02
by @kitty
A CIKIN DUHU
kitty💕
Wattpad@ Mssmeemah
02
Babu wanda ya runtsa daga Karime har mahaifyarta babu wanda ya rutsa a daren, babu wani sauti dake tashi sai na numfashinsu sai kuma iskar da ke giftawa mai azabar sanyi da duk lokacin da ta gifta sai jikinsu ya d'auki karkarwa.
Asubar fari suka fice daga rumfar a lokacin kayan jikinsu duk sun bushe haka ma fuskokinsu, gidansu wanda babu abinda yayi saura suka nufa sukayi sallah karime ta d'auki kwanukansu ta fara wankewa saboda kawar da zuciyarta daga tunanin mutuwar habu.
Sha'kuwarsu da habu ta tuna lokaci guda hawaye ya fara kwaranyowa daga idanunta fuskarsa na mata gizo a idanunta. Habu shine 'kaninta na farko da ya girma har ya kai shekaru biyar kafin ya rasu, wanda yasa suka yi wata irin sha'kuwa suna nuna mishi gata marar misaltuwa.
Dukda ba'kin jinin karime da mahaifiyarta hakan bai hana habu danna kansa cikin jama'a ba, Allah ya bashi farin jinin mutane da saurin sabo hakan yasa duk nacin iyaye a kan su raba 'ya'yansu da habu ya gagara, dalilin habu kaso mai yawa na tsangwamar da ake musu ya ragu saidai shima ya tafi yanzu zasu koma gidan jiya.
Kama kwanon hannunta da baaba tayi ne ya dawo da ita daga hayyacinta. Basuyi yun'kurin dafa komai ba domin duk cikinsu babu mai jin yunwa sannan abincin da zasu ci ma babu.
"Karime akwai kud'i a jikinki?" Baaba ta tambaya a lokacin da gari ya fara wayewa, kama gefen zaninta tayi ta kunce ta zaro 500 ta mi'ka wa karime tace "idan akwai ki had'a da wannan ki sayo gyad'a sai a soya ki fita da ita tunda waccan ta wanke a ruwa".
Ba tareda karime ta kar'bi kud'in ba tace "ki ri'ke wannan a hannunki ko da wata bu'katar zata taso, akwai kud'i a jikina amma baaba jiya fa habu ya rasu".
Murmushi Baaba tayi tace "karimatu kenan, wanda ya rasu ya riga ya rasu suna can aljanna suna gina mana mazauni na alfarma, addu'a zamuyi Allah ya kawo mana 'karshen wannan abun. Kije ki sayo gyad'ar yanzu ko kya samu ki fita da wuri".
Tafiya kawai karime takeyi amma sam hankalinta baya jikinta. Rumfar sani ta nufa ta tarar baya nan hakan ya bata mamaki saidai bata kawo komai ba tayi gaba tana tambaya amma duk wanda ta doshi rumfarsa sai ya fara ja baya yana korarta, haka ta ha'kura ta koma gida ta zayyanawa baaba abinda ya faru.
Shiru baba tayi na d'an lokaci sannan tace "banaso kud'ad'en su salwanta ne kinga anyi asarar wasu idan kuma muka zauna haka bama juyawa cinyesu zamuyi. Ko zaki shiga kasuwar cikin gari ki sayo koda kwano ce".
Amsawa karime tayi da toh sannan ta gyara mayafinta da yasha daud'a daga jiya zuwa yau ta nufi hanyar fita, kiranta baaba tayi tace "ki tsaya ki saka wani abun a cikinki kafin ki fita ko".
Shiru karime tayi domin ita sam zuciyarta bata son wannan fitar kawai dai zata fita ne saboda umarnin mahaifiyarta kuma ta san gaskiya ta fad'a zasu iya cinye kud'in su koma ruwa kamar yanda sukayi a baya. Amsawa tayi tace "zan ci a hanya ki samu kema ki ci".
"To Allah ya tsare Allah ya dawo dake lafiya, ki kula sosai". Amsawa tayi da to ta fita cikin sauri.
Dubu uku da d'ari takwas ne a jikinta saboda gudun irin wannan yasa mahaifyarta hauwa sam bata bari ta aje kud'i a gida, koyaushe kud'inta na jaka d'aure a 'kugunta. Mutane ta gani tsaitsaye a 'kofar gidan su Sani wanda yasa tayi saurin sauke kanta ta wuce cikin hanzari.
Da kyar ta samu mashin d'in da ya d'auketa zuwa babbar kasuwa wadda take cike da mutane ana cinikayya. Babu wanda yasan wacece ita hakan ya sanya tayi sayayyarta cikin tsanaki har ta sayi hijabi d'aya ta sayawa baaba d'aya sannan ta d'an yiwa baaba tsaraba tana tunawa da habu.
Wasa wasa sai yamma sosai sannan karime ta samu fita daga kasuwa, bata isa gida ba sai ana sallar magriba.
Cike da damuwa ta shiga gidansu tana 'kwalawa baaba kira taji shiru, a hankali ta furta "baaba banso nayi dare ba wallahi kasuwa ce ta ri'keni, kina ina ga gyad'ar, na taho miki da rogo".
Shiru babu wanda ya amsa mata hakan yasa ta d'an shiga damuwa ta san baaaba bata shiga cikin gida. Rumfar da suka kwana ta koma ta duba babu baaba. A yanzu hankalinta ya tashi sosai ta bi hanya ta fara tambaya saidai duk wanda ta dosa cikin yara da 'kananun 'yammata sai su gudu wasu ma har su saka kuka.
Abokin habu marigayi ta gani yana wasa da kyaura ta dafa kafad'arsa tace "lawwali kaga babata?"
"Eh tun safe wasu mutane suka zo suka d'auketa suka tafi da ita wai ance itace ta kashe sani".
Wani mummunar fad'uwar gaba taji tace "wani sanin?"
"Sanin wawo, ya mutu shine aka ce ita ta kasheshi shine wasu mutane suka tafi da ita kuma tace idan na ganki nace karki zauna ki gudu".
Hawaye ke bin fuskar Karime a gigice tace "ina sukayi da ita?"
"Nima ban sani ba farko dai gidan wawo aka tafi da ita sai kuma aka fito da ita ana jifanta shine wasu suka kamata sukayi can da ita daga nan safiya tacena dawo gida".
Kuka sosai Karime take da gudu ta nufi hanyar da aka ce anyi da mahaifyarta tana kiran "ina kuka kai babata!! Ku fito min da baaba!! Dan Allah karku kashe min ita!! Baaba!! Baaba!!"
Babu wanda ya tanka mata har tayi nisa ga duhu na shiga saidai bata fasa tafiya ba, wani tunani ne ya kawo mata na ta koma ta gani ko 'buya baaba tayi ta dawo daga baya. Haka ta sake juyawa idanunta sunyi suntum saboda kuka ta koma ru'ba'bben gidansu.
Shiga tayi bata ga kowa ba ta d'auki kayanta da ta ajiye saidai kafin ta fito taji hayaniya ta fara kaurewa, dake zuciyarta tayi ta fito saidai jifan da ya sauka a kanta ne ya kusa gusar mata da hankali saboda tsananin azaba, lokaci guda jini ya fara kwarara daga goshinta ta dafe cikin sauri tana neman hanyar fita.
"Karku bari ta fita ku kasheta itama, indai ba 'karewa sukayi ba maitarsu da bala'insu bazai ta'ba dena bibiyar wannan garin ba, ku kasheta itama ta bi mahaifyarta".
Jin an ambaci kisan mahaifyarta yasa karime ta fidda rai daga rayuwa, ta za'bi su kasheta d'in ta huta da bala'in da take ciki hakan yasa ta runtse idanunta tana jiran abinda zai faru, saidai tamkar daga sama taji an fizgi hannunta anyi cikin gida da ita, bata lura da fuska ba kasancewar duhu ne gaba d'aya gidan sannan duk matan suna ta d'ayar 'kofar suna kallon izayar da ake mata.
Saida sukayi tafiya mai nisa ko nace gudu bata ga fuskar matar dake ri'ke da hannunta ba ta san dai macece. Tsayuwa sukayi matar tace "ki fita daga garinnan kiyi nisa dashi ta haka ne kad'ai zaki tseratar da rayuwarki, ki sani Allah yana tare dake kuma shine gatanki".
Cikin kuka tace "babata fa? Kina ji sun kashe babata, meyasa kika taimaka min wacece ke?" Waiwayawa karime tayi domin samun amsar tambayoyinta saidai bata ga kowa a tsaye ba, iyakar dubanta babu alamun mutum wanda hakan ya matu'kar tsoratar da ita. Buhun sayayyar da tayo a kasuwa yana gefenta wanda bata san yanda akayi ta taho dasu ba, iyakar tunaninta bata ri'ke komai ba lokacin da aka fizgi hannunta. Cikin sauri da tsoro ta d'auki hanya cikin duhun dare ba tareda sanin inda ta dosa ba zuciyarta cike da tunaninta rayuwarta tun daga yarintarta har zuwa yanzu
A tsorace Karime ke tafiya cikin tsohon dare saidai batada wata mafita da ta wuce wannan tafiyar. Lokaci zuwa lokaci takan ji alamun mutane wanda yake sanyawa ta tsaya cak ko kuma ta nemi wurin la'bewa domin dad'ewarta a cikin duhun yasa idanunta sun bud'e.
Wata iska taji ta gifta ta gefenta wanda ya sanyata saurin waiwayawa ba tareda taga kowa ba, dawowa tayi da idanunta taga alamun mace na tafiya kuma yanayinta yayi yanayi da matar da ta taimaka mata dukda bata tunanin mutum ce. Cikin sauri tabi matar saidai kafin tayi nisa ta nemeta ta rasa.
Tana sake gaba ta had'u da wani mutum yana dur'kushe gaban wani 'karamin yaro yana kuka, saidai yanayin kukan ya tabbatar mata ba mutum bane. Cikin tsananin kad'uwa ta 'kara sauri har tana tuntu'be saidai abinda tayi tuntu'be dashi yafi komai d'aga mata hankali.
Wata irin halitta ta gani mai siffar maciji saidai 'kafafunsa tamkar dutse maimakon jela, ga idanunsa tamkar na mutane. Ihu ta sake ta fara yun'kurin addu'a tareda runtse idanunta saidai tana bud'ewa taga babu komai. Babu shiri ta d'iba da gudu dukda nauyin buhun dake hannunta.
Wani 'karamin titi ta nufa wanda babu mutane a cikinsa, ganin titin yasa hankalinta ya kwanta ta jefar da buhun dake hannun ta a gefe ta tsuguna tana maida numfashi, bata san dalilin da ya hanata jefar da wannan kayan ba dukda wahalar da take ciki.
Addu'a ta fara tana fad'in "ya Allah ka ceci rayuwata, Allah ka tsareni daga sharrin duk wani abun sharri, Allah ka kawo min mafita ka yanke min wannan wahalar". Tana addu'ar idanunta na zubda 'kwalla.
A hankali motoci suka fara giftawa ta wannan titin da take tsugune a gefensa, sai a lokacin ta tuna batayi sallar magriba ba, batayi isha ba ga sallar asuba na gabatowa saidai babu alamun ruwa a kusa, haka ta ha'kura ta had'a kanta da gwiwa cikin 'kan'kanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita.
TIMIYA, AGADEZ,
JAMHURIYAR NIJAR
SHEKARU GOMA SHA BAKWAI BAYA...
Timiya 'karamin 'kauye ne a cikin garin agadez dake 'kasar nijar, adadin mazaunan wannan yaki bazasu wuce dubu goma sha uku ba (13,000). Gari ne dake kewaye da manyan duwatsu wanda cikin hikima ta ubangiji ta cikin wannan duwatsun ruwa ke fita wanda suke amfani dashi.
'Kauye ne sosai na buzaye wanda babu komai daga cikin abubuwan zamani, tun daga farkon hanyar timiya har zuwa cikin garin babu kwalta sai duwatsu da rairayi.
Kamar kowacce 'karamar 'kabila mutanen timiya suna zaune ne tamkar 'yan uwan juna domin kusan kowa yasan kowa. Sana'arsu itace kiwo da noma, ta wannan hanyar suke samun abincin da zasu ci.
TAISHU, wanda shine asalin sunan Hauwa sunanta na al'adarsu buzaye. Taishu ta kasance d'iya d'aya tal ga iyayenta tina da agalher. Tina da agalher auren zumunci sukayi kasancewar agalher yana cikin masu arziki na garin timiya. Bayan aurensu tina ta d'auki tsawon shekaru goma ba tareda haihuwa ba wanda ya sanya dangi da 'yan uwa aka fara damuwa har tsaiko ya fara shigowa ciki.
Duk yanda akayi da agalher akan ya 'kara aure yayi funfurus yace bazai 'kara ba duk da arzi'kin da yake dashi, wannan al'amari yaso ya haifarwa sa tina tsana daga 'bangaren dangin agalher. Ana cikin wannan yanayi Allah ya azurta tina da juna biyu, dukda ri'ko da al'adarsu wanda mace bata ta'ba bayyana ciki har sai ya bayyana kansa wannan bai hana tina bayyanar da wannan abin farin ciki da ya sameta ba.
Kafin cikin tina ya girma duk wasu makusantanta sun san da wannan cikin masu farin ciki nayi masu ba'kin ciki nayi. Tina ta sha ba'kar wahala wurin rainon cikinta domin cikin yazo da matsaloli da dama, sosai take zub da jini har sai anyi tunanin cikin ya fita sai kuma ya sake bayyana kansa, haka tina ta sha fama har sau uku tana zubar da jini wanda karo na 'karshe har anyi tunanin an rasa ta. Irin jinin da ta zubar yasa akayi tunanin ta rasa abinda ke cikinta a wannan karon.
Saidai Allah mai yanda yaso wata biyu taji cikinta ya fara motsi, bata fad'ama kowa ba ciki harda agalher ta sanya faifai tana d'aure cikin dashi tana addu'ar Allah ya raya mata abinda zata haifa. Bayan watanni kad'an tina ta fara na'kuda tana zaune ita kad'ai a cikin gidanta, dukda cewar batada nisa da mutane saidai wahalar da take ji ta sanya sam ta kasa ko da motsi domin nemawa kanta mafita.
Kawaici, kunya da dauriya irin na buzaye yasa ta dinga danne ciwon da take ji babu wanda yaji sautinta har ta haifi d'iyarta ita kad'ai abinta. Da kanta ta yankewa yarinyar cibiya wadda ta fara tsanyara kuka tana ma kanta maraba da zuwa wannan duniyar.
Tina bata damu da 'kazantar dake jikin yarinyar ba ta d'auketa ta rungumeta a jikinta tareda sakin murmushi had'e da hawayen murna. Bayan ta sami kanta ta nad'e d'iyarta a zani ta ajiyeta gefe sannan ta gyara jikinta ta gyare d'akinta tsaf bazaka ta'ba cewa anyi haihuwa a cikinsa ba.
'Kofar d'aki ta fito sai kuma tayi turus tana tunanin yanda zatayi ta sanar da haihuwarta, domin abin kunya ne ace mace ta sanar da haihuwarta da kanta. Komawa tayi d'aki tana ta sa'ke-sa'ke har taji sallamar 'yar uwarta ghaishe. Cikin hanzari ta amsa tare da mata iso cikin nutsuwa ghaishe ta shiga d'akin wanda shigarta yayi daidai da kukan jaririya.
A tsorace taja da baya tana tambayar tina cikin harshensu na buzaye "tina kyanwa ce d'akinki ko mutum?"
Kan tina a 'kasa tace "mutum ce".
Dafe 'kirji ghaishe tayi tace "a ina kika samo yaro?"
"Haihuwa nayi". 'Kura mata idanu ghaishe tayi sannan ta dubi d'an dake nad'e cikin zani taga dai tabbas d'a ne sabon haihuwa ta sake duba gefenta taga mahaifa a nad'e cikin zani, kallon tina tayi cikin tuhuma tace "ya akayi haka?"
Tina bata 'boye mata komai ba ta bayyana mata nan dai ghaishe ta ja mata kunne akan abinda tayi sannan tace zata 'boye maganar a matsayin itace ta kar'bi haihuwar.
Bayan magana ta fita aka yita mamaki saidai hakan bai hana agalher farin ciki da shagali mai girma ba na samun wannan albarka da yayi. Anyi suna mai rai da lafiya an sanyawa yarinya suna taishu, saidai tun daga haihuwar TAISHU arzi'kin agalher ya fara lalacewa, ra'kumansa gaba d'aya lokaci guda suka kamu da wani irin ciwo da aka gaza gane kansa d'aya bayan d'aya suka dinga mutuwa ya rage ra'kumi biyu tal gareshi.
A 'bangaren noma kuwa ba iyakar gonar agalher ba har wad'anda ke kewaye dashi saida suka lalace wanda hakan ya fara haifar da zargi a cikin mutanen timiya.
Saidai ibtila'in bai tsaya haka ba domin tunda aka haifi taishu duk yaran da aka haifa a timiya mutuwa suke, wasu a haifesu babu rai wasu suna zuwa basu cika sati suke mutuwa. Hankalin mutanen timiya ya tashi sosai sukayi ittifa'kin lallai 'yar da Tina ta haifa ce tazo da wannan masifar.
A wannan yanayin d'aya daga cikin faccalolin tina ta haifi 'yan biyu maza wanda a ranar suna suka mutu, ta fusata sosai bayan mutuwar ta lafa ta fita can bayan tsaunuka wajen wani boka ta sanar mishi abinda ke faruwa a wannan garin nasu, bayan 'yan surkulle bokan ya sanar mata matu'kar taishu na raye to garin timiya bazai ta'ba zamowa mai albarka ba domin ba 'ya'yansu kawai ba har tumakin su da ra'kuma sai sun 'kare, sannan kuma kashe taishu shine kad'ai zai zamo musu mafita.
Free page.
Ki biya 500 domin karantawa cikin nutsuwa
For your payment
0472624453
Musa maryam Aminu
Gtbank
Sai ki tuntubeni ta wannan number
***