A CIKIN DUHU

06

by @kitty

A CIKIN DUHU...

Kitty💕

Wattpad @ Mssmeemah 


06


"Hajiya sa'a magana ce nazo miki da ita ta 'karuwa idan har zaki fahimceni". Atime ta furta tana gyara zamanta ganin Hajiya sa'a ta maida hankali.


"To ina jinki ai matsalarki Atine idan zaki fad'i abu sai mutum ya gama za'kuwa tukuna".


Dariya Atine tayi tace "Hajiya yarinyarnan naga har yanzu shiru babu wanda ya d'auketa, ke kanki zamanta a hannunki barazana ne. Shine naga ga wata hanya mafi sau'ki ga kuma saurin shigo da kud'ad'e. Akwai 'kawata da mukayi magana da ita tana kai yara irin wannan kariman taki wurin alhazawannan da 'yan siyasa kwana d'aya zuwa biyu yarinya zatayi ta dawo miki da ma'kudan kud'ad'e. Wallahi hajiya yanda take d'innan 'yar 'kauye sai yanda aka sarrafata ga kyau ga diri babu laifi a watanni zaki sauke gidannan ki sake sabo ki saka gate da sabbin tiles su kansu yaran dalilinta farashinsu zai 'karu suyi daraja tunda gidanki zai gyaru".


Zubawa Atine idanu Hajiya sa'a tayi tace "yanzu dai kina nufin na sayar da mutuncin Karima saboda ni ban haifi 'ya mace ba ko?"


Zare idanu Atine tayi tace "lah hajiya ba haka nake nufi ba amma a bar maganar kawai, arzi'ki nake duba miki da alfarma".


Tashi Hajiya sa'a tayi tace "bana bu'katar kowanne idan har sai na saida mutuncin karima ko kuma wata 'ya da tazo hannuna neman aiki, sanin kanki ne ba abinda ke gabana ba kenan".


"Allah ya huci zuciyarki ba haka nake nufi ba mu bar wannan batun. Dama abubuwa biyu ne suka kawo ni nace bari na fara fad'a miki na farkon zai fi kar'buwa a wajenki amma tunda bakya so shikenan. Akwai wata mata da mijinta yake zaune a saudiyya tana neman 'yar aiki kinga ita babu ruwanta da kalar mai aiki tace min tafi son 'yar 'kwalisa mai kyau saboda yaranta na da tsirfa. Mijin baya dawowa amma tana binsa lokaci-lokaci idan ta tafi ita mai aikin zata zauna da yaran har lokacin da zata dawo". Atine ta furta cikin takaici saboda 'kudurinta na farko ya'ki shiga kuma taso ace wannan hanyar Hajiya sa'a ta za'ba domin ita kanta sai ta murmure saboda har ta fara tallan karime.


Numfashi Hajiya sa'a taja tace "wallahi Atine duk kin kashe min jiki maganar gaskiya abinda kika fad'a ban aminta dashi ba. Indai mace ba ita zata zo da kanta ta nemi karima a 'yar aiki ba bazan baki ita ki kaita wani wuri ba hankalina bazai kwanta ba. Marainiyar yarinya babu uwa babu uba bazan yarda a lalata rayuwarta ba domin nasan menene maraici. Maraici shine dalilin fad'awata wannan harkar".


"Wallahi hajjaju ba 'karya nake ba zan kawo ta ma kuyi magana idan kinaso har gidan zakije ki gani, babban gida ne kuma tace zata biya dubu ashirin da biyar duk wata banda d'auke ci da sha da sutura da duk jin dad'i na rayuwa".


Sallamar karime ce ta katse musu maganar da sukeyi cikin sauri Atine ta mi'ke tare da saka hijabinta tace "zan mata magana zata zo kiji komai a bakinta, idan kuma kinfi so kije can kuyi maganar ma duk d'aya".


Sallama sukayi ta kar'bi kayanta daga hannun karime tace "ri'ke canjin babu komai". Gaba d'aya zuciyar karime babu dad'i domin a rayuwa ta tsani laruwa da wani ko da kuwa mahaifiyarta ce, sai gashi ta zama 'karamar mabaraciya.


Godiya tayi 'kwalla na cikowa a idanunta domin canjin ya kai 300, Atine na fita karime ta mi'kawa Hajiya sa'a kud'in tace "Hajiya gashi kud'in abinci sai ki ajiye a hannunki, kiyi ha'kuri inason na soya gyad'ar da na taho da ita na saida idan na samu kud'in mota sai na tafi, ko ban je garinmu ba zan nemi garin mahaifina".


"Ri'ke kud'in naki ba sai kin bayar ba, ki shiga kitchen ki had'a wuta sai mu dafa taliya. Ni bance ki tafi ba tunda baki da wajen zuwa sannan akwai matar da ta nemi a bata ke a 'yar aiki zata zo cikin kwanakinnan sai ki zauna cikin shiri".


Godiya karime tayi ta shiga kitchen ta fara had'a wuta iya 'karfinta ta d'aura ruwa sannan ta hau had'in taliya jollof, gaba d'aya jikinta rawa yake saboda yunwa har saida Hajiya sa'a taji kunyar rowar da take mata, meyasa ba zata dinga bata abinci matsayin sadaka ba bakin mutum d'aya dai? Ta za'bi ta 'kirga riba a kowacce rana akan tayi sadaka.


Ko da aka sauke abincin yanda karime ta dinga ci da sauri saida ta 'kware, dare nayi ta shiga d'aki ta zauna tana tunanin gidan aikin da aka ce zata koma, ita dai matu'kar zata samu abinci da makwanci to ko me za'a mata tanada tabbacin zata d'auka domin sai yanzu tasan bala'in dake cikin yunwa, a baya zasuyi 'karma 'karmarsu da mahaifiyarta domin 'kauye ba'a rasa abinci ko ya yake, saida tazo birni ta gane a cikin rahama take rayuwa.


Saida aka kwashe kwanaki uku sannan mai d'aukan karime tazo. Babbar mace ce kana kallonta kasan ta ji'ku da jin dad'i, tana da tsayi da 'kiba hakan yasa karime taji har wata inuwa tayi mata lokacin da ta gaisheta kafin a basu wurin zama. Kallon karime takeyi har saida karime ta fara tsarguwa ta koma d'aki ta ra'be gabanta na fad'uwa domin matar tayi mata kwarjini sosai.


"Yauwa itace wannan yarinyar?" Matar ta tambaya cikin murya ta 'kasaita, a mutunce Hajiya sa'a ta amsa mata tace "eh itace tayi miki?"


"Tunda ba miji ne dani ba she's alright, besides yarana sunce sun gaji da munanan 'yan aiki domin uku suka kora saboda dressing d'insu da kamanninsu basu musu ba, nidai farin cikin yarana shine nawa. Inada Yara biyar maza biyu mata uku. Babbar tana da shekaru 17 sai mai bi mata 15 years sai matan su ke binsa 12 da 8 years sai 'karamin 4 years. Aikinta shine kula dasu 24/7, bana son matsala bana so yarana suna complain a kanta idan kinsan tana da wani matsala kar na 'bata time d'ina domin ba 'kananun kud'ad'e zan biya ba".


Hajiya sa'a bata ji dad'in yanda matar ke magana ba saidai ta kawar saboda ta rabu da karime tace "karima batada wani matsala idan ma kinje kikaga alamun matsala tattare da ita zaki iya dawo min da ita".


Wani kallo matar ta watsawa Hajiya sa'a sannan ta ciro 20,000 ta bata tace "sai ki kirata mu tafi ko?"


Kiran karime akayi ta fito ri'ke da buhunta, wata muguwar harara matar ta watsawa karime tace "ina zaki da wannan sharar? Aje wannan abun ki wanke hannunki ku tafi akwai abubuwan bu'kata a gidana idan ma babu zan tsaya a hanya na sayar miki let's just go".


Karime tana d'ari-d'ari haka tabi matarnan suka shiga mota, har suka isa gidan bata ce mata uffan ba karime kuwa hankalinta a tashe ko kula da sun shiga gidan batayi ba sannan motar tana d'auke da tint.


Bud'e motar matar tayi ta fita itama karime tayi saurin fita ta ra'be a gefe suka nufi cikin gidan tana biye da matar a baya. Suna shiga matar ta fara 'kwalawa yaranta kira. "Fatima!! Abdulyassar!! Umaima and zee!! Kuna ina ne?"


'Daya bayan d'aya suka fito kowanne da waya a hannunsa suka zauna kan kujera tare da ma mahaifiyarsu sannu, karime kuwa tana ra'be daga 'kofa domin tsoron taka carpet d'in take kar ta saka mishi datti, ta matu'kar muzanta ganinta a cikin wannan gida da kayanta masu azabar daud'a da tsufa, bata sake jin ta muzanta ba saida taga yanda fatima ke mata wani irin kallo sannan ta 'kwallawa wata kira "Habiba!"


Wadda aka kira da habiba ce ta fito cikin sauri jikinta na rawa tana gyara d'ankwalinta, macece da zata kai shekaru 30 zuwa 35 amma haka ta dur'kusa gaban fatima tace "hajiya gani".


"Ki ja waccan kiyi mata wanka sai kuzo na bata kayan da zata saka, ba zata shigo mana d'aki a haka ba har zuciyata ta fara tashi da ganinta".


Jiki na rawa habiba ta tashi tana ri'ke da zaninta da ya kunce ta ja hannun Karime sukayi waje ba tareda tace mata komai ba, suna fita Fatima tace "Mum ki sallami habiba yau ko na koreta, wallahi ballagaza ce ga ladabin banza da wofi wanda ba'a sakata ba, salon ta dinga sa mutane na zagina".


Dafe kai Mum tayi tace "Fatima ko me aka miki ba za'a birgeki ba, tuntuni kike complain kan Habiba banda abdulyassar da umaima sunyi complain suma kinsan bazan sauyata ba, amma yanzu ga karima nan idan anyi mata wankan sai mu gani tayi muku ko kuwa".


Karime kuwa tunda taji ance za'a mata wanka taji ta fara neman hanyar guduwa domin ba zata zauna da girmanta a mata wanka ba, wani 'karamin band'aki matar ta kaita a can bayan gidan ta kunna ruwan zafi da na sanyi sannan ta umarci karime ta cire kayanta, ganin zata mata gardama tace "kinga kiyi abinda aka ce idan ba haka ba daga ni har ke zamu rasa aikinmu".


"Amma...amma zan iya wanka da kaina". Karime ta furta kamar zatayi kuka, girgiza kai matar tayi tareda yiwa karime jan ido a dole dai karime ta tu'be ta tsuguna kunya duk ta mamayeta matar ta d'auko shaving cream ta fara saka mata sannan ta hau dirzar fatarta da gashin kanta. Daud'ar da ta fita a jikin karime ita kanta saida tayi mamakin daud'ar.


Bayan an gama wankan matar ta bata sabon towel ta saka a jikinta tace su koma palon. Zare idanu karime tayi saidai tasan bata da damar gardama haka tabi bayan matar tana ri'ke da gaban towel d'in ga gashin kanta na d'igar da ruwa. Suna shiga Fatima ta kalli karime tun daga sama har 'kasa sannan tace "mum for the first time kin d'auko wadda ta dace da gidannan. Ba laifi ta wanku". Kallon karime tayi tace "muje na baki kayan da zaki saka".


Da sauri karime ta bita saboda wani irin kallo da abdulyassar yake jefa mata da taji gaba d'aya ta tsargu, har wani cije baki yayi yana lashe le'bensa har ta shige yana binta da kallo. Tana shiga d'akin Fatima yace "mum wannan new maid d'in tayi fa".


Had'e rai mum tayi tace "Abdul I don't want any funny business this time. Tashi ka tafi d'akinka".


Doguwar riga marar nauyi Fatima ta bawa karime ta saka sannan tayi blow drying gashin karime da kanta ta bata hula ta saka ba tareda tace da karime komai ba sannan suka fita parlor. Suna zama karime ta hau surfa godiya Mum tace "babu komai. Yanzu zan miki bayanin yarana dukkansu".


"Fatima itace babba sannan tafi kowannensu tsari, duk abinda kika gani a d'akinta ko gyara zakiyi ki ajiyeshi a wurin da kika ganshi. A kullum zaki share d'akinta da safe ki wanke toilet ki wanke mata nightys da undies sannan ki gyara gado. Haka ma da dare zaki gyara mata d'aki da gado sannan idan akwai wani personal business da take da zata sanar dake".


"Abdulyassar ma haka zakiyi wa d'akinsa a kowanne rana amma shi yana da zubar da kaya saboda haka a kullum zaki gyara wardrobe d'insa. Umaima da zee suna sharing d'aki ne suma zaki gyara musu d'aki, zaki shiryasu da safe shirin school sannan duk dare zaki tambayi abinda sukeso na lunch da safe li fad'awa cook d'inmu. Akwai tutor da ke zuwa yana tayasu assignment zaki kirashi lokacin da suke free a kullum yazo yayi musu homework. Sai kuma hammad, zaki mishi wanka ki shiryashi sannan koyaushe kece mai rainonsa shima yana zuwa school. Kamar yanda na fad'awa uwar d'akinki aikin yarana kawai kikazo yi. Nan da 3 weeks zan tafi wurin babansu na d'aga ne ma saboda inaso ki sake amma next week ya kamata na tafi. Karima bana son 'kazanta, bana son abinda zai 'batawa yarana komi 'kan'kantarsa ina iya had'aki da police su hukuntaki matu'kar kika 'bata ma yarana, sai ki kula da kyau".


Ana gama yiwa karime bayanin yanda zata kula da yaran aka saka habiba ta zagaya da ita gidan aka nuna mata wuraren da ya kamata ta gyara sannan aka nuna mata d'akinta wanda yake cikin palo a gefen d'akin su umaima, suna gamawa Mum ta ciro kud'i a jakarta masu yawa ta baiwa Habiba tace "to habiba aikinki ya 'kare sai kuma Allah ya sadamu da alkhairi".


Habiba batayi musu ba domin taga abinda ya faru da masu musu, 'karshe zakayi biyu babu kud'in babu aikin babu ga wula'kanci maybe ma ta saka mai gadi ya fita da kai a wula'kance, godiya habiba tayi ta kalli karime cikin tausayawa a ranta tana fad'in "Allah ya rabaki da sharrin yarannan".


Free page


Littafina na kud'i ne 500 kacal🥰🥰ku nuna min solidarity ni kuma zanyi 'ko'kari na baku abinda zu'katanku suke so😁😁


Account details

0472624453

Musa maryam Aminu

Gtbank


Ku tuntu'beni ta wannan number WhatsApp 

***. Love you guys ❤️❤️❤️