5&6
*_📲Typing_*.
*_🪁ƊINYAR MAKAHO...!🪁_*
_(Ta nuna a hannunsa)🍀_
_*UMMU MAHER(MISS GREEN ce)🍀*_
_AREWA BOOK👉🏼_
Rabiattu0444
*GAWURTATTU 5🔥*
------------------------
P. 5&6
.............."Ummi!don Allah kada ki kashe,wallahi yanzu haka na fito ne daga meeting daga ɗakin shugaban ƙasa,kuma wata ƙwangila aka banine so shiyasa bazan dawo yanzu ba,kuma wannan aikin zai ɗauki kusan shekara ɗaya saboda aiki ne me matuƙar yawa."
Shiru Ammin nasa tayi sannan ta ce"Hmm a'i kullum haka kake ce wa Yazeed babu ranar dawowa,dai dai kullum ni in dinga zaryar zuwa ganinka,gashi mahaifinka yanzu abubuwa sunyi masa yawa da wanne zai fara yanzu?kafi kowa sanin kai kaɗai ne ɗansa namiji,ba shida wanda zai taimaka masa sai kai".
"Ummi ki yarda dani,wallahi badon na amshi aikin nan ba da gudowa zanyi ni kam,don na gaji da wannan aikin nasu wanda bana ƙare ba."
Nan dai sukayi sallama da mahaifiyar tashi,ya jingine wayar a ƙirjinsa ya ɗaga kansa sama yana kallon skye inda tayi kyau shar,sararin samaniya yana da wani irin kyaun daba kowa ke gane hakan ba,har sai kalleshi sosai amman fa kallon da glass don kallonsa haka musamman da rana yana kashe ido.
*******
*Noor pov*
...........sai da suka bincika asibitoci sun fi guda uku daga bisani suka yanke shawarar dawowa gida don a sanar da ƴan sanda.
Har sun ɗakko hanya Hadiza ta ce"ya sayyadi bamu je General hospital ba?".
da sauri ya sayyadi ya juya da babur ɗinsa zuwa general hospital,atare suka shiga suna tambaya ward ward(ɗaki ɗaki)a haka har suka gano inda Noor ɗin take,ta window suka hangota dukansu suka runtuma da gudu zasu shiga ɗakin,da sauri Ahmad ya dakatar dasu ta hanyar cewa.
"Kai!ku dakata mana ina zakuje?".
Ya sayyadi ya ce bawan Allah waccen yarinyar sunanta Noor tun kafin magrib ake nemanta,munyi ta dubawa asibitoci bamu ganta ba.
Kallon tuhuma Ahmad yake musu sannan ya ce"ok na fahimta amman bazan barku ju shiga ba,har sai ta farka da kanta zata shaida ku amman yanzu ku koma gida kuce tana nan asibiti ta samu accident ne(hatsari)kuma yanzu tana samun hutune."
sosai hankalinsu ya tashi,ya sayyadi ya ce"bawan Allah to kai waye ne?".
"Ni ne wanda ya buge ta".
ya sayyadi ya kalleshi yaji kamar ta shaƙesa ya mutu sannan ya ce"kuma shine mu zaka hanamu shiga ku ganta?a'i kai kace ma me laifine shine wato kaja bakinka kayi shiru ko?tunda ka buge kaza"?.
Ahmad ba mutum ne me faɗa ba,amman yahi haushin maganar da wannan mutumin ya gaya masa,ya ɗago jajayen idanuwansa ya ce"bawan Allah ashe kai bakasan ƙaddara ba?daga ganinka kana da ilimi kuma ya ratsaka don na gani a fuskarsa,amman me yasa baka aiki dashi?duk wanda yasan ƙaddara bazai faɗi haka ba.
Ɗan murmushi Ya sayyadi ya yi wanda hausawa suke cewa yafi kuka ciwo sannan ya ce"bawan Allah nasan ƙaddara mana,sai dai ma ince kai ne baka sani ba?yanzu tun sanda ka kaɗe ta me ya hana kayi bincike ka gano gidansu?amman sai kayi biris kaja bakinka kayi shiru,sannan kuma kace bansan ƙaddara ba"?.
Ahmad ya ce"haba Malan yaushe na sanu wannan nutsuwar?ai banida wannan nutsuwar da zanyi binciken gidansu,amman ai kowanne bawa yana yin kuskure ko Allahn daya haliccemu muna yi masa laifi kuma ya yafe mana".
Hadiza ta ce"ba komai Mlm mun gane abinda kakeji Allah ya kiyaye gaba,ya karemu ga dukkanin wata ƙaddara wacce baza mu iya da ita ba".
Amin Ahmad ya ce yana me jin daɗin addu'ar da Hadiza tayi,da kuma saurin gano shi data yi,dai dai nan mahaifiyar Ahmad ta shigo ta ce"Ahmad waɗannan fa Allah dai yasa lafiya"?.
"Eh lafiya ƙlau Hajiya,sune ƴan uwan wacce na buge".
Gaisawa sukayi a tsakaninsu sannan Hajiya ta nemi dasu rakata gidansu yarinyar don ta ƙara tabbatarwa.?
Haka kuwa akayi Hadiza da ya sayyadi suka hau kan babur yaja suka wuce.Hajiyar Ahmad kuma ta hau motarta driver yaja sukabi bayan Ya sayyadi,shi kuma Ahmad aka barshi awajen Noor.
Bandeji ne nannaɗe a goshinta,ƙafarta kuma an saka babbar Flasta an nannaɗe ta,fuskarta tayi fayau sosai ta ƙara wani irin mugun fari hakan kuma yana ga nasaba ne ga rashin jinin da take tattare dashi.
Tsaye yayi yana kallon kyakkyawar fuskar Noor,wacce ke ɗauke da murmushi wanda ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarta,ya yi yunƙurin ɗauke idonsa akan Noor amman ya kasa,sai ma ƙara gyara zama da yayi don ya fuskance ta sosai.
Tunda yake bai taɓa tozali da wata mace wadda tayu mugun ƙwanta masa ba,ya yi zama acikin turawa da dama da kuma kalolin fararan fata,irinsu india,saudi arabia,france,london,america da sauran ƙasashe,mata har kawo kansu da kansu suke don ya sosu amman bai taɓa basu wannan damar ba,saboda sam basu ƙwanta masa ba wasu daga cikinsu musulmai ne wasunsu kuma ba musulmai ba.
Bai san me yasa ba wani irin nishaɗi yake ji wanda ya gaza misaltuwa acikin ransa,yana jinsa kamar wani sabon shiga alhali kuma har aure ya taɓayi sai dai matartasa ta mutu yau shekara biyu kenan da faruwar wannan al'amarin.
Kuma yana da ƴa ɗaya me suna Afra,wacce taci sunan Hajiyarsa wato Maryam ake kiranta da Afra,shekararta uku kenan,shekararta ɗaya mahaifiyarta ta rasu sanadiyyar ciwon cancer(daji) me tsanani.
Tun bayan rasuwar Iklima matarsa bai ƙara jin nishaɗi irin na yau ba,sanadiyyar kallon fuskar Noor wacce yake jinta tamkar wata acikin Zahra.
jininsa dake shiga jikin Noor yake kalla,yadda yake jin wani irin daɗi mara misaltuwa yana addu'ar Allah ubangiji ya bata lafiya.
Umma na zaune a Ɗaki,duk fuskarta ta gama jiƘewa da hawaye,ga mahaifin Noor tsaye akanta yana surfa mata wulaƘanci Ita kuwa baiwar Allah Ƙala bata ce masa ba,kuka kawai take tana kiran sunan Allah don bata san da wanne zataji ba,da Ɓatan Ƴarta zataji ko kuwa da wannan masifar ta mijinta zata ji?.
Ana cikin haka Hadiza ta shugo ita da mahaifiyar Ahmad,kuma duk sunji Ɗibar albarkar da mahaifin Noor ke yi,da sallama suka shigo gidan sai duk hankalin mutanen gidan yayo kansu,musamman ma hajiya Maryam babbar macece kuma kana ganinta ba sai an faƊa maka ba kuƊi sun zauna sosai ajikinta.
Umma ta ɗaga kanta ta kallesu,ganin matar da Hadiza yasa ta ɗanyi fara'a tana mata sannu da zuwa.
Hajiyar Ahmad ta shigo ɗakin Umma,gashi dai matar kamar ta samu mutuwar ɓarin jiki amman ɗakin fes fes dashi,duk da kana kallon ɗakin kasan talauci ya yi musu cikas,don ɗakin ma babu ledar tsakar ɗaki,sai siminti wanda ya sharu tas tas dashi wannan kuma duk aikin Noor ne.
Hajiyar Ahmad suka gaisa da Baban Noor,abin mamaki sai ya dinga fara'a,sai gasu Inna Hafsa da Inna Saude suma sun shigo,don kada ayi rabo babu su fon daga ganin wannan matar kuɗi sun zauna mata.
Hajiyar Ahmad ta gyara zamanta ta ce"Sunana Hajiya Maryam,ina Zaune ne a Nassarawa G.R.A ina da ɗana guda ɗaya me suna Ahmad,yana da shekara talatin da biyar yanzu tsautsayi da ƙaddara yasa ya buge ƴarku jiya a hanyarta ta dawowa daga makaranta."
Kuka sosai Umman Noor ta fashe dashi sannan ta ce"Allah sarki Noor Allah ya baki lafiya me ɗorewa".
"Amin".
Inji Hajiyar Ahmad da kuma Hadiza.
Inna Hafsa da Inna Saude sai wani iyayi suke don su nuna su sunfi kowa iya mu'amala da mutane,Umma da Hadiza sai kallon ikon Allah suke,wai yau su Inna Saude ne aɗakin maƙiyiyarsu Hauwa'u wato Umman Noor?.
Su ma su Inna Sauden sun gane su Umma sun yarfosu,sai kuwa Inna Hafsatu ta ce"a to ai sai muje mu dubo ta ko?".
Umma ta ce"a'ah ku barshi kawai,mara lafiya bai fiya son hayaniya ba Allah dai ya bata lafiya Amin".
Hadiza ta ce"Umma to yanzu xamuje dake ne don ki duba ta?".
Share hawayen fuskarta tayi sannan ta ce"Ayya Hadiza ai ni yanzu ɗaukata kaya ne Hadiza,duk inda taje nasan Allah zai kulamin da ita,saboda idan naje ma ba wani abu zan iya yi mata ba".
Hajiyar Ahmad ta ce"Allah sarki baki da lafiya ne"?.
Murmushi Umma tayi wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo,sannan ta ce"Baiwar Allah yanzu shekarata Biyu kenan da shiga cikin wannan ƙaddarar,rana ɗaya kuma a lokaci ɗaya na tsinci kaina acikinta dumu dumu sai dai Allah(S.W.A)ya bani lafiya ɗorarriya".
Tana faɗar hakan ta fashe da kuka,Inna Hafsa da Inna Saude suka haɗa ido,suka ɗanyi dariyar mugunta suna cewa acikin zuƙatansu,ai mu da zaki mutu ma da kakarmu ta yanke saƙa,don yadda suka tsani mutuwarsu haka suka tsani Hauwa wato mahaifiyar Noor.
Hajiyar Ahmad ta ɗebo kuɗi,da dama ta miƙawa mahaifiyar Noor,Umma ta kasa amsar kuɗin ta ce"baiwar Allah ki barshi indai don an buge ƴata ce babu komai ai nasan ƙaddara don haka na yafe muku,ki riƙe kuɗin amman kiyi haƙuri mayar miki da hannun kyauta baya dana yi."
Da Hajiyar Ahmad taga Umma taƙi amsa sai ta ajje mata a gefenta,sannan ta ce"Baiwar Allah ba na baki bane don wani abu,a'ah babu komai a cikin zuciyata kawai dai wani irin abu naji a game dake wanda tabbas ba komai bane illa tausayi,ina me ƙara baki haƙuri akan wannan lalurar da Allah ya ɗora miki,ki sani duk wata lalura da Allah(S.W.A)zai ɗorawa bayinsa badon komai ba sai don ya gwada imaninsu,haƙiƙa ina me tabbatar miki Allah ya zaɓeki ne don kin cancanta,ba wai don ya tsane kiba dai don tsantsar so daya ke miki,ke bama ke kaɗai ba duk wani wanda ke ciwo yakw ganin kamar ubangiji ya ɗora masa nw don baya sonsa to ba haka bane,bisa cancantarsa Allah ya zaɓosa sannan ya ɗora masa wannan jarabta,ita kuma Jarabta aduk sanda ta kama haƙuri shine maganin komai,don haka ki daina kuka akan wannan don sai Allah yaga kamar don ya ɗora miki lalurane,kike butulce masa subhanalillah aƙwai mutanen da suke wani kuskure arayuwarsu zakiga idan Allah ya ɗora musu wata jarabta hat saƙo suke wai don Allah ya jarabcesu,wanda a musulunce bai kamata ba,kamata yayi ka ɗaga hannu ka godewa Allah,sai kiga Allah yajiƙanki ya yaye miki wannan lalura cikin sauƙi da kuma lumana."
Sosai Umma taji daɗin nasihar da Hajiyar Ahmad tayi mata,sai taji tamkar an ɗauke mata damuwa acikin zuciyarta ta ce.
"Hajiya tabbas kina ɗaya daga cikin mutane masu mahimmaci arayuwata,tabbas duk mutumin da zai faɗa maka zancen Allah to tabbas masoyinka ne,baka da tamkarsa don haka Hajiya na gode sosai,ki gaidamin da Ɗan naki da kuma Noor".
Murmushi Hajiya tayi,tana jin wani irin don matar acikin ranta ta kuma rasa dalili,don ita mutum ce mara yarda da wuya kaga ta yarda da kai,saboda abinda halin yarda da mutum yaja mata,shiyasa yanzu take kaffa kaffa da mutane.
Hajiyar Ahmad ta ce"amman Baiwar Allah ni aganina tunda da mota mukazo ki sanarwa mijinki sai muje tare ko?".
Umma bata son yi mata musu don haka tace"to babu komai ai yana gidanma sai ayi mishi magana."
Da sauri Inna Saude ta fita,da yake itace a bakin ƙofa kuma daman ita tafi Inna Hafsa wayo da kuma dabara,don haka ta fice har tana harɗewa don tayi sauri ta faɗi abinda zata faɗa ɗin.
Yana ɗakin Inna Hafsa,ta leƙa ta window ta ce"to sai ka taso ka biyoni ɗakina,ka wani zo ka zauna a ɗakinta wai ita matarso ko"?.
Kamar raƙumi da akala haka kuwa ya biyota,zungui zungui kamar ɗa da uwa tana tafiya tana mitar ita fa babu wata mace da ta i'sa ta ƙwace mata mijinta,itama Inna Hafsan abinda yasa take ɗan yi mara rangwame saboda kar tasan kar ne tsakaninsu,babu wacce bata san halin ƴar uwarta ba,na baƙin hali da kuma baƙin ciki.
Suna zuwa ɗakin ta zauna a bakin gado sannan ta ce"yauwa daman wannan matar ce naji suna cewa wai zasu tafi da ita,don kasan ita wannan matar ɗanta ne ya buge ita Noor,to shine wai zasu tafi kuma naga ta bata kuɗi,ka tubure kace baza taje ba. kaga daga nan sai ta miƙo maka rabonka muma mu samu namu don naga alamar wannan matar ba bamu zatayi ba."
Sosai ya harzuƙa ya hau faɗa,wai wataƙila ma acen yawon iskancinta suka haɗu ko ta shiga motar wani sukaje sukayi hatsari.
Inna Saude kuwa murna har baka,ta famfo mijinta zaije ya yi rashin mutunci,saboda tsabar murna kamar za tayi fitsari saboda dariyar ƙe ta,shi kuwa sako tumaki ɓallo jakar tuni yayo waje yana ta kumfar baki.
Acen ɓangaren kuwa Inna Saude na fita,Hajiyar Ahmad ta miƙawa Inna Hafsa Naira dubu biyar lakadan ba ajalan ba,murna kamar ta kashe Inna Hafsa,don duk sana'ar da take yanzu babu ko jarin arziƙi,ga yaranta aƙalla yanzu sunkai goma,gana Saude ma guda sha ɗaya gidan dai su ashirin da biyu kenan a lissafe.
Gashi daɗin daɗawa an mata kyauta Inna Saude bata nan,tasan yau babu zaman lafiya acikin gidan amman duk da haka ko ajikinta,sai taga dama zata kulata don babu wanda ta rainawa hankali kamar Saude don faɗanta yawanci ihu bayan hari ne.
Ana cikin haka sai ga mahaifin Noor ya shigo,suka ƙara gaisawa da Umma abin mamaki sai Baba ya kasa yi mata rashin mutunci kamar yadda ya gama faɗa,Inna saude sai kallon hannun Inna Hafsa take,ganin ƴan dubu dubu bugun Abuja a hannunta,a take taji wani irin mashi me tsini ya soki zuciyarta,kar dai ace ƴar fitar nan tata ne aka yiwa wannan munafukar kyauta?.indai kuwa haka ne wallahi ko da ba'a bata ba,sai ta saka masifar da zata saka a bata itama.
Mahaifin Noor ya amince,umma taje don ta zauna da ƴarta duk dama ba wani abu za tayi mata ba,tunda duka jiki ya shanye fuskarta ce kawai bata taɓu ba.don idan kaji muryarta ma sai ka ɗauka lafiyarta ƙlau.
Hajiya da Hadixa su suka kama Umma har suka saka ta a cikin mota,sannan Hadiza ta tsaya awajenta cikin zuciyar Hadiza tana tuna yadda zasu wanye da Inna Lami don tasan halinta,ita bama mahaifinta ne aranta ba,don tasan sai abinda Inna Lami ta faɗa shi yake yi.
Shima mahaifin Noor Hajiya ta bashi kuɗi dubu goma.
Inna Saude fa hankalinta ya tashi ganin har yanzu ba'a sallame ta ba,sai ta shiga dabarar yadda zatayi ta tsokani Inna hafsa don suyi cece kuce don a bata itama don taga ruwa yana so ya ƙare wa ɗan kada.
Don taga tana shirin tashi babu ko ƙwabo,ƙarshe kishiyarta Hafsatu tayi mata dariya.
Wafce kuɗin hannun Ina Hafsatu Inna Saude ta yi,tana haki ta fara cewa"wallahi Hafsatu baki isa ki cinye kuɗin nan ke kaɗai ba,tunda daman da ta bamu ce wa tayi mu raba amman saboda tsabar son zuciya irin taki,shine kika karɓe wai ke me tsinannan wayo".
Sosai abin ya ƙular da Inna Hafsatu,ta ce"ke Saude ki fita daga cikin idona in rufe wallahi akan kuɗin nan idan ban miki tsinannan duka ba,kice ni ba ƴar gidan Malam jatau bace sai inyi miki lilis anan."
Dariya ma abin yaso ya bawa Hajiyar Ahmad,ganin duk haɗin kan da taga sunayi kuɗi zai shiga tsakaninsu,ashe daman zaman ba na Allah bane.
Ta ciro dubu biyar ɗin ta miƙawa Inna Hafsa sannan ta ce"ke ki riƙe waccen ɗin,ita kuma na bata wani don haka sai ku zauna lafiya,kuma ina yi muku Nasiha da kubi halin wannan ƴar uwarku taku,duk da tana buƙatar kuɗi amman basu tsone mata i'do ba,don haka kuyi koyi da ɗabi'arta don mutuniyar arziƙice."
Tana faɗar hakan tayi fitowarta daga gidan,tana mamakin hali irin nasu Inna Hafsa da Inna Saude.
Inna Saude ta yiwa Inna Hafsa gwalo sannan ta ce"oho dai koma menene hausawa sunce 'ƊINYAR MAKAHO'(ta nuna ahannusa,don da ba'abani kuɗin nan ba da anga masifa ƙwando ƙwando.
Ya sayyadi ya ƙaraso inda suke akan lifan ɗinsa,yake gaya musu yaje don ya shaidawa mahaifiyarsa abinda ke faruwa don kada aga ya daɗe.
Sannan Umma ta nemi da aje gidansu Hadiza a faɗa don babu daɗi aji shiru,kuma gata budurwa baya ga haka ma yarinyar tana cikin wani hali agidansu,don ansha rabata da Noor amman kuma sai kaga gobe ma ta koma.
*GIDAN SARAUTA*
............Gidane ƙato wanda ya yi matuƙar tsaruwa,su kansu bayin gidan sarki Abdussalam shigarsu ta dabance,gidane wanda yasha fenti fari ɓangare huɗu ne agidan basu da fenti fari,kowanne fentinsa daban ɓangarorine masu matuƙar kyau da ban sha'awa.
Idan ka garzaya fadar sarki kuwa,dukiyace aka narka ba kaɗanba idan ka shiga ɗakin baza kaso fitowa ba,saboda yadda tsarin wajen yake tafiya da mutane da dama.
Sarki Abdussalam shine mahaifin Yarima Yazeed ɗan kyakkyawan saurayi,Sarki yana masifar son Yazeed don bashi da ɗa namiji wanda ya wuce shi,duk ƴaƴansa mata ne yana da matansa har huɗu amman uku daga cikinsu duk mata suka haifa,shiyasa ya ke masifar son Yarima Yazeed tun yana ƙarami baya nuna masa fushi koda kuwa ya yi abin fushinne,idan kuwa aka taɓa Yazeed ko kai waye to daga ranar kun ɓata,ko da kuwa mahaifiyarsa ce to yanzu zaka ga sun samu matsala.
Sarauniya Zulaihat ta ɓangaren mijinta bata samun matsalar komai,amman akan Yarima Yazeed yanzu zakaga sun samu matsala,aƙwai wani duka da ta taɓa yiwa Yazeed ɗin,abinka da mara ƙwari har bakinsa sai da ya fashe daya ke yana da masifar rashin ji yana ɗan ƙaraminsa,ga ɓarna kuma baya ganin kowa da daraja saboda ƙaunar da mahaifinsa ya ke nuna masa da kuma shagwaɓasa da ya ke yi.
Wannan abu da Sarauniya Xulaihat tayi,ai ba ɗan ƙaramin yaƙi akayi agidan ba sai da sukayi kusan wata ɗaya basa ga maciji,don ko ɗakinsa taje sai kaga yana wani cin magani ya ƙi koda kallonta ma,kuma Sarki aduk cikin matansa yana masifar son Zulaihat,kuma kowa ya sani harda abokan zamanta.
Wannan faɗan da sukayi sai ya zamanto hatta kishiyoyinta suna goranta mata akan wannan,ashe ɗanta na sonta sai gashi shine ya sasanta su tunda alokacin ya kai kusan shekara goma,don Yazeed tun yana ƙarami Allah ya yi masa kaifin basira da shegen wayo don duk abinda ka ke sai dai ya kalle ka kawai.
Tub daga kan wannan faɗa da sukayi,Sarki ya nemi shawarar Sarauniya Zulaihat akan a fitar da Yazeed ƙasar waje don ya cika burinsa na zama me tsara gine gine,a farkon farawa bata yarda ba saboda lalacewar tarbiyya wacce ayanzu ɗama yana gabanka ya ka cika balle kuma yana wata uwa duniya?amman ganin mahaifin ya dage yasa tabi ɗanta da addu'ah kawai.
Ganin kamar ran matarsa tasa baiso ba,sai ya haɗasu su uku yakai ƙasar waje.
Aƙwai ɗan ƙaninsa Muhammad Turaki,aƙwai kuma ɗan wazirinshi shi me suna Aliyu duk sai ya haɗasu ya kaisu,sai dai kowa aƙwai abinda yake karanta,shi Muhammad ɗan gisan saraki yana karantar law ne wato lauya,shi kuma Aliyu fannin likita ya ke karantawa,shi kuma Yazeed fannin tsara gine-gine.
Farkon fara karatunsa lafiya suka fara ba suda wata matsala,sai daga baya komai ya canja don farko awaje ɗaya suke ƙwana a wani gari me suna Le mains dake ƙasar France.
Sai abokai suka shiga jansu zuwa gidan Club,farkon farawa Yazeed bai bi ta kansu ba sai ya ɗaukesu tamkar wasu shashu.
Makarantarsu aƙwai wata yarinya ƴar asalin ƙasar india ce me suna Roshni ta na cewa Yazeed sosai duk alokacin bai fi shekara ashirin ba,akanshi yarinyar nan har hawa bene ta yi tace zata faɗo wai idan baice yana sonta ba,Yazeed mutum ne me matuƙar tausayi,don haka ya yarda yace kuma yana sonta amman ba har cikin zuciyarsa ba,don shi arayuwarsa babu ne yi masa tilas ɗin duk abinda baya so,mutum ne tsayayya da in har yaga abu yace yana so to ya soshi kenan har abadan abadan,idan kuma yaƙi abu to yaƙi shi kenan har abada.
Sosai Roshni taji daɗin abinda masoyinta ya ce,sai ta ƙara zurfafa sosai acikin kogin sonshi,sai ta tsira shiga gidansu gashi duk mutanen gidan basa nan,tunda wataran idan su Aliyu suka tafi yawon Club ɗinsu sai sukai ɗayan dare,basu dawo ba saboda haka yasan daman sun saba sai baya damuwa dai dai ya ɗakko littatafansa ya duba daga nan ya kira iyayensa susha hirarsu ta ɗa da mahaifansa.
To mafarin ƙaddarar Yazeed ita ce Roshni,don Roshni tayi ta ƙoƙarin son su aikata abinda bai kamata ba,amman daya ke tsayayya ne bata samu wannan damar ba,sai ta tsiri zuwa gidansu wai don tayi musu girki,Yazeed ya kyaleta kawai ya saka mata idanuwa don yaga iya gudun ruwanta.
Da wannan girkinne ta samu ta ƙara shiga zuciyar Yazeed,sai dai fa har yanzu bata samu abinda take so ba daga nan sai ta fara ƙwaɗaita masa shan giya,nan ma bata samu abinda takeso ba.
Daga nan Roshni ta tafi hutu ƙasar India,Roshni mahaifinta wani babban boka ne a ƙasar India daga ƙasashe ma da dama ana zuwa wajensa.
Don haka sai Roshni tayi amfani da wannan damar ta faɗawa mahaifinta wai wani saurayi takeso shi kuma baya sonta,me abu da abinsa nan da nan ya fara aiki kan Yazeed,sai dai fa ya yi mamaki sosai don ganin wannan yaron iyayensa sun tashi sosai aransa.
Sai aka saka masa son zuwa club,daga nan ita kuma sai ta samu abinda take so.
Hmm tsafi gaskiyar meshi,don tun kafin Roshni ta dawo Yazeed ya fara bin yawon Club Club,abin ya bawa su Aliyu mamaki sosai.
Yazeed ɗin da suka sani me matuƙar tsantseni da rayuwarsa,sai gashi shi kuma yanzu ya damesu sosai shi da ya ke musu nasiha sai gashi yanzu shine harda ƙwana?abin ya ɗaure musu kai sosai.
Roshni na dawowa aka ɗora inda aka tsaya,don Roshni ta samu yadda take so sai dai kuma haƙarta na cin ruwa su Yazeed suka koma gida,don suma sun samu hutun skull,kuma ayanzu ma sun kusa gamawa.
Roshni tana masifar son Yazeed,har ciwo tayi lokacin da Yazeed ya tafi ciwon da farko ƙaramine amman daga baya sai ya zama babba,daga hawan jini sai ya komai ciwon zuciya.
Aka aikawa iyayenta,akazo aka tafi da ita ƙasar India cen ma suka rasa yadda zasuyi da ita,don baki ɗaya hankalinta yana kan Yazeed,abinda yafi bata tsoro ma shine bai wuce yadda Yazeed ya manta da i'ta ba,don ya yi mata alƙawarin idan har ya koma Nigeria zai neme ta da sabon layinsa,amman sai taji shiru tamkar malam ya ci shirwa.
A wannan hutun dasu Yazeed suka dawo,Sarauniya Zulaihat ta lura sosai da sabbin halayen ɗanta Yazeed,sai ta saka masa idanu sosai,amman daya ke Yazeed ɗin yana da wayo sosai sai yaƙi bata damar gane waɗansu abubuwan,haka ya lulluɓe ta daga bisani dai da taga kamar tana zarginsa ne sai ta kyalesa,ta cigaba da yi masa addu'o'i.
Alhmdh yanzu Yazeed ajikinsa ya ke jin,tamkar ya zalunci iyayensa idan har ya cigaba da aikata ɓarna don haka sai ya daina wasu abubuwan,kamar shan giya da sauran wasu abubuwan waɗanda ya ke yinsu a ɓoye waɗanda ba kowa ne ya sani ba,Sai Aliyu da Muhammad sune suka san halin miskilancin Yazeed.
To bayan komawarsu makaranta hankalinsu baki ɗaya yana kan exam(jarabawa)wacce ta yi zafi sosai don duk abinsu basa wasa da jarrabawa suna tsayawa suyi karatu sosai.
Roshni ma ta dawo makaranta,ta nemi su koma yadda suke ada amman gogan ya nuna mata babu wannan zancen,ranta ya ɓaci sosai amman sai ta ɓoye sai ta shiga kyautata masa sosai.
Duk ɗan adam yana son me kyautata masa,daga haka sai ya fara kulata amman wani abu na banza baya shiga tsakaninsu,ta nemi shawararsa tana son ta musulunta amman bata san yadda za tayi ba?.
Sai ya bata shawara akan ta sanar da iyayenta,sai ta gaya masa ce wa idan har suka sani to bazasu barta ba,sai dai ta musulunta a ɓoye daga baya sai ta gaya musu.
Roshni ta musulunta,don aƙwai wani malami wanda Yazeed ɗin ke ɗaukar karatu awajensa wanda ke ƙasar France ɗin,cikin ikon Allah ya musuluntar da ita wanda ya tambaye ta wani suna takeso ta ce Farida.
To wannan musuluntar da Roshni tayi sai ya ƙara mata wani irin girma awajen Yarima Yazeed,kai hatta matsalar ciwon zuciyarta shine ya tsaya mata tsayin daka har ta samu lafiya.
Sai suka cigaba da soyayyarsu.
Wannan shine taƙaitaccen tarihin Yazeed.
*Noor Pov*
...........Lokacin da su Umma sukaje gidansu Hadiza,mahaifinta baya nan sai Inna Lami wacce ke irga wasu kuɗaɗen da ta siyarda gidanta,da ya ke su Lami gidansu suna da kuɗi sosai,kuma mahaifinsu ya bar musu dukiya sosai.
Tana jin shigowar mutane da sauri ta danne kuɗinta,idanuwanta sukayi jawur tayi wuri wuri da ficificin idanuwanta.
Da Sallama su Hajiya suka shiga,bayan sun Gaisa Inna Lami ke ta kallon ƙadan zanin Hajiyar Ahmad,don ganin irin atamfar da ta saka.
Hajiyar Ahmad tana ɗagowa suka haɗa idanu da Inna Lami,da sauri Inna Lami ta juya ta waske kamar ma ba ita ce ta yi wannan kallon rainin hankalin ba.
Hajiyar Ahmad ta yi murmushi,don ta saba haɗuwa da irin waɗannan matan masu masifar sa ido ga dukkanin kayan daka saka.
Inna Lami kuwa azuciyarta ce wa take"Caɓɓijan yau Allah ya haɗani da Hajiya?irin wannan tsadaddiyar atamfa haka?don atamfar da Hajiyar Ahmad ta saka ko ba'a gaya maka ba kasan ke tsada ce,balle kuma Inna Lami wacce tasan atamfofi sosai don tana siyarwa kuma tasan duk kuɗaɗensu tunda tana siyarwa da manyan mata.
Hajiyar Ahmad ta nisa sannan ta fara magana kamar haka:
"Hajiya daman nazo ne don tambayar izininku?akan daɗewa da Hadiza ta yi bata dawo gida ba,don Allah kuyi haƙuri a faɗawa Babanta cewar ƙawarta ce bayan sun dawo daga makaranta ta yi hatsari wato Noor,shine abinda yada ta daɗe don haka don Allah kuyi haƙuri".
Inna Lami ta ce"a haba babu komai Hajiya,a'i nasan yadda suke da Noor Allah dai ya bata lafiya,babu komai ta ɗebi kayanta ma ku tafi tare asibitin sai ta zauna da Noor ɗin,tunda dai ita mahaifiyar Noor ɗin ga shi tana fama da lalura,don haka ku tafi babu komai idan Babanta ya dawo za'a gaya masa."
Sosai Hadiza ta yi mamakin Inna Lami,don tasan halinta sarai masifa da kuma hantara da zagi,duk babu wanda bata yi mata dai gashi yau wai ita ce da wannan daɗin bakin.
Ko da zasu tafi Hajiyar Ahmad ta ajjewa Inna Lami kuɗi akusa da i'ta,da sauri ta saka hannu ta amshe kuɗin tana washe baki tare da yi wa Hajiyar Ahmad ɗin godiya,sai ga Inna Lami da rakiya har soro tana ta washe baki,kamar wadda aka yiwa albishir da gidan aljanna.
Abin sai yaso ya bawa Hadixa dariya ta maze kawai amman mamaki ya cika zuciyarta,sarai Hadiza ta san Inna Lami da masifar son kuɗi,Inna Lami babu abinda baza ta iya akan kuɗi ba,masoyiyar kuɗi ce sosai duk kuwa da yawan kuɗin da take dasu amman na hannunta basu isashe taba na hannun wani take kallo.
Kai tsaye asibitin muka koma,Ya sayyadi ma kasa tafiya gida ya yi,shima ya biyo mu don ya ce bazai tafi ba har sai Noor ta tashi,kana ganinsa kasan yana cikin tashin hankali don sai yanzu yasan me yake ji akan Noor.
Ahmad kuwa har yanzu kallon Noor ya ke,har likitan ya dawo ya sameshi ya yi dariya sannan ya ce"a'ah mutumina har yanxu gadi ka ke?na ɗauka ma ka tafi gida,ashe har yanzu kana nan kana gadin gimbiya."?
Murmushi Ahmad ya yi sannan ya ce"Hmm to ai ya zamarmin dole inyi gadi,saboda duk wannan jinyar ni na janyo ta,kaga kuwa dole inyi ni tunani ma kada ta tashi ta kama jin haushi na,don wallahi yarinyar tayi masifar ƙwantamin don ina ji ajikina kamar zata yarda dani ɗari bisa ɗari".
Murmushi Dr Zain ya yi sannan ya ce"haba Ahmad daga buge mutum kuma sai ka zarce"?..
Suna cikin wannan maganar sukaji sallamar su Hajiya,Umman Noor suka ƙwantar da ita akusa da gadon dake kusa dana Noor.
hawaye ne ya shiga ƙwaranyowa aƙwarmin idanuwan Umma,ta hangi ƴarta wacce ke ƙwance rai a hannun Allah,tamkar babu numfashi ga wajen karayar da ta samu har an ɗora ta.
Ahmad sai kallon Umma ya ke,duk da Noor bata yi kama da ummanta ba amman ta ɗakko waɗansu kamannin na ta,don Umman Noor ba fara bace ita ba fara ba ita ba baƙa ba,wankan tarwaɗa kenan Ita kuma Noor kama tayi sosai da mahaifinta fara ce sosai amman ba fari ɗau ɗinnan ba,wai a hakan ma don fatar tata bata samu kular da take buƙata ba.
Hajiyar Ahmad ta ce"My son wannan ita ce mahaifiyar Noor,tana fama ne da stroke mun nemi da tabarshi ta xauna ta huta,amman kadan ɗa da uwa sai Allah shiyasa tazo don ta ganta,sai Hadiza ta zauna dasu don mun nemi izinin iyayenta sunce ta zauna."
Har gaban Umma Ahmad yaje ya tsugunna ya ce"Umma ina wuni"?.
A hankali ta juyo da fuakarta tana kallon Ahmad.
Sai dai tana kallonsa cikin tsoro ta ce"kai ne"?... . . . .✍🏿
@@Miss green ce✍🏿🍀.
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
***
Masu turo kati MTN ta wannan number.
***
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
***
Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu.