A CIKIN DUHU

03

by @kitty

A CIKIN DUHU

Kitty💕

Wattpad @ Mssmeemah 


3


Hankali a tashe ta dawo batayi 'kasa a gwiwa ba ta fara sanar ma da sauran faccalolinta abinda ta jiyo har tana sanar musu duk wanda bai amince da ita ba ya biyota su koma su jiyo da kunnuwansu.


Tun magana na tsakanin faccalolin Tina har ta fita ta fara zagaye gari, bayan fitar maganar ne kuma awakinsu suka fara mutuwa yawancinsu ta hanyar haihuwa, ga mutuwar 'yaya abin sai gaba yakeyi.


Mutane da dama sun aminta da maganar wannan boka wanda ya sanya sukayi 'ko'karin d'aukar doka a hannunsu ta kashe taishu domin kawo 'karshen bala'in dake faruwa a garin nasu na timiya. A lokacin da agalher yaji labari baiyi wata-wata ba ya sanarwa tina abinda ke faruwa, a lokacin taishu na da shekara 3 da rabi.


Mafita suka zauna nema agalher ya sanar mata su fita daga garin timiya su nemi wani garin su fake har lokacin da 'kura zata lafa. Dare na tsalawa suka fita kan ra'kumi saidai duk hanyar da suka dosa sai suga ta koma ruwa, duk inda suka nufa sai suga wurin ya koma ruwa har ruwan yana neman had'iyesu.


Wasu kalamai tina taji agalher yayi yayi wanda sam irin wannan surkullen ba sabon abu bane garesu buzaye, gefen ruwan yabi yana maganganunsa tare da yarfa hannu har suka sami wata 'karamar hanya suka yanka.


Gari na wayewa aka nemi agalher da tina aka rasa wasu daga cikin mutane suka hau ra'kuma suka bi bayansu, agalher da tina suna kallonsu suka wuce saidai su basa ganinsu kasancewar agalhe ya sanya musu hijabi tsakaninsu.


An jima ana neman agalher da tina an rasa su haka mutanen timiya suka ha'kura suna murnar Allah ya raba su da masifa, saidai fa tanalher wadda take faccalar tina da ta rasa 'yan biyu sam ta kasa ha'kuri domin ta jima tana fatan samun d'a namiji saboda gado kasancewar duk kishiyotinta har ita 'ya'ya mata suke haifa, tunda ta sami ciki take yawon bokaye domin ta samu ta haifi namiji aka sanar mata tabbas yaya maza zata haifa, ga mijinsu na kwance yana jinyar ajali.


Mutuwar yayanta ba 'karamin girgiza tayi ba hakan yasa tafi kowa daurawa tina da agalher laifin mutuwar 'ya'yanta. Taso ace da hannunta ta kashe taishu domin suma suji abinda itama taji, a lokacin da aka tabbatar mata tina da agalher sun gudu batayi 'kasa a gwiwa ba ta koma ta sanar ma bokanta. Cikin 'bacin rai tace "yanda tina da agalher sukayi sanadiyyar rasa 'ya'yayenmu inaso su dinga d'and'anar mutuwar 'ya'ya har 'karshen rayuwarsu. Inaso 'yarsu taishu tayi 'bakin jinin da ba'a ta'ba halittar wata halitta dashi ba, banaso ta haifi 'ya'ya maza ko da zata haifa na sadaukar dasu gareka daga nan har 'karshen rayuwarta".


Dariya bokan yayi yace bu'katarta ta biya kuma baya neman komai daga gareta.


Ta 'bangaren tina da agalher kuwa sunyi tafiya mai nisa taishu ta fara kukan gajiya, wuri suka samu suka tsaya tina ta bata ruwa yayin da agalher ya zagaya neman wurin da zaiyi fitsari. Ihun gaishu ne ya sanyashi dawowa a razane ya sameta ta fad'i a sume yayin da mahaifiyarta ke gefe itama a kwance.


Taishu ya fara girgizawa har saida ta dawo hayyacinta sannan ya koma ga matarsa tina, sai a lokacin ya lura da alamun saran miciji a 'kafarta har fatar jikinta ta sauya kala ta koma shud'iya alamun dafin ya gama zagaye jikinta.


Yanka wurin da yaga alamun ha'korin macijin yayi ya fara zu'ke jinin wajen yana furzarwa saidai tuni rai yayi halinsa. Yayi kuka kamar ransa zai fita kafin ya nemi rami ya ha'ka ya binne matar tasa bayan yayi mata sallah ya d'an shafa mata ruwan da suke tafe dashi.


Tun daga lokacin bai sake tsayawa ba har saida ya isa wani 'kauyen, shima guzuri kawai ya nema ya sake gaba. Tun daga wannan 'kauyen duk inda ya tsaya baya samun taimako domin tsangwama da kyara ake nunawa 'yarsa wadda a duniya babu abinda yakeso sama da ita. Duk inda yaga ana ma 'yarsa kallon banza baya sake zama a garin saidai ya fita.


A wannan yanayi na zagayen 'kauyukan dake kewaye da nijar ra'kuminsa ya mutu, a wannan lokaci Kuma ya had'u da wani d'alibi mazaunin najeriya wanda yazo nijar 'kauyen damagaran karatu. Shi kad'ai ne mutumin da baya kyarar 'yarsa har ya kasance sha'kuwa ta shiga tsakaninsu nan yake sanar mishi an masa aure ne aka aikoshi ya haddace al'kur'ani a matsayin sadakin matar tasa, a wannan lokacin izu biyu ya rage ya kammala tilawarsa ta uku wadda ita zata tabbatar ya haddace daga nan ya koma najeriya ya tare da matarsa.


Agalher yayi bakin cikin jin wannan magana domin sha'kuwarsa, anan mutumin mai suna ibrahim yake sanar mishi ya bishi najeriya ya zauna tunda zaman nijar ya gagareshi, babu wani musu agalher ya amince har ya koma karatu a makarantar domin rage lokaci.


Bayan Ibrahim ya kammala haddar al'kur'ani ya d'auki agalher da taishu ya taho dasu najeriya cikin wani 'kauye dake kano ana kiransa tamaru 'kar'kashin 'karamar hukumar kibiya. A gidansu ya ajiye algaher kasancewar gida ne na almajirai sannan mahaifinsa malam d'ahiru ya karbi algaher da 'yarsa hannu bibbiyu aka ri'kesu tamkar sauran almajirai da mutanen gidan.


Shima Ibrahim d'akinsa na d'aya daga cikin d'akunan gidan inda aka aje masa matarsa saratu, kasancewarta amarya kuma yarinya yasa gaishu tafi sakewa da ita saidai saratu sam ta rasa dalilin rashin had'uwar jinin yarinyar da nata tana kulawa da ita ne kawai darajar Ibrahim. 


Gaishu bata da wata makusa kasancewarta cikakkiyar buzuwa kyakkyawa ce sosai ga gashinta dake cukurkud'e wanda ya kai tsakiyar bayanta, tana da manyan idanu da gashin ido ba'ki wulik wanda yake sanyawa matu'kar ka had'a idanu da ita sai ka kauda naka saboda girma da hasken idanun nata. Wasu daga cikin matan gidan har rantsuwa suke aljana ce kasancewar malam d'ahiru yana samun ba'kin aljanu amma matan basa sani har sai sun gama zamansu sun tafi, hakan yasa suka d'auki gaishu da mahaifnta a matsayin ba'kin aljanu suke taka tsantsan dasu har su gama zamansu su tafi.


Daga yara har manyan gidan babu wanda yake ra'bar gaishu dukda yarintarta da kyawunta, daga nesa zata matu'kar baka sha'awa tamke ka saceta amma kana kusantarta zaka ji tsanarta ta wanzu a zuciyarka. Wannan yasa gaishu take ware kanta domin sam yara basu son wasa da ita tana shiga cikinsu suke watsewa ga kuma rashin hausa saidai tayita binsu da idanu suna zaginta.


Sunanta gaishu sai ya zamo abin tsokana wasu na kiranta gassha, wasu suce gesha, wasu suce getso hakanan sunaye marasa dad'i, wannan yasa ibrahim ya sauya mata suna ta koma Hauwa'u ya kuma nemi mahaifinsa ya gargadi mutan gidan da kiranta da sunayen banza.


A haka Hauwa'u wato gaishu ta taso a takure babu wanda take zama dashi ta sake sai mahaifinta. Lokacin da ta kai shekaru 7 malam d'ahiru ya rasu Ibrahim ya kar'bi harkar malunta, a lokacin ta samu ta shiga makarantar allo ta malam ibrahim saidai tsangwama da kyara yasa ta fita daga makarantar saidai ta la'be a zaure taji karatun ko kuma idan dare yayi taje malam ibrahim ya 'kara mata ita kad'ai.


Mahaifin ta bai boye mata komai ba dangane da rayuwarta ya bata labarin duk abinda ya faru ya kuma bata kwatancen garinsu ko da watarana zata so zuwa ko su tafi tare, saidai Allah bai nufa ba domin tana shekara goma Allah ya d'auki ran algaher. A lokacij Hauwa'u ta gama fahimtar tsanar da mutane suke mata gashi gatan da ya rage mata d'aya ya rasu, tayi kukan maraici kamar ranta zai fita 'karshe ta ha'kura ta dangana ga Allah.


Hauwa'u (gaishu) ta cigaba da rayuwa cikin 'kunci da takura, d'akin da aka baiwa mahaifinta shi ya koma d'akinta batada aiki sai zaman d'aki, lokuta da dama sai ayi abinci a rabeshi a cinye a manta da ita tana d'aki, saidai dukda haka tana ganin sau'ki daga saratu sa'banin sauran matan gidan.


Watanni kad'an da mutuwar algaher ibrahim ya sake aure ya auro hadiza, a wannan lokacin Hauwa'u ta fuskanci tsanar da tunda ta taso gidan gwani (sunan da ake kiran gidan ibrahim) bata ta'ba ganinta ba, domin babu abinda ya tsonewa hadiza idanu kamar kyawun Hauwa'u, wannan yasa tun batayi wata uku a gidan Ibrahim ba ta fara azabtar da Hauwa'u duk domin kyawunta ya dusashe.


Duk yaran gidan saida ta san yanda tayi ta hanasu aiki komai ya koma wuyan Hauwa'u, haka zata tashi asubar fari ta had'a wutar abinci sannan ana gama ci ta had'a kwanukanta wanke, itace d'ebo ruwa, surfe, daka, wanki, babu abinda Hauwa'u batayi saidai Hauwa'u bata ta'ba nuna gazawarta ba sannan babu abinda ya sauya a kyawun halittar da Allah yayi mata. 


A wannan yanayin hadiza ta fara fiddo izayarta fili ta hanyar duka, wannan yasa Ibrahim ya shiga maganar ya hana hadiza dukan Hauwa'u saidai babu abinda ya sauya.


Duk dukan da hadiza zata ma Hauwa'u bata ta'ba kuka a gabanta sai taje d'aki, Wannan ya 'kara 'kular da hadiza watarana ta bita d'akin bayan ta gama dukanta.


Hadiza na zaune ta cire mayafin kanta da kullum yake kanta domin suturta gashinta tana goge gumi da hawaye taji alamun mutum, a tsorace ta d'aga kanta tareda ja baya tana nemawa kanta mafita, saidai kallon da hadiza ta mata da gashinta a bud'e sai taji tamkar ta murd'e wuyanta ta mutu.


Gashin ya sauka gadon bayanta da kafad'arta da kuma sashen fuskarta, hakan ya sake bayyanar da asalin kyawunta dukda rashin gyaran da gashin ke samu, a fusace hadiza ta fita ta d'auko almakashi ta danne Hauwa'u ta yanke mata gashin ta fita dashi a hannunta ta zubar.


Babu wanda Hauwa'u ta furtawa abinda ya faru ta cigaba da juriya har ta kai shekaru goma sha hud'u, a lokacin hadiza tana da 'ya'ya biyu ta rage muguntar da take mata sosai ganin babu wata riba da ta samu, a lokacin kuma Hauwa'u ta fara cika mace saidai babu wani namiji da ke kallonta da sha'awar aure.


A lokacin da ta shiga shekaru goma

Sha biyar ne 'kanin ibrahim wanda ake kira mahmudu ya fito yace yana son Hauwa'u, babu wanda ya amince har shi ibrahim yace saidai ya sake lale amma ba dai Hauwa'u ba domin shi kansa baya jin yarinyar a ransa uwa uba babu wanda ya san danginta. Mahmudu dai ya kafe kai da fata yace sai ya auri Hauwa'u ko ya shiga duniyar harda kwashe kayansa yayi yaji daga gidansu, ganin yana neman 'bata sunan gidan malamai yasa suka amince ma aurensa saidai har mahaifiyarsa ta zare hannu daga kanshi.


Ta 'bangaren mahmudu kuwa tsananin tausayi yasa ya auri Hauwa'u domin duk abinda ke faruwa da ita kan idonsa yake faruwa, babu soyayyarta a zuciyarsa saidai yana so ya fiddata daga wannan 'kangi.


Bayan auren mahmudu da Hauwa'u ba'a bashi d'aki ba kamar yanda aka saba hasali ma ko filin da zai tada gini hanashi akayi, ga amarya babu kayan d'aki balle na 'kyale-kyale, saratu ce ta bugi 'kirji ta bata kyautar kwalla guda biyu da zannuwa biyu darajar zaman lafiya da sukayi, haka mahmudu da Hauwa'u suka tattara 'yan komatsansu suka bar 'kauyen suka nufi 'kauyen dake ma'kwabtaka dasu.


Zaman lafiya ke wanzuwa tsakanin mahmudu da Hauwa'u tana masa biyayya daidai gwargwado shima kuma yana nuna mata kulawa, ya kan koma tamaru yayi noma sannan ya kawo musu amfanin noman suci qani su sayar suyi amfani da kud'ad'en har lokacin da Allah ya azurta Hauwa'u da juna biyu. Saidai tunda Hauwa'u ta shiga garin tamkar ta goyo ba'kin jininta daga tamaru domin a nan ma sabuwar tsangwama da tsana ne suka fara kewayeta dukda akwai sau'ki kasancewar tana gidan mijinta. Hakan yasa bata zuwa ko ina.


Wata tara Hauwa'u ta haifi d'anta namiji aka sanya mishi suna d'ahiru ana kiransa malam saboda suna da yaci, d'ahiru yana shekara d'aya ya fad'a rijiya yana rarrafe ya rasu, bayansa ta sake samun ciki ta haifi namiji saidai baizo da rai ba, shekara guda ta sake samun ciki ta haifi wani yaron aka maida d'ahiru saidai kafin suna ya rasu.


A wannan lokacin rayuwa ta fara yiwa mahmudu wahala ga tsangwama ta farai musu yawa shi da matarsa, ba'kin jinin Hauwa'u saida ya shafeshi domin ko aikin gona hanashi ake, ko kasuwa ya shiga neman 'kwadago sai kaga ana tofe dutse ana jefawa a wurin da ya taka kar ya shafa musu talauci. Mahmudu bai amince da batun mutane na cewar farar 'kafa ya aura ba yayi imanin duk 'kaddara mai kyau da marar kyau daga Allah take.


Hauwa'u bata jima ba ta sake samun ciki, ga wahalar rayuwa haka ta raini cikinta har ya girma ta haifi 'yarta mace aka sanya mata KARIMATU, yarinya sak uwarta tamkar kaki tayi ta tofo ta. Babu abinda karimatu ta bari na mahaifiyarta daga kyau har ha'kuri domin tun jarirantakarta tana da ha'kuri bata wani kuka sosai. A kullum Hauwa'u tana zuba idanu taga ko karimatu zata bi 'yan uwanta taga har tayi shekaru biyu a raye sai ma kara girma da take tana kyau. A wannan lokacin haihuwa ta tsayawa Hauwa'u sai kuma bud'in Allah yazo musu har mahmudu ya sake mallakar gonar kansa yana kuma ci da iyalinsa.


Saida karime tayi shekaru biyar sannan Hauwa'u ta haifi isyaku, wanda yana watanni shida ya rasu, daga shi ta haifi 'yan biyu har karo biyu na farko rud'en tuwo ya zubo musu suka mutu na biyun kuma aka samesu a d'aki sun rasu ba tareda sanin dalili ba. 


Tuni mutanen gari da 'yan uwan mahmudu sukayi ittifa'kin Hauwa'u ke cinye 'ya'yanta maza domin dama sunsan ko aljana ko mayya ce ita, idan ba haka ba meyasa macen ta rayu mazan suke mutuwa? Da alamu Hauwa'u da karimatu su ke kashe 'ya'yan suna shanye jininsu domin zubinsu bayada banbanci da na aljanu.


Karime tun daga 'kuruciyarya ta lura mutanen garin ba 'kaunarta suke ba wanda yasa bata da wurin hira sai wurin mahaifiyar ta. Sun matu'kar shak da juna har lokacin da Hauwa'u ta samu cikin Habu, cikin yana wata uku mahmudu ya fara ciwo.


Cutar kwana biyu kacal yayi zazza'bi a tsaitsaye a rana ta uku ya rasu. Hauwa'u tayi kukan da tun rasuwar mahaifinta bata sake irinsa ba, haka itama karime tayi kuka tamkar ransu zai fita. Dangin mahmudu kuwa Hauwa'u suka d'aurawa laifin mutuwarsa sukace ita ta kasheshi saboda nata mazan sun 'kare, suka kwashe duk wani abu da ya mallaka har abincin da Hauwa'u da karime zasu ci suka tafi dasu.


Hauwa'u ita ta dinga fita neman abinci da kanta tana roro ko ta soya gyad'a ta kai kasuwar cikin gari ta sayar su sami kalaci, a haka har ta haifi habu. Habu shi ya zamo silar farin cikin Hauwa'u da karime domin sa'banin su da suke shafe da ba'kin fenti Allah ya yiwa habu farin jini, saidai rabon shima bazai rayu ba yana shekaru bakwai gini ya fad'a mishi sanadiyyar ruwan sama ya rasu.


Wannan shine ta'kaitaccen tarihin mahaifiyar karime...


Free page


Littafina na kud'i ne 500 kacal🥰🥰ku nuna min solidarity ni kuma zanyi ‘ko’kari na baku abinda zu’katanku suke so😁😁


Account details

0472624453

Musa maryam Aminu

Gtbank


Ku tuntu'beni ta wannan number

***. Nagode