07
by @kitty
***
A CIKIN DUHU...
Kitty💕
Wattpad @ Mssmeemah
07
A zaman Karime da Amina (mum) bata fuskanci wasu manyan 'kalubale ba saidai bauta tamkar ba mutum ba saidai karime ganin abinda aka sayeta dan tayi kenan bata ta'ba nuna gazawarta ba. Aiki take tu'kuru ciki harda wanda bai kamata ba.
Har sati uku ya cika Mum bata samu zuwa saudiyya ba domin mijinta yace yana shirin zuwa da kansa yaga yaransa saboda shekarun da ya kwasa bai gansu ba, wannan dalilin yasa ta yanke tafiyar ta cigaba da harkokinta saidai mafi yawan lokutan bata zaune a gidan Karime dai itace uwa itace uba domin komai umaima, zee da Hammad ke so wurinta suke zuwa Fatima bata sakar musu fuska koyaushe tana d'akinta a zaune kasancewar tayi candy tana hutawa.
Kamar yanda karime ta saba bayan ta gama gyaran kowanne d'aki ta nufi d'akin Abdulyassar, tana tsoron gyaran d'akin abdulyassar da weekend domin ba 'karamin takura mata yake ba. A yau ma ya kama asabar tana shiga d'akin ta sameshi zaune kan gadonsa da wayarsa a hannu. Sannu ta mishi kai tsaye ta wuce toilet saidai kafin ta shiga yace "dalla malama koma ki rufewa mutane 'kofa".
Ha'kuri karime ta bashi gabanta na fad'uwa ta koma ta rufe 'kofar domin ba zaka ta'ba cewa ta girmeshi ba saboda yanayin jikinsa. Tana rufe 'kofar taji zuciyarta babu dad'i cikin sauri ta wanke toilet da 'kananun kayansa da ya cire sannan ta fito ta fara gyaran wardrobe d'insa. Earpiece ne a kunnensa amma tana tsugunawa gaban wardrobe d'in ya cire.
Wani sauti taji yana tashi daga cikin wayar saidai bata yi gangancin kallo ba har saida ya kira sunanta yace "saka min wannan a wardrobe daga 'kasa".
Juyawa tayi domin Kar'bar abinda ya nuna mata saidai tozalin da tayi da abinda ta gani a cikin wayar yayi matu'kar gigitata ta saki agogon da ya dan'ka mata ya fad'i 'kasa.
Mari ya kai mata yace "ke mahaukaciyar ina ce banza wawiya!! Kinsan kud'in wannan agogon? To wallahi indai ya lalace sai kin biya useless kawai".
Kauda kanta tayi ya kama kan nata da 'karfi ya juyo da ita tana kallonsa ga wayar da yake kallo a ciki tana cinyarsa wannan mummunan videon yana cigaba da playing, hankalin karime yayi matu'kar tashi ga ihu da Abdulyassar yake mata ga kuma 'karan dake fita daga wayarsa had'i da videon dake playing, kasa bud'e baki tayi ta bashi ha'kuri sai kuka da ya 'kwace mata.
Sakin fuskarta yayi ya mangareta da 'kafa yace "tashi ki 'karasa gyaramin d'aki ki fita kafin na duba agogon. Kud'insa dubu d'ari biyu ne indai ya fashe sai kin biya ko ta wacce hanya ce, idan ba haka ba wallahi 'yan sanda ne zasu rabam dake".
Tashi karime tayi ta cigaba da aikinta saidai jikinta karkarwa yake ga wani irin bugu da 'kirjinta keyi. Sautin da taji ne yake mata yawo a ka har ta gama gyaran d'akin Abdulyassar ta fita ta nufi nata d'akin domin wanke fuskarta. A ranar duk inda ta kalla gizo wannan video ke mata kuma babu wanda ya lura da yanayinta balle a tambayeta me ya sameta.
Tun daga wannan rana ta shiga takura da tsangwama a wurin Abdulyassar, lokuta da dama tana aikinta ma saidai ta jishi a kanta tun tana firgita har ta dena tana jin alamun inuwa tasan shine. Abu kamar wasa daga tsayawa a kanta kuma sai ya fara sunkuyawa yana kallonta ko kuma ya zauna a parlor duk giftawarta yana binta da idanu. BF kuwa har ya zame mata ba komai ba domin duk lokacin da zata gyara d'akinsa a weekend ko da dare saidai ta sameshi yana kallo, haka zata kauda kanta zuciyarta babu dad'i tayi aikin da ya kawota ta fita.
Saida tayi watanni uku a gidan sannan ya fara 'ko'karin kai hannunsa jikita, idan zata bashi abu sai ya had'a da hannunta ko kuma ya dinga 'ko'karin saka ta aiki yana ta'ba bayanta. Duk wad'annan abubuwan 'kidahumanci na karime bata ta'ba kawo abinda ke zuciyarsa ba har saida ya fito ya fara nuna mata a bayyane.
Tana zaune tana ninke kayansa yanda ta saba taji tsayuwarsa a kanta, bata nuna ta kula dashi ba domin yau kusan kaf kayan wardrobe d'insa ya fito dasu ya zubar ta kusa minti 20 tana ninki kuma tana yi yana cewa ba haka akeyi ba, ga Fatima ta saka ta aiki tana jiranta wannan yasa tsayuwar tasa bata dameta ba burinta ta gama abinda take ta fita.
Dur'kusawa yayi a bayanta ya zuro hannayensa ya d'aura a 'kirjinta, wata 'kamewa tayi ta fara yun'kurin cire hannuwansa daga 'kirjinta saidai wani irin matsa yayi wa 'kirjin nata har saida ta cije baki sannan ya d'aura kansa a wuyanta yace "kina bud'e bakinki zan yankaki da wu'ka kin ganta nan".
Cire hannunsa d'aya yayi ya zaro 'karamar wu'ka a aljihunsa ya nuna mata, 'kwalla ce ta ciko idanunta tace "dan Allah ka bari kayi ha'kuri".
"Ko a jikinsa yaci gaba da juya hannuwansa yanda yakeso idanunsa a rufe yace "kinsan kud'in agogon da kika lalata? Ki fad'a min ta yanda zaki biya".
"Zan...zan biya wallahi dan Allah ka bari Yaya Abdul banaso dan Allah". Kuka ne sosai ya 'kwace mata ta sake saka hannunta tana ture hannunsa domin wani zafi ke ratsata da wani irin yanayi da bazata iya fasaltawa ba, burinta kawai tayi nisa dashi domin directly a jikinta take jin hannayensa.
Duk kayan da Fatima ta bata dogayen riguna ne masu laushi babu atamfa ko d'aya a ciki, sannan ta had'a mata da vests babu bra. Karime bata damu ba ganin vest d'in na kama jikinta sai yau tayi nadamar yawo da take a haka.
Saida Abdulyassar ya d'auki kusan mintina biyar yana sarrafa 'kirjinta yanda yakeso kukanta ko damunsa baya yi sannan ya 'kyaleta kuma ya hanata fita a lallai sai ta gama ninke mishi kaya. A ranar taga tashin hankali kala-kala domin gadonsa ya koma ya kunna wayarsa tana jin sautin wayar na tashi had'e da sautinsa, tunanin abinda ke faruwa ma ba nata bane tana kuka tana ninki har Allah ya taimaketa ta gama ta fita.
Tana fita tayi kaci'bis da Fatima alamun kiranta tazo yi, kallonta Fatima tayi tace "ke, meye haka? Wai kuka kikeyi? Tun yaushe nake jiranki me kika tsaya yi?"
Bud'e baki karime tayi zatayi magana saidai hawaye ya 'kwace mata, Hard'e hannu Fatima tayi ta zuba mata idanu sannan tayi gaba tace ta biyota, suna shiga Fatima ta tura 'kofa tace "nasan akwai abinda ya shiga tsakaninki da Abdul, ki fad'a min me ya faru".
Kan karime a 'kasa tace "ta'bani yayi".
"Ta'ba ki kamar yaya?"
Shiru karime tayi hawaye na zuba daga idanunta Fatima taja tsaki tace "dalla malama ki fad'a min ta ina ya ta'baki domin ni kad'ai zan 'bata lokacina na saurareki, indai kina tunanin kai wa Mum wannan maganar to ki sani kinyi sallama da aikinki ne. Ban damu da a koreki ba amma babu wadda aka ta'ba kawo mana tayi kalar gidannan sai ke, saboda haka ki fad'a min abinda ya faru, ina ya ta'ba, me yace miki ni nasan ta yanda zan hanashi domin 'kanina ne. Ina ya ta'ba miki?"
Da hannu karime ta nuna 'kirjinta Fatima tace "that's all? Ina nufin shi kenan babu wani abun daban?" Gyad'a kai karime tayi alamin eh fatima tace "okay zan mishi magana amma inaso maganarnan ta zama daga ni sai shi sai ke, idan maganarnan ta fita zaki shiga gagarumar matsala kinji ko? Ki je kitchen akwai basket guda biyu chef ta gama had'a abincin ki jera min su a kwando sannan kiyi wanka ki shirya zamu fita tare".
Duk abinda Fatima ta fada mata hakan tayi bayan tayi wanka ta saka wata doguwar rigarta Army green da mayafin rigar green, mota suka nufa tana d'auke da kayan abinci a hannu suka nufi wani park mai matu'kar kyau inda fatima da 'kawayenta suka had'u domin sha'katawa. Ita ta zama mai musu bauta a wurin domin komai itace amma bata damu ba domin yanzu zaman gidan tsoronsa take.
Bayan sun dawo Fatima ta fad'a mata ta yiwa Abdul magana saboda haka komai ya wuce sannan itama ta kama kanta, godiya ta yiwa fatima ta cigaba da harkokinta a gidan kamar yanda takeyi a baya ganin shima bai sake kawo mata hari ba a 'yan kwanakin da suka wuce, saidai abin bai d'ore ba domin ba'a fi sati ba ya koma halayensa na baya.
Wannan dalilin yasa karime ta fara shirin barin gidan saidai bata san inda zataje ba, tana samun kud'i saidai hanyar da zata bi ta fita daga gidan shine matsala domin tunda tazo ko aikenta ba'a ta'ba yi ba, bazata iya cewa ga hanyar da suka biyo ranar da aka kawota ba balle ta koma gidan Hajiya sa'a saidai abu mai wuya ne Hajiya sa'a ta kar'beta a yanzu dama so take ta rabu da ita ta huta.
A kullum da wannan tunanin take kwana saidai duk ranar da ta shirya guduwa sai Mum ta bar mata Yara sannan Fatima itama ta fara yawan fita haka shima Abdul, ga kuma hammad ya sha'ku da ita indai ya rabu da ita to mahaifiyarsa ya gano, ita kuma duk yanda take son guduwa ba zata iya tafiya ta bar hammad shi kad'ai ba.
Ganin guduwar ta'ki yiwuwa yasa ta yanke shawarar kai 'kararsa wurin Mum. Tana zaune da dare tana tunanin yanda zata d'auko maganar domin Mum ita kad'ai ce a wurin sai ga Abdul ya shigo fuskarsa a had'e. Zama yayi gefen mum tace "me ya faru".
"Naji driver ya kawo 'karata".
Murmushi tayi tace "rabu dashi ko me kayi shi yana tunanin ya kai matsayin da zai kawo 'kararka wurina? Shiyasa yana gama fad'an problem d'in na koreshi bazan d'auki wannan ba, idan yanada matsala da kai sai yayi tunani da kansa ya gyara. Yayi sa'a ina cikin farin ciki da sai na had'a mishi da zazzafan cin mutunci. Tashi kaje d'akinka".
Jikin karime ne yayi sanyi ta kame bakinta ta tsuke ta koma shawararta ta farko ta barin gidan. A haka ta dinga gurgurawa har ta d'auki watanni biyar cikin wannan rayuwar, dukda cika mai kyau da take samu da makwanci hakan bai hana rama bayyana a jikinta ba saboda tsananin damuwar da take ciki, Abdul ya maidata tamkar wata saniya sarrafata yake son ransa a kowacce rana, idan har ta samu ta kauce sharrinsa saidai idan ta d'auki hammad ta shiga dashi d'akin shima wasu lokutan Abdul na korarsa yayi mata abinda yaga dama.
A kullum saidai tayi addu'a ta kwanta taci kukanta har bacci ua d'auketa tana neman Allah ya kawo mata mafita domin idan ta fita bata san masifar da zata tarar ba.
A wata ranar laraba ne ranar da tayi daidai da dawowar mahafinsu Fatima daga saudiyya, gaba d'ayansu suna cikin wata walwala da farin ciki har 'yan aiki aka 'karo domin a 'kal'kale gidan yanda ya kamata. Bayan anyi gyare-gyare da girke-girke mum da kanta ta d'auki mota tareda yaranta suka tafi d'auko mahaifinsu a airport, Abdul ne kawai basu tafi dashi ba domin ya tashi ranar da ciwon kai yanda ya fad'a musu.
Bayan fitarsu karime itama tayi saurin shiga d'akinta ta zauna tana addu'ar Allah ya hani Abdul kiranta har lokacin da zasu dawo, saidai tana gama addu'ar Abdul ya fad'o d'akin ya had'e rai tare da dafe kansa yace "ki duba cabinet d'in band'akin mum ki d'auko min magani ko kawomin d'aki".
Bakinta na rawa ta amsa da toh sannan ta yafa mayafi taje ta d'auko maganin ta shiga d'akinsa domin kai masa. Abdul na tsaye bayan 'kofa tana shiga yayi saurin tura 'kofar ya rufe ya jefa key d'in can gefe sannan ya juya ya kalli Karime da gaba d'aya ta kid'ime ganin abinda ke shirin faruwa, wani irin murmushi yake saukewa yana kallonta tareda lashe bakinsa yana cire kayan jikinsa d'aya bayan d'aya.
Dur'kusawa karime tayi ta fara ro'konsa da Allah yayi ha'kuri amma tamkar tana karantawa dutse, da wani irin 'karfi ya sha'ki wuyanta saida taji numfashinta na barazanar rabuwa da ita sannan ya saketa, wani irin 'karfi yake ji domin yaci alwashin yau sai ya ida nufinsa a kan karime domin tun zuwanta baida sukuni kullum burinsa ya ganta a 'kasansa yana juyata yanda ransa yakeso yayin da ita kuma tsoro da wahala yasa gaba d'aya 'karfinta ya rabu da jikinta.
Kama wuyan rigarta yayi da niyyar yagawa amma ya gaza, cukwuikuyo rigar ya fara daga 'kasa karime ta ri'ke rigar gam tana kuka iya 'karfinta tareda 'ko'karin 'kwatar kanta. Ganin zata 'bata mishi lokaci ya sanya ya danneta ya fara kai hannayena duk inda zasu iya sauka a jikinta saidai bai kai da nisa ba ya fara cije bakinsa jin wani irin murd'awa da gefen cikinsa yayi.
Duk yanda ya daure kan ya 'karasa abinda yakeda niyya saida ciwo yaci 'karfinsa ya sauka daga kan karime ya fad'i a gefe yana ri'ke da gefen cikinsa.
Karime kuwa ganin ta samu 'yanci yasa ta fara laluben mu'kulli tayi sa'a kan wasu kayan wanki ya fad'a. Tana juyowa da niyyar bud'e 'kofar taga Abdulyassar a kwance babu alamun numfashi tattare dashi, daga parlor kuma tana jiyo muryar Mum tana 'kwala mishi kira...
Free page
Littafina na kud'i ne 500 kacal🥰🥰ku nuna min solidarity ni kuma zanyi 'ko'kari na baku abinda zu'katanku suke so😁😁
Akwai discount ga wanda suka biya kafin free pages su 'kare, ki hanxarta kar ayi babu ke😁😁
Account details
0472624453
Musa maryam Aminu
Gtbank
Ku tuntu'beni ta wannan number WhatsApp
***. Love you guys ❤️❤️❤️