04
by @kitty
***
A CIKIN DUHU
Kitty💕
Wattpad @ Mssmeemah
04
Hayaniya ce ta tashi karime tayi firgigit tana waige-waige, sai a lokacin ta lura a da motocin da suka fara fitowa 'karamar tashar dake wurin.
Lokaci guda kanta ya juye ta rasa motar da zata hau ta koma can gefe ta ra'be jikinta a sanyaye. Tana zaune taga wasu 'yammata sun iso wurin sun kai su goma kowacce da 'kullin kayanta a hannu suna ta hira tsakaninsu, kasa kunne tayi domin taji inda suka nufa.
"Allah yasa mu samu aikinnan da wuri naji ance matar fa duk kwananka da abincinka sai ka biya idan baka biya kuma aka rasa wadda zata d'aukeka aiki korarka takeyi". D'aya daga cikin 'yammatan ta fad'a damuwa 'karara a fuskarta.
Wata daga can gefe ce ta cafe maganar tace "ai shiyasa innata ta bani laya tace indai layar na d'aure jikina zan samu aiki da wuri na dinga turo mata kud'in. Kuma sai kuyi addu'a da dabaru kuma ance matan birni basa son masu rawar kai da masu kyau".
Suna wannan hirar tasu wata mota ta 'karaso dukkansu suka nufi motar suna tururuwar shiga. Ba tareda karime tayi dogon nazari ba ta d'auki buhunta cikin sauri tabi bayansu ta samu ta zauna a maleji. Tunda ta shiga motar 'yammatan ke binta da kallo wanda ya sanya gaba d'aya taji ta tsargu.
Wata daga cikinsu ce ta kasa jurewa tace "kema neman aikin zaki birni?"
Gyad'a kai karime tayi alamun eh gaba d'aya suke bushe da dariya wata tace "wallahi matan birni ba mai d'aukanki shekararki nawa?"
A hankali karime ta furta "sha bakwai". Jikinta ya gama yin sanyi, tana yawan jin yammatan garinsu sun tafi aikatau amma bata ta'ba tunanin zata tsinci kanta a hanyar zuwa aikatau ba, ta yaya akeyi? Me ake samu? Ina ake zuwa? Babu abinda ta sani ta san dai birni ake zuwa.
"Ta'bdi, ai kin musu girma gaki fara, wallahi ko kin samu aikin ma in fad'a miki duka zaki dinga sha gara ma ki sauka tun kafin ayi nisa ki kkma gida ki cigaba da tallanki ya fiye miki".
Karime bata sake cewa komai ba dukda tana so ta tambayi yanda zaman gidan aikatau d'in yake, tafiya sukayi mai nisa wadda a lokacin karime ta fara jin yunwa, buhunta ta bud'e ta d'auki mangwaron da ta yiwa baaba tsaraba ta fara sha saidai sam ya'ki mata maganin yunwa.
A hanya taga sauran 'yammatan na sayen doya da 'kwai da su madara me sanyi da gurasa da biredi saidai kud'in jikinta 700 ne kawai kuma yanda taji kud'in motar tasu 400 ne, tana tsoron ta 'karar da kud'inta ta shiga matsala.
Kauda kanta tayi daga garesu ta cigaba da shan mangwaronta tana cin d'anyar gyad'ar da ta saro har suka isa tashar da za'a saukesu wanda tunda karime tazo duniya bata ta'ba takowa ba. Iyakar karime babbar kasuwar 'kauyensu da kuma 'kauyukan dake ma'kwabtaka dasu bata ta'ba sha'awar zuwa birni ba sai gashi yau dole ta sanyata tazo.
Fitowa sukayi daga tashar bayan sun biya kud'in motarsu sannan suka tsaya. D'aya daga cikinsu ce ta zaro wata 'karamar waya daga 'kugunta wadda ke d'aure da kyauraye ta danna tayi kira tace gasu nan a tasha, sunyi jira na kusan minti talatin sannan wata dattijuwar mata ta iso garesu.
Ganin yanda ake fad'uwa ana gaida matar yasa karime ta tabbatar itace uwar d'akinsu ta neman aiki, babbar mace ce da zata kai shekaru arba'in tana sanye da hijabi da 'karamar jaka a hannunta, tunda ta iso idanunta suka sauka a kan karime ta kasa kauda idanunta daga gareta saidai bata ce komai ba.
Adaidaita sahu ta tsayar tace mishi "gasunan ka kaisu gwammaja..." tayi mishi kwatancen daidai inda zai ajiyesu nan fa suka fara tururuwar hawa, gaba d'ayansu su goma suka shige wasu a kujera wasu a can baya wasu a gefe. Suna hawa wadda ta kira wayar ta sanar musu kowa zai bada naira hamsin kud'in adaidaita sahu yana kaisu suka biyashi suka sake cirko-cirko a hanya.
Tambayoyi ne fal a ran karime ta dubi yarinyar da ke gefenta wadda bazata gaza shekaru 12 a duniya ba tace "ina zamuje yanzu?"
"Ita wannan matar itace zata kaimu gidan uwar aikin tamu wadda zamu zauna a gidanta har lokacin da zamu samu gidan aiki".
"Ance zaman biya ake ko?"
Gyad'a kai yarinyar tayi tace "eh biya akeyi ance idan baki biya ba korarki take ki koma garinku".
Wani yawun wahala karime ta Had'iya tace "nawa ake biya?"
"Kamar kullum d'ari biyu ne kud'in abinci idan kinason sabulun wanka da wasu abubuwan tana saidawa sai ki saya, kud'in kwana kuma kullum naira 50 ko d'ari na manta".
'Kwalla ce ta ciko idanun karime domin 250 ne kacal a jikinta, ta bud'e baki zata sake tambayar yarinyar Wannan matar ta iso tayi gaba suna binta a baya.
Wani gida suka nufa madaidaici, a cikin gidan akwai yalwataccen tsakar gida da aka malale da siminti sai d'akuna guda uku da rijiya da kitchen wanda yayi ba'ki 'kirin na haya'ki.
Matar da suka tarar tana zaune kan tabarma ana mata kitso yayin da 'yammata ke ta kaiwa suna kawowa a cikin gidan, wasu na wanki wasu na shara wasu na shirin had'a wutar girki.
Zubewa sukayi suna mi'ka gaisuwa matar ta amsa a ciki sannan ta kalli wadda ta kawosu tace "Atine na fa fad'a miki banason ki kawo min yaran da zasu zamarmin matsala, kin tabbatar da wad'annan kinsan iyayensu?"
Murmushi Atine tayi ta cire hijabinta tare da zama tace "karki damu hajiya sa'a insha Allahu babu matsala duk da yardar iyayensu jiya duk saida naje na gana da iyayen nasu na kuma kar'bi lambobinsu na waya".
Gyara zamanta tayi bayan an 'kare kitson ta fara binsu da kallo sannan tace "kin sanar musu tsarina da dokoki na ko?"
"Sun san komai hajiya bakida matsala waccan ce dai ban ganeta ba ina tunanin itace naje aka ce ta tafi talla". Ta 'kare maganar tana nuna karime. Irin kallon da hajiya sa'a ta yiwa karime saida taji gabanta ya fad'i tace da karime "iyayenki sun san kin taho?"
Cikin sauri karime ta gyad'a kai alamun eh tareda sunkuyar da kanta, kallonta sukayi dukkansu Atine tace "ai hajiya banda wannan a 'kauye ta taso ai ba 'karamin jari zata zama ba, ki dubeta fa tamkar ba ruwan karkara take sha ba".
Hajiya sa'a bata tanka mata ba tace duk su gabatar da kansu, anan karime ta fahimci duk cikinsu itace babba domin daga shekara 14 zuwa 'kasa yaran suke, a lokacin da ta fad'i shekarunta saida hajiya sa'a ta kalli Atine a fusace tace "na fad'a miki karki sake kawo min yarinyar da ta wuce shekara 14 meyasa zaki kawo min 'yar sha bakwai? Wace mahaukaciyar ce zata d'auki wannan a 'yar aiki ga kyau ga girma dubeta ki dubi 'kirjinta yanda yake a cike, ko ni da inada miji wallahi bazan zauna da ita ba, saboda haka ki san yanda zakiyi da ita ki maidata gida bazan d'auketa ba gaskiya domin fad'uwa Zanyi".
Kallonta Atine tayi tace "to kinji, kuma lokacin da naje 'kauyenku saida na jaddada muku 'kananun yara nakeso amma kika biyosu, sai ki tashi ki koma garinku".
Hankalin karime ya tashi domin batada inda zata nufa, babu wanda ta sani kuma babu yanda za'ayi ta koma garinsu su kasheta, magiya ta fara tana neman hajiya sa'a ta barta ta kwana washegari sai ta koma, ba tareda damuwa ba hajiya sa'a ta amince da sharad'in zata biya kud'in abinci da na kwana kamar sauran. Babu musu karime ta amince tana godiya dukkansu suna mata kallon mamaki suna tunanin 'kwallafa rai a kan aikin ne ya sanya ta gigice haka.
Karanta musu dokoki hajiya sa'a tayi sannan ta basu d'aki guda d'aya wanda dukkansu a cikin wannan d'akin zasu zauna. Dokokin nata gasu kamar haka:
A kullum zaka bada kud'in abincin safe, rana da dare naira 500 saidai kinada damar zama da yunwa babu mai tilasta miki ki biya.
Ayyukan gida shara, wanke-wanke, wankin band'aki za'a raba kowa da ranarsa har sai lokacin samun aikinki yayi.
Banda satar kayan juna duk wadda aka kama da zata za'a hukuntata kafin a maidata garinsu.
Bakida damar le'kawa ko 'kofar gida ba tareda iznin hajiya ba, idan aka sameki a waje hukuncinki shine ki koma 'kauyenku.
Kud'in aiki naira 3000 ne zuwa sama, albashin farko za'a baiwa hajiya rabi a kai rabin ga iyayenki, albashi na biyu za'a raba uku hajiya ta d'auki kaso d'aya, a baki d'aya a baiwa iyayenki d'aya, haka za'a cigaba da kasafi har tsawon wata shida sannan a ciki za'a fitarwa da Atine nata kason. Idan aka kamaki kina 'boye kud'in aikinki za'a d'auki tsattsauran hukunci a kanki.
Idan aka kamaki da huld'a da miji ko ya'yan matar da ta d'aukeki hajiya zata tsame hannunta daga kanki suyi duk hukuncin da suka ga dama a kanki.
Daga lokacin da kika cika wata shida kina aiki zaki rabu da hajiya har abada zata dena Kar'bar kud'inki da bin sahunki a kan aiki.
Duk wanda yake ganin doka ta mishi tsauri zai iya fad'a tun kafin ayi nisa.
Babu wanda ya tanka domin duk sun san dokar hajiya sa'a kafin zuwansu karime ce kawai dokokin suka zo mata a sabbi saidai babu wani amfani da zasu mata tunda ba zama zatayi ba.
D'akin da aka basu babu komai cikinsa sai tabarmi manya guda biyu, a kusurwar d'akin kowacce ta ma kayanta wuri yayin da suke d'an ta'ba tad'i kasancewar babu wani aiki da zasuyi kowacce tana fatan kar ta cika sati gidan hajiya. Karime kuwa tana ra'be jikin bango rungume da buhunta ta rasa me ke mata dad'i a duniya, sai yanzu take dana sanin tahowa da tayi ta gwammace ta zauna a kasheta ta hucewa wannan 'kuncin rayuwar da take ciki, Baaba ita kad'ai ta rage mata a duniya gashi itama an raba ta da ita.
Had'e kanta tayi da gwiwa tana shesshe'kar kuka a hankali wanda ya janyo hankalin wannan 'yammatan saidai babu wadda tayi yun'kurin tambayarta meke faruwa ganin yanda hajiya ta koreta dalilin shekarunta. Saida taci kukanta mai isarta sannan ta tuna tulin sallolin dake kanta tun sallar magriba ta jiya gashi la'asar ta kunno kai.
Tashi tayi ta janyo ruwa a rijiya domin alwala ta lura duk kayan ajiyar ruwan hajiya babu komai a ciki, bata yi alwala ba saida tabi duk robobin ajiyar hajiya sa'a na ruwa ta cikasu harda tukwane. Kallonta hajiya tayi cike da mamaki tana tunanin halayya na karime.
Tun shigarsu ta lura karime ta banbanta da sauran yaran ta fuskoki da dama, kallo d'aya zaka mata ka fahimci ba bahaushiya bace domin babu abinda ta d'auko a kamannin mahaifinta. Suturar jikinta ta bayyana daga karkara take saidai fuskarta da tsarin dirin da Allah yayi mata bazaka ta'ba cewa tuwon 'kauye taci ba.
Karime batada 'kiba sam siririya ce ta gaske, daga baya idan ka kalleta tamkar sanda babu wani alamun 'kira a jikinta saidai 'kirjinta a cike yake dukda shekarunta basuyi wani nisa ba. Tana alwala idanun hajiya sa'a na kanta yanda take karantar kowane yaro da aka kawo mata, a lokacin da karime ta d'an zame hijabin kanta domin shafar gashin saida hajiya sa'a ta furta masha Allah ba tareda ta lura da hakan ba saboda yanda gashin yake ba'ki wulik, dukda bata ga wutsiyar gashin ba tana da tabbacin akwai yalwar gashi a kan yarinyar.
Mamakin 'kazantar kayan jikinta hajiya sa'a tayi ganin yanda take da tsantseni, ko da ta gama alwalar saida ta sanya tsintsiya ta share bakin rariyar tas sannan ta nufi d'akin. 'Dabi'un yarinyar sun d'aure ma hajiya kai domin 'karara fuskarta ta nuna damuwa kuma alamu sun nuna ba son ranta ne ya kawota gidan ba wanda shine ma dalilin da yasa hajiya sa'a tayi 'ko'karin korarta, saidai tayi mamaki ganin yanda karime ta rude tana neman a bata dama ta kwan anan.
Ko dai kishiyar uwa ce ta takura mata? Ko kuma sharrin namiji ne ya fad'a mata? Ko dai aure aka mata ta gudo? Ko kuma shirin auren ake bataso ta gudu? Sa'ke-sa'ke hajiya sa'a ke yi a ranta har akayi sallar la'asar ta kira 'yammata su fito su fara shirin d'aura abinci.
Tunda aka fara girkin karime ke d'aki tana tunanin ta inda zata fara ga azabar yunwa da takeji ga kuma
Kud'in kwana da zata biya wanda shi kad'ai ya rage mata. Bud'e buhunta tayi ta zaro takalmi da hijabin da ta sayowa baaba ta rungumesu a 'kirjinta tana kuka tana fad'in "Allah ya ji'kanki babata, Allah ya saka mana abinda sukayi mana. Allah ya bi mana ha'kkin mu, Allah ya fitar min da mafita ko ta dalilin addu'ar da kike min ne ba domin halina ba".
Hajiya sa'a na gefe tana sauraron maganganun karime lokaci guda tausayinta ya shiga ranta, ta kan had'u da yaran kirki sosai wanda rabuwarsu har bata mata dad'i, wasu har yanzu suna zumunci wasu sunyi rabuwar mutunci, wasu ta ri'kesu 'ya'ya wasu 'kanne har akwai wad'anda tayi silar aurensu, saidai wannan ne karo na farko da ta had'u da yarinyar da tausayinta ya shiga ranta take jin zata iya komai domin taimaka mata.
Tana ji karime ta gama koke-kokenta sannan ta ciro d'anyar gyad'ar da ta sayo taci ta maida sauran ta 'kulle ta fito tsakar gida ta zauna. Tana zaune hajiya ta kammala girki da taimakon 'yammatan da suka samu a gidan sannan aka fara d'aukan farantai ana zubawa kowacce ta d'auka ta bada kud'inta.
Wani 'kara cikin karime yayi na alamun yunwa ga yawunta da yayi bala'in tsinkewa domin rabonta da abinci cikakke kwana biyu kenan tun kunun da tasha kafin ta tafi talla ranar da habu zai rasu bata sake saka komai a cikinta na abinci ba sai wannan mangwaro da gyad'a.
A kan tabarma 'yammatan suka jere kowacce na cin abincinta suna hira, kallon karime hajiya tayi tace "ke baza kici abincin ba?"
Murmushi karime tayi na ya'ke tace "na 'koshi hajiya".
Tana rufe baki wata cikin 'yammatan tace "babu wani baki son dai fidda kud'i ne".
Karime bata tanka mata ba ta tashi ta fara neman aikin da zatayi domin rage lokaci saidai babu wani aiki haka ta zauna ta takure cikinta na murd'awa saboda yunwa.
Magriba nayi 'yammatan suka biya kud'in kwanan da zasuyi itama karime ta kunce zaninta ta ciro 250 da suka rage mata ta bayar da 200 hajiya ta bata canji, kallon kud'in tayi taga zai isheta ta sake kwana saidai fa bata jin zata iya kwana guda ba tareda abinci ba gyad'a d'anya bazata ta'ba mata maganin yunwa ba kuma babu alamun hajiya sa'a zata barta ta sake kwana a gidanta.
Dare na tsalawa tsoro ya fara ziyartarta na abubuwan da ta gani daren jiya a jejin 'kauyensu, ita kad'ai ta dinga firgita tana waige-waige ga azabar yunwa haka ta kwana bata runtsa ba. Kiran asubar fari tayi zumbur ta tashi ta d'auro alwala tana janyo addu'o'in da ta iya domin bata samu isasshen ilmi ba dalilin tsangwamar da ake mata a 'kauyensu, iyayenta kuma babu wanda yayi yun'kurin koyar da ita ba tareda ta san dalilin hakan ba dukda itama baaba ba wani cikakken ilmi ta samu ba.
Free page
Littafina na kud'i ne 500 kacal🥰🥰ku nuna min solidarity ni kuma zanyi ‘ko’kari na baku abinda zu’katanku suke so😁😁
Account details
0472624453
Musa maryam Aminu
Gtbank
Ku tuntu'beni ta wannan number WhatsApp
***. Love you guys ❤️❤️❤️