A new phase
by @azizat
*Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*
Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat
*Free page*
*19- a new phase*
Bismillahir Rahmanir Rahim
Tana kashe gas ta ji sallamar Auwal. Ta amsa sallamar tareda wucewa ta je ta buɗe ma sa ƙofa, indai ita ɗaya ke gidan haka ta ke kulle ƙofa da key saboda zuwan bazatan da Muntari ya tsiri yi, Yanzu kam ya fito ma ta da Maitan sa fili.
*"Har yanzu ina son auren ki Maryam. Ba zan kuma haƙura ba har sai kin zama tawa*
Abinda ya faɗa kenan wani rana da ya zo jim kaɗan bayan ya dawo daga kai Zaytoonah Lagos.
"Ya Allahu! Mommy ashe haka kika yi fama?"
Dariya Maryam ta yi ta ce "haba son, tun shekarar farko"
"Gaskiya na jinjina miki Mommy, Allah karatun nan da wahala"
"Sai ka ƙara ɗaura ɗamara, its not easy being a Barrister"
"Akwai juice ɗin kankana a fridge,ɗazu na sa inaga yayi sanyi yanzu"
"Barin watsa ruwa tukunna. Ina Junior?"
"Yayi bacci"
Shigewar Auwal ɗaki yai dai-dai da tsayuwar mota a ƙofar gidan na su.
Ko ba ta duba ba ta san Muntari ne, ta ja dogon tsaki ta wuce kitchen dan ta kwashe abincin da ta sauke.
Sallamar sa da Auwal ya ji ne ya sa shi fasa cire kaya ya fito falo yana gaisheshi. Da ba ya ma gaishe da Muntarin sai da Iya ta ma sa faɗa.
"Ina Salman?" Ya tambaya yana gyara hannun babbar rigan sa.
"Yana Islamiyya"
"Kira min Maryam" ya faɗa yana zama a kujera.
Bai musa ba ya shiga kitchen ya gaya ma ta saƙon Muntari duk da kuwa daga kitchen ɗin tana jin maganganun sa.
Sai da ta gama abin da za ta yi a kitchen ɗin kafin ta fito bayan kusan minti shabiyu.
"Na zo ne domin na shaida miki daga gobe Salman zai koma gida na. Ina ga aikin da ki ke yi ya ɗauke miki hankali akan tarbiyyan yaran ki"
Kallon Auwal ta yi wanda ya fahimci mi ta ke nufi yai saurin barin falon.
"Ban gane Salman zai koma gidan ka ba. Zaytoonah da ka ɗauke bai isheka ba sai ka koma kan Salman. Idan shima boarding school ɗin ne ka kaishi har bangon duniya idan ka ga dama" ta ƙarisa maganar tana juyawa za ta shige ciki.
"Salman na shan sigari" chak ta tsaya jin abinda ya ce.
"Sigari kuma?, ta nan kuma ka ɓullo. Ka ɗaurawa ɗan cikin ka sharri"
"Maryam kenan, ga shi nan ki karanta saƙo ne daga makarantar su. Shi da wasu ɗalibai an kama su suna shan sigari a bayan makaranta yau"
Ta karɓi takardar ta karanta.
"Na riga na kashe maganar amma na ɗau matakin da ya dace, dan haka ki haɗa kayan sa gobe zan aiko Dreba ya zo ya ɗauke shi"
"Ba inda Salman zai je. Ka kalleni da kyau ba inda zai je"
Miƙewa yai yana faɗin sai na gan shi.
Ta kasa gaskata abin da Muntari ya faɗa da kuma takardar makarantar su. Gashi an rubuta cewa an ba su suspension na sati ɗaya bayan an mu su bulala goma-goma a gaban assembly.
Innalillahi Salman da sigari a ina ya koyi shanta? A ina ma ya santa? Kwata-kwata nawa Salman ya ke yaro ɗan shekara shabiyu da ke JSS 2.
Ɗazu da ya dawo daga school ta gan shi wani iri da ta tambayeshi ko lafiya ce ma ta yai kan sa ke ciwo.
Zama ta yi a falon tana karkaɗa ƙafa hannunta riƙe da wayan radio, Auwal na gefe yana tararradin abinda zai faru. Dai-dai Maghrib ta kawo kai yai sallama ya shigo falon. Tuni dama idon sa yai ja saboda kuka da ya sha, ba ma Islamiyya ya je ba ya je ya ɓoye ne a ɗaya layin su. Yana son gayawa Mommy Abinda ya faru amma kuma yana tsoron ba za ta yarda da shi na.
Yana ganin Mommyn na sa hankalinsa ya kuma tashi.
"Zo nan" ta daka ma sa tsawa ganin ya ƙi ƙarasowa.
"Mommy..." saukar wayar a bayan sa ya hanashi magana.
"Sigari ko?, sigari Salman" ta sake yarɓa ma sa wayar. Ganin dai Mommy ba ta da niyyar sassautawa ya sa Auwal ya shiga tsakani yana ba ta haƙuri. Da ƙyar ta haƙura ta bar dukan Salman ta jefar da wayar tana huci ta shige ɗaki. Daren ranan kasa cin abinci ta yi saboda baƙin ciki, ba ta taɓa ɗauka renon yara da tarbiyyan su na da wahala ba sai yanzu da T J baya nan. Lokacin da ya je yai Phd ɗin sa ta ɗan wahala amma lokacin an san inda ya je hakanan ba su kai haka girma ba to yanzu kuma da su ka yi wayo shine ma su ke ba ta matsala.
Kafin su kwanta Auwal ya rarrashi Salman akan ya gaya ma sa gaskiyar abinda ya faru sai ya sanar da shi.
Lokacin break ne ya nemi littafin sa na Maths ya rasa to ya san Hassan wanda su ke zaune seat ɗaya ya tambayi littafin da safe akan zai kwafi home work da aka ba su da ke suna da Maths period immediately an dawo daga break. Salman ya hanashi littafin ya ce miya hanashi yai assignment ɗin.
A ta bayan school inda su Hassan ke yawan zama shi da gang ɗin sa ya je dan ya tambayeshi maganar littafin to yana zuwa ya samesu suna shan sigari, ya fara yiwa Hassan magana kenan sai ga wani Malamin su ya ritsasu a wajen.
Shi Hassan haushin Salman da ya ke ji ya sa shi rantsewa kan cewa Salman ma na sha. Shine aka haɗa su aka mu su hukunci, an kira numbar Maryam switch off shine Auwal ya ba da na Muntari aka kira tunda numban Maryam da T J kaɗai ne a file ɗin makaranta.
Auwal ya gamsu da bayanan sa dan da Salman na shan sigari da zai gane tunda tare su ke kwana.
Washegari da ƙyar Mommy ta nitsu ta saurari bayanin Auwal ta kuma haɗa da yiwa Salman ɗin tambayoyi wanda ya sake gamsar da ita gaskiya Salman ɗin ya faɗa. Abunka da lawyer tuni ta ce za ta je Makarantan a sake bibiyar case ɗin dan ba za a ɓatawa ɗanta suna ba.
Saboda ta ɗan rarrasheshi dukan da ta ma sa jiya sai ta buge da dafa ma sa favourite dish ɗin sa, ranan har da yi ma sa oil base lemon cake saboda yana so sosai. Da yamma kuwa sai ga Dreban Muntari wai ya zo ɗaukan Salman ta ce ma sa ya wuce ya tafi ba inda Salman zai je. Kashe gari sai ga Muntari da sassafe ya zo wai a dole zai tafi da Salman. Ta kuwa wankeshi tatas, ta haɗa mishi da cewa da Salman ya zauna gidan sa gara ta kai shi Almajiranci, hakan ya sosa ran Muntari.
Wasa-wasa sai ga shi har sati ana hayya-hayya tsakanin Maryam da Muntari, shi ya kafe akan dole zai tafi da Salman ita kuma ta ƙi. Har sawa yai Yayan T J wato Baban Auwal ya kirata akan ta bari Salman ya koma wajen Muntarin tunda dai kusa suke duk lokacin da ta ke son zuwa ganin sa za ta ganshi. Ta yi mamakin maganganunsa duba da yadda ita kuma ta riƙe ɗan sa Auwal tun yana yaro har yanzu da ya ke aji ɗaya a Jami'a amma ace na ta ɗan sai an kai shi wani waje, and gidan Muntari for that matter wanda ta san duk strategem na shi dan dai ya hana ta farinciki ne tunda ta ƙi shi.
A cikin satin kuwa maganar makarantar sa ta warware domin kuwa bayan Hassan ya sha rikitattun tambayoyi a wajen Barrister Maryam sai da ya faɗi gaskiyar Al'amari da bakin sa hakan ya sa aka janye punishment ɗin Salman tareda ba wa mahaifiyar sa haƙuri, aka kuma sa Hassan ɗin ya bashi haƙuri.
***
2 weeks later
In-hearing za su yi dan haka a offishin Alkali su ka haɗu inda za ayi sasantawa tsakaninta da Muntari da ya kai ƙaranta.
Tareda lawyansa ya zo ita kuwa ita da kan ta ta representing kan ta.
Lawyansa ya ba da bayani tareda gabatar da manufar Muntari na son ɗauke Salman a hannun Maryam, wai Junior ma idan ya shekara uku zai karɓeshi.
Bayan ya gama karanto labarun ƙaryan kuregen sa sannan Maryam ta faɗi na ta bayanin na son cigaba da kula da ɗan ta. Ta yi referencing da Auwal da ta yiwa tarbiyya har yanzu babu wanda ya taɓa yi ma sa shaida da mummunan hali.
Lawyan Muntari ya nuna cewa ai lokacin ba ita kaɗai ta yi tarbiyyan sa ba, lokacin ita da mijinta ne yanzu kuma ba ta da miji. Ya kuma kawo batun suspension ɗin da aka ba wa Salman saboda an kama shi yana shan cigari.
Kafin ta yi magana ta ɗauko takardar ban haƙuri da makaranta ta rubuta saboda sharrin da aka yiwa Salman.
Nan jikin Lawyan Muntari yai sanyi amma duk da haka bai gaza ba ya kawo batun yadda rashin Uba a rayuwar Salman ka iya jawo taɓarɓarewar tarbiyyan sa, sannan ko a musulunci Muntari ya fi Maryam iko da Salman, Uba ya ke ga Salman.
Maryam ta yi murmushin gefen baki ta ce "idan har ba zan iya ba wa ɗana tarbiyya mai kyau ba to ba ta inda Muntari zai iya ba shi tarbiyya. Muntari mutum ne mai shan giya, idan ya musa hakan za a iya kiran matar sa ta ba da shaida ko kuma aje a binciki gidan sa za a samu shaidar giya. Na biyu Muntari dukan mata ya ke yi ga report nan na dukan matar sa da yai lokacin tana ɗauke da ciki wata shida, akwai numbar wayar likitan da ya duba ta lokacin da aka kaita asibiti zai iya ba da shaida kan hakan. Muntari ba shi da lokacin kan sa saboda ɗan kasuwa ne yau Kano gobe Lagos. Idan wannan ba su gamsar ba inada wasu hujjojin da zai tabbatar da rashin dacewar zaman Salman tareda shi"
Da Alkali bai ba ta nasara ba ta yi niyyar faɗin nemanta da ya ke yi da aurenta lokacin da T J ya ke ƙasar waje dan har photo copy na letters da cards ɗin da ya ke aiko ma ta ta zo da shi. Ta yi niyyar sanar da Alkali ƙoƙarin fyaɗe da Muntari ya ma ta a shekarun baya amma Alkali ya ba ta nasara kuma Muntari bai ja da hakan ba dan yana tsoron tone-tone. Idan aka je bincika ma sa gida neman giya ba giya kaɗai za a samu ba har da Ƙwaya.
Maryam ta fito daga office ɗin ranta fari. Tana dai-dai da Muntari duk inda zai je ya dawo...
Ta yi kewar 'yar ta ba kaɗan ba, amma ba ta da lokaci ko means na zuwa ma ta visiting har Lagos ta dai ma ta alƙawarin za ta je graduation ɗin su.
Bayan maganar Salman ta lafa Muntari ya zo da wata fitinar kuma, wai yana so ya sai da gidan da Maryam ke ciki saboda za'a raba gadon T J. Yayi hakan ne dan ta tada hankalinta sai kuma ta ce ma sa Bismillah idan ya isa ya siyar tunda gida dai da sunanta aka siya kumama takardun gidan na hannunta sunan ta ne kuma akai. Da ya ga ba ta damu ba sai ya je ya kawo dilallan gida aka fara cinikin gida har da zuwa ya ce ma ta wai cinikin gida ya faɗa dan haka ta fara shirin tashi. Hakan ya sa ta buga waya ta kira Baffa Umar wanda Yaya ya ke ga mahaifin su, cikin 'ya'yan Modibbo maza shi kaɗai ke raye yanzu.
Shari'a ta kai su sai da aka je Ringim aka yi family meeting aka yiwa Muntari tatas. Wannan karan hatta Iya sai da ta nuna rashin dacewar abunda ya ke son yi. Cike da ɓacin rai ya bar Ringim yana jin haushin ta yadda Maryam ke winning ɗin sa duk ta inda ya ɓullo.
Zuwa yai ya fara tunanin mi zai yi ya baƙantawa Maryam rai, mi zai yi Maryam ta yi kuka da hawayen ta ta zo ta nemeshi tana durƙusawa tana roƙon ya sassauta ma ta. Ya jima yana tunanin abunda zai yi kafin zuciyar sa ta bashi amsa da Zaytoonah...
***
Satin farko da aka kai Zaytoonah makaranta kullum sai ta yi kuka amma haɗuwarta da Bilkisu sai ta yiwa kan ta karatun ta nitsu. Bilkisu mata-maza ce wacce halittan ta na mace ya fi na namiji yawa amma yanzu an yi mata aiki ta koma mace sai dai idan ka ga ɗan ƙaramin gefun da ta ke da shi wanda ta ke yawan cireshi sai kuma muryarta da ya ke a buɗe kaman ta maza.
Mahaifin Bilki makaniki ne da ke aiki a Lagos mutum ne da rayuwar wajen ya sa shi zama taƙadirin ɗan bariki. Bayan ta bayyana ma sa 'yar da matar sa ta haifa mata-maza ce bai jima ba ya sawwaƙa wa Kande wacce ba ta san inda za ta je ba a faɗin Lagos. Daga baya ta samu wajen ma su bara tana zama tana bara. Iyayenta sun rasu da jimawa, 'yan uwan ubanta ba su riƙeta da kyau ba. Lokacin da Isa ya fara 'yan ɗauke-ɗauke da rashin ji aka haɗa su aure yana shekara shatakwas tana sha uku. Sun shekara biyu a ƙauyen su kafin Isa ya tafi Lagos, shiru-shiru bai dawo ba sai da ya kai wata tara. Da ya zo ya ɗauki Kande su ka koma Lagos da zama tunda su ka tafi kuwa bai sake waiwayan ƙauyen su ba itama bai bari ta je ba.
Bilki ta taso cikin tsangwama da ƙyama. Bayan Kande ta yi shekara uku tana bara kuɗin da ta tara ta kama mu su haya a wani ɗan tsurkukun ɗaki, tana sana'a goma da ishirin dan ta ciyar da su.
A shekarun Bilki goma shaɗaya ne depression ya sa ta a gaba har ta kai ta yi yunƙurin kashe kanta. A wajen da ta ke son faɗowa daga bridge ne wata mata ta ganta ta ceci rayuwar ta.
Madam Bisola ita ta inganta rayuwar Bilki. Ba ta taɓa haihuwa ba kuma tana da dukiya shiyasa ta ke son yara sosai. Ita ta biya aka yiwa Bilki aiki aka maidata mace kuma ita ta sata a makaranta tun daga primary da ta ƙarisa zuwa yanzu da ta ke secondary. Kande ma yanzu kasuwanci ta ke yi kuma Allah ya rufa ma ta asiri, ta sake wani auren inda ta auri wani makaho da su ka yi zaman bara da shi amma yanzu ya dena har da 'ya'yan su biyu ma.
Labarin Bilki ya taɓa zuciyar Zaytoonah sosai. Ashe ita na ta kukan na jin daɗi ne lokacin da ta ke kuka idan ana bullying ɗinta saboda ƙibarta. Ya za ta ji idan da ita ce Allah ya halicce ta kamar Bilki? Dole ta godewa Allah bisa ni'imar da Allah ya ma ta. Akwai mutane dayawa irin Bilki da ba su samu privilage ɗin da aka yi mu su aiki ba. Kamar yadda Mommynta ke yawan faɗa ma ta cewa yadda ta ke ƙin ƙibarta akwai ma su nema ido rufe.
Ta kuma haɗuwa da wata 'yar class na su mai suna Pelumi wacce ake kira paper saboda sirantakar ta. Yarinyar kuma ba sickler ba ba komai ba amma siririya ce har na muntaha. Ba ta da shape ko kaɗan komai ya kwanta.
Wasa-wasa kafin first term ya ƙare Zaytoonah ta yi baki, abu da zama da Yarabawa wanda ba ƙaramin iya yanka magana su ka yi ba . Yadda ta ke zuba kamar Anty Rukky 😂.
Cikin ikon Allah ta maida hankalinta kan karatu sosai ta cire damuwa a ranta, she wants to make her Mommy proud kamar yadda ta ma ta Alkawari. A lokacin hutu tana murnan za ta je gida sai ga Muntari ya zo ya ɗauketa ya kaita gidan sa na Lagos wai a nan za ta yi hutunta ba zuwa gida. Ta yi kuka kam amma babu ruwan sa.
Daɗin abin ma a ɗaya ɓangare na gidan akwai wasu magidanta Igbo da ya ba wa haya Mr Emmanuel Okereke da matar sa Mrs Florence da 'ya'yan su biyu Miracle da Joseph. A wajen su ta ke wuni dan mai aikin sa sai yana gari ta ke zuwa.
Ɓangaren Maryam da ba ta ga ya dawo da Zaytoonah gida ba da akayi hutu hankalinta sai ya mugun tashi tana tsoron kar ya je ya yiwa 'yarta fyaɗe ko wani mummunan abin. Sai da Zaytoonah ta kira ta da wayar Mrs Florence kafin hankalinta ya kwanta. Ƙarshe ta roƙi alfarma a wajen su akan Dan Allah su dinga kula ma ta da 'ya.
Jan kunne sosai ta yiwa Zaytoonah akan duk lokacin da Muntari ya dawo ta yi hankali da shi saboda yana da matsalar ƙwaƙwalwa.
A hutun second semester kuma sai yai abun kai ya taho da ita. Maryam ta yi niyyar da bai je ya ɗauko Zaytoonah ba da kuɗi za ta turawa su Mrs Florence ta roƙe su su sa ma ta Zaytoonah a babbar motar Macapolo ta zo gida.
Zaytoonah ta ƙara kyau ta yi fresh da ita, whether ɗin Lagos ya amshi jikinta sosai. Maimakon ace ta rame kowa cewa yai ƙiba da ƙara. Zama da mutane daban-daban yare daban-daban ya sa ta ƙara wayewa in terms of socialization. Duk wani shiru-shiru da kunya da ta ke da shi babu yanzu. Falli da tashen 'yanmatan taka ta ke ji da shi.
Ita kan ta Maryam ta ga positive changes a wajen 'yar tata wanda ta san rayuwar boarding ce ta gyarata haka.
***
A wannan hutun ne kuma Hajiya Fatima wacce Maryam ta zauna a gidan su lokacin da ta ke Law school a Abuja ta kirata tana gayyatar ta bikin Autan ta Mardiyya da za ayi har da cewa a taho ma ta da 'yarta Zaytoonah. Hajiyar na son Zaytoonah sosai, duk da an jima da rabuwa ba ta manta da Maryam ba balle Zaytoonah da aka haifa a gabanta. Lokacin T J yana nan akwai lokacin da ta roƙi alfarmar Zaytoonah ta zo ta ma ta hutu, duk da bai cika son ire-iren hutun nan ba amma ya amince amma kwana goma kacal ya bayar sai dai da ta tafi sai da tayi kwana shabiyar kafin Dreba ya dawo da ita ɗauke da tsaraba.
Zaytoonah da ji za aje Abuja da ita ta fara murna ta cika gida da ihu.
"Lafiyar ki ƙalau kuwa?" Auwal ya tambaya ganin yadda Zaytoonah ke tsalle wanda ya sa shi rasa nitsuwar sa na 'yan daƙiƙu.
"Dole ka ce haka, daga ji za a je Abuja da ita shine ta ke wannan kauɗin"
"Saura aje a mu su ƙauyanci"
Zaytoonah ta buga hips ɗinta tana faɗin "Ya Auwal wuce nan kuma. Wallahi wuce nan"
"Ki ka yi kauɗin nan kuma sai dai ki ji ki a silencer" Mommy ta faɗa tana dariya
Ita kuwa Zaytoonah ta fara faɗin "haba haba ai indai ban je bikin nan ba ba mai zuwa a gidan nan"...
Kayan anko da komai an ɗinka mu su measurement kawai su ka tura, amma komai Hajiya ce ta yi. Bikin za a fara shi ranan Laraba a ƙare Asabat. Laraba za ayi bridal shower, Alhamis za ayi kamu sai Jummu'a ayi dinner, ranan Asabat kuma za'ayi reception bayan ɗaurin aure, biki ne na manya saboda Mardiyya ɗan wani ƙusar gwamnati za ta aura.
Ranan Alhamis su ka isa Abuja da rana. Inda ake ta shirye-shiryen Kamu.
Tun a gida Mommy ta ce ba za ta je dinner ba, za ta je Kamu da reception tunda da rana za ayi ba ta yarda da zuwa dinner ɗin daren nan ba, itama ba zuwa za ta yi ba.
Zaytoonah na ganin yadda ake ta shirye-shiryen zuwa Dinner sai ƙunƙuni ta ke yi. Ɗaki ɗaya aka basu su uku, Ita da Mommy da Junior da aka zo da shi.
Tunda gidan ya watse tsit ka ke ji, Maryam ta kwanta da Junior ita kuma Zaytoonah na gefe tana jiran baccinta yai nisa sosai ta fita ta san ba za a rasa wanda su ka rage ba su tafi ba.
A hankali ta buɗe ƙofa bayan ta tabbatar Mommy ta yi nisa da bacci, tana fita ta fara baza ido ko za ta ga mutane 'yan zuwa dinner. Tana fitowa compound ɗin da takalmi a hannu ta ga mota ɗaya tsaye ana jiran wata mata ta fito da ta yi mantuwa ta koma. Zaytoonah na zuwa ta kutsa kai cikin mota. Aka fara cewa ta fito don akwai wacce ke wajen amma Zaytoonah ta yi biris da su, ta juyar da kai gefe tana turo baki, su ka yi ta zage-zage ƙarshe da wancan ta zo haka mutum biyu su ka zauna a gaba. Dreba ya ja su sai Sheraton Hotel.
Tun a mota ta ke tanka mu su ganin abun na su ya ƙi ƙarewa dan haka da haushinta kowacce ta fito daga motar. Zaytoonah ta ce "aikin ɓur inji tusa"
Tsayawa ta yi saka takalmin ta wanda ya ke wedges sandal mai tudu dan ba ta iya saka heel ba.
Ɗagowan da za ta yi ta ga sun shige. Ta tambayi security aka directing ɗinta zuwa wajen da ake event ɗin.
Ta zo shiga aka sa hannu aka tare.
"Ma'am gate pass please"
Ta yi saurin buɗe purse ɗinta dan ta san cewa dinner ɗin card permit ne. Wayam ba komai. Innalillahi ta furta a hankali.
Shiyasa indai iyayenka ba sa so ka yi abu ka yi da wuya idan ba ka samu matsala ba. Ta manta katin a saman drawer.
"You see, i'm a very very very close relative to the bride. Infact i'm the bride younger Sister"
Dukkan su biyu su ka zuba ma ta ido suna jin bayani.
"I forgot the card at home, please let me enter"
"Sorry Ma'am for security issue we cant allow you to enter"
Ba ta zaci cikin su biyun akwai mai jin Hausa ba dan haka ta ce " Dan Kakan ku ba ku ga ankon gidan su Amarya a jikina ba ne?"
"Dan Kakan mu ko?" Ɗaya baƙin ya faɗa yana jijjiga kai
"Ya Subhanallah! Oga sir ni ba abinda na ce ba kenan. Cewa na yi..."
"Ki tafi kawai dan ba za ki shiga ba indai ba ki da kati tunda abin na ki rashin kunya ne"
Ɗayan da baya jin Hausa ya tambayi mi ta ce shi kuwa ya ma sa bayani. Shima ya jaddada ma ta indai ba ta da pass to ta koma gida.
Ta haɗa hannu tana ba su haƙuri amma su ka ma juya su ka ƙi kallon ta.
Cikin takunsa mai cike da haiba da izza ya ke shigowa wajen. Da ka ganshi ka san yana cikin kwanciyar hankali domin fiskarsa shimfiɗe ta ke da annuri ya kusa kai wa wajen wayar sa ta hau ruri ya ɗaga wayar haɗe da sallama cikin muryarsa mai sanyi da saka nitsuwa ga me saurare.
"One two three go" ta irga a zuciyarta ta kutsa kai za ta shiga ta karfi saboda ta ga hankalinsu baya wajenta amma tana kutsa kai hannun su ya dawo da ita.
Dariyar yaƙe ta yi ta ce "Oh! ashe dai kun ganni"
Yana daga tsaye yana amsa waya bai san lokacin da murmushi ya suɓuce ma sa ba. Bai ji mi ta ce ba amma ya ga lokacin da ta fakaici idon securities ɗin za ta shiga su kuma su ka maidata waje dan duk jan balance da ta yi kafin ta yi yunƙurin shiga ciki suna kallonta ta wutsiyar ido.
"See dis pikin fa, wai wayo za ki mana"
"Haba Kawu, kana ɗan uwa Bahaushe amma ba za ka yi haƙuri ba"
"Ni ba bahaushe ba ne na dai zauna da Hausawa"
"To ka gani, ai an riga an zama ɗaya"
Shi yarinyar dariya ta ke bashi, da gani ba za ta wuce 16/17yrs ba dan girman jiki ne kawai ba shekaru.
Tana cikin yi mu su daɗin baki dan su barta ta shiga ciki ya iso wajen. Suna ganin sa su ka ƙame da ganin sa ba ƙaramin mutum ba ne, yana shirin fito da card ɗin shi Zaytoonah ta matso jikinsa sosai har kamar za ta shige babbar rigan sa. "Uncle Muhammad ashe kana tafe" ta faɗa tana washe baki
Securities ɗin saura kaɗan su yi dariya saboda yadda Zaytoonah ta yi ka san ƙarya ne.
Ta kalle su ta ce "He's my Uncle, we are family, ba ku ga idon mu ba iri ɗaya, same to same"
Zai yi magana cikin shagwaɓa ta ce "Uncle Muhammad tun ɗazu na ke jiranka, sun ƙi bari na na shiga" ta yi magana tana kallon sa amma kwarjininsa ya sa ta yi saurin saukar da idonta ƙasa.
Ɗaya mai jin Hausan kam sai da ya fashe da dariya. Yana ganin Uncle ɗin dole da Zaytoonah ta samu.
Mutumin ya mu su nuni da su barta ta shiga dan haka su ka buɗe mu su waje. Suna shiga Zaytoonah ta juya tana mu su gwalo. Juyowar da za ta yi ta ga mutumin na kallonta ta yi saurin haɗe fiska ta ce "angode, amma ko da ba ka zo ba dama zan shiga dan bikin gidan mu ne"
Murmushi yai ya yi gaba ya barta tana gyara ɗaurin ɗankwalinta.
Tana shiga hall ɗin kuwa ta fara baza ido tana neman Hajiya Fatima. Chan ta hangota ta ƙarisa kujeran su tana dariya. Wani kujeran ta saka a wajen ta zauna cikin Manya.
Tunda ta shigo ya ke binta da kallo har ya ga inda ta zauna. Yadda ya ga ta sake a wajen tana taɗi tana dariya ya sa ya amince da batun ta na cewa bikin gidan su ne, saboda ankon tawagar Amarya ta sa, yana ganin relative ɗin Amarya ce.
Ba tareda yayi niyyar kallonta ba juyawar da zai yi ya hangota tana cin abinci, in between mouthful tana surutu, ga cinyar kaza a hannunta anci rabi saura rabi. Yarinyar kam tana da abun dariya ya faɗa a ran sa...