10
by @kitty
A CIKIN DUHU...
Kittyđ
Wattpad @ Mssmeemah
GAMJI WRITERS ASSOCIATION
10
âSunana Ismaâil Muhammad nazo Bailing karima ne wadda matata ta shigar da âkararta jiyaâ. Abbu ya fadâa bayan DPO ya bashi wurin zama sun gaisa a office dâinsa.
Hardâe hannuwa DPO yayi yace âranka ya dadâe ai bazia yiwu ba wanda ya shigar da âkara dole shine zai janye sannan wannan magana ake ta kisa, ko da kun janye dole yarinyarnan a hukuntata domin haâkkin gwamnati ne ta hukunta mai laifin da aka kama a âkasartaâ.
Hadâe rai Abbu yayi yace âzancen banza zancen wofi, yaronnan dâana ne kuma na fito nace a janye. Idan har gwamnati tasan da haâkkin âyan âkasarta da tun fari yarinyar bata zo aiki gidana ba balle wannan tsautsayin ya rutsa da itaâ.
Wani murmushi DPO yayi yace âAlhaji idan har ka cigaba da magana irin wannan zamu saka ka a jerin suspects a cikin wannan case dâin. Tunda har case yazo hannunmu ka barmu muyi aikinmu kawaiâ.
A fusace Abbu ya fito daga office dâin ya kalli Sergeant Ahmad dake tsaye a wurin, sunkuyawa Sergeant Ahmad yayi kadâan sannan ya danna kansa cikin office dâin DPO.
__________________________
Mata ne fal a cikin gidan ana ta harkokin dâaura tukwane, yanda ake kaiwa ana kawowa ba zaka taâba tunanin mutuwa akayi ba daga cikin gidan saidai idan ka fita kaga rumfunan maza a waje.
Mum tana dâaki da wayarta a kunnenta tana kiran Atine saida ta mata kira uku a ba hudâu ta amsa. Sallama tayi saidai ba tareda Mum ta amsa mata ba tace âinason kizo gidana da yamma ke da matar da ta bani âyar aikiâ.
âTo? Hajiya wani abu ne ya faru?â Atine ta tambaya gabanta na fadâuwa Mum tace âba wani abu bane inason dai ganawa da ita neâ. Atine dai zuciyarta bata aminta da hajiya ba amma tayi mata alâkawarin zasu je bayan magriba.
Mum na gama wayar ta fita parlor nan dai mata suka hau mata gaisuwa tareda miâko buâkatu akan girkin da akeyi ita kuma tana zaro kudâi tana miâka musu. Bayan ta gama sallamarsu ta nufi dâakin Fatima domin tunda mata suka fara cika gidan âyan uwa da abokanan arziâki fatima ta rufe kanta a dâaki. Tura âkofar Mum tayi tareda sallama ta zauna kan kujerar mudubin dake dâakin tace âFatima ba zaki fito cikin mutane ba? Cousins dâinki sunzo Atleast ki fito su dâebe miki kewaâ.
Murmushi fatima tayi tace âMum Iâm okay i just need some me time. Mutanennan sunyi yawa ciwon kai zasu sakani kuma ba komai ya kawosu ba sai cin abinci. Indai mutanennan suna gidannan bazan iya fitowa baâ.
Numfashi Mum ta sauke tace âshikenan bazan miki dole ba fatima, Allah ya jiâkan Abdul nasan abinda kikeji shiyasa ma zan sanar miki wannan tun da wuri. Idan har Allah ya kaimu akayi kwana uku aka âkare zama zamu shiga kotu inaso ki bada shaida akan Karimaâ.
Zumbur Fatima ta tashi ta zauna tace âMum kotu fa kikace? Shaida a kan me? Bana nan ta kasheshi bazan iya shaida akanta ba kuma ko da shaidar halayenta zanyi batada wani mummunan hali da muka gani a watanni shida da tayi damuâ.
âNasan bakya nan nima ai bana nan amma dole zamu bada shaida kuma idan munaso a dâaure yarinyarnan ko a mata hukunci mai tsanani sai mun âkirâkiri wani abun mun fadâa. Idan aka je kotu kice tana da kwadâayi da son duniya da dai duk abinda zai saka a hukunta yarinyarnan. Karki manta dâan uwanki ta kashe idan har kasheta akayi ba ko dâaurin rai da rai ba zamu taâba samun kwanciyar hankali baâ.
Girgiza kai Fatima tayi tace âMum duk abinda nasan gaskiya ne kan yarinyarnan zan fadâa amma bazan iya mata âkarya ba. Mum nifa ina tunin⊠karima ba itace ta kashe Abdulyassar baâ.
Wani irin kallo da mum ta jefawa Fatima tamkar ta watsa mata garwashin wuta tace âkema Abbu ya kitsa miki ko? Fatima adalci zaki bi ko son zuciyar mahaifinku?â
Hawaye ne ya gangaro fuskar Fatima tace âMum ba son zuciya bane gaskiya ce. Nasan abinda ke faruwa tsakanin Karima da Abdul kuma ni na hana ta fadâa miki saboda nasan korarta zakiyi ki goyi bayan Abdul. Da idanuna naga abubuwa da dama kuma a waje ma ina samun complain dangane dashi from their school. Mates dâina na fadâa min abinda yake ma âkannensu da sauran students. Mum kiyi haâkuri amma bazan iya shaidar Abdul a kotu ba. Idan har case dâinnan ya cigaba Mum zaâa âbaro abinda bazai ma kowa dadâi. Abdul yana buâkatar tsananin adduâa daga garemu musamman ma ke mum. Dan Allah a janye wannan case dâin ki kawo ta gida ki tambayeta da kanki abinda ya faru zata fadâa miki. Ni kuma inada shaidar da zan bayarâ.
Kafe da idanu Mum tayi tace âyau kwanan dâana dâaya a cikin âkasa amma ke da mahaifinki kuna nuna halin ko in kula da abinda aka aikata mishiâ.
âMum ba halin ko in kula muke nunawa ba, bansan dalilin Abbu na aikata haka ba amma ni inada dalilina. Dan Allah mum ki janye wannan âkarar zan fadâa miki komai. Indai aka hukunta karime a kan laifin da bata aikata ba Abdul bazai samu nutsuwa a âkabarinsa ba dan Allah mum ki bari ya samu rahmar ubangiji ko yaya takeâ.
Ran Mum ya gama âbaci ta fice a fusace bata sake zuwa dâakin Fatima ba har dare yayi. Shima Abbu bai shigo gidan ba ko sau dâaya domin zaman makokin ma gagararsa yayi, zuciyarsa ta kasa aminta da cewar karime ce ta kashe yaronsa sannan akwai wani abu na daban da yake ji a zuciyarsa, tamkar yana da alhakin kula da ita da tsaron rayuwarta haka nan ya tsinci kansa cikin damuwa saboda laifin da aka dâaura mata.
Lokacin da ya shiga gida babu kowa ya nufi dâakinsa ya watsa ruwa sannan ta dâauko waya yana duba messages da sukayi da Abdulyassar, a message dâinsa na farko yake fadâa ma Abbu bazai je dâaukoshi daga airport ba saboda akwai surprise da zai shirya masa, murmushi Abbu yayi yace âAbdulyassar ashe surprise dâin mutuwarka zan samu. Wannan shine mafi munin surprise da na taâba samu a rayuwata. Allah yayi maka rahma yasa ka hutaâ.
Knocking yaji anyi ya amsa Fatima ts tura âkofar a hankali ta shiga, ajiye wayar yayi ganin yanayinta yace âyaya dai Fatima?â A gefen Abbu ta zauna ta dâaura kanta a kafadâarsa tace âMum ta fita Station ita da wasu mutaneâ.
Shiru yayi lokaci guda ta fashe da kuka tana fadâin âAbba dan Allah kar ka bari a hukunta Karime wallahi ba ita ta kashe Abdul baâ.
Ba tareda ya kalleta ba yace âFatima mahaifiyarku ce kawai take da wannan damar domin naje station dâin domin su bada belinta suka ce wanda ya shigar da âkara shi zai janye kuma baâa janye âkarar kisan kai. Banida hujjar da zan kareta in fact sun sakani cikin suspects ma saboda na nemi belintaâ.
Dâago kanta tayi tace âto Abbu kenan idan akwai hujja da shaida mai âkarfi zaâa saki karima?â
â âkwarai kuwa. Indai akwai hujja mai âkarfi ba zasu riâketa ba. Fatima ba wai goyon bayan yarinyarnan nake ba domin ina jin ciwon rashin dâana, banaso muyi hukuncin da zai dinga bibiyar mutuwar Abdul saboda son zuciyarmu. A yanayin da likita yayimin bayanin mutuwar Abdul jikina ya bani akwai âboyayyen alâamari a cikiâ.
âAbbu inada shaida, shaidar da zata tabbatar ba ita ta kashe Abdul ba. Nidai Abbu a dena maganar mutuwarnan dan Allah a bar Abdul ya runtsa a makwancinsa mu bishi da adduâa kawaiâ.
Kafin Abbu ya amsa ta miâka mishi memory card dâin hannunta ba tareda ta sake cewa komai ba ta fita daga dâakin.
__________________________
Kira Atine ta dinga surfawa Hajiya saâa bata sameta ba, âkarshe âkofar gidan Hajiya saâa taje ta zauna domin bata nan. Ta dâauki kusan awanni uku a wajen sannan Hajiya saâa ta dawo.
Da murmushi ta tari Atine tace âkiyi haâkuri nasan kin kirani wallahi wayar ce ta fadâi a dâan sahu tayi daga-daga. Kin dadâe ne anan?â
âHaba Hajiya saâa meye na tambaya tunda kika ganni a zaune ai kinsan na dadâe a wurinnan nayi kusan awa biyarâ.
Murmushi Hajiya saâa tayi tana budâe gidan tace âto ai ko ni banyi awa biyar da fita ba. Mu shiga ciki ki samu ki sha abin sanyi kinsan nayi fridge sabo yanzu bana rabo da âkanâkara da ruwan sanyiâ.
Yashe baki Atine tayi suka shiga saida ta take cikinta sannan ta baje tace âwallahi har na manta abinda ya kawoni. Hajiya Amina ce tace tana son ganinki wadda ta dâauki karime, ina tunanin dai yarinya tayi dâanyen aiki saboda yanda naji muryar Hajiyanâ.
Cikin ko in kula Hajiya saâa tace âbabu inda zani saboda ke kinsan tsarin contract dâina matuâkar yarinya tayi wata shida ta fita daga hannuna, sannan idan yarinya tayi laifi babu ruwana da hukuncin da zaâa mata a gidan aikinta ruwansu ne wannan. Idan ta manta ne ki fadâa mata bazani baâ.
Atine batayi âkasa a gwiwa ba ta kira Mum ta zayyana mata batun Hajiya saâa, tana gama magana Mum tace a baiwa Hajiya wayar. Kafin su gaisa Mum tace âYarinyar da kika kawo min ta kashe min yaro saboda haka ko dai kizo police station ki amsa tambayoyi a kanta ko kuma kema a hadâa dake. Daga ke har Atine ana buâkatarku a station zan turo muku addressâ.
Salati Hajiya saâa tayi ta dafe âkirji ta katse wayar. Zama tayi ta zuba tagumi tace âna shiga uku, yarinya ta jamin balaâi da masifa Atine. Karime ta kashe dâan gidan Hajiya Amina shikenan kashina ya busheâ.
Idanun Atine âkulu-âkulu yayi tace âna shiga uku shikenan nima tawa ta âkare, wallahi Hajiya indai naje police station aurena ya âkare kenan domin Abban Nawal saida ya min kashedi yace idan ya sake jina a police station a bakin aurena. Hajiya ki rufa min Asiri dan Allah ki fiddani daga wannan balaâinâ.
âWallahi yanda muka shiga tare haka zamu fita. Ki sani kin ma fini shiga matsala saboda kece kika kawo min karime. âKafars âkafarki sai munje anyi komai ya âkare. Kuma kar kiyi tunanin zanyi amfani da kudâina na taimakeki kowa tashi ta fissheshi. Ke Allah ya isa ma ban yafe ba kin dâauko min tashin hankali ina zaman zamanaâ.
Kuka Atine ta fara tace âdaga taimako? Nima Allah ya isa tunda ke nake kawowa yaran kin fini samun riba dasuâ. Haka suka cigaba da sukar junansu har magriba ta kawo kai, babu yanda suka iya kowacce rai a dagule suka fito suka nufi gidan Hajiya Amina.
Suna zuwa ko gaisuwa bata bari sunyi ba ta tasa âkeyarsu zuwa police station. A hanya babu irin adduâar da Atine bata janyo ba gashi mijinta tunda suka dâauki hanya ya addaba mata da yawa, surutan da take yasa saida hajiya Amina ta daka mata tsawa sannan ta shiga hayyacinta. Hajiya saâa kuwa tsara âkarairayin da zatayi a police station takeyi har suka isa.
Free page
Littafina na kud'i ne 500 kacalđ„°đ„°ku nuna min solidarity ni kuma zanyi âkoâkari na baku abinda zuâkatanku suke sođđ
Account details
0472624453
Musa maryam Aminu
Gtbank
Ki a tuntu'beni ta wannan number
***