ZAYTOONAH

Patience

by @azizat

*Chronicles of*

*...... ...... .......ZAYTOONAH*

Rubutawa.....Azizat

Wattpad@Azi_zat

*Free page*

*8-patience*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Wata huɗu aka saka auren Tijjani da Hajjo. Aure ne harga Allah babu yadda za ayi ya kauce ma sa tunda Iya ta ce idan bai auri Hajjo ba har abada ba zai taɓa ganin rahama a rayuwar sa ba. Wannan furuci ya birkitashi sosai.

Goggo ta bashi goyon bayan yayi auren wataƙila Allah zai sa Iya ta sausauta ƙin sa da ta ke yi. Bai taɓa ra'ayin mace fiye da ɗaya ba, tun ma kafin ya haɗu da Maryam Nkiru ba shi da ra'ayin auren mace sama da ɗaya. Balle kuma da ya samu macen da ya ke ganin har duniya ta naɗe ba zai taɓa iya son wata mace bayan ta ba, bai taɓa jin zai haɗa soyayyar Maryam da wata mace ba balle har ya ƙara aure.

Iya ta ci darajan haihuwa, indai yana so ya gama da duniya lafiya to dole ne yai wa Uwar da ta haifeshi biyayya.

Yafi sati abun na damunshi ya rasa yadda zai yi ya gayawa Maryam. He failed her, tun daren farkon su ya ma ta alƙawarin ita kaɗaice babu ƙari, ita ɗaya ce matarshi har idan yana numfashi a duniya, ita da kishiya sai dai a Aljannah da za ta zamo sarauniyar Hurul ayn. Amma yanzu ya karya alkawari.

Kusan sati uku abun na cinsa kafin ya summoning courage ya gaya ma ta abinda Iya ta sa shi. Ba ta ce komai ba har kusan minti biyu.

"My Dear please say something" ya faɗa yana kallonta yana ƙoƙarin karantar yanayin fuskar ta.

Ta yi murmushi mai ciwo ta ce " na san Iya ba ta so na and na san she'll always come between US sooner or later. The only thing da ya hanata rabamu tun da shine maganar Baffah"

Ta ja dogon numfashi sannan ta ce " This is just a step to break us, and ba za ta tsaya a nan ba she'll do more and more and more. Abu ɗaya na ke tsoro Barkindo..."

T J ya kamo hannunta ya kai dai-dai ƙirjinsa ya ce " then, now and the future zuciyar Tijjani taki ce. Jikina zai raɓi wata mace amma zuciyata ta mace ɗaya ce. Zuciyata will always beat for you Maryam-Inkiru"

"Its Nkiru, N N N Nkiru" ta faɗa tana turo baki

"Afuwan Sarauniyata N N N Nkiru"

Yadda yai maganar ya sa ta fashe da dariya tana dariyan har da hawaye, ya rungumeta shima yana dariyan.

Bubbuga bayansa ta ke yi tanajin zuciyarta na zafi kamar zai fashe.

"I'm sorry my love, i'm very sorry" ya fara faɗi yana shafa bayanta lokacin daya ji sheshsheƙar kukan ta.

"I love you, I'll always love you, ki rinƙa tunawa da wannan"

Rarrrashin na ta daya ke yi ya sa ta ƙara sautin kukan ta. Hakan ya sa shima hawaye su ka fara zubo ma sa, ya sani its not easy for her, shima kuma daurewa kawai ya ke yi amma abin na ma sa zafi.

Sai da ya ga kukan ya ƙi tsayawa ne ya sa shi chanja salon rarrashin, duk yadda ta so ta kauce ma sa sai da salon na sa ya birkitata. Daga kuka ta koma amsa saƙon zazzafar soyayyar sa...

Daga wannan rana ta fara koyawa zuciyarta yadda za ta saba da sharing T J idan Amarya ta zo.

***

Bikin na matsowa T J na ƙara nunawa Maryam kulawa duk dan ta kwantar da hankalinta. Daurewa kawai ta ke yi tana nuna ma sa ba komai but deep down she's hurting. Wani lokaci idan baya nan haka za ta zauna ta sha kuka ta ƙoshi, daga baya ta sanyawa kanta salama. Yanzu ita musulmace dole ta karɓi hukuncin Allah daya halatta auren mata huɗu.

Haka ranakun su ka yi ta wucewa har aka ɗaura auren Tijjani da Hajara. Kusan shiyayi komai saboda Hajara da mahaifiyarta sun bari acewa ita ƙanwar sa ce dan haka ko ba aure haƙƙin sa ne ya siya ma ta kayan ɗaki. Bayan wannan sai da ya biya Alhaji Rabe kuɗin daya kashe wa Hajjon tunda ta ci kuɗinsa kuma ta ƙi auren sa.

Su gani su ke aikin koyarwa da ya ke yi wani kuɗi ya ke samu na azo a gani. Ba dan Noma da kiwo da ya riƙe ba da ba ƙaramin jin jiki zai yi ba. Shi duk kuɗin abinda aka ce ya kawo kawowa ya ke yi saboda a zauna lafiya. Shi lokacin auren Maryam ba abunda yai tunda komai su Baffah ne su ka ma sa.

Cikin ɗakuna uku da su ke gidan shi ya bawa Hajjo ɗaki ɗaya aka zo aka mata jere.

Cikin kashi sittin na 'yan uwan sa sun yi na'am da auren da yai, hujjar su kuwa shine ita Maryam ƙabila ce gara ya haɗa da 'yar gida.

Sauran kuwa sun nuna ba a yiwa Maryam adalci ba tunda auren su kwata-kwata shekara uku ne kuma kowa ga shaida halin Maryam na da kyau...

Faɗin ƙazantar Hajjo ma ɓata lokaci ne. Abun daya fara sa ta fitawa T J a ka kenan. Ƙazantar jiki da muhalli duk ta haɗa shi, shi idan na muhalli ne ma da sauƙi amma jikinta ta kasa gyarawa. Daya dinga takura ma ta akan wanka kuwa sai ranan girkinta idan ta ji sallamar sa ya dawo daga office zakaga ta shige banɗaki da gudu ta yi wanka fuyaaa ta fito ba tareda ta cuɗa jikinta da kyau ba.

Kasancewar Hajjo ita ɗaya ce 'ya mace a wajen mahaifiyarta ya sa Inna Saratu ta sakaltata, kwata-kwata ba ta kwaɓarta, a haka sai ta sangarce. Ba ta iya girki ba balle gyara gida. Ba abinda ta sani a ƙauyen su sai dai ta yi kwaskwarima ta banka foda a fiska ta cikawa bakin nan janbaki ta fita gari tana yawon ƙawance.

Ranan da ta fara girki cikin su ba wanda ya iya cin abincin, wannan ya sa Maryam ta ce ma ta duk ranan girkinta kar ta yi girki da ita. Ta kuwa gayawa T J ba za ta iya cin abincin Hajjo ba tunda 'yar wannan shinkafa ta kasa dafata da kyau. Duk rashin wayewar su Goggo Maryam ba za ta taɓa cewa ba su iya girki ba, tun lokacin da ta soma cin abincin gidan ba ta taɓa ganin aibun sa ba iyaka dai ba su yin varieties na vegetables kamar yadda Mommynta ke yi. Yadda su ke dafa Alayyaho ma ya banbanta da wanda ta sani. Ba ta cin miyan kuka amma idan Goggo ta yi miyan kuɓewa har suɗe hannu ta ke yi, dan za ta ji miyar ta ji citta, daddawa, masoro da sauran natural ingriedients ma su inganta abinci.

Shima dai T J ganin da gaske fa ba ta iya girki ba ne ya shi cewa ta tsaya Maryam ta koya ma ta girki . Ita kuwa ta kama ƙugu ta ce Allah ya sawwaƙa ta je ta koyi girki a wajen kishiyarta, kishiyar ma Inyamura. Ya kuwa daka ma ta tsawa ya ce lallai duk inda za ta je ta je ta koyi girki amma duk ranan da ta kuma kawo ma sa jagwalgwalon abinci sai ya zuba ma ta a ka sannan zai maida ta gidan su. Hakan ya sa ta ɗan tsorata da shi.

Wata maƙociyarsu ta samu ta nuna ma ta yadda ake girki na ɗan kwana biyu. Itama dai sammakal ne dan girki ne da aka yi amanna da kafi zabuwa.

Maganar saka Kafi zabuwa ko Ajinomoto a abinci kuwa tun yana maganar har ya dena dan Hajjo ta kasa denawa ta dai rage gambaɗawa, ita kamar yadda Maman Bilkisu ta koya mata haka ta ɗauka, wai girki a Ajino baya daɗi.

Shikam duk ranan girkin Hajjo baya ƙoshi dan baya cin abinci sosai saboda ba jin daɗin abincin ya ke ba yana dai haƙuri ne. Yana gama ci yake brush saboda zaƙi-zaƙin Ajinon da ke tsaya ma sa a harshe. Wani lokaci ko yayi brush ɗin sai ya haɗa da asuwaki.

Gyaran gida kam Maryam ke yi ko ba ranan girkinta ba ne dan idan ta ce ba za ta gyara falo da kitchen da sauran wajajen ba sai dai cikin kwana biyun da T J zai yi a wajenta idan sun yi baƙi su ji kunya saboda Hajjo ba sharewa za ta yi ba. Ɗakinta ma sai ta yi sati bai ga tsintsiya ba, idan ka ga ta yi shara T J ne ya tsaya akanta ya ce dole sai ta share ɗakin. Ba abunda ta sani sai dai ta kunna T V da ke falo tayita kallon Films ɗin Indiya, tana yawon neman sabon casette daya fito.

A ƙoƙarin sa na son ganin Hajjo ta gyaru yai tunanin sa ta makaranta. Kasancewar ko Primary ba ta ƙarisa ba ta bar zuwa ya sa ya sama ma ta primary school aji huɗu. Ko yanene ta yi shekara biyu ta ƙare primary sai ta fara JSS one. Sai daya gama shirin sa har Uniform ya ɗinka ma ta Hajjo ta ce ba za ta yi makaranta ba. Ƙarshe ta ce irin makarantar da Maryam ke zuwa zai sa ta idan yana so ta yi karatu. Makarantar manya ba ta yara irin su Bilkisun maƙotan su ba.

Duk wani bayani yayi ma ta ta ƙi ji, ƙarshe ta ce wai ai ba dole ba ne tayi karatu. Da ya ma ta jan ido sai ta nitsu.

Kullum za ta shirya ta sa uniform ta wuce gidan Maman Bilkisu ta zauna su yi ta kallo sai da rana idan anfara dawowa daga makaranta sai ta koma gida.

Kusan sati uku ana haka T J bai taɓa ganewa ba, sai da watarana headmaster ɗin makarantar ya samu T J akan matarsa da ya ce za ta fara zuwa har yanzu form master ɗin ajin su ya ce bai ganta ba. Kunya ta sa T J ya rasa mi zai ce.

Da ya je gida ya tsare Hajjo kuwa sai ta sa kuka wai ita ba za ta yi makarantar yara ba. Haushi ya kamashi ya ce ta cigaba da zama a jahilci tunda Ilimin ne ba ta so, watarana za ta yi kuka da kan ta.

Daga ranan batun makarantar ta ya bi ruwa. Ba abinda ta ke yi sai kallo da yawon gulmace-gulmace. Da farkon kawo ta Amarya wasu cikin maƙotan su Maryam Hausa/Fulani su ka fara ja baya da Maryam suna cusuwa jikin Hajjo tunda acewar su 'yar uwa ce ba kamar Maryam da ta ke ƙabila ba.

(Kamar Hausa/Fulanin ba Ƙabila ba ne)

Dama Maryam ta fi harka da Madam Mitchele wata baturiyar ƙasar Poland wacce itama lecturer ce sai kuma Mama Lucas wata Igala sai wata Bayarabiya Iya Korede. Ita Iya Korede gidan su baya layi ɗaya amma duk da haka su na zumunci dan itama mijinta ya barta ta fara karatu, duk da ba Course ɗaya su ke da Maryam ɗin ba amma su kan haɗu wani lokaci a cikin School.

Daga baya da Hajjo ta nuna halinta na haɗa guri sai su ka fara ja baya da ita. Yanzu Maman Bilkisu ce kaɗai su ke ɗasawa da ita itama halinsu ne ya zo ɗaya.

Maryam kam duk wani shirmen Hajjo ba ta biye ma ta, ba ma ta da lokacinta karatun ta kaɗai ya isheta ga wanda su ke a gida da T J. Ganin ba ta samu fiska a wajen Maryam ba ne ya sa ta dena taƙalarta da tsokana.

Watarana T J na Office aka zo aka kirashi wai matar shi na Asibiti. Gaba ɗaya ya tsorata dan bai san wacce ba ce cikin matan na sa. Sai da ya je ya ga Hajjo. Faɗa su ka yi da Maman Bilkisu, garin faɗan ne Maman Bilkisu ta tureta cikinta ya bugu da centre table shine ta yi ɓari.

Haushi takaici duk ya cika T J wai matar sa ta rasa cikinsa garin kokawa. Bayan an sallamesu ya ɗauketa su ka dawo gida tsabar ɓacin rai bai san mi zai gaya ma ta ba. Ya hanata yawo amma ba ta ji. Daya fara magana sai ta fara kuka wai bai tausaya ma ta bayan ta rasa gudan jinin su, hakan ya sa shi yin shiru.

Bayan kwana biyu ya ce ta je gida ta huta, shi da kan sa ya kaita gidan su ya kuwa yiwa Goggo maganan duk halin Hajjon ya kuma ce dan Allah ta ma ta faɗa. Bayan tafiyar sa da Goggo ta kira Hajjo tana ma ta faɗa sai ta fashe da kuka wai sharri T J ya ma ta dan ya fi son Maryam a kanta. Wai Maryam ce ta tureta har ta bugu ta yi ɓari. Takaici ya kama Goggo dan ta yarda da maganan T J. Duk faɗan da ta ma ta yana shiga ta kunnen dama ne yana fita ta hagu.

Bayan sati ɗaya da T J ya zo ɗaukanta Iya ta sa shi a gaba da faɗa wai ya jawa Maryam kunne, dan ita ba ta haihuwa ba zai sa ta dinga kashewa Hajjo 'ya'ya ba. Ga ainihin abinda ya faru amma Hajjo ta juya zancen akan Maryam ce ta tureta ita kuma Iya ta yarda da hakan. Ba ta ma bashi dama ba balle yai ma ta bayanin gaskiya, haka dai ya ɗau Hajjo su ka tafi ran sa a ɓace.

Bayan ɓarin Hajjo da wata biyar ta sake samun ciki, a lokacin ne kuma Maryam ta fara tsorata ko dai ita ce ba ta haihuwa tunda gashi Hajjo ta samu ciki har sau biyu. Ta je Asibiti aka ma ta duk wasu gwaje gwajen daya kamata aka ce lafiyarta ƙalau za ta iya samun ciki kowani lokaci.

Hajjo kam banda laulayi har da iskanci, ta dinga tsirface tsirface dan taga T J ya ɗan damu da ita saboda cikin jikinta. Gaba ɗaya sai girki ya koma hannun Maryam da rana girkinta da na Hajjo duk ita ke girki. Hakan bai dameta ba dan girki a wajenta ba abun ɗaga hankali ba ne. Sai da Hajjon ta fara iskancin sai dai a dafa ma ta kaza ko kuma sai Maryam ta gama girki ta ce ba za ta ci ba ita kaza da kaza ta ka so sannan Maryam ta fara yiwa T J ƙorafi. Da farko T J ya fara biye ma ta saboda laluran ma su ciki amma daga baya da ya gane harda iskanci a lamarin na ta sai ya taka ma ta birki.

A hankali dai ciki ya girma Hajjo ta haifi ɗanta namiji. Zo ka ga murna a wajen ta ganin yanzu kam za ta karɓi gida tunda ita ta fara haihuwa ga shi ɗa namiji.

A Zariyan a ka yi suna kuma 'yan uwan sa na Ringim sun zo dayawa. Yaro ya ci sunan Baffah wato Abubakar suna kiran sa Sadiq.

Tun watan farkon Sadiq ya fara rashin lafiya. Yau suna asibiti gobe su na gida. Na da nan Hajjo ta tada Hankali wai Maryam ce Mayya ta kama mata ɗa. Ita da Inna da ta zo mata wanka su ka kama Maryam da zagi da faɗa. Har Inna Saratu ta je ta nemo tafarnuwa su ka fara sakawa a duk gidan. Da Maryam ta shigo kuwa za su fara jifanta da Tafarnuwa. Ba ta taɓa gayawa T J ba dan ba ta son tashin hankali.

Ranan da ciwon Sadiq ya tashi aka kaishi babban Asibiti nan Inna Saratu ta wuce gida wai za ta zo da sarkin mayu.

A asibitin bayan anyi gwaje-gwaje ne aka tabbatar wa T J da cewa Sadiq SS ne wato sickler. Nan aka gwada jinin sa da na Hajjo aka tabbatar dukkan su genotype ɗin su AS ne. Wannan ya sa washegari ya taho da Maryam aka gwada ta amma ita AA ce nan hankalinsa ya kwanta.

Da yamma yana Asibiti saboda ana ƙarawa Sadiq jini sai ga maƙocinsa Mr Badmus wato Baban Lucas. Ya ce maza-maza ya zo gida ba lafiya. Da ya tambayeshi miyake faruwa sai ya ce wai wasu tsofi ne su ka taho da Sarkin Mayu gidan sa an ɗaure Maryam ana dukanta wai sai ta sake kuruwan Sadiq. Jiki na rawa haka ya bi Mr Badmus hankali tashe duk da kuwa Mr Badmus ɗin ya ce ma sa an tafi da Maryam Asibitin cikin makaranta shi kuma Sarkin Mayu an kira ma sa security yanzu ma ana maganar za a wuce dashi police station ne.

Asibiti su ka wuce inda su ka samu an sallami Maryam ɗin, dama ciwukan da dorinar Sarkin mayu ya ji ma ta ne aka treating.

Gidan Mr Badmus su ka wuce tunda matar sa ce ta kai Maryam ɗin Asibiti. Su na shiga Maman Lucas ta nuna ma sa ɗakin da Maryam ɗin ta ke.

Yana shiga ya ganta zaune a kan gado. Ya ƙariso da sauri ya hau gadon ya kamo hannun ta.

"I'm sorry Dear, i'm very sorry, ya jikin na ki? Are you Ok? " ya shiga kissing ɗin hannuta

"Divorce me" ta furta hawaye na bin kumatunta

Girgiza kai ya farayi yana hawaye.

"Mahaifiyar ka ta tsaneni, she'll keep coming between us. Lets just go our separate ways"

"Nooo, Nooo. Dear ba zan iya rabuwa da ke ba. You are my world, you are my happiness"

"Barkindo ba zan iya cigaba da zama da kai ba, ka sake ni kawai, for Peace sake lets go our separate ways b..."

Haɗe bakin su yai ya shiga kissing ɗinta da sauri sauri. Da ƙyar ta samu ta ƙwace bakinta daga zazzafar kiss da ya ke ma ta.

Tana hawaye shima yana yi haka su ka ƙurawa juna ido suna maida numfashi.

Da ƙyar T J ya ce " Maryam Dan Allah kiyi haƙuri, ba zan iya rabuwa da ke ba. Please..."

"Idan saboda maganar Baffah ne kar ka damu ai bai ce idan na nemi saki kar ka bani ba. Ba wai dan Iya ta ce ka sake ni ba, nine na ke so ka sakeni. I want peace Barkindo i want peace" ta ƙarisa maganar da ƙarfi.

Ba abinda ya ke cewa sai Sorry...

***

Kwana shida kenan da faruwan wannan abu, Iya da Inna da su ka taho da Sarkin Mayu kam suma kaɗan ya rage a rufe su sai da T J ya shiga ya fita kafin aka rufe case ɗin. Da kan sa ya je Ringim ya samu Alhaji Isa ya ma sa bayanin duk abinda ya faru da ma abin da ke damun Sadiq ɗin. Alhaji Isa shima ya kaɗu da maganar, bai taɓa tsammanin rashin hankalin Iya ya kai har haka ba.

Goggo kam sai da ta yi hawaye saboda tausayin Maryam. Tana ina ma Baffah na raye.

Meeting mai zafi Alhaji Isa ya kira wanda ya haɗa da Iya, Inna Saratu da ma Hajjo wacce an sallame su saboda Sadiq ya ji sauƙi. Ya kira Maryam ma amma ba ta zo ba saboda exams da su ka fara har lokacin gidan Mr Badmus ta ke kwana ta ƙi komawa gidan T J. Yayi kukan yayi magiyan ta ƙi sauraron sa.

Sosai Alhaji Isa ya jawa Iya da su Hajjo kunne akan Maryam. Yai Allah wadai da halin su da ɓatawa Gidan Modibbo suna ta hanyar zuwa ɗauko wani Boka wai Sarkin Mayu. Ya haɗa da cewa dukkan su suje su bawa Maryam haƙuri.

Shi T J ya so a raba auren sa da Hajjo ne ma musamman saboda yadda dukkan su suka kasance AS that is akwai probability za su yi ta haihuwan SS amma Alhaji Isa ya ce a'a tunda har sun samu rabo ya cigaba da haƙuri kawai. Duk bayanin daya ma sa akan rashin compatibility na su da Hajjo bai gane sosai ba haƙuri kawai ya bashi akan ya cigaba da zama da ita su yi jinyar ɗan su.

A wajen kuwa Alhaji ya ce da Iya da Inna bai yarda ko ɗaya ta sake zuwa gidan T J ba idan suna son ganin su su bari sai sun zo Ringim. Idan da matsala za a aika wasu cikin 'yan uwa su je mu su.

Bayan taro ya watse ko ta kan Hajjo bai bi ba ya koma Zaria. Duk wani hanya ya bi akan Maryam tayi haƙuri amma ta ƙi tace abu ɗaya ta ke so shine ya saketa. Ya ma ta bayanin babu wanda zai sake zuwa gidan su cikin Iya da Inna amma ta ƙi sauraren sa. Ya aika abokanan sa da dama amma ta ƙi komawa. Ƙarshe aka bashi shawaran ya barta ta huce tukunna.

Hajjo da ta yi sati a gida ta ga T J bai bi ta kanta ba sai ta tattara ta dawo. Gaba ɗaya ba ta gane kan T J ba, idan ba tambaya gameda Sadiq ba baya kulata.

Wasa-wasa har Maryam ta gama exams ba ta koma gidan T J ba. Itama daurewa ta ke yi domin har yau tana tsananin son T J amma dole ta katse alaƙarsu saboda a yadda ta hango auren su za ta cigaba da fuskantar ƙalubale matuƙar Iya ba ta son ta. Its better to quit now tunda ma ba haihuwa tsakanin su. Ba ta ji za ta iya son wani bayan T J ba amma kuma rabuwa shine mafita.

T J ya gama marking scripts na student ya fito daga office zai tafi gida ya yanke jiki ya faɗi. Buɗe idon da zai yi ya ganshi a Asibiti. Jinin sa ne ya hau abunda aka ce da shi kenan.

Matuƙar Maryam ta cigaba da demanding saki a wajen sa ƙila zuciyar sa ne za ta buga ya mutu kawai. Bai ji zai iya rabuwa da Maryam ba ko da ita Maryam ɗin ne ta nemi rabuwa da shi...

Maman Lucas na sanar da ita an kwantar da T J a Asibiti hankalinta ya tashi, hankalinta a tashe ta shirya su ka wuce asibitin, lokacin da su ka je bai farfaɗo ba. Gaba ɗaya ya rame ma ta dama ina jikin yake balle yanzu da damuwa ya ƙara busar da shi. Ganin yana bacci ne ya sa ta koma gida dan ta haɗa ma sa abinci. Zuwanta gidan na su kenan na farko tun bayan abinda su Iya su ka ma ta kusan sati biyar da su ka wuce. Ta samu gidan kaca-kaca as expected, dama haihuwa ya sake sawa Hajjo ƙazanta.

Ɗakinta ta buɗe shima ya ɗan yi ƙura ta cire kayan jikinta ta sa kayan gida ta fito ta shiga kitchen babu wasu abubuwan da ta ke buƙata dan haka ta fita gidan su Maman Lucas ta aiki Lucas ya siya ma ta kayan miya.

Faran shinkafa ta dafa da miyar ugwu wanda ya ji stock fish da kayan ciki. Ta haɗa komai sharp-sharp ta wuce Asibiti wannan karan ta samu T J ya tashi har ma suna taɗi da wani abokinshi lecturer daya zo duba shi.

Ganin Maryam ya sa ya ƙara langwaɓewa yana ma ta shagwaɓa musamman dayaga hankalinta a tashe ya ke da ciwon na sa. A baki ta dinga bashi abinci, ya kuwa ci sosai. Rabon da ya ci abincin kirki tun tana gidan sa...

Ƙarfe Shida ta baro Asibiti dan ta taho ma sa da wasu kayan buƙata. Ashe tana tafiya ya ce a sallameshi duk da kuwa likita ya ce ya bari sai bayan kwana biyu tukunna kafin nan ya warware sosai amma ya ƙi. Shi kam maganin sa Maryam ne ba zaman Asibiti ba.

Ta gama haɗa komai ta shiga wanka ta fito tana saka kaya da sauri-sauri saboda taga lokaci ya ƙure dan har an fara kiran sallar Magariba. Kawai ta ji sallamar shi.

Ta tsaya kallon shi da mamaki.

Yana ƙarasowa ya rungumeta

"Ke ce maganina Maryam, idan ki ka dawo rayuwata na warke kenan har abada"

"Likita ya ce ba..."

Rufe ma ta bakinta da yai da na sa bakin ya sa maganar ta ƙare. Yadda kasan first night ɗin su haka yake sarrafata jikinsa na rawa. Its been over a month rabon sa da ita.

Amidst soyayyar su ya ce " Maryam idan ki ka barni mutuwa zan yi, Dan Allah ki ce kin janye maganar ki"

Ta gyaɗa ma sa kai tana hawaye, hawayen zafi da daɗi.

Yanzu kam ta amince ba za ta taɓa iya rabuwa da T J ba, kamar yadda ya ke ji da ita haka ta ke ji da shi. Soyayyar shi ya riga ya mamaye zuciyarta. Lokacin da ta ganshi kwance a asibiti ba abun da ta kawo a ranta irin what if he dies because of her? Da kuwa za ta ƙare rayuwarta cike da nadama may be ma baƙin ciki itama ya kasheta.

Yanzu kam sai dai ta cigaba da zaman haƙuri, da daɗi ba daɗi she has to stay by his side saboda ba ta da rayuwar farinciki idan babu T J a ciki...

Ƙoƙarin maimaita aikin ladan da su ka yi da ya ke son yi ne ya sa ta dakatar da shi ta hanyar cewa

"Love ba ka da lafiya fa"

"Ai ke ce cutar kuma ke ce maganin" ya faɗa yana kissing cikinta

"An idar da sallah fa"

"Har yanzu muna mukhtarin ta sannan akwai lokacin daruri. Ki bari na sake jin ɗumin ki Maryam- N N N Nkiru na"

Ta yi dariya daga nan zancen ya chanja dan ta san dole ne ta bar shi ya je second round.