08
by @kitty
A CIKIN DUHU...
Kitty💕
Wattpad @ Mssmeemah
08
Ta'ba 'kofar da akayi ne ya sake gigita karime ta nufi Abdulyassar ta fara jijjigashi, tayi mamaki ganin boxer a jikinsa saidai ba wannan ne gabanta ba ya tashi shine mafita a gareta. Buga 'kofar aka sake yi ana 'kwala wa Abdul kira saidai sam Abdul baya motsi.
Tsugunawa Karime tayi a gabansa ta fara jan "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Mutuwar 'kannenta ce take dawo mata sabuwa fil tare da maganganun mutanen garinsu _karfa ce, duk namijin da ya ra'beta saidai kaji labarin wani ba shi ba domin tabbas sai ya mutu..._
Hakan yana nufin ita ta kashe Abdulyassar kenan, ko kuwa bala'in dake bibiyarta a 'kauye ne ya biyota birni? A 'kauye ma sani ya rasu an kashe mahaifiyarta balle a birni? Ta tabbatar yau saidai kuma labarinta.
Tana tsugune daga gefen kan Abdulyassar taji an bud'e'kofa d'akin, ja da baya tayi a tsorace ganin Mum, Fatima da wani mutumi sunyi cirko-cirko suna kallonsu, a gigice Mum tayi kansu tana fad'in "me kika masa karima? Me ya faru? Meye haka?"
Karima kuwa tamkar zaren kad'i haka jikinta ke rawa da 'kyar tace "wallahi babu abinda na masa". Babu wanda ya saurareta a cikinsu dukkansu suka dur'kusa gaban Abdulyassar. Mum tana ri'ke da hannunsa yayin da Fatima ke jijjiga 'kafarsa mahaifinsa kuma yana kai hannu wuyansa da goshinsa tareda danna 'kirjinsa yaga ko zai tashi saidai ina... rai yayi halinsa.
Wani irin kukan kura mum tayi ta nufi Karime tare da kasheta da wani mari da saida karime ta dena gani na wasu sakanni kafin ta dawo hayyacinta, sake kwasheta da wani marin tayi wanda ya sanya karime fad'uwa daga zaman da take. Banda wani 'kara a kunnenta babu ajinda take ji haka idanunta basa ganin komai sai wasu taurari, tana dai jin alamun ana magana daga 'karshe abinda ta iya tsinta shine "wallahi kema sai kin bishi". Kafin su kama Abdulyassar su fita dashi sannan mum ta 'kwace key d'in hannun Karime ta rufe 'kofar ta saka Fatima gadinta suka tafi kai Abdulyassar asbiti.
Suna zuwa aka d'auko wheelchair aka d'aurashi aka nufi emergency ward dashi, a wani gado aka shinfid'eshi shi aka fara duddubashi na tsawon lokuta kafin likitan ya sanar musu Allah yayi masa rasuwa. Wani ihu Mum ta kurma mijinta ya ri'kota tareda danne bakinta yace "Amina what's this? Ya zaki mana abu na jahilai a cikin asbiti? Mutuwa tana kan kowa muma bamu wuceta ba idan har kina sonshi da rahma addu'a zaki mishi".
Kuka Mum take tace "wallahi Abbu na rantse da girman Allah yanda d'ana ya tafi itama yarinyarnan sai ta tafi, Abbu itace ta kashe min Abdulyassar. Wallahi lafiya na tafi na barshi ya dawo daga school nace ko zai bimu yace a'a kanshi na ciwo ya gaji, minti nawa Abbu daga fitata nazo na tarar da d'ana ya rasu, Abbu lafiya yake fa".
"Ummu Fad'ima kiyi ha'kuri, kiyi ta kiran sunan Allah wannan ba maganar yanzu bace, mu samu mu tafi da gawar Abdulyassar ayi mishi sutura a kaishi makwancinsa duk abinda za'ayi sai ya biyo baya". Wani sabon kuka Mum ta fashe dashi tace "yanzu d'ana har ya zama gawa? Ya Allah ka ji'kan Abdulyassar Allah ka yafe mishi, Allah...". Lasa 'karasawa tayi saboda kukan da ya kufce mata nan dai Abbu ya lallasheta da 'kyar sannan Abbubya samu yayi abinda ya kamata aka bashi gawar d'ansa.
Kafin suje gida mutane sun cika gidan masu jiran janazah, a gurguje aka had'a Abdulyassar domin magrib na kawo kai aka mishi sallah aka kaishi. Duk wannan abubuwan da ake karime na d'akin Abdulyassar batun tashin hankali kuwa ba tsohon abu bane a wurin karime. Domin tunda aka haifeta bata san menene kwanciyar hankali ba kuma a yau ta gama tabbatarwa da kanta a 'kuncin da aka haifeta a shi zata mutu, gara ma mahaifiyarta ta mutu a inda aka santa ita ko mutuwarta babu wanda zai sani, to wa take dashi da zai damu da mutuwarta?
Tana ri'ke da gwiwoyinta a hankali ta furta "baaba". Hawaye na zuba daga idanunta, har wannan lokacin tana jin a ranta mahaifiyarta tana raye, amma tasan zuciyarta ce kawai ke rarrashinta babu yanda za'ayi su bar baaba ta rayu.
Mum taso yiwa mutane shelar 'yar aikinta ce ta kashe Abdulyassar saidai Abbu ya tsawatar mata yace kar ya sake maganarnan ta fita, domin a asbiti an tabbatar masa babu alamun duka ko rauni a jikin Abdulyassar, babu alamun yasha poison sannan babu wata alama da ta nuna sha'keshi akayi ko wasu hanyoyi da zasu katse mishi numfasho, bayanin da likita yayi na 'karshe ne yasa Abbu ya hana Mum magana domin yana da tabbacin 'karshe sune zasu ji kunya kuma Mum zata d'auki tabo mai girma da har ta mutu yana cin zuciyarta.
Saida dare ya tsaga duk 'yan zaman makoki sun tafi gida ya rage nasu su kad'ai sannan Abbu ya zaunar da Fatima da Mum yace "Amina nasan zaki shiga tsananin tashin hankali amma kiyi ha'kuri, Allah da ya kar'beshi ya fimu sonsa sannan a yanzu addu'armu yake bu'kata, idan har kina jin wannan rad'ad'in a ranki ni ya kike tunanin zanji? Dawowa ta silar Abdulyassar ce shi yake takura min yana cewa watarana zasu zo su manta da kalar fuskata idan har bana zuwa ganinsu, shekara biyar banga fuskar d'ana ba banji muryarsa a zahiri ba sai gawarsa na tarar. Na dake zuciyata ne kawai saboda yarda da 'kaddara".
Fatima tafi mahaifiyarta dakiyar zuciya domin tuntuni ta share hawayenta ta adanasu take ma d'an uwanta addu'a, a yanzu bazaka ce ma tayi kukan mutuwa ba saidai damuwa ce bayyane a fuskarta. Murmushi tayi tace "Allah sarki Abdulyassar, kayi ha'kuri Abba, kema mum kiyi ha'kuri muyi ta masa addu'a domin Abdulyassar yana tsananin bu'katarta".
Wani kallo Mum ta jefa musu da rinannun idanuwanta tace "zaku nuna min Kar'bar 'kaddara ne? Abbu nasan kana son Abdulyassar amma duk soyayyar da zaka mishi bata kai tawa ba da nayi jigilarsa a jikina shekara da shekaru, na yarda da mutuwa na kuma yarda da 'kaddara amma wallahil azim wata banza ba zata kashe d'ana na zauna na zuba mata idanu ba, yanda ta kashe Abdulyassar sai ta kar'bi hukuncin da zata gwammaci mutuwarta a kan rayuwarta".
Dafa ta Abbu yayi yace "Ummu fad'ima... bance yarinyarnan ba zata kar'bi hukunci ba idan har ita ta kashe Abdulyassar sai na tabbatar da an yanke mata hukuncin kisa idan anyi mata sassauci a yanke mata hukuncin rai da rai a gidan yari. Amma kar muyi gaggawa mu kira ta ta fad'a mana abinda ya faru idan..."
Katseshi Mum tayi tace "Abbu bazan amince da maganarka ba domin a yanzu zuciyata sa'ke-sa'ke take min saboda yanda kake kare yarinyarnan. Bazan saurareta ba taje can police station zasu fi sauraronta yanda ya kamata domin har na kira 'yan sanda yanzu haka suna hanya".
"Idan har inada iko dake Ummu fad'ima ki bi yanda nakeso". Ya furta a fusace, wani kallo ta jefa masa tace "wani iko ne ya rage gareka? Abbu a shekaru goma sau nawa kazo kaga yaranka? Sau nawa suka je gareka? Me ka sani kan yaranka banda sunayensu? Abdulyassar yana shekaru biyar ka tafi ka tsallake ka barni ni nake jigilar 'ya'yana, duk dawowar da zakayi aikinka shine ka d'ura min ciki ka tafi ka barni zan rayu ko zan mutu ba damuwarka bace. Tunda na haifi umaima sau uku ta zauna da kai mahaifinta, zainab sau biyu ta zauna da kai duk zaman satittika zuwa wata d'aya, hammad kuwa bai sanka ba tunda nayi cikinsa baka sake zuwa ba saidai ni na bika. A yanzu zaka nuna min 'ya'ya naka ne? Ka fad'a min na'kudar kwana nawa kayi ka haifesu? Laulayin wata nawa kayi? Wanne ka shayar daga cikinsu? 'Ya'ya nawa ne kuma duk yanda naso haka zanyi".
Abba shiru yayi domin ya rasa bakin magana, amma yasan tabbas mum ta d'aga wannan maganar zata yi dana sani nan ba da dad'ewa ba. Fatima kuwa tunda taga inda magana ke neman tafiya ta kwashe 'yanmatan 'kafafunta ta koma d'aki ta kwanta tana tunanin abinda ya faru. Itama tana da tantama akan kisan da Karime ta yiwa Abdulyassar domin ita kad'ai tasan abinda Abdul ke yiwa karime. Lokuta da dama a gaban idanunta zai ta'ba karime sai ta tsawatar masa tukuna, sannan tayi masa warning akan molesting d'in karime da yakeyi a d'aki ya'ki ji ta fad'a mishi idan har bai dena ba zata sanar wa Mum. Dariya yayi a lokacin yace "to ki fad'a mana kina da evidence ne? Besides siyota akayi baiwarmu ce, ko a addinance ina da damar sauke desire d'ina kan baiwar da aka sayarmin ko 'karya nayi?"
Dafe goshi Fatima tayi tace masa "Na farko Karima ba baiwa bace da aka sayota da kud'ad'en da suka kai na fansarta da rayuwarta, tamkar aikin contract aka d'auketa kuma a tsarukan da aka shimfid'a babu satisfying d'inka sexually. Ba ma wannan ba Abdulyassar baka tunanin wannan muguwar d'abi'ar taka ina zata kai rayuwarka a gaba? You're just 15 for God's sake ka zauna kayi tunanin rayuwarka amma baka da aiki sai kallon BF, masturbating, molesting and harassing innocent girls. Kana tunanin bansan me kake aikatawa a school bane? Shuhuda, Amra, Lubna, Sadiya duk kaine silar fitar dasu da akayi daga school. Abdulyassar a shekarunka me ka mora a duniya da zaka fara tarawa kanka zunubai irin wannan? Ka mutu kace da Allah me?"
"Kafin na mutu zanyi tunani naga abinda nake daidai ne ko kuwa? Yanzu ki fitar min daga d'aki I'm already on edge idan kuma zaki kalla ne kema be my guest. mum kuma ki fad'a mata kiga ni dake da wa zata yarda".
Ran Fatima ya 'baci sosai tace "zanbi duk hanyar da zan samu evidence a kanka sai na kunyata ka wurin Mum".
Dariya yayi yace "kin dad'e bakiyi ba".
Fita tayi zuciyarta cike da takaicin halayen Abdulyassar, a duniya ta tsani namiji mai irin halayensa sai gashi yazo a 'kaninta. Zatayi duk 'ko'karinta ganin halayensa sun sauya by fire by force. Ta jima tana sa'ka yanda zatayi da Abdulyassar har wata dabara ta fad'o mata wadda take yawan gani a finafinai. Camera ta siyo 'karama aka koya mata yanda zatayi amfani da ita domin tayi dogon video.
A kowacce rana kafin ya shiga d'akinsa da dare tana ajiye camerar har lokacin da karime zata gama aikinta, idan karime ta fito ita kuma cikin dabara sai ta shiga ta d'auko taga abinda ya faru, idan ya yima karime wani abun ta nuna mishi tace zata nunawa Mum daga baya ta goge.
Ranar da zai rasu ma saida ta ajiye camerar kuma tanada tabbacin tayi recording abinda ya faru. Tashi tayi zumbur ta fita ta tarar da 'yan sanda biyu a 'kofar d'akin sunzo su tafi da karime. Bud'e 'kofar sukayi karime ta razana ta sake ma'kalewa jikin gado fuskarta tayi jajawur ta kumbura. Tsoro ne 'karara a fuskarta tana kallon 'yan sandan ta fara sumbatu.
"Wallahi ba kasheshi nayi ba babu abinda na miki ku tambayeshi kuji. Allah ne shaidata ban mishi komai ba Fatima ki fad'a musu na rantse da girman Allah ban kasheshi ba. Fad'uwa kawai yayi na juya neman mu'kulli naga ya mutu. Ku yarda dani ban ta'ba kashe kowa ba".
Wata muguwar tsawa macen 'yar sandan ta dakawa Karime sannan ta ja hannunta cikin 'karfi ta fita da ita, ganin karime na tirjewa yasa matar ta wawureta ta sa'ba a kafad'a suka fita mum na biye dasu.
Suna fita Fatima ta shiga d'akin saidai d'an sandan ya hanata ta'ba komai a fad'arsa zata iya tempering da evidence. Safa d'an sandan ya saka ya fara lalube d'akin bai samu wani makami ba sai wannan 'karamar wu'kar da Abdulyassar yake ri'kewa. 'Daukanta yayi sannan ya d'auki wayar Abdulyassar ya dannata yana dannawa ta bud'e, videon da yake kallo ne ya bayyana a fuskar wayar d'an sandan ya girgiza kansa ya ajiye wayar ya cigaba da lalubensa Fatima na tsaye tana kallonsa tana addu'ar kar ya hango camerar da ta 'boye. Ganin zai nufi wajen camerar yasa tace "wai ba an tafi da ita ba me kake nema? Wannan d'akin Abdul ne ga d'akinta can idan evidence d'in kake nema kaje can ka duba".
Kallonta yayi fuskarnan babu walwala yace "okay muje ki nuna min d'akin nata".
Tare suka fita ya bincika d'akin Karime banda kayan sakawarta da kud'in albashinta babu komai a d'akin sai katifar kwanciyarta, numfashi ya sauke lokacin da wayar hannunsa tayi 'kara ya kai kunnensa yace "Assalamu alaikum inna kiyi ha'kuri wani aiki ne ya taso oganmu ya turani yanzu zan dawo...okay to shikenan".
Ratse Fatima yayi ya wuce ba tareda ya kalleta ba ya fita, yana fita tayi sauri ta shiga d'akin Abdulyassar ta d'auko camerar ta koma d'akinta, 'kirjinta na wani irin bugu ta kunna camerar ta fara kallon abinda ya faru...
Free page
Littafina na kud'i ne 500 kacal🥰🥰ku nuna min solidarity ni kuma zanyi 'ko'kari na baku abinda zu'katanku suke so😁😁
Account details
0472624453
Musa maryam Aminu
Gtbank
Ki a tuntu'beni ta wannan number
***