ZAYTOONAH

Anger (next Pg is Anorexia not confessions)

by @azizat


*Chronicles of*

*...... ...... .......ZAYTOONAH*

Rubutawa.....Azizat

Wattpad@Azi_zat

*Free page*

*14-Anger*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Shekara biyu da wata huɗu da dawowan Muntari Zaria wanda yanzu ya ke matsayin Alhaji Muntari Abubakar Modibbo Djibo yai aure. Aure ne da ba wai dan Iya na so ya yi shi ba, Iya ba ta isa ta tursasa shi yin abu ba. Ya yi ne domin ya nunawa Maryam cewa yayi hankali ko na ce ya nitsu, da kan sa ya je office ɗin ta ya kai ma ta invitation ɗin auren tareda sake ba ta haƙuri bisa abinda ya faru tsakanin su. So ya ke ta yarda da shi su koma mutunci kamar da har ya samu ta amince da soyayyar sa cikin sauƙi.

"Sorry Muntari ba zan iya zuwa ko ɗaya cikin hidiman bikin ka ba. And kamar yadda na faɗa a baya ka fita a harkana, ba zan shiga huruminka ba kai ma kar ka shiga nawa. Idan ka yi haka za a zauna lafiya idan ba haka ba kuwa zan ajiye duk wani kunya a gefe na yi shari'a da kai"

"Maryam kenan. Na ji amma dan Allah ki sassauta min, ki rage takurawan da ki ke yiwa su Zaytoonah. Ko ba komai ni fa Baban su ne"

Wannan karan ido cikin ido ta kalleshi ta ce "Muntari Oh Alhaji Muntari. Bayan Zaytoonah da Salman akwai Humairah da Sadiq. Ba ni da hurumi da sauran amma wanda na haifa da kaina ba zan taɓa bari su yi tarayya da mutum kamar ka ba. Stay away from my kids"

"Ba zan gajiya da baki haƙuri ba Maryam har sai kin haƙura. Ki yi haƙuri dan Allah"

Daga haka ya ajiye ma ta katin bikin ya fita daga office ɗin. Yana fita ta sauke ajiyar zuciya...

Biki aka yi tun daga Ringim aka zo Zaria aka ƙarisa, ba inda Maryam ta je ita da 'ya'yanta. Su Iya da Hajjo su ne ƙirjin biki musamman ma saboda ɗan Yayan Iyan zai aura. Su ka ƙare tsiyar su aka kawo Amarya gidan Muntari.

A ɓangaren Ango kuwa ba wani murna ya ke yi da bikin da zai yi ba. Aure ne da ya ke da ƙaddararren lokaci a wajen sa, da ya samu kan Maryam zai tura ta gaba.

Bayan kowa ya watse aka bar Amarya ita ɗaya. Muntari bai shigo gida ba sai wajen ƙarfe shaɗaya da rabi na dare, kai tsaye ɗakin Amarya ya wuce.

Tana nan dai zaune kan gado ta yi lulluɓi, da Misalin ƙarfen goma 'yan biki su ka watse za su je su kwana a gidan Hajjo.

"Hannatu" Muntari ya kira sunan ta da ƙarfi.

Ba ta amsa ba sai ma mutsu-mutsu da ta fara ta cikin gyalen.

"Ko ki ɗaga gyalen nan ko na zo na rufe ki da duka. An gaya mi ki ban san ko ke wacece ba ne, na sani ragowan Salisu aka kawo min"

Nan da nan ta ɗage gyalen tana kallonsa jikin ta na rawa saboda ba ta ɗauka ya san wannan sirrin ba.

"Ki buɗe kunnen ki da kyau. Na zaɓe ki ne a maimakon Rabi'atu saboda ita nitsatstsiya ce ke kuma watsatstsiya ce"

"Dan Allah ka yi haƙuri Hamma Muntari" ta faɗa tana fashewa da kuka.

Ya daka ma ta tsawa nan da nan ta haɗiye kukan.

"Mace ɗaya na ke so kuma ita kaɗai ce zan aura mu yi rayuwar soyayya. Kasancewa kin riga kin sayarda mutunci a wani kinga babu wani mutunci na ki da zan gani. Ki zauna a matsayin Matata ki bi dokoki na, duk lokacin da na buƙaci mace saboda rage zafi zan neme ki, bayan wannan ba na son shishshigi. Kuɗi da mahaifiyar ki ta hango ta zuga Iya akan ta zaɓe ki dai za ki samu amma idan ki ka ce sata za ki yi kamar yadda ma su tarbiyya irin ki ke yi to Wallahi ba za ki ji da daɗi ba a gidan nan" yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin ya bar Hannatu tana rusa kuka. Yau wa gari ya waya ta biyewa daɗin lokaci kaɗan ta ba da mutuncinta tun a waje.

Hannatu dai 'ya ce ga Sama'ila wanda ya kasance Yayan Iya amma uwar su ba ɗaya ba. Lokacin da Iya ta fara nemawa Muntari Mata Rabi'atu ta nema ma sa wanda ita kuma 'yar ƙanin ta ne, tana da hankali ga ilimi dan har tana gab da ƙarisa secondary school ɗin ta kuma a makarantar ana ji da ita sosai saboda ƙwazonta.

Da ta yiwa Muntari magana sai ya ce baya son ta. Shi baya son Ustaziya da za ta zo gidan sa ta rinƙa takura ma sa da Allah Annabi. Hannatu kuwa da ta ma sa tayinta sai ya sa aka ma sa bincikenta. Abu ne na kuɗi shiyasa duk wani dark secret ɗin ta sai da aka faɗa ma sa.

Akwai wani Malamin su Salisu mutumin Jos ne, ya zo bautar ƙasa su ka ƙulla soyayya da Hannatu har ta kai ya rinjayeta, ta kan saci jiki ta je gidan sa su nunawa juna soyayya, a tunanin su fa. Alƙawarin aure ya mata amma daga ƙarisa bautar ƙasa sa da ya tafi bai ƙara waiwayanta ba, ya ci banza.

Bayan ta ƙare secondary school aka saka bikinta da Nura wani ɗan uwanta sai aka fara ƙananun gulmace-gulmace akan ta, hakan ya sa mahaifiyar Nuran ta ce a fasa auren. To da Iya ta zo Ringim ta fara batun haɗa Muntari da Rabi'atu ne shine Umman Hanne ta shiga zancen tana son a haɗa Muntari da 'yar ta. To da ya ce ba zai auri Rabi'atu ba shine aka yi maganar Hanne kuma ya amince da auren ta...

Shekaru shabakwai da su ka wuce Muntari ya tafi Lagos. Aiki ya ke tuƙuru shi a ganin sa hakan zai sa ya samu kuɗi. Duk wani aikin wahala indai akwai kuɗi to yana nan. Shekaru biyu yai yaga bai wani tara abin a zo a gani ba, har yana son jona aikin wani abokin shi wato sata sai kuma labari ya chanja lokacin da ya haɗu da Madam Talatu.

Madam Talatu tsohuwar karuwa ce da ta yi tashe a zamaninta. 'Yar Kafanchang ne da ke Jihar Kaduna, auren dole za a ma ta ta gudu wai ta shiga duniya. A garin Lagos ta tsinci kan ta bayan doguwar tafiya da ta yi. Bayan ta samu masauki a gidan karuwai ta shiga karuwanci, ba ta da wani kyaun fiska amma akwai ta da kyaun diri, irin wanda ke ɗauke hankalin duk wanda yai tozali da ita. Cikin loƙaci kaɗan ta zama ɗaya daga cikin manya-manyan karuwai da ake ji da su a Lagos, wanda Turawa ke ɗauka, 'yan siyasa da manya manyan sojoji ke rububi. Daga gidan karuwai ta ɓalle ta samu gidan kanta ta zauna wanda cikin kuɗaɗen da ta tara ne ta siya da shi. Ta yi karuwanci na shekaru talatin kafin ta yi retire ta bazama kasuwanci, dama tana ɗan taɓa kasuwancin amma yanzu da ta dena karuwanci sai ta riƙe kasuwanci zallah.

To abu ne da ta jima tana tatsan kuɗi daga mazan da ba sa iya kama abun su, dan haka ba ƙaramin maƙudan kuɗi gareta ba. Tana da manya-manyan shaguna da kuma hannun jari.

Bayan ta bar karuwanci ta kan dai nemi yara ƙanana wanda za su biya ma ta buƙata lokaci zuwa lokaci ita kuma ta ba su kuɗi.

Lokacin da ta haɗu da Muntari tana shekaru Arba'in da takwas a duniya. Ta gan shi ne lokacin da su ka zo sauke ma ta kaya a ɗaya daga cikin shagunan ta. Nan da nan ɗan farin Bafulatanin ya burgeta. Bayan ta nemi ganin shi ta ce ya zo washegari za ta bashi aiki. Ganin kuɗin da za a dinga bashi a wata ya ninka wanda ya ke samu a da ya sa shi amincewa da aikin.

Yana aiki da Madam Talatu ita kuma tana daɗa lura da shi, bayan wata biyu ta fito ma sa da maitar ta fili, ya ce baya so. Ta sanar da shi kuɗin da za ta dinga bashi duk wata idan ya amince amma still bai amince ba. Da ta dameshi sai ya ajiye aikin da ya ke yi ya kama gaban sa. Bayan ya tafi ta kasa haƙuri da shi ta neme shi ya dawo tareda ma sa alkawarin aure ta ke so su yi kuma indai ya amince to za ta ba shi ɗaya daga cikin shagunan ta, da yai lissafi sai ya ga arziƙi ne ya zo ma sa cikin sauƙi. Auren shekara goma su ka yi alƙawarin za su yi da shi kafin nan zai saketa ya kama gaban sa.

Bayan sun yi Aure kuwa ta bashi ɗaya daga cikin shagunan ta ya zama shi ke sarrafa shi. Ta sa mishi ido sosai akan ko zai ci amanarta kaman sauran ƙananun samarin da ta ke yi sai taga shi Muntari ba ruwan sa da mata. Daga baya ta tambayeshi dalilin zuwansa Lagos ya ce ma ta ya zo neman kuɗi ne saboda matar da ya ke so.

A mafiya yawancin lokutan da ya ke saduwa da ita yana ambatun ta da Maryam hakan ya sa ta san ba ƙaramin so ya kewa wannan Maryam ɗin ba.

Shi kuwa Muntari saboda a dole ya ke tarayya da Madam Talatu ya sa ya fara shan giya da sigari saboda ya dinga ɗauke ma sa hankali a duk lokacin da ya ke tarayya da ita, hakan ya sa ya ke ganin Maryam a tareda shi a lokacin da ya ke tare da Madam Talatu.

Cikin shekaru tara da su ka yi tare yana aika kaya Kano ana sayar ma sa da shi hakan ya sa kasuwancin sa ya haɓaka sosai ga shi ba shi da matsalar komai, cin sa da shan sa da suturan sa duk Madam Talatu ce.

Bayan shekara tara da auren su MadamTalata ta fara jinya ashe cervical cancer ne. Ana magani ana jigilar asibiti amma abin ya mata mugun kamu saboda ba a gane shi ke damunta ba da wuri. Ganin fa kullum jigilar Asibiti ake ya sa Madam Talatu ta fara tunanin iyayenta da 'yan uwanta da ta baro shekaru ma su yawa da su ka wuce. A da ƙasar waje Muntari zai fita da ita ta ce ta fasa ya kaita Kafanchang za ta nemi iyayenta su gafarta ma ta. Da su ka je ta samu mahaifinta yana nan amma mahaifiyarta ta jima da rasuwa. Yayyenta da ƙannenta da ba ta san su ba kafin ta tafi duk sun girma suna da iyali. Anyi koke-koke kafin daga baya aka karɓeta hannu bibbiyu.

Saura wata biyar shekara goman auren su ta cika Madam Talatu ta ce Muntari ya saketa saboda tana son zama da 'yan uwanta zuwa lokacin da za ta mutu.

Cikin kaso ɗari na dukiyarta kusan kashi talatin ta ba wa Muntari wanda shima a lokacin side business ɗin sa ya haɓaka sosai. Sauran dukiyarta kuwa 'yan uwanta ta rabawa sannan aka gina Makaranta da Asibiti a ƙauyen su da ke Kafanchang. Shekara ɗaya bayan rabuwar su da Muntari ta rasu.

Shi kuwa Muntari tunda su ka rabu da Madam Talatu ya fara ƙoƙarin yadda zai dawo da kasuwancin sa Kano saboda ya kasance kusa da masoyiyar sa. A shekaran ne kuma ya tafi Umara dan ya fito a Alhaji ya bawa kowa mamaki.

Tunda kuɗi su ka fara zama ma sa ya fara bibiyan labarin ɗan uwansa Tijjani da kuma halin da masoyiyar sa ke ciki. Bai sha wahalar samun information da ya ke so ba. Nan ta ke ya sayi fili a anguwar ya fara gini, ya so ace kusa da gidan Maryam yai ginin amma bai samu fili a wajen ba, duk da haka tunda anguwa ɗaya ne ba shi da matsala.

Wannan kenan

***

Assembly ake yi da sassafiyar ranan Litinin. Kowa da ka gani a cikin uniform za ka gan shi tsaf-tsaf da shi.

Kamar kullum a layin na su ita ce ƙarshe saboda ba ta son tsayiwa a gaba ko a tsakiya 'yan ajin na su su dinga tsokalar ta.

"Zaytu Mama kin yi assignment ɗin Maths kuwa?" wata yarinya da ke gaban Zaytoonah ta faɗa.

Nuratu kenan wacce duk cikin 'yan matan ajin na su ita ce su ke ɗan mutunci, itama ayi faɗa a shirya ne.

Anguwar su ɗaya ne kuma Islamiyya ɗaya su ke zuwa hakan ya sa su ka ɗan shaƙu.

Sai da ta haɗiyi baƙin cikin da ya taso ma ta sannan ta ce " na yi" ta tsani kalmar Maman nan da su ke alaƙantata da shi. Duk cikin sunannakin da su ke kiranta ba wanda ya fi tsaya ma ta a rai irin Maman aji ko Zaytu Mama da su ke ce ma ta.

"Za ki bani na kwafa dan Allah"

Shiru ta yi ba ta amsa ma ta ba.

Bayan an gama assembly su ka wuce aji. Tana zuwa kuwa Nuratu ta tsareta sai da ta bata notebook ɗin ta na Maths.

Nuratu na cikin kwafa sai ga Zaliha ma ta leƙo kai ta fara kwafa. Kan kace me duk waɗanda ba su yi assignment ɗin ba sun yiwa desk ɗin su Zaytoonah rumfa. Zaytoonah na gefe ta cika ta yi fam, ba dama ta yi assignment ita ɗaya musamman ma dai idan Maths ne.

A haka za su kwafi assignment ɗin ta amma hakan ba zai hana su dinga tsokanarta ba.

Wasu ba su gama kwafa ba ma Mr Isaac Maths teacher ɗin su ya shigo saboda shi su ke da shi darasin farko.

Bayan ya gama darasin ranan ya tattara Assignment ɗin ya tafi da shi dan ya yi marking a staff room.

Ko da ya je sai ya ga kusan duk matan class ɗin sun cinye Assignment ɗin bayan ya san acikin matan Ajin Zaytoonah, Kabirat da Felicia su kaɗai ne su ka iya Maths sosai, su ke kuma fahimtar darussan sa. Bayan ya gama marking ɗin ne ya je class ya nemi izinin Malamin English ɗin su a kan yana son ganin Tijjani Zaytoonah.

A staff room ta sameshi. Faɗa Mr Isaac ya fara ma ta akan ta ya za ta ba da assignment ɗin ta a kwafa. Ba ta da ta cewa tunda ba iya magana ta ke mu su ba. Daga ƙarshe ya ce duk lokacin da ta yi assignment ya ga irin na ta a wajen wata sai ya ma ta bulala. Bayan ya gama faɗan ne ya ba ta books ɗin ya ce ta je ta raba a class.

Tafiya ta ke yi ɗauke da litattafan 'yan ajin su idon ta cike da hawaye.

She wasnt like this before, tana da rigima tanada ƙiriniya amma kuma cikin ƙanƙanin lokaci ta chanja. Ba komai ne ya chanja ta ba face yadda mutane ke ma ta magana akan ƙibanta. There are days da ta ke cewa ba za ta kuma zuwa school ba amma Mommy sai ta korata dole ta je. There are days da ta ke raba dare tana kuka duk dan saboda wata kalma da wani ko wata ya ma ta. A da ba ta ɗaukan abun da zafi amma a hankali-a hankali abun ya fara damunta. Ta kai ko kallonta ka yi sai ta ga kamar kana judging ɗin ƙibanta ne.

Ta sani ƙiba halittanta ne tunda mommyn ta ma na da ƙiba, but kamar yadda Mommy ke yawan faɗa shine ta bari ciye-ciyen ta ya sa ƙiban ya zama unhealthy.

"Shikenan dan inada ƙiba ba zan ci kayan daɗi ba" amsar ta kenan a mafiya yawancin lokutan da Mommyn ta ma ta magana akan ta rage ciye-ciye.

Da karfin hali ta ke zuwa makaranta saboda yadda kowacce rana ke zuwa ma ta da sabbin salo. Suna kam da su na tabo a jikin mutum da duk jikinta ya nuna.

Ba matan ba har mazan suna kiranta da annoying sunaye. Abinda ba ta sani ba shine ba ƙiban kaɗai ke jawo ma ta wannan izgilanci da 'yan class ɗin su ke yi ba, tun JSS1 har yanzu da su ke JSS 3 ita da Smally su ke ɗaukan na ɗaya da na biyu. Idan ta ɗauka wannan karan zaka ga wani karan Smally ya dage ya ƙarɓa itama wani term ɗin ta ƙwace kayanta haka su ke yi.

Saboda wannan jarraban judging ɗin ta da su ke yi ne ya sa ba ta da ƙawa. Ba ta da wanda ta ke wani mu'amala da ita, Nuratun ma ita ke shishshige ma ta...

***

Shekara biyu kenan da dawowar T J kuma cikin shekaru biyun nan abubuwa da dama sun faru ciki kuwa hadda wani faɗa da su ka yi wanda ya sa Maryam ɗin ta yi yaji, ba yaji kaɗai ba barin garin Zaria ta yi gaba ɗaya kuma ba Ringim ta je ba hakan ya saka T J cikin tashin hankali.

Abunda ya faru shine, kafin T J ya dawo Maryam ta yi sauka amma ba Hadda ba Tartil. Bayan tafiyan T J ƙasar waje ta shiga wani Islamiyya da ake yi da safiyar Asabat da Lahdi, a nan ta cigaba da ɗaukan karatu. To ganin T J ne malamin ta na farko ya sa ta ɗaga Waliman saukar ta zuwa sai ya dawo.

Bayan wata biyar sai gashi ya dawo ya kammala Phd ɗin sa ya zama Dr Tijjani Abubakar Modibbo Djibo.

Waliman saukan Maryam da ta kammala Phd ɗin sa su ka haɗa bayan sati biyu da dawowa aka yi.

To daren ranan saukar su ka fara buɗe kyaututtukan da aka ba ta, kasancewarta revert wato wacce ta musulunta kuma har ta tsaya ta yi karatun Ƙur'ani ta gama, hakan ya sa mutane da dama da su ka halacci waliman su ka ba ta kyaututtuka.

Bayan an gama buɗe kyaututtukan ne T J ya fito da makullin mota ya damƙa ma ta, har ta fara murna sai ya ce kyauta ce daga ƙanin sa Alhaji Muntari. Tana jin sunan Muntari ta yi cilli da key ɗin motar ta ce ya mayar ba ta so.

"Maryam wai mi ya ke faruwa ne? The last time da na ce mu je mu gaishe da matar sa da ba ta da lafiya kin ce Allah ya kiyaye ki taka gidan Muntari. Na tambayeki ba ki bani takamaimai amsar abinda na tambaya ba"

"Ni dai ka mayar ma sa key ɗin nan, idan ma akwai wani kyautan da ya fito daga hannunsa a nan ka cire ba na so"

"Maryam miyake faruwa ne? Akwai abinda ya miki da ya kamata na sani ne? Duk abinda yai Maryam bai kai ki dinga nuna ma sa ƙiyayya haka ba. Ba tarbiyyan musulunci ba ne"

A lokacin tana son faɗa ma sa komai gameda Muntari amma abinda ya faɗa ya ɓata ma ta rai shaiɗan ya kuma tunzura ta sai ta hau tabarmar fushi ta tashi ta bar ma sa ɗakin. Ranan a ɗakin Zaytoonah ta kwana.

Washegari dukkan su suka tashi da jin haushin junan su. Ba wanda yai magana da ɗan uwansa.

Zuwa yamma Tijjani ya nemi su sasanta tareda ba ta haƙurin tsawa da ya ma ta. Ce ma sa ta yi komai ya wuce ashe ba haka ba ne. Ranan da ya koma gidan Hajjo ta haɗa wa su daga cikin kayan ta ta bar gidan. Takarda ta bawa Zaytoonah akan idan Daddynta ya zo ta ba shi. T J bai samu ya zo duba su ba sai yamma liƙis. Zaytoonah ta ba wa T J envelope ɗin ta ce Mommy tun safe ba ta dawo ba har su ka dawo daga Islamiyya ba ta nan, Auwal ne ya mu su girki.

Hannu na rawa ya buɗe envelope ɗin ya fara karantawa.

*Ba kai kaɗai ke da 'yan uwa ba da za ka min gori akan Muntari. Na tafi neman 'yan uwana tunda ba daga sama na faɗo ba. Kar ka neme ni dan ba zan dawo ba sai na same su. TARBIYYAN MUSULUNCI bai ce na yi watsi da 'yan uwana ba ko da su kafirai ne*

Sun taɓa maganan sake neman 'yan uwan mahaifiyarta a shekarun baya ta hanyar ba da sanarwa a gidan talabijin a Calabar amma kuma T J ya nuna ma ta ba lallai su same su ba haka nan kuma zai iya yiwuwa garin son neman 'yan uwan mahaifiyarta ta ci karo da Uncle ɗin ta wanda ya kashe ma ta iyaye. Haka dai yai ta convincing ɗin ta har ta haƙura da batun neman, musamman ma da ya ke wani hidiman kashe kuɗin za su yi kuma ba su da kuɗin a lokacin.

Sun bar shi akan idan lokaci yayi da kan sa zai rakata su neme su.

Wasa-wasa kwana biyu ba Maryam ba dalilinta, faɗin tashin hankalin da T J ya shiga ma ɓata lokaci ne har Ringim ya je ba ta nan kuma Goggo ma ba ta da masaniyar inda ta tafi.

A kwana na huɗu ne ya shirya tafiya zuwa Calabar zai tafi nemanta duk da bai san ta ina zai fara ba. Idan bai samu labarin ta a nan ba dole ƙauyen su zai je.

Muntari ma jin labarin Maryam ba ta gida hakan ya tayar ma sa da hankali shima ya kawo motar sa da dreba akan su tafi neman tare. Har sun kama hanya

sun fara tafiya sun yi nisa aka kira wayar Muntari saboda lokacin ne aka fara yayin waya kuma Alhaji Muntari ya siya saboda waya a lokacin sai Alhaji wane ko Honorable wane.

Daga gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga ne aka yi kiran aka bawa Auwal yai magana da Muntari ya ce Mommy ta dawo. Jiki na rawa T J ya karɓi wayan ya shiga jerawa Auwal tambayoyi dan ya tabbatar gaskiya ne ba ƙarya ba.

Kusan shaɗayan dare ta gota su ka iso Zaria. Kai tsaye a ƙofar gidan Maryam su ka tsaya T J ya shiga gidan da gudu. Shi ma Muntari ya so shiga amma kuma baya son Maryam ta gan shi ta fara masifa dan haka ya ce Dreba ya juya da shi gida.

"Maryam why? Kasheni za ki yi ne? "Kin san tashin hankalin da na shiga a rashin ki? I love you Maryam, please dont ever leave me again" Ya faɗa kamar zai yi kuka yana rungume da ita ƙyam a jikin sa.

"Gidan Hajiya Fatima na je a Abuja" abunda ta faɗa kenan bayan ya saketa.

"Maryam dan Allah kar ki sake irin wasan nan kin ji. Idan na rasa ki mutuwa zan yi"

Ehem kawai ta iya cewa...

Daren ranan T J bai iya baccin kirki ba, motsi kaɗan ya tashi ya duba ko Maryam na nan ko kuma ta tafi.

A ɓangaren Maryam ta yi niyyar tafiya neman 'yan uwanta kamar yadda ta rubuta amma bayan ta bar gidan ta rasa ta ina za ta fara. Shekaru sun ja kuma ba ta da wani valueable information akan 'yan uwan mahaifiyarta da ya wuce sunan Kakanta Chief James Asibong, mahaifiyarta na da ƙanne 'yan biyu maza Paul and Peter sai sunan Kakarta mace Elizabeth. Wannan kaɗai bai isa ta same su ba ga uwa uba ba wani kuɗi ta riƙe a hannun ta ba.

Gidan Hajiya Fatima ta wuce a Abuja dan a lokacin tana buƙatar kaɗaici.

Kwana biyun da ta yi ba ta tareda Mijinta da 'ya'yan ta ba, kwata-kwata ba ta da kwanciyar hankali. T J da 'ya'yan su biyu su ne familyn ta yanzu. Ta ya ma za ta yi tunanin tafiya wata duniya ta bar 'ya'yan ta, jinin ta?.

May be she's just exaggerating about Muntari. Yes ya ma ta laifi a baya amma kuma tun bayan da yai aure da watanni kaɗan ya dena aiko ma ta da abubuwan da ya ke aikowa da. Ya dena shiga sabgar ta, iya ka ci yana aikowa 'ya'yan ta kyaututtuka. Bayan ta gama ba wa kanta haƙuri ta koma gidan ta...

T J bai sake ma ta maganar Muntari ba dan Kaffa-Kaffa ya ke da ita. Duk wani abun da zai ɓata ma ta rai har ta kawo tunanin rabuwa da shi baya so.

Shekara ɗaya bayan faruwan haka aka ma ta transfer zuwa Kaduna. T J bai yi wata-wata ba ya amince ma ta ta fara zuwa, duk da kuwa jigilar jeka ka dawo ta ke yi kullum tsakanin Zaria zuwa Kaduna. Bai taɓa complain ba duk da jigilar kuɗin mota da ake yi.

Wata takwas ta yi tana aiki ta ajiye aikin ta cewa T J za ta zama Barrister mai zaman kan ta kawai. Akwai wani private Law firm da wani babban Lawyer ya buɗe a Zaria nan ta koma tana zama a chamber ɗin su...


Page 15 shine Anorexia daga nan sai confessions. Nayi mistake wajen ɗaurawa