A CIKIN DUHU

05

by @kitty

A CIKIN DUHU 

Kitty💕

Wattpad@ Mssmeemah 


GAMJI WRITERS ASSOCIATION


05

      Ana sallar asuba aka fara shirin abin kari, 'kosai da shayi da guntun biredi hajiya sa'a ta had'a musu wanda basa 'kyashi haka suka fidda kud'ad'ensu suka biya, wannan dalilin yasa yammata ke tururuwar zuwa gidan hajiya sa'a zaman neman aiki domin akwai cima mai kyau, kudinka zai saya maka abincin da a garinku ba ka cin irinsa.


Karime na ganin abincin ta Had'iye kwad'ayinta da yunwarta ta sake ra'bewa a gefe tana tunanin inda zata nufa idan gari ya gama wayewa hajiya ta sake korarta. Bayan an gama rabon abinci hajiya ta kira karime gefe tace mata "meyasa bakya cin abinci?"


"Banida kud'i ne". Karime ta furta a tsorace tana kallon Hajiya.


"Ba'a sanar miki tsarin gidannan bane kafin ki taho?"


Ganin 'boye-'boye bazai haifa mata d'a mai ido ba yasa ta fito ta fad'a ma hajiya gaskiyar abinda ke faruwa da ita sannan ta fiddo kud'in da ya rage mata ta nunawa hajiya tace "dan Allah hajiya ki barni na sake kwana wannan kud'in su suka rage min idan yaso gobe sai na fita na tafi na nemi inda zan nufa".


"Ina zakije idan kin tafi?"


"Ban sani ba hajiya amma zan nema idan kika barni na sake kwana".


Cike da tausayawa hajiya ta kalleta tace "jeki kar'bi abinci a kitchen".


Girgiza kai karime tayi tace "iyakar abinda suka rage min kenan kud'in kwana saidai idan zaki kar'bi gyad'a a matsayin kud'in abincin".


Murmushi Hajiya sa'a tayi tace "karki damu jeki Kar'ba". Kiran d'aya daga cikin masu tayata aiki tayi tace a zuba ma karime abinci kud'inta na hannunta. Godiya karime ta fara harda 'kwalla hajiya tace ta bari kar sauran yaran gidan su fahimta suce anyi son kai.


Cikin 'kan'kanin lokaci karime ta cinye 'kosai da biredin da aka kawo mata ta d'aga kofin shayin ko zafinsa bata ji ba ta shanye tare da hamdala, jikinta har rawa yake saboda azabar yunwar da tasha saidai bata d'auki lokaci da cin wannan 'kosai ba ta fara ciwon ciki mai tsanani.


Hankalin hajiya ya tashi ganin yanda karime ke cije baki tana kama cikinta ga amai da take yun'kurin yi, gaba d'aya nadama ta kama hajiya na bata abinci da tayi. Flagyl hajiya sa'a ta bata tace ta sha saidai tamkar an 'kara ma karime ciwon, daga baya kasa jurewa tayi ta kwanta a tabarmar tsakar gidan tana juyi tana kiran sunan Allah sauran 'yammatan na zagaye da ita jiki a sanyaye.


Ganin ciwo ya'ki 'karewa yasa hajiya ta tambayeta daga ina ne ciwon, cikinta ta nuna sannan ta nuna mararta wanda yasa hajiya ta sauke ajiyar zuciya tace "watanki yayi ne?"


Da 'kyar Karime ta furta "ni...nima ban...sani...ba amma kamar...yayi".


'Ya'yan hulba hajiya sa'a ta sanya aka tafasa ma karime ta zuba mata man habba a ciki ta bata ta sha, bata jima da sha ba ciwon ya lafa ta tashi ta shiga harkokinta bayan ta baiwa hajiya ha'kurin abinda ya faru. 'Dankwalin kanta ta cire ta yayyanka tayi 'kunzugu dashi ta shiga aikin gida. Kafin wani lokaci ta wanke duk kwanukan da aka 'bata ta fara shirin shara saida hajiya tace ta zauna ta huta tunda batada lafiya tukun ta zauna.


Kamar wasa karime ta samu shiga jikin hajiya sa'a sosai da sosai har abin yana bata mamaki yanda ta baro zallar tsangwama ta samu soyayya a 'kan'kanin lokaci. Har kyautar zani hajiya sa'a ta bata wanda shi take d'aurawa ta cire kayan jikinta ta wanke duk lokacin da sukayi datti.


Saidai 'sha'kuwar karime da Hajiya bai yiwa sauran 'yammatan gidan dad'i ba ganin yanda kowa ke 'ko'karin ya kyautatawa hajiya amma sam bata gani, idanunta karime kawai suke kallo da yabawa hakan yasa suka ware karime a cikinsu. Basu da aiki sai yada mata magana a lokacin da suka zo bacci saidai sam maganganunsu basu damunta domin taji wanda suka fisu muni ta kuma shanye.


Saida sukayi kwana hud'u sannan aka fara samun masu zuwa neman 'yan aiki. Wadda ta fara zuwa 'karamar mace ce da ciki a jikinta. nan ta yiwa Hajiya bayanin tana amarya ce ita tana neman 'yar tayin aiki ne mai shekaru 11 ko 12 wadda zata iya raino da ayyukan gida kuma bata son 'kazama, ta dai lissafo irin yarinyar da takeso hajiya ta kira shida daga cikin 'yammatan tace su jere.


'Kare musu kallo amaryar tayi da 'kyar ta za'bi d'aya ita a fad'inta sunui kalar 'kazanta. Lalla'bata hajiya sa'a tayi ta d'auki yarinya akayi sharad'ai suka tafi.


Da kad'an-kad'an 'yammatan aka fara kwashesu saidai babu ma wadda ke hangen karime balle ya taya, yau da gobe sai Allah dama ribar da Hajiya sa'a ke samu har take baiwa karime kyautar abinci daga kud'ad'en da 'yammatan ke biya ne na kwana da abinci, tunda suka fara watsewa karime ta fara fuskantar sauyi daga hajiya sa'a, hakan yasa take danne yunwarta lokuta da dama tana kallo za'a raba abinci masu kud'i su saya saidai taci gyad'a ko kuma ta danne har lokacin da hajiya zata mata tayi da kanta.


Satinsu biyu a gwammaja aka kwashe duka 'yammatan ya rage saura karime kawai. Dukda basa harka da ita amma tafiyarsu sai karime ta kasance cikin kewa gashi gaba d'aya hajiya ta dena kulawa da ita, idan ta tashi da safe zatayi abin kari ita kad'ai taci ta fice ba zata dawo ba sai yamma, idan ta dawo haka zata 'kullo abincinta ta taho dashi ta shige d'aki ta cinye domin kar ma karime ta gani ta saka rai.


Cikin 'kan'kanin lokaci karime ta sake zabgewa idanunnan sukayi zuru-zuru, dama abinka da mai idanu masha Allah ga yunwa ta cinye ita idan kayi mata kallon sauri sai ta tsorata ka. Kamannin karime gaba d'aya sun fara sauyawa saboda wahala ga aiki da take ma hajiya sa'a darajar makwanci da take bata ga zama da yunwa.


A wannan yanayi ta d'auki sati biyu a gidan hajiya wata guda kenan da zuwanta, tashi tayi da matsananciyar yunwa wadda ta sanya ta kada billenta ta ro'ki hajiya sa'a ta taimaka mata da abinda zata ci. Wani kallo hajiya sa'a ta watsa mata sannan ta tura mata ragowar biredin da take ci a wula'kance. Jikin karime har karkarwa yake ta zauna ta cinye biredin tas sannan ta yiwa hajiya godiya ta tashi ta d'ebo ruwa a rijiya ta sha ta had'a kwanuka ta fara wanke-wanke. Cikin sa'a kuwa taga takardar gurasar da Hajiya taci daren jiya tana bud'ewa ta tsinci yanka biyu a ciki, tamkar wadda taga nama haka ta cinye ta dinga lashe takardar.


Ta gama aikinta ta shiga d'aki taji sallama. Bata yi yun'kurin fitowa ba domin tasan ko masu neman 'yar aiki ne babu mai d'aukanta. Sosai take dana sanin baro garinsu da tayi gwara ta zauna a kasheta a can ta huta ma ranta.


"Atine sai yau kenan". Taji hajiya sa'a ta furta, jin an ambaci atine yasa ta fito ta dur'kusa ta gaidata ta koma d'aki ta zauna. Shigarta ke da wuya Atine tace "hajiyarmu wai yarinyarnan dama bata tafi garinsu ba?"


Tsaki Hajiya tayi tace "ki bari wallahi gaba d'aya na ma rasa yanda zanyi da ita, a dai kano babu mahaukaciyar da zata d'auki wannan aiki na barta ne kawai saboda bansan hannun da zata shiga ba idan ta fita amma banda haka tuni zan iza 'keyarta ta tafi".


'Kwalawa karime kira atine tayi ta bata kud'i tare da jera mata aike wanda ta san zata jima. Tana fita atine ta fara bayyana niyyar dake zuciyarta tun farkon ganin karime...


Free page


Littafina na kud'i ne 500 kacal🥰🥰ku nuna min solidarity ni kuma zanyi ‘ko’kari na baku abinda zu’katanku suke so😁😁


Account details

0472624453

Musa maryam Aminu

Gtbank


Ku tuntu'beni ta wannan number WhatsApp 

***. Love you guys ❤️❤️❤️