01
by @kitty
A CIKIN DUHU…
Kittyđź’•
Wattpad@ Mssmeemah
01
Kwanon gyad'ar da ta sayar ta kifa a kanta tana neman wurin fakewa saboda mamakon ruwan dake sauka. Da 'kyar ta samu rumfa 'kofar gidan wani mutumi da ta kasa gane wane gida ne saboda duhun da ya bayyana domin tanada tabbacin idan har ya fito ya sameta a wurin sai ya koreta. Tsanar da mutanen 'kauyennan ke musu ta rasa dalilinta, wannan labari ne da mahaifiyarta kawai zata iya bada shi.
Jikinta gaba d'aya karkarwa yakeyi domin duk ta ji'ke gashi ruwan babu alamun zai tsaya nan kusa gashi gidansu da tazara. Hawaye ne ya biyo fuskarta wanda ya wanke a cikin ruwan yayin da ta tuna halin da mahaifiyarta da 'kaninta suke ciki a yanzu, idan anyi ruwa kad'an ma ya suke 'karewa balle mai yawa? Duk gidan nasu ruwa ya wanke 'kasar d'akin da suke kwana ne kawai ya rage shima Saida mahaifiyar tasu da kanta ta had'a 'kasa ta tottoshe wasu wuraren.
Tana tsaye tana ri'ke da hannayenta har ruwan ya tsagaita yanda zata iya tafiya gida. Sauri take sosai cikin ruwan da ya kusa shanye rabin unguwar tasu domin ruwa ya kusa kaiwa gwiwarta amma bata damu ba, a wannan yanayin zata iya fad'awa rami ko rijiya amma sam ba wannan ne tunaninta ba, tunaninta kawai taje taga halin da mahaifiyarta da habu 'kaninta ke ciki.
Tunda taga katangar 'kofar gidansu ta wanke taji gabanta na fad'uwa, da gudu ta fad'a tana Kiran "Baaba, Baaba!!"
Turus tayi tareda mutuwar tsaye ganin mahaifiyarta dur'kushe bakin d'akinsu da ya ruguzo tana kuka tana kiran habu. Dur'kusawa tayi gefenta tace "Baaba me ya faru? Ina habu?"
"Karime katanga ta ruftawa habu, tun d'azu nake lalubensa da kiran sunansa Karime na kasa samo shi".
A gigice karime ta zuba gwuiwoyinta a 'kasa ta fara ture 'kasar dake wurin, Banda karkarwa babu abinda jikinta keyi tana 'kwalawa habu kira saidai babu alamun habu ko muryarsa, can 'kasan wani gini ta hango yana motsi, nufar ginin tayi tana fad'in "habu, habu, kayi magana dan girman Allah" saidai hannunsa kawai ta hango yana motsi, muryar karime na rawa tace "Baaba mu nemi taimako a wurin ma'kwabta".
" Karime bazasu sauraremu ba, nayi kuwwa nayi kuwwa amma babu wanda ya kawomin taimako".
Karime tuni tayi jifa da mayafinta ta fice daga gidansu ta fad'a gidan dake gefensu wanda keda mata da yawa a ciki, da'ki d'aki take bi tana fad'in "Dan Allah ku taimaka mana gini ya fad'awa habu kar ya mutu, dan Allah ku taimaka mana".
Babu wanda yayi yun'kurin taimaka mata hasali ma tamkar tana magana da iska haka wasu matan suka mata, kad'an daga ciki ne suke da 'karfin gwiwar jefa mata magana d'aya daga cikinsu tace "au shima zaku cinyeshi ne kaman yanda kuke cinye 'yan uwansa? Tir da hali irin naku Allah ya wadaran wannan zuri'ar taku, yanda shima ya mutu Allah ya kasheku duka mu huta".
'dayar kuwa turo 'kofarta tayi sannan ta d'ebi ruwan kanwa ta watsa tace "mugun alkaba'in dake bin danginku shi kikazo ki kwasawa 'ya'yana? Wuce ki bar min 'kofar da'ki kafin na karairaya ki na kashe banza dama kun addabemu, yaje ya mutu mana ko an ceceshi zaku barshi ya rayu ne?"
Maganganu marasa dad'i da zagi babu irin wanda karime batasha ba haka ta baro gidan jiki a sanyaye ta gama sarewa cewar habu ya rasu kamar yanda sauran 'yan uwansa dukka suka rasu kuma aka la'kanawa ita da mahaifiyarta cewar sune suke kashe su. Ta yaya uwa zata kashe d'an da ta haifa da cikinta?
Ruwan gaba d'aya ya d'auke haka taje ta samu mahaifiyarta ta gama ture ginin da ya fad'awa habu ta janyoshi gabanta ta zuba mishi idanu. Shigowar karime yasa ta mi'ke tsaye tana kallon d'iyar tata, dukkansu abu guda ke yawo cikin ransu.
Mahaifiyar karima da kanta ta d'auki d'an nata ta mishi wanka karima ta d'auki ji'kakken mayafinta ta rufeshi dashi. Fuskarsa fes kamar ta sauran 'yan uwansa a yayin da suka rasu, wannan itace gawa ta shida da karime ta gani mahaifiyarta kuwa wannan ce gawa ta tara na 'ya'yanta da ta gani saidai har yanzu ta kasa sabawa da mutuwa.
Karime da kanta ta fita ta nemo likkafani suka rufe yaron dashi sannan taje ta sanarwa liman mutuwar 'kanin nata, da 'kyar liman ya had'a kan mutanen da basu fi goma ba aka mishi sallah, wurin binneshi ma sam mutanen garin suka 'ki yarda a binneshi cikin jama'a sai can nesa aka ha'ka kabarinsa aka binneshi.
Duk wannan abubuwan da akayi a kan idon karime aka yisu, ta rasa wannan tsananin tsana da ake ma danginsu ace gawar ma bata tsira ba?
A gida ma bata sauya zani ba domin mata ne suka ma mahaifiyarta caaa akan sai ta fice ta bar gidan tunda ta gama cinye 'ya'yanta maza babu mamaki kan nasu zata koma, mahaifiyar karime bata tanka musu ba har suka gama maganganunsu cikinsu harda mai jifanta suka fita suka barta anan.
Kafin karime tayi magana mahaifiyarta ta katseta tace "karime ko basu koreni ba banida wurin zama a gidannan, d'akin namu ya wanke bamuda inda zamu zauna".
Girgiza kai karima tayi tace " baaba idan mun tafi ma ina zamuje? Bamuda kud'in da zamuyi tafiya da guzuri har mu samu gidan zama. Ko haya ce mu nema anan har lokacin da Allah zai kawo mana 'karshen wannan abun mutanennan su san cewa ba laifinmu bane".
Shiru mahaifiyar karime tayi amma tasan da wuya su sami wanda zai basu gida a garinnan, su basu 'ki ma ruwa ya cinyeta da 'yar tata ba su huta. Da 'kyar karime taja ra'ayin mahaifiyarta suka tattara 'yan kwanukansu da sauran kayan da zasu iya suka aje a gefe suka fita.
Karime bata ta'ba ganin anyi ma wani d'an uwanta zaman makoki ba ko kuma wani ya mutu azo a ma mahaifiyarta gaisuwa, mutuwar 'yan uwanta tamkar mutuwar 'beraye take a garinnan domin ko kaza ta mutu sai azo ana ma mutum jaje su kuwa saidai a kallesu ayi tir dasu.
Cikin samarin unguwar akwai wad'anda suke d'an kulata amma a 'boye inda babu idanun mutane, d'aya daga cikinsu take fatan zai iya basu matsuguni kafin su samu su farfad'o da nasu.
Sani, shine saurayin da karime ke sayen gyad'a a wurinsa wanda shine kad'ai mutumin dake nuna mata ita mutum ce. Zasuyi magana har su d'an yi hira tsakaninsu tana jinsa tamkar d'an uwanta, a yanzun ma wurinsa ta dosa tana fatan Allah ya sa ya taimaka musu.
Tayi sa'a ko ya fito zai nufi masallaci sallar magriba ta tareshi, cikin murmushi ya amsa mata tareda gaida mahaifiyarta wadda ta amsa cikin sauri domin rabon da wani saurayi ya gaidata a wannan garin har ta manta.
"Sani taimako mukazo nema a wurinka, d'akinmu ne ruwa ya wankeshi shine sanadiyyar rasuwar habu domin ginin a kansa ya fad'a. Shine nake neman taimako dan girman Allah da darajar Muhammadu rasulullahi ka taimak mana da wajen da zamu zauna na haya kafin mu sami yanda zamuyi ku gyara gidan".
Shiru Sani yayi yana tunani sannan yace " karime ai gini bazai yiwu a damina ba, zan dai duba na baku inda zaku zauna har zuwa rani saidai ba gidana bane na abokina ne banida tabbaci Kuma ko zai bayar".
Dur'kusawa karime tayi gabansa tace " Sani ka taimaka mana, bamuda kowa a garinnan bamuda inda zamuje, ko da mahaifiyata ka bata wurin da zata zauna ni zan iya neman wata mafakar".
" A'a karime ke dai ya baki wajen zama ni banida matsala ko cikin rairayi zan iya kwana, yaro ka taimakawa 'yarnan tawa kaji?"
Cike da tausayi sani yake kallonsu saidai bashida yanda zaiyi ya taimaka musu, shima d'aki d'aya gareshi a cikin gidansu kuma iyayensa bazasu barshi ya kaisu ba. Dukda yana mutunci da karime amma fa zuciyarsa cike take da tsoron mahaifiyarta saboda irin labaran da yaji a kanta tun daga tasowarsa, yana tsoron ya ra'beta abinda ya faru da sauran mutanen da suka ra'beta ya faru dashi.
Suna ta faman masa magiya mahaifinsa ya fito, kallon sani yayi da karime da mahaifiyarta yace "la ilaha illallahu mahammada rasulullahi....wannan bala'i da nake gani a 'kwar gidana fa? Kai d'annan me wad'annan mutane keyi anan".
" Baba wai taimako suke nema gidansu ya zube".
Matsowa yayi ya kalli mahaifiyar karime yace " yanzu ke Hauwa ki rasa d'an wanda zaki kama sai nawa? To wallahi kurwar d'ana kur kuma ahir d'inki naji d'ana yayi ko da ciwon kai ne, na rantse da mahaliccin sama da 'kasa sai na kasheki na kashe wannan 'yar taki mai zubin mayu, wato naku mazajen sun 'kare kun fara bin namu ko?"
" Kayi ha'kuri....". Bai jira sauraron karime ba yayi wani tsalle ya karyo reshen bishiyar dake 'kofar gidan ya fara binsu da duka, da gudu karime da mahaifiyarta Hauwa suka bar wurin banda kuka babu abinda karime keyi mahaifiyarta kuwa idan da sabo ta saba da hakan, abinda take ma karime gudu kenan yasa tace kar su fita neman taimako.
Sunyi yawo sosai a cikin garin har duhu ya shiga babu mai niyyar basu wurin fakewa, sai rumfar kasuwa suka samu suka fake kasancewar kasuwar ba'a cinta sai alhamis, jiya anci kasuwa sunada lokaci kafin a sake cinta har sun samu su gyara gidansu.
Rumfar tanada rufin kara a samanta haka 'kasan an shafeshi da siminti, babu ta'bo a wurin sai bala'in sanyi amma a haka suka daure suka zauna babu alamun bacci a idanunsu. A hankali karime tace "baaba har yau na kasa gane dalilin da yasa mutanen 'kauyennan suke mana irin wannan tsanar, nasan tanada ala'ka da mutuwar 'yan uwana amma meyasa?"
Murmushi Hauwa tayi dukda tasan 'yar tata bata ganinta tace "Karime abinda nakeso dake ki cigaba da addu'a babu abinda ya gagari Allah, wannan ma jarrabawa ce Allah yake jarrabarmu da ita, muyi tunanin abinda ke gabanmu a yanzu Ina zamu samu muhalli?"
Shiru karime tayi bata cema baaba komai ba ta fara tunanin yanda ta tashi taga rayuwarta.
Karime itace 'ya ta biyu a wajen hauwa, saidai bata tashi taga 'yan uwan nata ba domin duka sun rasu, d'aya ya rasu kafin a haifeta d'ayan kuma tana shekara guda ya rasu.
Tunda karime ta fara wayo take ganin banbanci a wurin mutanen garinsu, bata isa tayi wasa da 'yan uwanta yara ba sai kowa ya janye 'ya'yansa daga gareta, tun bata fahimta har tayi wayon da ta fara fahimtar iyaye basu so ta ra'bi 'ya'yansu wanda a lokacin ne ta fara ganin gawar 'yan uwanta.
'kaninta na farko salisu ya rasu ta hanyar 'konuwa, yana da kimanin shekaru uku tana shekara biyar ita kuma a lokacin. Bata mantawa mahaifiyarta ta d'aura tuwo ya tunkud'o rud'en tuwon a kansa gaba d'aya wanda wannan shine sanadiyyar mutuwarsa, dukda yarinta irin ta karime amma har yanzu tana tuna yanda jikinsa ya koma kafin ya rasu.
Rabi'u shine na hud'u wanda a ranar da salisu yayi shekara guda da mutuwa shima Allah ya kar'bi abinsa. Rabi'u ya rasu yanada shekara biyu kwanaki kad'an da yayeshi suka farka suka tarar da ya rasu.
Kamisu kuwa kafin yayensa yana watanni 10 ya rarrafa ya fad'a rijiya sai gawarsa aka tsamo, bayansa mahaifiyar karime ta haifi wani namijin babu rai, sannan ta haifi Sadi wanda ya mutu ta sanadiyyar amai da gudawa.
Saminu shima yana da shekara uku yayi ciwon da ba'a san menene shi ba, ya dinga ramewa yana bushewa shi kad'ai har Allah ya kar'bi abinsa. Tasi'u yana kwana biyar da haihuwa ya rasu.
Duk wannan mace macen da 'ya'yan Hauwa keyi mijinta sulemanu bai ta'ba kawo wani abu a ransa ba duba da gwagwarmayar da yasha kafin aurenta, wasu 'ya'yan shi kad'ai yake binnesu saboda tsabar tsangwama da ake masa da matarsa. Damuwarsa d'aya itace karime wadda takeda shekara 22 a lokacin amma ta kasa samun miji saboda ba'kin fentin da aka shafawa zuri'arsa da matarsa da shi.
Hauwa tanada cikin habu Allah ya yiwa sulemanu rasuwa, Hauwa ta shiga tashin hankali marar misaltuwa domin mutuwar farat d'aya yayi, ya gama cin tuwon dare ya yiwa karime nasiha ya shiga d'aki yace zaiyi nafila, daga wannan nafila sai shiga Hauwa tayi ta sameshi a kwance ya rasu.
Hauwa bata ta'ba ma mutuwar 'ya'yanta kuka a fili ba sai mutuwar mijinta, tayi kuka tayi kuka tamkar ranta zai fita haka ma karime, ko da Hauwa ta tura karime fad'ar mutuwar mahaifin nata 'yan uwansa rufeta da duka sukayi suna fad'in ita da uwarta sun kashe musu d'an uwa. Ga zafin mutuwa ga zafin duka da 'kyar karime ta 'kwaci kanta a wurinsu.
Tana komawa gida ta sanarwa mahaifiyarta itama suna zuwa da kuka da ihu suka far mata da duka a lallai sai ta fad'a musu abinda ta yiwa d'an uwansu ya mutu ko kuma ta sakar mishi kurwarshi ya dawo da rai.
Karime ita ta dinga kare mahaifiyarta saboda halin da take ciki ga ciki ga ciwo ga mutuwar miji wanda yasa duk jikinsu yayi rud'u rud'u dukkansu da duka. Idan Hauwa ta tuna da maganar da sulemanu ya mata ta 'karshe sai taji wani sabon hawayen ya zubo mata.
'yan uwan sulemanu d'auke gawarsa sukayi tareda kashedi ga hauwa akan babu sauran ala'ka tsakaninta dasu, a wurinsu sulemanu baida wasu 'ya'ya ko mata saboda haka Kar ta sake ta tunkaresu domin a yanzu basu ma santa ba.