ABUL-KHAIR

chapter 12

by @autarmama

👬ABUL-KHAIR👬



(the identical twins)



TSARAWA DA RUBUTAWA DAGA SALMEERT SANI SALMAN TRIPLE S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️)




*WANNAN  LITTAFIN NA KUDINE ,KUMA WANDA SUKA FARA BIYA KAFIN A GAMA FREE PAGES TO ZAI BIYA #300 NE, WANDA KUMA BASU BIYA BA HAR AKA GAMA TO ZAI BIYA #400, IN KUMA BAKA DA RA'AYIN SIYA TA NAN, TO SAI KAJE CHAN AREWABOOKS KA BIYA KASHA KARANTUNKA CIN FARASHI MAI SAUKI KUMA CIKIN KWANCIYAR HANKALI* 



https://arewabooks.com


           

*yi a Amfani da wannan 👆 link din domin shiga cikin manhajar kai tsaye*







*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.*







PAGE 13.






"""""""""""""""""""Mai martaba ma idanun nan sunyi jaajir, Abbu kuwa Ƙanin Mai martaba, sai wani makirin murmushi yake saki a boye, Ummie ma matarshi kar kaso ka tona zuciyarta domin haushi ne, taf a ciki, dan ita ta gama tsara plan din yarda zatasa Khair ya Auri Ƴarta sai kuma ga wannan Alamarin ya faru,hakan tasa gaba daya baka gane irin yanayin da take ciki, farin ciki ne ko kuwa baƙin ciki, gaba daya yanayinta ga dai shinan.....






duk abinnan da yake faruwa Nanni bata sani ba, dan tana chan sashenta yau da zazzaɓi ta tashi da ciwon kai, hakan yasa ta lafe a kan gado kamar wata mage, sai dai numfashinta ne ke fita a slow, dama kuma ga murar da ta Uzurawa rayuwarta, kamar Sadeey(Ƴar gatan Royal) a gari , dan baya sati biyu batayi mura ba, kasantuwar ciwo iri daya garesu da Khair.....






gashi itama bata natsuwa guri daya, ga wasa da ruwa kamar wata Yarinya, gaba dai daya tass Khair nata ya kwaso, hakan yasa take mugun sonshi da tausayinshi........







yana fita daga sashen ya wuce nasu, cikin sauri sauri, yake haɗa komai da yasan nashi ne, kama daga kan laptop Phones ATMs da dai sauransu, komai da yasan nashine ya dauka, wanda kuma yasan ba nashi bane bai dauki ko haki ba.......






paper ya dauka da biro, cikin good hand writing dinshi ya fara dan short note, wanda ga dukan alamu Abul yawa rubutun, car key dinshi ya dauka tare da ficewa daga cikin bedroom din........







parking space ya nufa, idon nan nashi har wasu hawaye suke fita tsabar, ɓacin rai , wata mota ya nufa kirar Benz mai masifar kyau Fara tarr da ita,da sauri wani ya taso tare da nufarshi.....







daga mishi hannu ya yu, tare da shigewa cikin wani mugun speed ya bar gurin, tun kafin ya karasa zuwa gurin get , get man ya bude masa, hakan yasa ya cilla hancin motar kan titin kai tsaya........







sai da ya yi nisa da Masarautar kafin ya tsaya gefen titin, kanshi ya daura jikin sitiyarin motar kusan 10 minutes kafin ya dago, sai haɗa zufa yake, wayarshi ya fiddo tare da dearling wata number..........







ring biyu ala dauka daga chan ɓangaren naji ana cewa, "Yallaɓai barka da rana an yini lafiya?", ba tare da ya amsa gaisuwar ba yace, "ina som amin booking din jirgin da zaije Dubai,sannan ka faɗamin lokacin da zai tashi", ya fada a gajarce.......






cike da girmamawa yace, "to shikenan Ranka ya dade, akwai jirgin da zai tafi Dubai nan da 40 minutes sai dai, sai ya biya ta Japan kafin ya karasa chan din, in kuma ba shi ba, tofa gaskiya sai jibi", ya fada cike da ladabi......





"uhmmm kamin booking nashi" yana fada ya kashe wayar tare da figar motar kai tsaye ya airport din ya nufa tun kafin lokacin ya cika........







*BANGAREN MUNEEBAT*






Daukarta Matar tayi ta wuce da ita sama, wanda achan room dinta yake, kwantar da ita tayi kan bed dinta tare da wucewa toilet wanka tayi, kafin ta fito, sai da ta shirya kafin ta kwanta, lokacin Muneebat har tayi bacci, bakin ta a gaba , alamar shagwaɓa....







*WASHE GARI*






tun da sassafe su Hysome suka fara mata kiciniyar samun visa ta tafiya Dubai dan achan, sukeson kai ta, dan a chan ne kawai, za'a oya biyan duk yarda sukaso a kanta, dan sun dauketa ne a matsayen Kadara .....






basusha wahala ba sosai, gurin ganin sun haɗa mata komai, a ranar komai suka haɗa mata, na tafiya, ita kuwa tana a hannun Anty Mamu, wadda take mata komai takeso, wanda yanzu sun riga da sun saba sosau, kullum koma ko da yaushe tana jikinta......






yanzu ma zaune take kan ƙafarta tana game, ita kuma tana bata Abinci a baki, a haka Hysamo ya shigo ya samesu, sai da ya ƙare musu kallo kafin yace", Sannu Uwa da Ƴa gobe dai za'a tafi da ita Dubai, sai ki kammala mata duk shirin da zaki mata", ya fada yana zama.......







dafe kirji tayi, dan yana fadar za'a tafi da ita taji gabanta ya yi, wani mugun faduwa, cikin sanyin jiki tace "Oga Hysome nima zan biku Dubai din", ta fada tana kallonshi......







nurmushi ys yi tare da cewa, "uhmmm dama ai kece bakiso zuwa ba, amma so nawa ina miki tayin tafiya, sai ki shirya gobe 2pm, jirgin zai tashi, ai nasan Passport dinki na gurinki ko?", ya fada yana kai dubanshi kan wayar hannunshi....







"E yana hannuna", ta fada tana juya kai, "to shikenan sai ko ci gaba da shiri", ya fada yana mikewa tare da hayewa sama.....






*Washr gari....*






da wur wuri Anty Mamu, ta gama musu shirin su, sai da ta kira Alhajawan ta kaf sukayi Sallama kafin su wuce airport lokacin saura duka 20 minutes jirginsu ya tashi.....







basu wani jima sosai da zuwa ba, jirginsu ya tashi zuwa Japan daga Japan kuma zuwa Dubai, a Special side suke, daga Anty Mamu sai Muneebat sau kuma wani da ya haɗa kai da guiwa ya yi, shiru wanda tun da sukazo a haka suka sameshi.....






a haka har suka isa Ƙasar Japan, wasu daga cikin fasinja suka fara sauka, su kuwa ko niyyar sauka basu dashi dan .......






 

kusan 1 hour babu wsni duriyw, yasa Anty Mamu ta ajiye Muneebat dake bacci, ta nufi hanyar fita a jirgin, har ta kusa fita ta dawo, tare da kallom Khair wanda duk abinda takeyi , yana kallonta ta ƙasan ido.......







"Bawan Allah ga ajiyar Baby na nan, please ka kullamin da ita kafin na dawo", ta fada tana kallonshi, shiru baice da ita komai ba,kuma bai nuna wani reaction ba na nuna yama ji abinda tace......







gajiya tayi da tsayuwar ta fice daga jirgin, kai tsaye gurin masu siyar da kayayyaki ta nufa, ruwa ta siya da cakes har ma da ice cream kafin ta koma......







yana shiga ta tarar da Muneebat zaune, sai zazzare ido takeyi Alamar ta tashi, da sauri ta karasa gurin ta tare, da riketa tana cewa "lazy girl, har kin tashi ", ta fada tana dan dukan kumatunta.....







batace komai ba sai cakes da ice cream din da tabi da kallo, ganin tana kallo ne yasa ta mika mata, karɓa tayi tare da fara sha.....







sai da tasha roba biyu na ice cream din, dan ko abinci bata ci ba sai ice cream, kwanciya tayi jikin Anty Mamu din, kyarma jikinta ya fara yi, alamar rabar ice cream din, da yanayin garin da snow yake zuba ya haddasa mata........






Abu kamar wasa tuni, Muneebat ta fara kyarma kamar mai, jikinta na wani ɓari, in ka kalleta da kyau zaka lura da yada har naman jikinta yake kyarma, alamar ciwonta ne ya tashi.......







*MASARAUTAR NRI.....*







Muɗi'at na jikin Gimbiya Ochchi jikinta ya fara wani mahaukaciyar rawa, har cikin namanta, da sauri ta mike zaune haka ma Gimbiya Ochchi , kuka Muɗi'at ta farayi babu kama hannun Yaro .......







cikin ruɗu Gimbiya Ochchi tace "lafiya Yarona, menene yasa kakeyin kuka, yi sjiru stop cry", ta fada tana dan dukanta......







ai kamar kara mata volume akayi, cikin tausayawa Gimbiya Ochchi tace, "mai yaka damun ka fadamin", ta fada cikin gurɓatacciyar hausarta........







cikin shasheka tace".............








ga wanda zasu fara biyan kuɗinsu zasu biya #300 , ga wanda zai bari har a gama free to zai biya #400, ku biya kuɗinku ta wannan account number din👇.





1499884120

Umma salma sani. access bank.




ko katin waya ta wannan number👇.



***.




ku tabbatar kun turo da shaidar biyanku ta hanyar yin screenshot sannan ku turo ta wannan number din👇.




***.




Salmeert Sani Salman triples S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍)