09
by @kitty
A CIKIN DUHU...
Kittyđ
Wattpad @ Mssmeemah
09
Rufe baki Fatima tayi kuka na âkwace mata ta danne camerar a kan gadonta, girgiza kanta take zuciyarta na wata irin âkuna, yanayin da dâan uwanta ya mutu a ciki ya matuâkar girgiza ta ji take inama zata iya taso dashi ya samu ya nemi gafarar ubangiji kafin mutuwarsa, ya mutu a mummunar hanya da mummunan nufi a zuciyarsa âInnalillahi wa inna ilaihi rajiâun, ya Allah ka gafartawa Abdulyassar Allah ka jiâkansa ka yafe mishiâ. Tana wannan kukan Umamima ta turo âkofar dâakinta muryarta a sanyaye tace âSister Abbu na kirankiâ.
âDago kanta tayi tace âkice mishi ina zuwaâ. Umaima bata fita ba ta nifi gadon Fatima ta zauna a gefenta ba tare da tace komai ba ta fara shafa bayan Fatima cikin sigar lallashi har fatima ta dâan samu nutsuwa suka nufi wurin Abbu. Tayi tunanin zaiyi maganar mutuwar sai taji baice komai ba yana ta jan yaransa da hira su kuwa kallonsa kawai sukeyi tamkar baâko musamman hammad da yake zaune a cinyar Abbu ya âkura mishi idanu tare da dâaga gira. Zee kuwa can gefe ta koma ta zubawa TV idanu umaima ce kawai ta zauna a gefensa yana mata tambayoyi tana amsawa har bacci ya fara dâaukansu.
Abbu da kansa ya kai kowannensu dâaki sannan ya koma parlor suka zauna shi da fatima, ba tare da âbata lokaci ba yace âfatima nasan zaki fi mahaifiyarki sanin halayen abdulyassar, banaso mu fadâi komai a yanzu domin malaâiku suna zagaywa suna Karâbar mishi shaida, amma kina tunanin yarinyarnan ce ta kasheshi?â
Shiru Fatima tayi na tsawon lokaci sannan tace ânima ban sanibaâ. Numfashi Abbu ya sauke yace âshikenan tashi kije abinkiâ.
__________________________
âHajiya kiyi mana bayanin abinda ya faru dalla dalla ni kuma zan tabbatar da hukunci ya hau kan yarinyarnanâ.
Gyara zama Mum tayi tace âyarinyarnan na dâaukota ne wata shida da suka wuce tana tayani aikace-aikacen gida da kula da yara. A yau mun fita da yaran dâauko mahaifinsu a airport muka dawo muka tarar da dâakinsa a rufe domin shi baije ba baya jin dadâi, ina budâe dâakin na sameshi a kwance ita kuma tana durâkushe a kansa. Muka kaishi asbiti aka sanar mana ya rasuâ.
Rubutu dâan sandan yayi sannan yace âdama tana nuna âkiyayya gareshi ko sauran yaranki? Ko kuma tana da wasu halaye wanda kike zargi?â
Shiru Mum tayi tana tunani sannan tace âgaskiya ba nace ba tunda yarana babu wanda ya taâba kawo min complain a kanta har shi marigayin sannan babu wasu alamu da take nunawa da zan zargi matsala, infact muna da CCTV camera a parlor ko da tayi wani abun zan iya ganiâ.
âMasha Allah abinda zaâayi ita ki barmu da ita zan saka a tambayeta sai ta fadâa da bakinta ita ta kasheshi sannan mu samu zuwa gobe ko jibi a miâka case dâin kotu, saurin amincewa da zatayi da laifinta ne zai taimaka ku shiga kotu da wuri idan bata amince ba zata jima anan gaskiyaâ.
Cikin damuwa Mum tace âduk abinda zakuyi mata kuyi idan ta kama ku karairayata ma duk kuyi ta furta da bakinta ita ta kashe min dâa, yanda ta kashe dâana itama sai na tabbatar ta dâandâani zafin mutuwaâ.
Murmushi yayi yace âHajiya indai wannan ne karki damu matuâkar zaki kula da wadâanda zasu tambayeta to zasu miki abinda kikeso, yanda zaâayi ki basu na shayin dare tunda kinga kwana zasuyi yanda zasu samu âkarfin tambayarta yanda ya kamataâ.
Babu wata-wata Mum ta zaro 10,000 a jakarta tace âgashi, idan na dawo da safe zan basu na kari indai zasuyi abinda ya kamataâ.
Miâka kudâin yayi daidai da shigowar wannan dâan sandan da ya tsaya bincike, yana shigowa ogan nasu ya hadâe rai yace âSERGEANT AHMAD me aka samu?â
Pocket knife dâin da ya tsinto ya ciro a cikin leda ya miâka mishi yace âwannan ne kawai suspicious evidence da na samu a cikin dâakin. Itama na duba nata dâakin babu wani abu a cikiâ.
Karâba ogan nasu yayi yace âGood job, saida safeâ. Kallonsa sergeant Ahmad yayi ya kalli Karime dake bayan canter a tsugune ko motsawa batayi saidai ba wannan ne damuwarsa ba kudâin da ya gani a hannun ogansa shine abinda ya tsone mishi idanu domin 700 ce a aljihunsa kuma ya fito ya bar kakarsa ba tareda kudâin cefane ba, tunaninsa ko 1000 ne ya âkara mishi ya samu ya musu cefane amma yafi kowa sanin halin ogan nasu.
Fita yayi tareda alwashin wannan case dâin ba zai bar wajennan ba sai ya yagi iya rabonsa shima domin ya lura matar tana shirin fidda ko nawa ne. Yana tsananin buâkatar kudâi saboda haka zai shiga ya tabbatar ta samu abinda takeso idan har zata fiddashi daga talaucin da yake ciki.
Kiran Inna yayi a waya ya tambayeta abinda zai taho dashi tace babu komai amma yafi kowa sanin halin innarsa, zata iya zama da yunwa ta kwana da ita akan ta budâe baki tace mishi babu wani abu.
Shinkafa ya siya rabin kwano sannan ya tafi gida. âKaramin gida ne sosai domin dâakuna biyu ne kawai a ciki da bandâaki da kitchen sai âkaramin tsakar gida. Sallama ya doka Inna ta amsa mishi daga dâaki tana mishi maraba.
âDakin inna ya nufa ya zauna tareda maida numfashi suka gaisa tace âtunda naga kayi dare na san akwai abinda ya faru, anya Ahmad ba cin hanci ka sake Karâba aka kama ka ba?â
Murmushi yayi saidai ransa babu dadâi amma bai nuna mata ba yace âInna tunda nace miki bazan sake Karâbar kudâin mutane a titi ba na dena Karâba, wallahi wani case ne aka kawoshi a darennan âyar aiki ta kashe dâan gida shine oganmu ya turani aka dâauko ta da wasu abubuwan sai yanzu na samu na kai mishiâ.
âKai amma abu baiyi dadâi ba Allah ya kyauta. Me ya mata ta kasheshi?â Inna ta furta tana ajiye carbinta a gefe, cikin ko in kula yace âban sani ba amma dai ko me tayi zata sha wahala saboda yaron dâan masu kudâi ne sosaiâ.
Shiru Inna tayi bata sake tankawa ba ya miâka mata shinkafar da ya siyo da canjin yace âyau na fita ban bar komai ba ga wannan gobe sai a samu ayi ko da abin kari ne ko abincin ranaâ.
Murmushi Inna tayi tace âAllah yayi maka albarka ya jiâkan iyayenka. Ai dake ma bayan fitarka aka kawo min gero daga âkauye mai yawa sosai, na gyara shi na daka da safe sai nayi mana kunuâ.
Murmushi yayi yace âmasha Allag aiko sun kyauta da suka kawo, bari na shiga daga cikiâ.
âTo saida safe Allah yayi maka albarka ya tashe mu lafiyaâ
*****
Da Sasafe Ahmad yayi shirin fita saidai duk sammakonsa Inna ta rigashi har ta dama kunu ta ajiye masa da tuwon âbula da tayi d dâumamen na dare. A gurguje yaci tuwon ya fita domin tun biyar ogansu ya kirashi yace ya shigo da wuri.
Yana shiga police station dâin nasu ya fara jin shessheâkar kuka, sai yanzu ya tuna da mai aikin da aka kawo bai bi ta kanta ba yaje yayi signing da abubuwan da suka kamata sannan ya tambayi masu night duty âtayi confessing kuwa?â
âInafa, ai nidai ban taâba ganin yarinya irinta ba ga laifi âkarara amma sai rantse rantse take mana ba ita ta kasheshi ba. Mun tambayeta har saida tayi passing out three times but still babu sauyi yanzu zamuyi handing over gareka saboda matarnan idan tazo taji bata amsa laifinta ba zamu shiga matsala, oga kanshi tun 4 am ya kiramu yana fadâa mun gaza gudanar da aikinmuâ.
âOkay babu matsala ai ko bata amsa ba nasan yau oga zai shigar dasu kotu a can zata fadâi gaskiya ko bata shirya ba. Bari naje na gantaâ.
A kwance ya tarar da karime bata motsi sai shessheâkar kuka da takeyi, rigarta tayi kaca-kaca da jini ta wurare da dama ga gashin kanta ya bayyana, cikin muryarsu mai firgitarwa sergeant Ahmad yace âke tashi ki zauna!â
Da âkyar karime ta zaune tareda jingina a bangon cell dâin mai balaâin datti, dâago kanta tayi suka hadâa idanu da Ahmad lokaci guda wani irin yanayi ya ziyarceshi da ba zai iya fasalta shi ba.
Fuskarta tayi rudâu-rudâu da shatin mari haka rinannun idanuwanta sunyi âkwala-âkwala dukda uban kukan da tayi, sunkuyar da kanta tayi jin jiri ya dâauketa wanda yasa gashin kanta ya zubo gefen fuskarta ya sauka a âkirjinta, rabon da karime ta zauna babu hula ko dâankwali tun ranar da aka mata wanka a gidan Mum sai gashi yau ta kwana da kanta a budâe, dâan âkaramin ribbon dâin ma ya cire saboda juyin da take jikinta kuwa ita kadâai zata iya fasalta abinda takeji domin ciwukan dake zubda jini ma suna da yawa. Karime dai ta gama yanke rai da rayuwa jira kawai take su âkarasa ta, domin idan har wannan dukan zasu cigaba da mata da sunan tambaya tabbas tana gab da amsa laifin wannan kisan gara ayi mata mai gaba dâaya ta huta da rayuwa.
Ahmad kuwa tunda ya âkura ma karime idanu yaji yawun bakinsa ya âkafe saboda wani irin kyau da tayi masa a yanayin da take ciki, tausayinta ne ya kamashi sai kuma ya tuna abinda ya kawoshi ya tsuguna âkofar cell dâin yace âke taurin kai ba zaki fito ki amsa laifinki ba kin gwammace ki sha wahala ko?â
Girgiza kai tayi ta budâe bakinta da niyyar magana saida babu kalmar da ta fito daga bakinta sai shaâkewa da tayi ta fara tari ya tashi ya dâauko pure water ya budâe cell dâin ya shiga, tsugunawa yayi ya miâka mata ruwan da âkyar ta Karâba ta sha cikin dasasshiyar muryar tace âba ni na kasheshi baâ.
âIdan ba ke kika kasheshi ba me kikeyi a dâakinsa a wannan lokacin âkofarsa a rufe?â
Hawaye ne ya gangaro fuskarta ta girgiza kanta tana cije baki, a cikin duhun rayuwarta bata taâba ganin duhu irin wannan ba. Ta rasa uwa da uba da duka âyan uwanta amma ko gudun ceton ranta bai kai wannan halin da take ciki âkuntatawa zuciyarta ba. Samari da dama sun mutu sanadiyyarta yanda ake fadâa a âkauyensu amma mutuwar sanin wawo da Abdulyassar su suka jefata cikin balaâi. Mutuwar sanin wawo tayi sanadin mahaifiyarta ta yiwu mutuwar Abdulyassar itace ajalinta. Gara ma danginsu su âkare ko a samu nutsuwa cikin alâumma domin yanzu kam ta aminta ita dâin masifa ce a cikin mutane.
Tambayoyi yake mata amma hankalinta ya fara gushewa sama-sama take jin muryarsa domin bacci ke dâibanta dalilin jinin dake zuba a jikinta, a jinginen da take ta lumshe idanunta tayi loosing consciousness.
Taâbata Sergeant Ahmad yayi yaga ta âbingire ya sanya hannunsa yaji numfashinta na fita amma sama-sama. Fita yayi cikin sauri ya dâauko ruwa ya kwara mata tayi wani irin firgita ta sake komawa ta rufe idanunta. Wannan ba sabon abu bane a wurinsu amma sai yaji hankalinsa yayi matuâkar tashi yanayin da yarinyar take ciki. Fita yayi daga cell dâin sukayi kaciâbis da ogansu ya shigo tareda AbbuâŠ
Free page
Littafina na kud'i ne 500 kacalđ„°đ„°ku nuna min solidarity ni kuma zanyi âkoâkari na baku abinda zuâkatanku suke sođđ
Account details
0472624453
Musa maryam Aminu
Gtbank
Ki a tuntu'beni ta wannan number
***