Mrs Zaytoonah
by @azizat
*Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*
Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat
*Last Free page*
*20-Mrs Zaytoonah*
Bismillahir Rahmanir Rahim
Shirye-shirye ake yi na zuwa graduation ɗin Zaytoonah. Jiya Muntari ya kawo ma ta ticket ɗin jirgi amma ta yi banza da shi ta ce ya kwashe tsiyar sa ba ta so. Ta riga ta tsara tafiyar tuntuni dan haka ba ta buƙatar taimakon sa, da gayya ya tura 'yarta gari mai nisa dan kar ta dinga zuwa ma ta visiting. A Kaduna za su je su shiga babbar Mota da zai kai su Lagos. Hatta inda za su sauka sai da ta tsara shi kafin ta ɗau aniyar tafiyar. Gidan wata ƙwarta ne da su ka yi Law school tare a Abuja. Lokacin da su ka yi Law school ɗin ba ta yi aure ba amma yanzu aure ya kai ta zama a garin Lagos.
Dukkan su sabbin ɗinkuna su ka yi har Auwal ma, Salman da Junior ɗinki iri ɗaya ta mu su.
Ana gobe za su tafi ta je gidan Muntari ta yiwa Hanne sallama wacce yanzu zaman ƙaddara kawai ta ke da Muntari. Lokacin da ta ke da cikin Maryam ta gano Muntari Maryam ɗin Tijjani ya ke so. Hotunan ta birjik a kan gadon sa watarana da ta shiga ɗakin sa za ta kira shi saboda yayi baƙi.
Tana cikin duba hotunan ya fito daga banɗaki.
Hawaye fal a idonta ta ce "yanzu dama duk wannan haukar da ka ke yi akan Maryam ashe Anty Maryam ɗin Hamma Tijjani ka ke so?"
"Ba na son shishshigi ki tashi ki bar min ɗaki"
"Haba Muntari ka ji tsoron Allah. Ka san fa tana da aure kuma Yayan ka ta aura amma ka gaza haƙura da ita ba wallahi ka ji kunya"
"Kar ki sake min maganar banza Hannatu, zan mugun saɓa miki"
"Tir da wannan halin rashin kunyar na ka, haba Muntari ko kunyar nan ta Fulani ba ka da ita balle ta musulunci. Matar Yayan ka fa, Matar Yayan ka Uwa ɗaya Uba ɗaya"
Harzuƙa yai da kalamanta ya shiga dukanta. Ihun ta da Iya ta ji ne ya sa ta haura sama da sauri ta je ta samu Muntari na dukan Hanne wanda sai da aka haɗa da zuwa Asibiti saboda jini da ya fara fitowa daga gabanta. Da rabon Maryam za ta zo duniya ne da ta mutu tun a ciki a lokacin.
Lokacin Iya ta yi fushi sosai da Muntari amma ba ruwan sa ko haƙuri bai ba ta ba, bai kuma nuna ya damu ba. Daga baya kuma a cikin shekarar ya biya ma ta Umara nan da nan zance ya wuce a wajen Hajiya Iya. Lokacin da ta dawo sai da ta je Ringim ta yi sati biyar kafin ta dawo. Ana zuwa ana ma ta barka sai burga ta ke yi a dole ita Hajiya. Wani abun idan Iya ta yi sai ka kama baki saboda shirme ne kawai da jahilci. A lokacin kuwa an samu cikin 'yan uwa dayawa da su ka yi tallen 'ya'yan su ko za ta haɗasu Aure da Muntari amma ta sani ko ta amince ma kunya za ta sha dan Muntari ba Tijjani ba ne, Hanne ma da ya yake zama da ita balle a masa zancen ƙarin aure.
Da ke Allah ne ke kiran bayin sa a shekara na gaba da Iya ta je Umara Goggo ta je Hajji. Mijin jikanta Asma'u ne ya biya mu su ita da Asma'un da mahaifiyar sa da wata yayar sa su ka yi tafiyar ayari.
Ikon Allah sai kallo domin kuwa ganin Goggo ta je Hajji ya sa tsohon kishi da Hassadar Iya ya tashi. Ta shiga yiwa Muntari maganar itama na son zuwa Hajji. Da farko bai kulata ba daga baya kuma da 'yan mutuncin su ka shigeshi sai ya biya ma ta. Yanzu haka kwanan ta biyu da dawowa daga Hajjin ta wuce Ringim satin ta ɗaya ma a chan.
Maryam da ta je wajen Hanne ne ta ke ma ta tsegumin komai. Maryam ta ce ita Iya ta daina ba ta mamaki tausayi ma ta ke ba ta. Su na cikin hiran ne sai ga Humairah ta shigo gidan tana ganin su zaune amma ta kauda kai za ta wuce su, Hanne ta ce "yanzu Humairah cewa za ki yi ba ki ganmu ba? Idan ni ba za ki gaisheni ba Mommyn ki fa?"
Ta wani juyo a yangance ta ce "Sannu Mommyn Zaytoonah"
Maryam ta ce "Sannu Humairah ya karatu?"
"Ƙalau" ta faɗa ta wuce ba tareda ta yiwa Hanne magana ba.
"Humairah ce ta zama haka?" Maryam ta faɗa tana kallon Hanne"
"Ai Anty Maryam kaɗan ma ki ka gani, a gidan nan ba mai gaya ma ta magana ta ji idan ba Muntari ba shi kuma ba ruwansa da tarbiyyan ta. Shi dai kawai indai kuɗi ta ke buƙata zai ba ta. Yanzu haka wata ƙatuwar wayar blackberry ya siya ma ta"
Maryam ta ce Allah ya kyauta...
Zaytoonah ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba ganin dukka 'yan gidan su sun zo ma ta. Sai nan nan ta ke da su, tana nunawa manyan ƙawayenta iyayenta. Anci an sha kuma an yi hotuna. Zaytoonah ta karɓi kyaututtuka har guda uku wanda ya sa Maryam ta yi farinciki da chanjawar 'yar tata. Atleast ba ta bari ɓatar Mahaifinsu ya dawo da ita baya ba.
Bayan kwana biyu da yin graduation ɗin dukkan su suka dawo gida.
Bayan ta huta ta tafi hutu Ringim dan ta jima ma ba ta je ba. Mutum biyu su ke sa ta farinciki su ke kuma sa ta ɗokin zuwa Ringim ɗin wato Yadikko da Goggo. To Yadikko ta rasu saura Goggo, da ta je ma a ɗakinta ta sauka ta dinga ma ta tsiya wai ta zama gurguwa tunda ba ta iya tafiya mai nisa sai da sanda.
A kwananta na biyar da zuwa gidan da yammaci tana farfajiyyan gidan tana yiwa Goggo yankan farce, wasu mata na wanke masara mai yawa dan zai yi rabin buhu za su jiƙashi saboda a bushar a niƙa shi saboda garin tuwo.
Tana yiwa Goggo yankan farce tana tanka mu su saboda surutun su da gulman su yayi yawa sai ga yaro yayi sallama wai ana kiran Zaytoonah. Zaytoonah ta ce waye? yaron ya ce bai sani ba.
"Ka ce ma sa ba ta nan"
"Ke kuma kin yi mashinshini za ki kore shi? Ki ka sani ko shi ne Angon"
"Allah ya kiyaye. Ba Mashinshini ba Mai lashe mutane na samu"
"Allah ya baki haƙuri jikar Iya da Goggo, 'ya a wajen Boɗɗiyon Tijjani"
"Gyara maganar ki na baki ƙwandala. Jika ce a wajen Goggo da Baffah Habu Allah ya jiƙan rai" tana maganar kuma sai ga Iya ta fito daga ɗaki kuma sarai ta ji mi Zaytoonah ta ce. Ranta ya sosu da maganar Zaytoonan amma ya za ta yi tunda koma mi Zaytoonah ta ce ita ta jawa kan ta...
Washegari ma sai ga shi an sake aikowa wai Zaytoonah ta fito. Wannan karan kam so ta ke ta ga wani ɗan iskan ne ke neman faɗan ta.
"Ehen, miye ka ke nemana?" ta faɗa tana riƙe ƙugu.
Sai wani sunne kai ya ke yi irin kunyar nan.
"Idan ba ka da abin faɗa ni zan shiga ciki kuma idan ka ƙara sawa a kirani tafasashshen ruwan zafi zan zo na zuba ma ka"
"Dama Baffa Muntari ne ya ce na zo mu dai-dai ta"
Ta fashe da dariya har da riƙe ciki. Sai da ta yi mai isharta kafin ta ce "mu dai-dai ta, Kaji ka ke sayarwa ko Raguna?"
Ya ɗan ɗago ya kalleta amma yadda ta tsareshi da ido ya sa shi sunkuyar da kai ya ce "shi ne ya turoni wai mu yi zance mu fahimci juna"
"Bakin ka ne mu fahimci junan ai. Look, kar ka ƙara aikowa a kirani dan zan watsa ma ka ruwan zafi" Ta shige gida ta barshi a tsaye.
Wonders shall never end. Wai Uncle Muntari ne zai turo ma ta saurayi.
Haka dai ta yi sati biyu ta dawo gida har lokacin kuma Bello kamar yadda ta gane sunan shi daga baya bai sake zuwa ba. Matan gidan su kuwa duk wacce ta ma ta maganar aure tsayawa ta ke ta silleta son ran ta.
Da ta koma gida ne cikin taɗi ta yiwa Mommy maganar abinda ya faru. Nan da nan Maryam ta ankara da abinda Muntari ke shirin yi. Wato nufinsa auren dole zai yiwa Zaytoonah. To kuwa tana dai-dai da shi dan abinda ba za ta taɓa bari ya faru ba ne. Amma dai bari ya zo ya sameta da maganar za ta nuna ma sa cewa ita ta haifi Zaytoonah ba shi ba.
Kyautar sabuwar waya andriod Maryam ta siyawa Zaytoonah lokacin da result ɗin ta na WAEC ya fito mai kyau. Tana da A biyu da B guda biyar sai C uku.
Tuni ta saka numbar ƙawayenta wanda su ke da waya aka hau network...
Ranan ta dawo daga Islamiyya ta samu Muntari da Mommynta a falo suna masifa. Ta jima da sanin rashin jituwar da ke tsakanin Uncle Muntari da Mommyn na ta, duk da ma ba ta san takamaimai miya jawo hakan ba.
Ko gaishe su ba ta yi ba ta wuce ciki amma ta kasa kunne daga jikin ƙofa tana jin mi ake faɗi.
"Ka san Allah, ko sama da ƙasa za su haɗu ba ka isa ka aurar min da 'ya ba. 'Ya ta karatu za ta yi, ban roƙe ka kuɗi ba balle ka ce za ka takura da hidimar ta. Idan hauka ka ke yi ka je ka nemi magani amma ba ka isa ba Muntari, ka yi kaɗan"
"Maryam kenan, Zaytoonah dai sunan Tijjani Abubakar ta ke amsawa ba na Maryam ba. Dan haka a matsayina na shaƙiƙin Tijjani na yiwa 'yar sa miji. Ki gama borin ki nan da wata biyu za ayi biki"
"Idan mafarki ka ke yi ka farka Muntari domin indai nina haifi Zaytoonah ba ka isa ka ma ta auren dole ba ina dai-dai da kai"
Yai Murmushin mugunta ya ce "to mu zuba mu gani"
Bayan tafiyar Muntari Zaytoonah ta fito da gudu ta faɗa jikin Mommy tana kuka. "Mommy do something dan wallahi idan aka min auren dole kashe mijin zan yi ko kuma na kashe kai na"
Maryam ta ce " ba zai kai ga haka ba ma Insha Allah"
Bayan kwana biyu Maryam ta kira Goggo ta sanar da ita abinda Muntari ya ce. Goggo ta ce idan ta samu lokaci ta taho Ringim ayi maganar.
Abunda Maryam ba ta sani ba shine. Tun zuwan Zaytoonah hutu Muntari ya fara mission ɗin sa ta hanyar hura wutar fitina cikin familyn su. Dalilan da ya gabatar na son aurar da Zaytoonah mafiya yawa cikin family sun gamsu da shi. Goggo da ta ji batun da ake a cikin gida sai ta samu Iya da maganar lokacin ba ta koma Zaria ba. Iya ta ce Muntari Uba ya ke ga Zaytoonah ba zai cutar da ita ba. Da ta ga abin yana son zama gori sai ta yi shiru ta bar zancen.
Muntari cewa yai Zaytoonah ta yi girma dayawa sannan tana da rashin kunya da reni. Ga uwa uba shiriritar 'yan fari da ke damunta.
Kusan kaf matan cikin gida sun yi gulmar Zaytoonah lokacin da ta koma Zaria hakan ya sa mazajen su da su ka ji dalilin aurar da Zaytoonah da Muntari ke yi ya sa su ka fara yaba ma sa acewar sa yana ƙoƙarin tseratar da mutuncin Zaytoonah ne kafin ta lalace ace saboda Ubanta baya nan ne aka kasa yi ma ta tarbiyya mai kyau.
Ba kaɗai dalilin ba ne ya sa su ka amince, Muntari ya jima yana yiwa 'yan uwansa Alkhairi na kuɗi da kayan abinci. Wanda ya ke ganin za su kawo ma sa cikas akan manufar sa tuni ya yi mu su abinda ba za su taɓa yi ma sa gargadama ba. Ya biya mu su kujeran Makkah.
Abu dai ya koma ba don Allah su ka amince da Muntari ba sai dan 'yan chanji da ya ɗauki watanni yana ba su...
Da Maryam ta je Ringim ta samu Goggo su ka tattauna abinda ke faruwa. Maryam ta yi mamakin goyon baya da 'yan uwan T J su ka ba wa Muntari a wannan hukunci na son zuciya da ya ke shirin yi. Dan kaf sun yadda da auren Zaytoonah da Bello wanda yaron shekaransa ashirin da ɗaya, sakandare kaɗai yai ya kama aikin makanike, a ƙarƙashin wani ya ke ba wai yana da garejin sa ba ne.
Har wajen Baffah Umar ta je akan ta ganar da shi kuskuren wannan haɗin da Muntari ke yi. Amma sai ya ce ma ta indai saboda karatun Zaytoonah ta ke tsoro shi Muntarin yayi alkawarin zai biyawa Zaytoonah ta cigaba da makaranta bayan aure. Hadda cewa ai karatun 'ya mace a gidan mijinta ya fi kwanciyar hankali.
Ba ta samu abinda ta yi niyya ba dan haka ta chanja maganar ta hanyar roƙon a bari Zaytoonah ta auri Auwal instead of Bello. Shi Auwal ya ma fi kusanci da Zaytoonan kuma tare su ka taso sun saba da juna. Baffa Umar ya ce to magana ce mai kyau amma bari yai shawara da sauran 'yan uwa tukunna.
Kamar wanda Muntari ya mu su magani haka su ka haɗu su ka ƙi karɓan wannan shawara. Su ka ce anriga anyi nisa da zancen Bello kuma ba daɗi azo a ce an fasa hakan zai jawo matsala tunda da Bellon da Auwal ɗin 'yan uwan juna ne.
Maryam na komawa Zaria ta tattara kayan Zaytoonah ta ɗauketa su ka fita, ita kan ta Zaytoonah ba ta san inda za su je ba kawai binta ta ke yi. Yadda ta dawo babu walwala a fiskarta ya sa Zaytoonah ta sha jinin jikinta.
Bauchi su ka je inda Maryam ta damƙawa Pendo amanar Zaytoonah zuwa lokacin da za ta buƙace ta. Ta kuma ja ma ta kunne akan kar ta yarda ta faɗawa kowa kan cewa Zaytoonah na wajen ta. Mijin Pendo lecturer ne a Jami'ar ATBU shiyasa tuntuni su ka bar Dutse da zama su ka dawo Bauchi. Itama Pendo ɗin ta cigaba da karatu dan ta kusa kammala degree ɗin ta a jami'ar. Ga sana'ar gyaran jiki da ƙunshi da ta ke yi ya karɓeta sosai, yanzu Pendo wacce 'ya'yanta ke kira da Ummi Hajiya ce.
A ranan da ta dawo Muntari ya kira Maryam a waya, tana ɗauka sai ya kwashe da dariya ya ce "kin ɗauka ban san shige da fice ɗin ki ba ne? To ki ce Pendo ta yiwa Amarya Zaytoonah gyaran jiki da kyau dan aure ba fashi"
"Muntari stalking ɗina ka ke yi?. For Allah's sake ka fita a harkata dan wallahi akan maganar Zaytoonah har kotu za mu shiga da kai kuma ba zan daddara ba sai na ci galaba a kan ka"
*"idan kina so ki cececi 'yar ki daga auren nan, abu biyu za ki yi. Ki je a raba auren ki da Tijjani sannan ki aureni, ni kuma na miki alkawarin ko professor Zaytoonah ke son zama kafin ta yi aure to sai ta zama, babu mai ma ta auren dole. Kuma duk ƙasar da ta ke son zuwa karatu sai na kai ta"*
Tana jin abinda ya faɗa ta kashe wayan tana huci. Ba za ta yarda ba, ba zai ma yiwu ba.
Wasa-wasa sai ga shi a date ɗin da aka sa har ya saura wata ɗaya. Muntari har da turo ma ta text wai ya siyawa Zaytoonah kayan ɗaki ta zo ta gani idan akwai abinda babu ta faɗa. Ta yi tsaki ta tura ma sa "keep on dreaming"
Tunda su ka yi zancen auren Zaytoonah da Auwal ya shiga cikin tashin hankali. Abu ne da ta jima da karanta cewa Auwal na son Zaytoonah, itama ta yi kwaɗayin zumuncin amma ba ta nuna ta san komai ba ne saboda tana so dukkan su su maida hankali a karatu. To gashi kuma Muntari ya zo da wata sabuwa.
Ɗakin su ta buga ta ce ya zo tana son ganin shi. Kamar marar lafiya haka ya tashi daga kan gado ya sa jallabiya ya fito falo.
"First son ya jikin?"
"Da sauƙi Mommy"
"Dan Allah kanada wani numbar Baffan ku Suleman ne? Wanda na ke da shi ba ya shiga"
"Ya dena amfani da tsohuwar wayar sa an sace wayar. Ina da sabuwar numbar sa barin kawo miki" ya shiga ɗaki ya ɗauko wayar sa ya ba ta numbar ta saka a nata wayar. A take a wajen ma ta kira kuma aka ci sa'a ya ɗauka. Tana fara magana ya shiga ba ta haƙuri na rashin jin sa da su ka yi. Ta ce ma sa ba komai sha'ani na rayuwa. A tsanake ta ma sa bayanin abinda ke faruwa ya ce ta ba shi kwana biyar zai zo Zaria sai su yi maganar da kyau.
Suleman ya bar Ringim da daɗewa ya koma Taraba da zama.
Yadda ya ce ɗin hakan kuwa aka yi bayan kwana biyar da maganar su sai ga shi ya zo. Ya je ya samu Muntari ya ma sa faɗa ya nuna rashin jin daɗin sa akan abinda ya ke shirin yi. Amma sai Muntari ya ce ba ruwan Suleman cikin maganar 'ya dai tashi ce, ya fi shi iko da ita tunda yanzu T J baya nan.
Suleman ya samu Maryam akan wannan magana fa inda ya hango shine tarihine ya ke son maimaita kan sa. Shawaran da zai ba ta shine ta kai ƙara Fada a sasanta su kawai. Tunda da shi da sauran Baffanun na su ba wanda zai ƙi bin maganan Sarki.
Ya ce ta samu Dattawa ma su daraja su je su jagoranceta a Fada a yi maganar, ya tabbata Sarki zai sa a fasa auren nan domin adali ne.
Da wannan shawara ta kwana bayan ta yi istikhara akai.
Washegari da hantsi ta je gidan Alhaji Iliyasu. Bayan an ma ta iso wajen sa ta gaishe shi ta ce ma sa ta zo neman Alfarma ne akan ya representing ɗinta a Fadar Sarkin Ringim.
Ya tambayeta mi ya ke faruwa ya ce ta gaya ma sa gaskiya. Maryam ta yiwa tsohon bayanin abinda ke faruwa gameda hukuncin da Muntari ya ɗaukar na aurar da Zaytoonah. Ba ta ɓoye ma sa sharaɗin da ya gindaya ma ta ba na ta aureshi shi kuma zai fasa aurar da Zaytoonah.
"Ikon Allah. Duniya dai sai dai mu godewa Allah kawai. Yanzu Hassada da gaba ta mana yawa Allah ya shiryemu ya sa mu fi gane gaskiya"
Maryam ta amsa da Amin.
Shiru yai na kusan mintina goma har Maryam ta yi zaton ko dai akwai matsala ne dan tsohon sai a hankali.
"Da za ki yarda ma sai na haɗa yarinyar da jikana da ke ƙasar waje. Sai ta yi karatun a chan dan shima Muhammadun Sarkin Boko ne. Abinda ya sa na faɗi haka shine ko da an fasa wannan auren ba haƙura zai yi ba. Ko ta ƙarfi ne zai iya ba da auren 'yar ki ko mi kika gani"
Maryam ta sauke ajiyar zuciya. Ana wata ga wata. Ta bar gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga da niyyar za ta yi shawara ta dawo.
***
It was a tough desicion amma kuma ta tabbata alama da ta gani kaman akwai Alkhairi a shawaran da ta yanke wa 'ya mace guda da ta haifa. Her first sign of motherhood...
Idan Muntari na ji da kuɗi, Alhaji Iliyasu ya taka shi. Idan Asali ya ke ji da shi Alhaji Iliyasu ya ma sa fintinkau dan Alhaji sananne a ciki da wajen ƙasa, dan haka ƙarya ne ya ce zai ja da shi. Sai da aka je Fadan ma ashe Mai Martaba Sarkin Ringim ya san Alhaji Iliyasu domin Malamin sa ne, ya koyar da shi a Sakandare.
Sarki yayi mamakin wai case ɗin da ya kashe shekaru kusan ishirin da biyar shine ya sake dawowa hannun sa. Bayan an gabatar da bayanai Sarki yai nasiha sannan ya zartar da hukunci na bayar da auren Zaytoonah ga Jikan Alhaji Iliyasu. Ranan da aka saka dai za ayi bikin ranan ɗin aka bari sai dai maimakon a family house da aka sa auren an maida shi cikin Fada za a ɗaura auren kuma kamar yadda Sarki ya zama Alwalin Maryam a lokacin auren su wannan karan ma shine na Zaytoonah.
Ko Zaria ba ta koma ba ta aikawa Muntari da gajeren saƙo.
*"Check Mate"*
Yadda Muntari ya sha kunya a shekarun baya haka wannan karan ma ya amshi kashin sa a hannu.
Maryam da kan ta je Bauchi ta ɗauko Zaytoonah.
Da su ka koma gida ta zaunar da ita ta ma ta bayanin hukuncin da ta yanke ma ta.
As expected kuka ta fashe da shi.
Fushi sosai ta yi da Mommyn ta kulle kan ta a ɗaki tana faɗin Mommy ta tsaneta tunda ta yadda a aurar da ita duk da ta san burinta na son zama babbar Lawyer.
As days past, Maryam ta dinga kwantar ma ta da hankali tana nuna ma ta karatu kam za ta yi shi dan sai ta samu admission ma kafin ta bar ƙasar.
Still ba ta ji nitsuwa ba har da cewa ƙila mutumin mummuna ne.
Maryam ta nuna ma ta hoton da Alhaji ya ba ta. Nan da nan Zaytoonah ta fara washe baki, atleast ba da wani mummunan mutum za a haɗa ta ba ko kuma wanda bai yi karatu ba. Tsabar ɗoki sai ta je ɗakin Auwal tana nuna ma sa hoton shi kuwa kishi ya sa ya korota. Ya riga ta ganin hoton infact ranan da su ka yi waya da Mommy ma yana wajen. Dan Maryam ba ta yarda da Auren ba sai da ta yi waya da yaron ta ji shi ɗin wani irin mutum ne ya kuma ɗauki Alkawarin zai bar Zaytoonah ta yi karatu har ta gama sannan ba zai walaƙantata ba...
Ranan Jummu'ah 1 November 2009 aka ɗaura auren Zaytoonah Tijjani Abubakar da Muhammad (Zuhayr) Muhammad Iliyasu bisa sadaki dubu Hamsin wanda Kakan sa ya bayar.
'Yan uwa sun hallara kuma anyi hidima dai-dai gwargwado sai dai babu Muntari ciki. Shi tun da Sarki ya yanke hukunci a Fada bai sake zuwa Ringim ba.
Zaytoonah kam kamar ba matar aure ba tunda ba yanzu za ta tafi wajen miji ba. Ta cigaba da rayuwar ta normal. Sai dai Mommy da ke takura ma ta da nasiha once in a while. An bata numbar Zuhayr amma bai kirata ba itama ba ta kirashi ba.
Bayan wata uku aka sama ma ta admission a University of Nevada, Las Vegas. Shi mai girma Ango ɗin a Las Vegas ɗin ya ke aiki.
Lokacin da aka gaya ma ta ranan wuni ta yi tana farinciki, barin ma da aka turo ma ta admission ɗin ta gani. Ita Auren ma baya gabanta karatu kawai ta ke hangowa tunda wata ɗaya da ya wuce Zuhayr ya kirata kuma sun tsara komai. Auren na su suna ne kawai amma zama za su yi tayi karatu har ta ƙare kafin ya saketa ta kama gabanta (🤔Tam)
Bayan an confirming admission ɗin ne ta je ta fara processing visa wanda Alhaji Iliyasu ne ya ɗau nauyi. Ita da Mommy su ka je embassy aka yi cike-ciken takardu har komai ya kammala. Bai jima ba bayan sun dawo gida aka kirata akan Visa ɗin ta ya kammala. Dan haka aka fara shirye-shiryen tafiya.
Sai da tafiyar ta zo kusa ne kuma jikin Zaytoonah yai sanyi, duk wani ɗoki da ta ke yi ya tafi. Kewar Mommy da ƙannenta ya fara shigarta. Komawa ma ta yi tana kwana da Mommy saboda wai ta ji ɗumin mahaifiyarta. Maryam ma daurewa ta ke yi amma tana jin wannan rabuwan a ranta. Addu'arta a koyaushe shine Allah ya sa auren nan ya zamewa Zaytoonah Alkhairi.
A Abuja su ka kwana gidan Hajiya Fatima. Dukkan su suka zo rakiya, hatta Auwal da ke baya-baya da ita tun lokacin da aka yi aurenta sai da ya zo rakiyan. Anyi koke-koke tun ma kafin a je airport ɗin, saboda rabuwa ce da ba a san ranan haɗuwa ba kuma iya ka ci sai dai su ga juna a waya ko computer idan su ka hau skype.
Rungume Mommy ta yi tsam tana kuka.
"Mommy i'll miss you, i'll miss you so much. I love you"
Maryam ma hawayen ne a idonta tana ɗan bubbuga bayan 'yar tata a hankali.
Sai da aka fara kiran passenger ɗin jirgi mai number A2265 kafin Maryam ta breaking rungumar tana faɗin ki je kar ki missing jirgin.
Ta rungume Salman wanda shima hawayen ya ke yi.
"Ki dinga kiran mu kullum kin ji"
Zaytoonah ta ce "Insha Allah"
Auwal kam da sauri ya bar wajen ganin yana shirin yin kuka shima.
Ta ɗaga junior sama tana faɗin " big boy ban da rigima"
Ya girgiza ma ta kai yana dariya.
Sai da ta ajiye shi ta fara jan jakarta tana tafiya bayan ta yiwa Mommy last hug.
"Aytoonah" ta ji muryan Junior ta juya ta ganshi yana ɗaga ma ta hannu, yana hannun Mommy dan da bin Zaytoonah ya ke son yi.
"Aytoonah Bye Bye ya ke faɗi har Zaytoonah ta ƙule"
***
With full excitement ta shiga jirgin wannan ne karo na uku da ta taɓa shiga jirgi, sau biyu ta taɓa shiga jirgi zuwa Lagos tareda Muntari. Sau biyun kuma da za a tashi sai da cikinta ya wani juya ta sa hannu biyu ta riƙe shi dan kar ya zazzago a yadda ta ke tunani. Lokacin tashi da lokacin saukan jirgi duk sai ka ga ta tsure saboda fargaba.
Business class ticket aka yanka ma ta dan haka za ta ɗan samu ta wataya kaɗan ba kamar zuwan su Lagos da su ke tafiya a ticket na economy class ba.
Tana zama ta kalli mutumin da ke gefenta wanda ya ɗaga littafi yana karatu, littafin ya tareshi ba ta ganin full fiskarsa sai dai gefen fiskar sa sannan fararen dogayen yatsun da su ka riƙe littafin zai ƙara tabbatar ma ka mutumin fari ne sosai, tana tunanin ma ƙila Balarabe ne.
Ta gyara zamanta da kyau tana miƙe ƙafa saboda akwai space sosai. Jakar da ke hannunta ta buɗe ta fidda wani ziplock bag da ke cike da plantain chips wanda Mommy da kanta ta soya ma ta.
Ya san an zauna a gefen shi kuma ya lura mace ne shiyasa bai ma yi ƙoƙarin duba ta ba amma wani ƙanshi mai sanyi da ke fita a jikinta ya sa shi tantamar ko dai ya juyo ya kalleta ne, chan kuma ya ce ƙila matar aure ce.
Ƙurumus ƙurumus ƙurumus. Ya fara ji alamun dai ana tauna crispy abu haka. Hakan ya sa ya ɗan sauke littafin da ke hannunsa ya juyo a hankali ya kalleta. Cikin abinda bai kai 2 seconds ba ya gane inda ya taɓa ganin yarinyar, ya ƙura ma ta ido yana tunanin irin wannan coincidence ɗin. Juyowar da Zaytoonah za ta yi sai su ka haɗa ido lokacin ta cika hannunta da plantain chips za ta kai baki. Sai da ta tura duka a bakinta ta miƙa ma sa ledar tana faɗin "wants some?" Ya girgiza ma ta kai ya maida littafin sa ya cigaba da karatu, ya ce a ran sa da alama ba ta gane shi ba.
Ba a jima ba aka fara announcing akan a saka seat belt ayi wata tsiya-wata uba. Zaytoonah ta saka seat belt ɗin bayan ta maida sauran chips ɗin cikin jaka.
Lokacin da jirgi zai tashi rufe ido ta yi ta damƙe hannun kujeran tana jero addu'o'i. Tsabar tsoro addu'ar da ta zo ranta kawai ta ke karantowa.
"Subbuhun Quddusun Rabbil Mala'ikati War Rooh. Rabirhamhuma kama Rabbayani Sagira. Ya Mujibussalihina, Ya Malakul Mulk" haka tai ta ɓuruntun addu'o'i kala-kala har sai da jirgi ya dai-dai ta a sararin samaniya tukunna ta yi ajiyar zuciya ta buɗe ido, juyawar da za ta yi ta sauke su kan na Mutumin da ke gefenta. Shi ba ma'abocin dariya ba ne sai murmushi, amma da ya yi dariyar kalar addu'o'in da ta yi ta yi, yadda bakinta ke motsi ma kaɗai abin dariya ne.
"What?" Ta faɗa tana ɗaga gira bai ce komai ba ya juya yana kallon window.
Da aka zo za a serving na su lunch Zaytoonah har da na jaraba ta zaɓa. Yana gani yadda ta zage tana cin abincin da ya ke tunanin wannan cin kaɗai ya isa ya sa ta ƙiba. Duk abinda aka kawo sai da ta cinye shi tas.
Shi ba ma'abocin surutu ba ne da ya tambayeta ko da sunan ta ne dan yarinyar ta burgeshi, she's funny.
Da tafiya ta yi nisa TV da ke gabanta ta fara kallo ta sa headphone a kunnenta tana sauraro amma hakan bai hana bacci ɗaukan ta ba.
Lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalleta zuciyar sa cike da tunani kala-kala akan ta.
Ƙila ɗaliba ce za ta koma makaranta.
Ƙila kuma hutu za ta je. Ko kuma ma dai gidan Iyayen ta za ta koma ta zo Nigeria hutu ne. Dan da ka ganta ka san ita ɗin 'yar manyan mutane ce. Kayan jikinta da yanayin fatar jikinta kaɗai ka kalla ka san 'yar hutu ce.
Da su ka zo sauka ne ya mustering courage ya ce "are you a student?"
"Kutmelesi. Ashe kana magana? Shine tun tasowar mu ka yi shiru. Ikon Allah" ta faɗi da Hausa. Ganin ya ƙura ma ta ido ya sa ta tabbatar bai ji abinda ta ce ba.
Ta wani turo baki ta ce "Yes, i'm a student"
Ta yi gaba ta bar shi. A wannan lokaci he wished shi ma'abocin magana ne da ya nuna ma ta cewa ya ji abinda ta ce. He wish zai iya bin ta ya tambayeta sunan ta da makarantar da ta ke amma ƙasaita da sarautar sa ba za su bar shi ba. Tambayar da ya ma ta ma ya jima yana jujjuyawa a ransa kafin ya fito da shi waje da ƙyar ganin fa tabbas rabuwa za su yi daga nan kuma bai san komai gameda ita ba...
*A nan na kawo ƙarshen free pages na chronicles of Zaytoonah. Za ki iya supporting ɗina ta hanyar biyan #300 domin samun cigaban labarin*
***
*ya rayuwar auren Zaytoonah za ta kasance da Zuhair Muhammad Ilyas wanda ba ta taɓa gani ba sai a hoto?*
*shin wace irin ƙaddara ke tattare da Zaytoonah ayayinda ta buɗe wani sabon babi a rayuwarta akan wannan aure da akayi bisa sharaɗi mai sarƙaƙiya?*
*Muntari zai haƙura da Maryam kuwa? Ko kuma dai zai tuba ne ya faɗi abinda ya sa aka yiwa T J?*
*shin bayan aurar da Zaytoonah Maryam za ta samu kwanciyar hankali? Ko kuma dai ya rayuwar ta zai kasance with the beast Muntari?*
*wai ina T J ne? Yana raye ko ya mutu? Shin ma wai zai dawo ga iyalinsa kuwa?*
*shin wanene wannan mutumin da Zaytoonah ta haɗu da shi har sau biyu sannan wani rawa zai taka a rayuwar ta?*
*daga ƙarshe shin Barrister Zaytoonah za ta iya jayayya da ƙanin kakanta kuwa? Wato Augustus Udodiri Uzodinma, wanda ya kashe Kakannin ta ya kuma cinye dukiyar su?*