ABUL-KHAIR

chapter 11

by @autarmama

.👬ABUL-KHAIR👬



(the identical twins)



TSARAWA DA RUBUTAWA DAGA SALMEERT SANI SALMAN TRIPLE S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️)




*WANNAN  LITTAFIN NA KUDINE ,KUMA WANDA SUKA FARA BIYA KAFIN A GAMA FREE PAGES TO ZAI BIYA #300 NE, WANDA KUMA BASU BIYA BA HAR AKA GAMA TO ZAI BIYA #400, IN KUMA BAKA DA RA'AYIN SIYA TA NAN, TO SAI KAJE CHAN AREWABOOKS KA BIYA KASHA KARANTUNKA CIN FARASHI MAI SAUKI KUMA CIKIN KWANCIYAR HANKALI* 



https://arewabooks.com


           

*yi a Amfani da wannan 👆 link din domin shiga cikin manhajar kai tsaye*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

    {R.S.W.A}


***

 *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Faɗakarwa, ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alƙalaminmu ƴancinmu*





 *BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.....*






PAGE 12.






"""""""""""""""""Kwananshi biyu, aka sallameshi dan jikin ya warke sosai,hakan yasa suka fara shirye shiryen komawa Nigeria, amma fa sai dai Khair ya bigewa Abul warning, akan kar ya fadawa kowa ciwon da ya yi,shakuwa da soyayyar dake tsakaninsu, yasa ya yarda bazai fadawa kowa ba....







*ƁANGAREN MUƊI'AT.*






Zama tayi tare da jingina kanta da jikin bangon gurin, tana cigaba da kukanta, fitowar Gimbiya Ochchi daga bedroom dinta kennan, ta fito domin zuwa kitchen ta dauki ruwa, taji kuka...








da farko ta tsorata sosai sai kuma daga baya, ta nufi inda takejin kukan, tana shiga ta fara arba da dogon gashin Muɗi'at da ya rufe illahirin fuskarta, dago fuskarta tayi a tsorace jin motsin mutum , sosai Gimbiya Ochchi ta tsorata, dan tunda take bata taɓa ganin halitta mai kyau irin ta Muɗi'at ba.......






a tsorace, gaba dayansu suke kallon juna, Muɗi'at tanajin tsoron Gimbiya Ochchi itama kuma tana jin tsoron Muɗi'at din.....






cike da tsoro Gimbiya Ochchi tace "waye kai, mai kakeso anan(bakin Yarbawa suna maida mace namiji namiji mace)", ta fada tana kallonta, cike da dan ruɗu tace "N...n...nice Muɗi'at", ta fada wasu hawayen na kara zubowa......







cike da mamaki Gimbiya Ochchi take kallonta kafin tace, "daga ina kake, mai ya kawoka nan", ta fada tana kallonta, kuka ta kara saki kafin tace "Twin dina, tanachan ni a mai dani gurinta", ta fada cikin muryar kuka.......







dakyar Gimbiya Ochchi ta iya harhada maganganun da Muɗi'at ta mata, har ta aunashi akan ma'auni na fahimtarta, hakan kuma ya sa ta gane, tana daya daga cikin mutanan da aka kawo za'ayi shagalin bikin dasu ce, tausayinta ne ya kama Gimbiya Ochchi, take taji Yarinyar ta kwanta mata Arai, sannan kuma tana som riketa a matsayin Ƴa kasantuwarta ta wadda Allah bai taɓa bawa Haihuwa ba, sai dai kyan Yarinyar tsoro yake bata.......







rike hannunta tayi,tare da mikar da ita, ta sanyata jikinta, ganin tana kuka yasa, ta dauketa chak ta nufi part dinta da ita, Muɗi'at kuwa tana lafe a jikinta ...





kan tafkeken bed dinta ta ajiyeta, tare da nufar wata kofa, bathroom ne ya bayyana haɗaɗe mai kyan gaske, gashi fess sai kanshi ke tashi alamar Matar dai na da tsafta sosai....







sai da duk ta gama abinda zatayi kafin ta kwanta kan bed din kusa da Muɗi'at, tare da jaa musu blanket, shigewa jikinta Muɗi'at tayi, kasantuwar sun saba da son jiki, hakan yasa, indai sukaji mutum a kusa dasu sai sun shige jikinshi...






murmushi Gimbiya Ochchi tayi, tare da fara shafa gashin Muɗi'at bacci ne ya farayin Awon gaba da ita, ba tare da an dauki wani lokaci mai tsayi ba baccin ya dauketa, tana fitar da numfashi tare da jaan ajiyar zuciya.....








*WASHE GARI*






tunda sassafe Gimbiya Ochchi ta tashi kasantuwar ranar ne akeyin bikin shekara, wanka tayi, kafin ta haɗawa Muɗi'at,itama tayi sai da ta tabbatar ta gyarata cikin shiga mai kyau ta kayan yan kanti , masu kyau wanda duk in suka fita cikin gari in ta gani suka burgeta sai ta siya, set set na Yara masu kyau sosai, dan sosai takeson Yara amma Allah bai bata ba.......







sai da ta shiryata tsaf kafin ta kalleta tace "karkaje ko ina, za'a kawo maka abinci da komai, kar ka fita, dan banason a ganka, in ba haka ba Oba Eri ko Oba Aroma zai tafi dake, kuma zasu yankaka ne", ta fada tana zare mata ido....






cike da tsoro, ta zare ido itama tare da rakuɓewa guri daya, alamar ta tsorata, ganin ta tsorata yasa Gimbiya Ochchi tayi murmushi tare da cewa "kar ka damu kai Yarona ne, bazan bari a cutarmin da kai ba", ta fada tana mata kiss a goshi, kafin ta fice tana ɗaga mata hannu.....







Abinci aka kawo mata, mai rai da motsi, sai dai kasa cin komai tayi sai, amalan da aka ajiye mata da miyar Egusi taji naman ganda, da busasshen kifi, shi kawai taci ta koma kan bed , dim ta ƙudundune,tana tunani halin da Muneebat take ciki, tana cikin tunanin bacci ya yi awon gaba da ita......




haka suka ci gaba, da bidirin bikin shekarar, har zuwa dare kafin kowa ya watse.....








tunda sassafe jirginsu ya tashi daga New York zuwa Nigeria, some hours suka sauka, tun kafin su karaso gungun mutanan da sukazo tararsu suka karaso, suna isowa aka daukesu sai ~Masarautar Suzanna~, suna karasowa part din Nanni suka nufa.....






zaune take ta wani naba'a, hannunta rike da hankichif hancin nan ya yi jajir, ido sai tsiyaya yakeyi,tunda ta musu kallo daya da suka shigo bata kara kallonsu ba,har suka karaso cikin palon, zama Abul ya yi chan kan wata kujera, Khair kuwa zama ya yi, kusa da ita, tare da kama dogon hancinta ya jaa, bige hannun tayi tare da cewa "kai sakini dan nema, babu ruwana dakai kar kamin fitsara", ta fada tana matsawa daga kusa dashi.....






murmushi ya yu, tare da cewa "uhmmm to me lelen ya miki?", ya fada yana fiddo wata jika tare da mika mata, washe baki tayi tare da cewa "to!, to!!, to!!! Abin Arziki muka samu, ai kasan ko ina fushi bazanyi da Lelana ba, da dai wanchan Buskutun ne", ta fada tana dallawa Abul harara, taɓe baki ya yi tare da mai da kanshi kan TVn da yake kallo....






Jikkar ta bude tare da fiddo abin da yake ciki, manyan kwalin turaruka ne kwara ukku, masu ƙanshi sosai, washe baki Nanni tayi tare da cewa "kaii! Lelena na kuwa gode, dama turarena ya kare yanzu nake cewa azo a siyomin, dan bazan iya zuwa shupin ba saboda murar da ta uzuramin", ta fada tana murmushi....






wata mahaukaciyar dariya Abul ya saki tare da cewa "mai kikace Nanni?", ya fada yana dariya, harararshi tayi tare da dauke kanta daga kallonshi....





"Please dan kara maimaitawa", ya fada yana dan marairaice fuska....




"nace Shupin, ko dole sai na fada da karyarku ta yan boko, wai sai kaji ana cewa Markat, Plasma ko uban mai", ta fada a dan halasale...






ba Abul ba har Khair sai da ya murmusa, dan ba karamin bashi dariya tayi ba, "kin ga bafa Markat ake cewa ba, cewa akeyi Market da Plaza, kar kije ki ɓata mana suna, ace Kakar *Abul-Khair* guda bata iya faɗin abu da turanci ba", ya fada yana dariya...






haɗe rai Nanni tare da kyaɓe baki tace "duk wanda ya fada faɗa yaci Ubatar Ubanshi, an dade ba'a fada ba, kai nifa babu ruwa na, da karyar Nasara, yo menene cikin Yaren Nasara banda gantalewa, duk wanda kaji yanayi shima Gantalalle ne , yo waya aikeni, inje Allah ya ƙonani, ah'ah Wallahi babu ruwa na, dan ko Ubanka Abdul-jabbar bai isa ya sani yin yaren Nasara ba balle kai , karan Kaɗa miya, waye kai ma?, wai Abur sai kace wani tusa, uhmmmm Allah ya kyauta, dama zuwa kayi aka chanja maka suna, suna babu dadin gaba balle na baya Abur, hahahahaha", ta fada tana dariya, tarine ya sarketa cikin dariya sai ji kake bit bit bit bit, tana sakin tusa, dakyar ta samu ta tsayar da dariyar da takeyi....






mai Abul zaiyi banda dariya, har yana dafe ciki, kafin yace "Allah dai ya kyauta, amma dai gaskiya Nanni ki dunga matse wannan Abur din taki kar ki kumburawa mutane ciki da ita" ya fada yana dariya......






nuskutawa Nanni tayi tare da cewa, "kaji Dolo bakasan ita tusa Lafiya bace, yo ai mu lokacin mu, in baka tusa har magani ake nenan maka, baka da lafiya, kune dai yan zamani, kuka mai da ita wani abu, amma ai tusa lafiya ce, bakaji ba har akace, in zakayi ka ringa shiga ɗaki kanayi, in kayi ka shaƙe abunka kafin ka fito, zama ka iya samun wani, ya ringa yi maka domin dai daita bugun zuciyarka, Likitoci ma suna fada", ta fada tana wani fuskewa.







dariya ce ta kama Khair har ya kasa riketa, sai da ya saketa, sakin baki Kuyangar Nanni tayi tana kallon yarda Khair yake dariya, ciki da ban sha'awa take karewa jerarrun Haƙoranshi da suke da mugun haske kallo, dan bada ban kar tayi karya ba, da sai tace har hoton fuskarta take gani a jikin haƙoran nashi.....







lura da itan da ya yi ne yasa, ya daure fuskarshi tamau, kamar ba shine yake dariya ba yanzu, Abul kuwa ai har da fadowa daga kan kujerar da yake, cikin dariya cewa "uhmmmm lallai naga Alama Likita Nanni, Allah dai yaja mana rayuwarki, mu cigaba da shan dariya" kar kacewa ta karayi zatayi magana, da sauri Abul yace "uhmmm nidai kunga tafiyata na gaji da wannan dariyar haka kamar zararre", ya fada yana ficewa....






tsaki Nanni tayi kafin tace "Shashasha bai fa yarda ba, gantalallen, ke Hansai kawowa Lele tuwon nan, da fura suna cikin Firigen, ki tabbatar kinsa Tuwon ya yi zafi, sannan akwai yajin daddawa da man shanu sunanan cikin Samirori ki kawo mishi", ta fada tana kallon Kuyangar tata....






da sauri ta nufi kitchen din, sai da ta gama komai kafin ta kawo mishi, bai wani ci sosai ba, ya yi Hamdala tare da yiwa Nanni Sallama ya fita, direct Sashen Gimbiya (Mahaifiyarshi) ya nufa, achan ya tarar da Abul suna fira ita dashi, tana ganinshi ta gimtse fuska tare da yin shiru da bakinta.....






kallonta Khair ya yi, tare da cewa "good Afternoon Momma", ya fada yana sunkuyar da idonshi ƙasa, jinjina kai tayi kawai ba tare da ta amsa ba, shiru ne ya biyo baya babu wanda ya kara magana ita Gimbiya tana jin nauyi yin magana a gaban Khair kasantuwarshi na Ɗan fari, shi kuma Khair yana jin nauyi da kunya na rashin sabo da Mahaifiyarshi kasantuwar bata janshi a jiki.......






a haka suka ci gaba da zama, har lokaci ya dan jaa, kafin su fice sashensu suka nufa, a tsaftace komai yake need abin sha'awa, bathroom Khair ya nufa , ruwan wanka ya hada tare da yin wanka, yana fitowa ya shirya cikin kayan shan iska ya fice palo.........





Abul ma wankan ya yi, ya shirya cikin kanyanshi iri daya da na Khair, palon ya fito shima, kusa da Khair ya zauna, tare da kwace Ice cream din dake hannunshi yana sha..






bude lumsassun idanunshi ya yu, masu mugun firgita mata, watsa mishi ya yi kan fuskarshi, tare da mishi alama da ya bashi, cikin ɓacin rai Abul yace "wai kai mai yake damunka ne, kullum kai sai an maka faɗa kan shan abu mai sanyi sai kace wani ƙaramin Yaro, kafi kowa sanin irin Situation din da kake ciki kake shan sanyi, jiki duk gayyar pneumonia ,amma bazaka daddara ba, ya kamata ka ringa kiyayewa ko dan wahalar da kakesha in ta tashi", ya ƙarasa fada cikin muryar tausayawa......





shiru Khair ya yi , ba tare da yace komai ba, gannin hakan yasa Abul bai kara cewa komai ba, shima.....





sai bayan Magrib kafin suka shiga gurin Mai martaba, sosai sukayi fira kafin su wuce sashensu su kwanta.....






*Bayan sati daya.....*





zaune duk suke tsakiyar wani tankameman palo, mai cike da kayan Alatu kala kala, kallo daya zaka masa , ka shaida tabbas palon wani mai mugun fada aji ne a kasa, domin palon ya tsaru iya tsaruwa 





cikin wata kakkausar murya Mai Martaba Abduljabbar ya fara magana, cike fushi tare da zallar ɓacin rai, "Khair har ni zan zo maka da , magana ka bujere kace bazakabi ba, to har in kanason cigaba da zama cikin wannan Masarautar a karkashen ikona, to dole ne ka karɓi wannan kujerar ta Sarauta, in ko ba haka ba to dayan biyu ne, ko ita ko kuma ka barmin gida", ya fada yana girgiza kafarshi irin na manya Sarakai.







cikin Razani duk suka dago suna kallon Sarki, banda Khai da tunda ya fara magana jijiyoyin kanshi suka fito sukayi raɗo raɗo, ga idonshi da ya yi, wani mugun jaa, ga fatar jikinshi da tayi wani mugun jaa sakamakon tashin da ya mishi yawa.







Momma kuwa, tuni zufa ta fara karyo mata, dan tasan babu Khair ya tsana sama da Sarauta , shi yasa ta tsami ayi maganar, yin murabus din Mai Martaba, Abul kuwa jikinshi kyarma kawai yakeyi, musamman ma da yaga Khair yana shirin Yin magana.





"Abba ka yafen a gaskiya, ni A rayuwata, banason Sarauta ko kaɗan, sannan kuma w........" bude lumsassun idanunshi ya yi, masu masifar kamar da na Khair ya ce, "Daga yau na Haramta maka, babu ni babu kai, na baka 30 minutes ka barmin gida, sannan ban baka izinin fitarmin da ko da haki nawa daga cikin gidan nan ba", ya fada cikin wata shaƙaƙiyar murya.





"Ab....." daga mishi hannu ya yi, tare da lumshe idonshi, sanin cewa Mahaifin nashi ƙaifi daya ne, yasa ya mike zai bar Palon, da sauri Momma da Abul suka mike, zasu mara mishi baya.







wani mugun kallo Mai martaba ya watsa musu, da sauri suka shiga cikin hankalinsu, kasa jurewa Abul ya yi, hakan yasa, ya bi bayan Khair.




cikin daga murya Mai martaba yace, "taƙu daya ka kara ban yafe maka ba", ya fada cikin lafazi mai nuna zallar gargaɗi, zubewa Abul ya yi, a gurin ya rushe da wani kalar kuka mai ban tausayi, Momma mai kanta ta shigar tsakanin cinyoyinta ta fara raira nata kuka............








ga wanda zasu fara biyan kuɗinsu zasu biya #300 , ga wanda zai bari har a gama free to zai biya #400, ku biya kuɗinku ta wannan account number din👇.





1499884120

Umma salma sani. access bank.




ko katin waya ta wannan number👇.



***.




ku tabbatar kun turo da shaidar biyanku ta hanyar yin screenshot sannan ku turo ta wannan number din👇.




***.




Salmeert Sani Salman triples S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️)