CHAPTER FOUR 4
by @misshajo
🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸
```MALLAKAR```
*HAJARA L SADEQ*
Arewabook👉@Miss Hajo✍️
🅿️...........*7 & 8*
Washegari Kasancewar dad da kanshi ya kaita school suna tsayawa bakin get ta marairaice fuska tare da kallonsa ta ce "Dad I want you to give me money please"Yana shafa kanta ya ce " how much do you need My Angel?"10k dad anma karka fad'awa mom"ta karasa bada Tana turo Baki".
Murmushi dauke da fuskar dad ya ce "shikenan daughter bazataji ba 10k ya ciro tare da Mika Mata"Cikin murna ta amsa tare da Rungume dad Cikin farinciki ta ce "I'm very proud of you my dad thanks so much,"
Shidai dad murmushi kawai yake Yana kallonta cike da so da kaunar tilon y'ar tasa da Allah ya mallaka Masa a duniya a rayuwar dad Babu wacce yake so a fadin duniyar Nan sama da sabren baya son bacin ranta Yana kaunar farincikinta fiye da nashi kodan hakan ya samo nasaba ne bisa ga wahalar da suka Sha kafin Allah ya mallaka musu ita".
Ai sabren ganin kud'in wannan hannunta da mulki ta shiga school din tanajin kanta na k'ara Mata wani girma ta na cikin tafiya ta hango wata safiya y'ar s s two Daman basa jituwa Aiko taki Bata hanya itama Taki Bata hanya Suna kurewa juna Kadan ya Hana Suyi Karo da juna ja safiya tayi ta tsaya tare da fardo sabren ta ce "ke maras tarbiya Dan Ubanki Baki ganina a hanya ne watau ke isashshiya ban Isa ki bani hanya ba ko"Ta fada ta na huci".
Fincike wuyanta sabren tayi tare da Galla mata harara ta ce "dallah sakarni nonsense Ni nafi karfin na hada jiki da stupid irinki Mai warin Kashi Amma ki sani yau zakisan kin tabo babbar Yarinya a school dinnan ki saurari result anjima kazama"Tana Gama fadar haka tayi gaba Tana Jan tsaki.
Ranar anayin break da 10k din da Dad ya Bata suka shiga shop ita da duka y'an class dinsu suna take Mata baya suna kirarata da big girl gaba daya 10k din ta kashe musu har zey da itama sun shirya yanzu ganin Yan class dinsu sun Goya Mata baya liyafa sosai tayi musu a class din ,anan NE take fada musu Tana son su hadu su ci Mata uban safiya yanda Nan gaba ko harararta Bata Isa tayi ba Nan suka hau hargagi Suna cewa
"Aiko yau safiya saita ci ubanta zatasan ta tabo Mana sarauniyar class din haka dai har aka tashi Suna kitsa yanda zasu jibgi safiya Wanda zey ta bada shawarar a bari sai an tashi ai a kasa take tafiya su bita da bulalu suci ubanta.
Haka ko akayi Ana tashi gaba daya Saida suka ga safiya ta rabu da class mate d'inta tayi hanyar gida suka bita suka tareta suka zagayeta sabren dake tsakiyarsu ta kwashe da dariyar ta ce "Daman ba Saida na fad'a maki ba saina ci Ubanki zakisan yau kin tabo *KHADIJATUL SABREEN* a makarantar Nan kafin ta kalli Yan class dinsu ta ce "Hey guys ku Fara aiki"kafin safiya tayi wani motsi yaran su harar Mata sosai suka dinga jibgarta Tana ihu Tana kuka Yara Sha hudu a kanta hada maza sabren ko Banda dariya ba abundai take ganin yanda safiya ke kuka Tana Bata Hakuri bazata sake ba,.
Uncle dinsu yazo wucewa gida kenan yaga wanna ta asar saukowa yayi Daga motarsa ya nufo wajensu hankali tashe sabren na ganinsa ta ce "Mu gudu ga Uncle Nan ku rabu da ita" kafin uncle ya ciro bulala a bishiyar dake gefensu sabren ta kwasa a guje sauranma suka bita da gudu kowa ya watse,.
Da dare sabren na jikin dad dinta da anjima anjima saita kwashe da dariyar tunowa da irin dukan da ta Sanya akayiwa safiya da yanda take Bata Hakuri duk wanna karyar da take a school,kallonta dad yayi ya ce "Yadai daughter dariyar me kike tun dazu"wata dariyar ta kumayi kamar mahaukaciya Shima dad dariya yayi ya ce "ga alamun dai yau Daughter na cikin farinciki take"Tana dariyar ta Mike zaune tare da Kama hannun Dad ta ce "Dad Bari na baka Labari ".
wayarsa ce tayi ringing ya sanyata yin shiru bata karasa abunda takeson fad'a ba Kallon Mom tayi dake yi Mata gugar uniform harma ta Gama ta Mike ta ce "Dan Allah mom Gobe karnaje school"Harararta mom tayi ta ce "ki zauna Kiyi me a gidan saikinje ",
Kwabe fuska tayi tare da turo Baki batace koma ba "ta bud'e robar ice cream din da dad ya sayo Mata ta Fara Sha "Gama wayar dad yayi tare da kallon sabren dake Shan ice cream d'inta hankali kwance saikuma ya kalli Mom dake kallonsa ya ce"Wai kinji malaman Makarantarsu baby ne suke son gani na Gobe da safe tare. Da daughter,"
"ikon Allah to Allah kiyaye ba wani laifin tayi ba har ina murna an kwana biyu ba a kirani case d'inta ba kafin ta kalli sabren ta ce "laifin me kika yi kuma"Wara hannu tayi irin I don't care dinnan ta ce "Nima bansaniba"Tana Gama fadar haka ta Mike ta wuce bedroom d'in su Mom ta ce "Bacci zanyi mom Dad good night".
Numfashi dad yaja bayan barinta Dakin da damuwa ya kalli Mom ya ce"Muje matsala ta gaba wacce tafi damuna Amina ta tsoratar da yarinyar Nan da ake Ina mamakin al'amarin Nan Wata ukku kenan muna haka nifa na Fara tsorata da Al'amarin meyasa saimun tashi.....kasa karasa maganar yayi sakamakon shigowar sabren Dakin Tana Hamma Kai tsaye wajen dad ta nufa Tare da kama hannunsa ta ce "Muje mu kwanta dad bacci nake ji banason a tsorata ni"okay Muje daughter Dad ya fad"a Yana mik'ewa,, da harara mom ta bisu har suka wuce,Dan ita har yanzu Bata yarda da Ana tsoratar da sabren ba.
Washegari a tare da mom suka je school din Dan tasan halin dad akan fad'a da malaman makaranta da yake Akan sabren a pri makarantun da ya sauya Mata Akan dalili marar tushe ita kanta bazata iya lissafasu ba.
Kamarko ta sani yanzun ma fada ne ya kusa kaurewa dashi da vice principal din makarantar tare da Iyayen safiya da suka kawo Kara sauran iyayen yaran da aka Kira duk sun bada Hakuri bayan anyiwa yaransu furnishment da bulala ukku ukku nanfa Dad ya ce wlh Bai yarda ba in duniya zata hadu kasa da sama ba Wanda ya Isa ya tabar Masa y'a saidai ya cireta daga makarantar gaba d'aya,.su kansu iyayen sauran yaran Saida suka tsaya kallon ikon Allah su da yarshi taja aka Dakar musu y'a y"a suce me,sabren ko duk ta tsure jin dad yana cewa zai cireta Bata ta'ba yin school din da taji dadinta irin wannan ba saboda yanda take juya Yan class dinsu son ranta sanna yanda ta Fara Suna a school din duka term dinsu Daya Taya zata yarda Dad ya cireta "Kuka ta fashe dashi tare da cewa "Dad na yarda a dakeni d'in Dan Allah karka cireni".
Daga mom har dad kallon mamaki suke binta dashi yanda suka San Yar tasu da tsoron bulala "Kamota dad yayi ya ce "Bamai dakar mun ke daughter Muje na cireki daga school din ai ba ita kadai ce school a garin yola ba duk ga su Aliyu mustapha academy, Con codia, da yawansu gasunan birjik sai Wanda na zaba,cikin sauri mom ta karbe sbabren daga hannunsa tare da Had'e rai sosai tasan ba abunda ya Tsana sama da yaga ta Had'e rai ta ce .
"Ka rabu da ita tunda tace ta yarda a daketa din Kuma kaga laifi tayi su sauran daliban da aka dakesu finta sukayi,banason haka daddyn sabren ka fita waje gani Nan zuwa yanzu Dan Allah"zaiyi magana mom tayi sauri ta amshe da cewa "Please ka fita zamuyi solution matsalar"Yana fita mom ta bawa Vice din Hakuri murmushi yai ya ce "Bakomai Hajiya mun Saba da irin wadannan case din "Kama hannun sabren data tsure mom tayi sosai tare da kaita gaban vice ta ce "ga ta malam yi sauri dakarta karya dawo".iyayen sauran yaran tuni sun bar office din Daman.
Kunsan ance ko mutuwa na tsoron idon mahaifi vice kasa dukan sabren yayi girgizawa Mom Kai yayi Dan ta burgesa yanda ta Bashi Hakuri Sannan da kanta ta ce a daketa ya ce"rabu da ita Hajiya Nan gaba ta sake tasan sauran zamu Had'e da ita"
" a a Kar ayi haka malam kaga sauran yaran an dakesu ita kadai Aki dakarta "Girgiza Mata Kai yayi Yana murmushi ya ce "ba yafe mata nayi ba zamu Had'e next time ta sake wani laifin zanyi Mata double purnishment sakarta ta tafi class"Mom na sakin sabren ta saki wata Ajiyar zuciya Dan da dukta tsure da gudu ta ruga hartaje bakin office ta juyo tare da cewa "Mom "Tana juyawa ta yi Mata gwalo tare da yin dariya ta ce "Ai dai ba a dakan ba lolololo"Tana Gama fadar haka ta kwasa a guje ,.
GirGiza Kai kawaii mom tayi tare da cewa Allah shiryeki Vice dai dariya yayi kafin yacewa mom" ba komai hajiya Dan Allah ki k'ara kula da yarinyar Nan lurar da nayi tundaga haka kina k'ok'ari ki k'ara Akan yanda kike kinsan icce tun Yana Karami ake tankwarashi idan ya girma baya tankwaruwa ku rage sangarta yarinyar Nan da yawa ko ba yanzu ba saboda gaba mace ce sannan Dan Allah a daina Bata kudi da yawa budewa yaro Ido da kudi babbar matsala ce ".,
Murmushin da yafi kuka ciwo mom Tayi ta ce"insha Allah na gode"a mota ta samu dad Tana shiga ya banka Mata harara Wanda Saida ta sanyata ta Dara ta ce "maida wukar na Amina ikon Allah ba a dake ta ba".
"Cikin sauri ya juyo ya ce Da gaske ko wasa"Da gaske sun Mata Hakuri kafin ta bashi labarin yanda sukayi da malamin Nauyayyar Ajiyar zuciya dad ya sauke Yanajin wani sanyi a ranshi Jin ba a Dakar Masa yar lele ba murmushin yayi ya ce "sai Yanzu hankalina ya kwanta yanzu muyi sauri muje gida muna Da Free time kinsan nayi Kewarki sosai...murmushi kawaii mom tayi Tana kauda Kai.,
sosai ta Lula duniyar tunanin yanda zata tankwara sabren kamar yanda malaminsu ya Bata shawara tasan ba karamar sangartata dad yayi ba tun Tana ciki kafinma tazo duniya ya d'auki son duniya ya Dora mata ,itama zata iya cewa tanama yiwa sabren fiye da son da yake mata Amma Dole ta danne son wajen ganin ta samu tarbiya me kyau Amma yanzu Tana ji Tana gani ko yawo batayi da sabren saboda kunyatata din da take cikin mutane tunowa da wahalar da ta dingasha kafin a haifeta Saida tayi b'arin ciki har sau biyar Wanda ana shiddar ne dakyal da Addua Allah ya zaunar musu Wanda shine silar zuwan sabren duniya,.
dalilin operation din da akayi Mata da rashin hutu da mahaifarta Bata samu saboda akai akai ta dinga samun ciikin dan shekaransu ukku da aure tayi barirrikan Nan ya Sanya mahaifarta samun matsala Wanda akayi Mata aiki aka ma cire Mata ita gaba d'aya tasan ita da Kara haihuwa har Abada shiyasa take Kara godewa Allah da mallaka Mata sabren da Kuma Mijinta Mai matukar kaunarta tsakani da Allah ،dan tasan da wanine aure zaice zai Kara dukda tasan yanda yake fama da danginshi akan rashin Karin auren ya samu wasu y'ay'an Suna tunanin ita ta Gama dashi tayi mashi asiri Amma Yayi burus ya kyalesu ya ce Matarsa da y'arsa d'aya sun isheshi Albarka yake nema ako yaushe ba yawa ba .
,.tunowa tayi da duk lokacin da zatayi b'arin cikunnan Daren ranar mafarkin da take na wata Mata ta juya Mata baya Bata ganin fuskarta Ta Rufa da wani k'aton bargo ta baya take Chaka Mata wani Abu a cikinta Wanda da zarar ta farka take tashi da ciwon da zaiyi Sanadiyar misscarrige d'inta tunowa tayi da haihuwar sabren sau ukku Tana mafarkin ta Sai tazo zata Chaka Mata abun Daddy yazo ya dauketa yayi Sama da ita ana gobe zata haifi sabren ma Saida tayi mafarkin matar lokacin cikin fushi take harta iya juyowa gareta Amma Bata yarda taga fuskarta ba saboda gaba daya ta rufe fuskarta Cikin fushi Ta dauko abunda ta Saba Chaka Mata harta tillo abun kawaii saitaga Wani hasken Abu ya fito daga cikinta ya mayar mata da abun Wanda Saida matar fa fadi kasa cikin fushi ta Mike zata Kara dab'a mata wani Dad din sabren Yasa hannu ya fardota jikinshi harta farka "Daga lokacin ya dage da Bata adduo'i na azhkar da sauransu sannan ya Kara karfafa Mata gwuiwa akan ruk'o da addini da adduo I tundaga lokacin Bata sake mafarkin Mai Kama da wannan ba Saboda Kara riko da ibada da ta yi Dan tasan Mijinta mutum NE Mai tsananin ibada da ruko da Sunnar manzon Allah s a w ".
"Tab'in da Dad yayi Mata Ne ya sanyata dawowa daga duniyar tunanin da ta Lula "ya ce "Ranke Dadi wannan dogon tunanin fa"murmushi ta kirkira Tana fitowa daga mota ta ce "Har munzo kenan"hannunsu sakale Dana juna suka shiga palour mom sai farinciki take yau daga Ita sai dad a gida gabanta ne yaja ya fad'i cin Karo da Sadiya da tayi a palourn ta hakimce Tana Cin tuffa ,.
Cikin sauri ta Mike Tare da Fara gaishe da dad cikin Fara a ya amsa Mata tare da cewa "Ya su BaBa"Lafiyansu qlau "ta fada Tana Yar in Ina "tare da kallon mom da tayi tsaye ta ce "Ina kwana Aunty Amina Yau cewa nayi kwana biyu Bari nazo mu gaisa"
"Daidaita nutsuwarta mom tayi ta ce "Muntashi lfy Sadiya yasu baba ya yaran"Lafiyansu qalau"Ina Momynmu sabren ko ana makarantar "Eh ana school "Mom ta fada Tana maida gabanta ga television Takaici duk ya Gama isarta Dan harga Allah tanabukatar mijinta feel free daga Ita saishi a gida Amma kullum gidan su tunda yazo baya rabo da Baki daga kowani bangare wannan yazo wannan yazo...
Sabren dawowarta kenan daga School duk ta gaji tun a compound ta Fara cire takalmi da safa tare da wurgar da hijab din a palourn farko Tana ta turo Baki ita yunwa take Ji harta karaso babban palourn.
Aunty Sadiya dake tsaye a bakin dining table ta bud'e Zane Tana barbada wani magani a abinci Taji shigowar SABREEN ta na ganinta tayi sauri ta maida maganin bayan ta Gama barnadawa a miyar ta matsa daga wajen hankali Tashe dukta rude, kirkiran murmushi tayi tare da nufo sabren Tana cewa"oyoyo oyoyo Mamanmu ke nake ta jiran dawowarki Yar albarka"Ta fada Tana nufarta da niyyar rungumeta".
Sauri sabren tayi ta matsa Tana wani yatsine fuska ta ce "Ni karki tab'ani Malama"me nake gani haka sabren rashin kunyar Taki har mamantaki zakiyiwa manya ma Baki Bari ba"cewar Mom ta na fitowa daga kitchen"
"Allah kiyaye Ni ba mom d'ita bace wannan shirgegiyar Allah kiyaye ta Zama mom Dita"ta fada Tana turo Baki
"Salati mom tayi ta ce "Kanwar Baban naki kike fad'awa hakan dan Baki da mutunci sabren"Mom ta Tana nufota Aunty sadiya duk ta tsure tsoro take Kar aje sabren taga abunda ya zuba dukda tasan Daman yarinyar ba kaunarsu take ba Bulala Daya mom ta tsala Mata ta charger waya Wanda ihun data kwalla Duka Saida ya kewaye Dakin wani irin ihu take kamar ana zarar ranta Aunty sadiya dukta rude ta ce.
"dan Allah Kiyi Hakuri Aunty Yarinta ce Ni wlh banjima komai ba"Haba Sadiya akanme komai tayi sai ace yarinta yarinyar Nan ba fa Yarinya bace da za ace a shekarunta Bata San darajar manya ba,sabren ihu kawaii take hange take wata barnan zatayiwa mom wacce zataji ciwo fiye da yanda Taji na bulalar.,
hango abinciccikan da ke jera a dining tayi tasan mom ba abunda ta tsana sama da barnan abinci Aiko ba Inda ta nufa Tana ihun kukan sangartata sai dining Tana zuwa ta hau watsi da komai Dake dining din miyar ta dauka Tare da watsawa a farin carpet din palour aunty Sadiya da suka nufo wajen hankali tashe mom da Dora hannu aka tace na shiga Ukku sabren abincin da tun safe nake wahalar girka sa Kika zubarmun miyar da Nayi ta kwana ukku Kika watsarmun ita Wasu hawayen bakin ciki NE suka zubowa mom saboda bakar wahalar da Tasha Ai Bata San lokacin da ta furta Cewar"Yanda Kika wulakanta abincin Nan wata rana saikin nemeshi da idonki kin rasa Dan ubanki".
( da yawa wasu iyayen fushi na sanyasu ga fad'awa yayansu mugayan kalamai na Baki wanda saisun Manta ma bakin ya dinga bibiyar yayansu saboda ance bakin uwa dafi ne Allah yasa iyaye su gane su dinga Kai Zuciyarsu nesa yayinda yayayensu sukayi musu wani Abun da basuji dadinshi ba Allah sa mu gyara). wayar wuta Mai kauri ta wawuro tare da nufarta da ita sabren na ganin haka ta kwalla ihu tare da nufar hanyar kofa
mom ta Mara Mata baya Dan Yau Mai raba ta da ita sai Allah sabren hankalinta duk ya tashi bude k'ofar palour tayi ta kwasa a guje Maigadi ya Mike Yana tambayarta Lafiya saijinshi yayi kasa sakamakon bangajesa din da tayi mom Kira take,.
",yusha'u karka barta ta fita ka rik'emun ita kafin ma yusha'u ya Mike ta bude k'ofar get d'in ta Kara kwasawa a saba'in Bata nufi ko Ina ba sai gidan su Affan..........✍️
*Domin magana da marubuciyar kai tsaye ****
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
***
Masu turo kati MTN ta wannan number.
***
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
***
*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿