KHADIJATUL SABREN

CHAPTER TWO 2

by @misshajo

🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸



    ```MALLAKAR```



   *HAJARA L SADEQ*


 

 Arewa book👉@Miss Hajo✍️





🅿️.............*3 & 4*



Ta ce "Dan ubanki Ni sa'arkice da Zaki dinga gulma ta Daman bakisan haushinki nakeji ba zako kici ubanki"


Ta k'arasa fada Tana shakota tare da Fara Kai Mata bugu shima Affan Hindu ya shak'a ya hau jibgarta kafin kace me dambe ya kad'ame tsakaninsu class sai hayaniya ake.



Dukda sabren tare suke jibguwa Dama d'aya ta samu ta kada ita nanko ta hau ruwan cikinta tahau jibga sosai zey ta Fara kuka ana haka Uncle ya shigo class d'insu hankali tashe yazo ya rabasu Wanda Saida ya tsoratasu da bulala kafin ya samu ya rabasu,.



 "Ku biyoni Office zanyi maganinku Gabaki d'ayanku harke Mai tsukakken bakin Nan jarababbiya Baki da aiki sai fad'a da mutane a aji Duka saina zaneku" .



ya fad'a Yana nuna sabren Da ta ke hura hanci Jin abunda yace NE ya sanyata sakin tsaki tare da murguda Masa Baki ta ce"Ni ba jarababbiya bace ai Ja na su ka yi".



nuna kanshi yayi Yana mamakin rashin kunyar Yarinyar ya ce "Dani kike"Ganin Yana Shirin lafta Mata bulala NE ya sanyata saurin buga ihu tare da zubewa a wajen ta Fara birgima da ihu kamar wacce ya buga,.



Tsaki Uncle yaja a ranshi ya ce "Allah wadararan irin wannan sangartar، iyaye karfi da yaji su maida y'ay'an su mahaukata da sunan so " juyawa ya yi ya kalli sauran abokan fad'an Nata ya ce .



"Ku biyoni office ke Kuma minti biyar na Baki Baki sameni office ba kinsan sauran "Yana Gama fad'ar hakan ya fice suna biye dashi Saida sabren taga ficewarsu kafin ta Mike Tana goge hawayen da ta Fara ta kalli Yan class d'insu Daman dukansu su 15 ne ta ce,.




 "idan uncle ya tambayeku shaida ku ce su suka Fara janmu su suka Fara Kai Mana duka suna zagar Mana iyaye shiyasa har muka Rama idan ba haka ba wlh Babu wacce Zan sake sayawa chocolate da biscuit har ice cream gobe Zan saya muku Indai kuka fad'i haka wlh".



"cikin sauri Yan class din suka hau ihu suna angama baby SABREEN Big girl ai gwara da Kika dakesu Baki da case zamu Kara abunda baki ma ce ba Amma wlh Allah saikin cika Mana alk'awarinmu na ice cream idan ba haka ba gobe mu tona"


Hararar Jamcy dake maganar tayi ta ce "na tab'a muku alkawari ban cika ba"Sudais "ya amshe da cewa "rabu da ita big girl karta b'ata maki time "Juyawa Sabren tayi ranta gall ga wani dad'i da takeji yanda Yan class dinsu ke kod'ata,



A office din uncle nura Koda ya bincike su, su zey suka ce ita ta Fara jansu ta karyata ta ce" Kuma ko Yan class za a tambaya su suka Fara janmu Saida suka Fara dukanmu tukwana muka rama",


Duk mamakinta su hibba suke kafin Zey dake kuka ta ce "Karya take uncle Kuma a tambayi y'an class d'in"gardamar da sukeyi ne ankasa gane Mai Gaskiya cikinsu ya Sanya uncle cewa muje na tambayi y'an class d'in naku sannan duk Wanda na Kama shike da laifi saina hukuntashi"



Duka suka amsa sun amince, ana zuwa ko Nan Yan class dukansu suka karyata su hibba ,sukace su suka Fara jansu sudais Ne Mai cewa "uncle Har zagin iyayenta suka dingayi ta kyalesu Saida suka Fara dukanta ne ta Rama ".



Sosai su Zey suka hau kuka Sabren ko wani dad'i takeji a ranta ganin yanda uncle ya hau musu fad'a har Saida yayi musu bulala biyu biyu inda ya had'a har Affan ita Kuma sabren Bai dake ta ba saboda ance janta akayi dukda yayi mamakin har sabren ce za a jata a daketa ta kyale yanda kullum suke fama da case d'in Yarinyar akan fad'a ,amma shaidar da duka y'an class suka Bashi ne yasan ba zaiyu suyi mashi k'arya su duka ba ranshi yace "ko ta Fara hankali ne".



Saida suka koma seat dinsu Ta dinga bawa Affan hakuri k'asa_k'asa Akan dukan da akayi mashi da hannu yasa ya bugar Mata cinya da k'arfi Wanda ya sanyata sakin dariya ba shiri kallonta uncle yayi Ganin yanda take dariyar ya murtuke tare da yi Mata warning Akan ta sake zai daketa "Hakan ya sanyata yin shiru,.



 ,bayan barin uncle class d'in Nan sabren ta hau yiwa su Zey dariya tare da yi musu gwalo ta ce gobe ma ku tab'oni kuji Irin abunda zanyi muku,.


Koda akayi break abubuwan da sabren tazo dashi su biscuits chocolate da soyayyar doya da kwai tare suka cinye da y'an class d'insu d'aya kad'ai ta samu taci da haka take saye class mate dinta kome ta samu saita kawo musu ita sai tak'i ci ma ta Basu saboda su dinga tsoranta suna Mata fadanci data shigo ana kitunzurata.

 big girl wanna abun sosai yake k'ara tunzurata .


,Koda a ka tashi motar Gidan su Affan tahau kamar ko yaushe a ita ake mayar da ita kaita Ne kawaii mom take shima wani Karin tare take kaisu su biyun,.




 sai yunwa takeji a palour ta tarar da Mom Tana latsa waya da gudu ta ruga Wajenta tare da yin hug dinta rungumota mom.tayi Tana cewa"oyoyo momyn dad andawo sannu ko ya gajiya"


"Thanks God mom abinci yunwa nakeji "ta fad'a Tana shafa cikinta Daya lotsa tare da marairaicewa ,Mom na rage Mata school materials dinta ta ce,



 "Wai ina kike Kai uban abincin da nake girka maki kina tafiya dashi sabren ,na tabbata abincin da nake zuba maki yafi karfin cikin ki dukda, nasanki ba wani abincin kirki kike ci ba Amma kullum Kika dawo da yunwa kike dawomun na kasa gane al'amarin Nan kodai Yaran gari nakewa wahala ta fad"a Tana Kama hannunta tare da nufar dinning Area da ita" 



"Mom ba Wanda nake ba fa yunwar ce kawai take zuwa "ta fad'a Tana janyo dining chairs tare da Zama "ta Fara cin lafiyayyar jolloup d'in macaroni da Tasha kifi sukumbiya da vegetables.


Tana ci tana yiwa mom surutu Tana cewa "Mom dad Bai Kira ba yau ki kiramun Shi vedio call Ina son ganinsa nayi kewarsa"ki Gama cin abincin sai na.kira maki Shi ".



Da yamma batayiwa mom gardamar islamiya ba saboda taga Affan harya tafi a chan dinma ba wani karatun kirki sukayiba rabi wasa rabi an dauka har lokacin tashin su yayi mom ta mayar dasu a gidansu sabren suka hau wasansu Tare da su anesa da suka dawo tare bama su wuce gidajen su ba suka yada zango Gidan su sabren ba Wanda ya cire uniform cikinsu sai bayan magriba mom ta hada su da sweet kafin su wuce gidansu da niyyar sai gobe ,



Da daddare sabren ta rasa yanda zatayi ta samu kud'in da zata sayawa y'an class dinsu alkawarin da tayi musu na ice cream ga dad baya nan Daman shine da ta tambayeshi ko nawa yake Bata a palour tayi jugum Kamar wata marainiya tunani ta dingayi idan fa Bata saya musu ba zasu Raina ta su dainayi Mata Kallon big girl ma ta koma small girl kamar su Hindu sannan Nan gaba ko tayi tsokana bazasu goyi bayan ta ba ,oh my God ta fada a cikin ranta kamar wata babba ,fitowar mom daga kitchen kenan ta gama simple girkin da tayi musu taga sabren Tana ta tunani zaunawa tayi tare da Kiran real name d'inta ta ce.



 "Khadija Lafiyanki qlau tunanin me kike?ba komai mom Tunanin dad nake yaushe zai dawo"




A sanyaye mom taje inda take tare da janyota jikinta Dan tasan shakuwar Sabren da dad baitaba dadewa basa tare ba tasan Dole ta damu cikin sigar lallashi ta ce,..



 "Zai dawo soon Insha Allah ki dinga yi Masa addu'a ya tafi wani Course ne da za a k'ara Masa babban girmama a wajen aikinsa nasan ai kina son dad ya k'ara samun kudin da zai dinga saya maki ice cream da chochulate ko?


Cikin sauri Jin abunda mom tace ya sanyata gyada Kai ta ce "Ina so mom"yawwa momyn dad saiki dinga Masa addua idan kinyi salla kina cewa Allah ya bawa dad sa a "Cikin sauri tace 


 "tO mom yanzuma idan nayi sallah zance "Allah ya bawa dad sa a yasa yasamu nasara duka ya cinye yafi kowa ya samo Mana kudi masu mugun yawa ya bud'e mun babban shagon ice cream nayi ta Sha"


Dariya mom tayi Tana Girgiza Kai ta ce "Ameeeen Daughter"a palour suka ci indomie din da ta girka musu a tare Bayan sunyi salla tare mom ta Bata littafin qur'ani ta dinga karantawa sura D'aya ta karanta dukda mom na cinta g'yara ta Kama hamma bacci take Ji Saida mom ta kaita har bedroom d'inta Tana Shirin fita ta Mike tare da turo Baki ta ce "Mom Ni dai mu kwana tare banason kwana Ni Daya"Naji rigimammiya kwanta to idan kinyi bacci Nima saina kwanta"mak'e kafad'a tayi ta ce "


"Nasan wayau kikeson kiyimun nidai saidai mu kwanta tare"Ba yanda mom ta iya Dole aka sanyata kwanciyar Dole ba shiri a ran Mom Tana Jin dad'in Ganin y"artata ta Fara daidaituwa a ranta ta ce "Daman nasan duk Kai kake rikitamun Yarinya wlh aka barni daga Ni sai ita na wata guda ma saita gyaru".



Washegari sabren duk hankalinta ya tashi akan kudin da zata samu ta sayawa Yan class dinsu ice cream Tana zaune a palour tayi jugum mom ta fito tare da Aje Mata Basket din abincin break d'inta ta ce "D'an jirani minti biyu na fito Daga Wanka saina kaiki saboda Ina son biyawa kasuwa nayi sayayya.



Mom na shiga Wanka a bathroom d'inta na bedroom sabren tayi sauri ta Mike tare da nufar dakin gabanta sai fad'awa yake yau zatayi abunda Bata tab'ayi ba watau daukar kudin da ba a Bata ba,.


Tana shiga taji k'aran ruwa a toilet cikin sauri ta shiga duba lockers d'in Dakin taga ba komai jakar mom da ta hanga a kan bed ya sanyata saurin zuwa tare da zagewa taga kud'i masu uban yawa y'an dubu dubu Tana waige ta d'auki guda hud'u tare da zugewa tayi sauri ta fita palour Tana sauke Ajiyar zuciya a school bag d'inta ta boye kudin Tana murmushin Jin dad'i..........✍️


*Domin magana da marubuciyar kai tsaye *** haka zalika masu buk'atar tallata musu hajarsu suma su tuntub'eni akan wannan number*



_Ummu Maheer_

*DINYAR MAKAHO*



_Miss Hajo_

*KHADIJATUL SABREEN*



_Mrs Bukhari_

*ANGULU DAKAN ZABO*


_Ummu Affan_

*SANDAR MAKAUNIYA*


_Mom Islam_

*TSAUTSAYIN TAUNA*


*Ga tsarin yanda biyan yake*


_Guda d'aya 300_

_Guda biyu 500_

_Guda Ukku 700_

_Guda hudu 800_

_Guda Biyar 1k_


Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.


0037219728

FATIMA RABIU SUNUSI

StanbicIBTC BANK


Shaidar biya ta nan


***


Masu turo kati MTN ta wannan number.


***


Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.


***


*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿




   _*Miss Hajo Ce*_🤙