryam amana ce a gareshi dan haka kada ya ci amanar ta Allah zai kama shi.
Ba su tafi tare ba amma bayan kwana huɗu da tafiyar sa ya dawo ya ɗau Maryam su ka koma garin Zaria. Hayar ɗaki ɗaya ya kama mu su suke zaune hankali kwance suna shan soyayyar su ba mai takura mu su balle a sa mu su ido.
Lokacin da T J ya ƙare Masters na shi ba ƙaramin karramawa ya sha ba saboda kasancewar sa haziƙin ɗalibi, gashi thesis ɗin da yai ya kawo cigaba a Faculty na su dama makarantar gaba ɗaya. Aikin lecturing aka bashi saboda makaranta na buƙatar haziƙin mutum kamar sa.
Bayan sun samu gida a quaters na school T J da Maryam su ka je Ringim inda su ka tattaro duk kayan ɗakin Maryam ɗin su ka kawo sabon gida tunda wannan a wadace ya ke ba kaman ɗaki ɗaya da su ka fara zama ba, aka ƙara da wasu siyayyan
Abu na gaba da ya fara yi shine ya fara bincika wa Maryam yadda za ayi ta samu takardun makarantar ta. Aka rubuta letter aka aika chan makarantar su. Kafin a dawo da reply sai da ya ɗau kusan sati bakwai, a saƙo na gaba da suka turo ne aka haɗo da sabbin copies na results ɗin ta. Nan da nan T J ya shiga nema ma ta gurbin karatu a nan ABU Zaria cikin ikon Allah kuwa ta samu. Law ta cika saboda tunda ta auri T J ta gaya mi shi ra'ayinta na son ɗaukan fansa kan abinda Uncle Udodiri yai wa iyayenta kuma T J ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari.
Zaman lafiya su ke ba wani tashin hankali, zai fita koyarwa ta fita ɗaukan karatu idan an dawo da yamma ya koya mata ƙur'ani da kuma iya litattafan addini. Duk ilimin da ya samu na addini to a wajen Kakan sa Modibbo ya samu kuma yana ƙara godiya daya sa alokacin ya maida hankali kan karatun gashi yau ta ma sa rana.
Duk ƙarshen wata T J ke zuwa ganin iyayen sa ita kuma Maryam Nkiru sai bayan wata uku ta ke zuwa duba su. Har lokacin babu wani chanji a tattare da Iya dan tunda Baffah ya ma ta faɗan nan ta sake watsar da kashin T J da Maryam ko kallon kirki ba su isheta ba, abun na bala'in damun T J musamman yanzu dayake ganin a hankali za su zo su fara tara iyali da shi da Maryam. Goggo na yawan kwantar ma sa da hankali akan ya cigaba da yiwa Iya addu'a watarana komai zai dawo dai-dai.
Muntari sai da yayi shekara ɗaya da wata biyar kafin ya zo gida nan ma zuwa yai ya leƙa Iya dan ya san ita kaɗai ne hankalinta zai tashi da rashin sa. Duk yadda ta ma sa faɗa akan ya dawo gida ya ƙi, cewa yai saboda Hamma Tijjani yayi boko shiyasa aka walaƙantashi aka aurawa T J Maryam bayan kuwa an sani shi ke sonta. Iya ta tsorata da lamarinsa saboda ta ɗauka iya lokacin nan ya manta da batun Maryam. Tsanar Maryam ya kuma dira ma ta a zuciya ta sawa ranta Maryam Mayya ce shiyasa ta kama ma ta 'ya'ya har biyu. Ga Tijjani ya zama tamkar wawa a kan Maryam shi kuma Muntari ma tana tunanin hauka yayi.
"Sai na yi kuɗi, Aradun Allah sai na yi mahaukacin kuɗi ta yadda ko ta Maryam sai ta yi nadamar auren Hamma Tijjani da ta yi. Sai na nunawa dukkan wanda su ka zalinceni cewa Boko ba komai ba ne, Arziƙi shine mutum"
Kamar Iya za ta yi kuka haka ta dinga roƙonsa akan ya haƙura da Maryam ya nemi wata a ma sa aure amma ya ƙi.
"Ni kam na shiga uku ni Aishatu, Yasin wannan Inyamuran ta gama da ni. Muntari ka dubi Allah ka dubi Annabi ka haƙura da ita, ga kyawawan 'yan mata nan ka nema ka aura. Ba wacce za ka nema da za ta ƙi ka"
"Iya ki bar zancen nan ko zan yi aure ba yanzu ba. Idan ban cimma burina ba bazan taɓa samun sauƙi ba"
Ya buga ƙirjinsa ya ce " ki yi haƙuri amma son Maryam yanzu na fara shi"
Kwana biyu yai a gidan ya bar garin wannan karan ba Kano ya tsaya ba Lagos ya wuce neman kuɗi...
***
Shekaru biyu kenan cur da auren Maryam da Tijjani kuma har lokacin ba ta samu ciki ba. Ita ne ma ta fara damuwa amma shi kam ba ruwan sa kullum ce ma ta ya ke lokaci ne bai yi kuma ai ba su jima da aure ba ma. Itama ta fara damuwa ne tun lokacin da su ka kai ziyara gida matan gidan ke ce mata sun ji shiru har yanzu. Yanzu kam ta iya Hausa kuma Fulatancin ma ba laifi ta kan ji kuma tana amsawa daidai gwargwado.
Zuwan su na ƙarshe gida bikin Pendo ne. Zainaba wacce ake cewa Pendo ta samu gudummawa sosai a wajen Maryam. Allah ya haɗa jininsu tun ranan da su ka fara haɗuwa kuma duk yadda aka ƙyamaceta a gidan kafin ta musulunta Pendo ba ta taɓa ƙyamar ta ba. Mijin Pendo ma dai duk ɗan cikin gida ne amma a Dutse ya ke aiki a wani ma'aikata, da Sakandare ya fara aikin amma yanzu ya fara karatu a Jami'ar BUK saboda mahimmancin Ilimi daya gani.
Ta so ta bi 'yan kai Amarya amma T J ya hana ya ce ta bari idan an kwana biyu za su kai ma ta ziyara har Dutsen.
Bayan bikin Pendo Baffah ya fara jinya wanda bai cika wata uku ba ya rasu mutuwar da ta girgiza iyalen gidan gaba ɗaya musamman ma T J da Maryam. A wajen rabon gado ne T J ya tambayi yayansa Usman Manga ko ya san inda Muntari ya shiga, ace Baffah yayi jinya har ya rasu amma Muntari bai zo ba.
Usman ya ce ai ya rabu da shirmen Muntari wai Lagos ya tafi neman kuɗi. T J ya taɓe baki yana mamakin halin ƙanin na sa. Sam tun tasowar yaron baya ji kuma daɗin daɗawa Iya da ta dinga ɗaure ma sa gindi ya sa ya sake botsarewa. Ko lokacin da ya gudu daga makaranta ma ya ce ba zai yi karatu ba Iya ce ta fara supporting ɗin sa, har ta kai dole Baffah ya haƙura ya barshi ya tafi Kano wai neman kuɗi.
T J ya ce Allah ya shirya shi.
Gadon Muntari aka damƙawa Iya ta ajiye mi shi zuwa lokacin da zai dawo...
Bayan rasuwan Baffah da wata shida watarana yayar Iya wacce su ke cewa Inna Saratu ta kawo ma ta ziyara da 'yar ta Hajara da su ke cewa Hajjo a wannan zuwan su ne kuma su T J da Maryam su ka zo gida. Yadikko ce ba lafiya, ita tun rasuwan Abubakar ma bata jin daɗi dan mutuwar ya girgiza ta, ɗan ta ƙwalli ɗaya a duniya ya tafi ya barta.
Hajjo ta ƙyalla ido ta ga T J nan ta sanar da Inna Saratu cewa ta samu mijin aure. Dama wani tsoho ta ke so saboda kuɗin sa a chan ƙauyen su amma yanzu da ta ga T J ɗan boko wayayye kyakyawan saurayi sai ta ji ba abinda za ta yi da Alhaji Rabe.
"Amma Hajjo kin san fa watan nan za a sa mi ki rana kike maganan kinga mijin aure a nan. Dan uban ki Alhaji Raben ba mijin aure ba ne?"
Hajjo ta yi dariya ta ce "Inna wallahi ina faɗa miki sunan sa za ki rikice, aiko an ɗaura auren za ki sa a warware"
"Waye?" ta faɗa fiska a ɗaure dan ta san halin 'yartata da rawan ido.
"Hamma Tijjani, Hamma Tijjanin Iya"
Inna ta zaro ido waje sai kuma ta fara murmushi...
Ba su bar Ringim ba sai da ta tabbatar ta zuga Iya akan ta haɗa auren Tijjani da Hajjo. Itama dama ba son Maryam ta ke ba dan haka ta yi saurin na'am da zancen tunda dai yanzu babu Baffah da zai taka ma ta burki. Amma wani hanzari ba gudu ba ta fi son T J ya auri Bafulatanar usul sannan gaskiya tarbiyyan Hajjo bai ma ta ba dan taga yadda Hajjon takeyi cikin kwana biyar da su ka yi a gidan, yarinyar idonta a buɗe ya ke.
Inna ta hau fushi tana faɗin Iya za ta nuna ma ta cewa 'yarta bare ce tunda Uban Hajjo ba Bafulatani ba ne. Mijinta Warjawa ne. Auren fari ta auri ɗan uwanta Bafulatani ba ta son sa haka su ka rabu ko shekara ba su yi ba, ta je ta auri Sama'ila wanda cirani ya kawo shi Ringim a lokacin.
Iya ta shiga ba ta haƙuri tareda cewa indai haka ta fassara maganan ta yi haƙuri ba manufarta kenan ba, za ta yiwa Tijjani magana ya auri Hajjo...
*still mu na kan share hanya ne a labarin domin jarumar mu ba ta ma iso ba tukunna. The sad truth is i'm inlove with Maryam-Nkiru and Tijjani😔*