A CIKIN DUHU

11

by @kitty

A CIKIN DUHU...

Kitty💕

Wattpad @ Mssmeemah


11


Suna shiga sukayi tsamo tsamo kana kallonsu kaga marasa gaskiya. Wajen zama aka basu 'yan sandan sai dur'kusawa Mum sukeyi domin da rana saida ta saka aka kai musu abincin sadaka fal da nama da lemuka. Har wannan lokacin da sauran lemu da ruwa kusan katan biyu a station d'in.


Bayan sunyi settling aka fito da karime daga cell, duk wanda ya kalli karime yaga yanda ta fita hayyacinta dole ya tausaya mata amma dukka mata ukun dake wurin ji suke tamkar su kasheta ta mutu kowa da dalilinsa a zuciyarsa.


"Kinsan wannan yarinyar?" Aka tambayi Hajiya sa'a, muryarta na rawa tace "eh...nice na bada ita aiki a gidan Hajiya Amina amma wallahi bansan abinda ta aikata ba sai yau, kuma saida na fad'a wa hajiyan idan yarinya tayi watanni shida ta fita daga hannuna..."


Wata tsawa aka daka wa Hajiya sa'a saida ta gigice sannan d'an sandan yace "ki amsa iyakar abinda na tambayeki. Kince ke kika bada ita aiki. 'Yarki ce ko 'yar uwarki ko kuma ina kika samota?"


Cikin sauri ta nuna Atine tace "na rantse da zatin Allah ita ta kawomin ita bansan komai a kanta ba. Amma Atine tana da lambar wayar iyayen yarinyar sai ta kirasu".


"Okay". Ya furta tareda rubutu sannan ya koma kan Atine yace "A ina kika samo yarinyarnan sannan su waye iyayenta". 


Kuka Atine ta fara itama aka daka mata tsawa, da 'kyar ta samu bakin magana tace "Wallahi bansan kowa nata ba. Naje 'kauyensu dai na samu iyayensu kuma inada lambar wasu daga cikin iyayen nasu. Ta fad'i sunan babarta sai na baku lambar gatanan amma bamuda masaniya a kanta".


"Okay... bakuda masaniya kuka d'auko ta har kuka bada ita aiki a gidan mutane ta kashe yaronsu ko? Kune masu safarar 'kananun yara da muke ta fafatawa dasu wanda kuke sato yara daga gidan iyayensu kuna saidasu ko?"


Rantse-rantse suka hau yi DPO yace "A jefa min su a cell!"


Kuka wiwi Atine keyi tana ro'kon Hajiya Amina ta rufa mata asiri, agogon hannu hajiya Amina ta duba tace "DPO a 'kyalesu kawai".


"Hajiya akwai case na child trafficking a kansu fa".


Murmushi tayi tace "wannan abu ne for another time yanzu rayuwar d'ana kawai nakeso a 'kwatarmin. Ku musu tambayoyi kawai ku sakesu na yafe".


Tambayoyi aka sake musu suka amsa aka sallamesu bayan su aka maida Karime cell, waige take tana kallonsu amma cikinsu babu wanda ya kalleta sai Mum, wasu zafafan hawaye ne suka zubowa karime tace "nima ki yafemin Hajiya na fita daga wannan azabtarwar, ki tambayi Fatima zata fad'a miki komai wallahi ba ni na kasheshi ba".


Mum bata bi ta kanta ba ta musu sallama domin Abbu ya addabeta da missed calls tace "jibi za'ayi uku banaso case d'innan ya kai ranar ba'a shigar dashi kotu ba".


"Hajiya karki damu za'ayi duk abinda ya dace". DPO d'in ya furta kamar zai mata ruku'u saboda yanda ya dur'kusa. Kallon Ahmad tayi tace "muje mota ka kar'bo muku sa'ko ko?"


Babu musu ya bita a baya yana takaicin rayuwar da yakeyi, ya za'bi kaki saboda martabar dake cikinsa a lokacin da ya za'bi wannan hanyar yana alfahari da kakinsa, saida ya shigo yaga 'kas'kanci yafi yawa a ciki musamman garesu masu 'kananun albashi. Ace da matsayinsa yana bin wata Kar'bar kaya tamkar d'an dako?"


Mota ta bud'e suna isa ta zauna kan kujerar baya sannan tace "Abinda yasa na kiraka na lura duk ka fisu himma ne, DPO d'inku yana 'ko'karin ya 'bata min lokaci ta hanyar tara jama'a ni kuma case d'innan banaso ya fita. Saboda haka nake neman alfarma a wajenka kayi duk yanda zakayi yarinyarnan ta amsa laifinta daga yau zuwa gobe, nikuma nayi maka al'kawarin naira dubu d'ari biyar. Idan har hakan bai samu ba to banaso ta fito daga wannan wajen a raye... aikinku ne ba sai na karanta maka ba. Idan har na samu nasara zan ninka maka abinda na fad'a".


Zare idanu Ahmad yayi jin uban kud'ad'en da hajiyar ta zayyano. Dubu d'ari biyar ai zata iya sakashi yayi arzi'ki. Baiyi wata-wata ba yace "hajiya karki damu babu za'ayi abinda kikeso".


Murmushi tayi tace "ina fatan hakan". Jakarta ta bud'e ta zaro bandir biyu na dubu d'aya ta mi'ka mishi, hannun Ahmad har rawa yakeyi ya Kar'ba tace "wannan naka ne daga ni sai kai zamu san wannan, sai kuma wannan kaje ku raba da 'yan uwanka".


Kasa magana Ahmad yayi saboda ganin kud'in, ji yayi kamar idan ya sakasu a aljihu zasu 'bace, ya jima yana jujjuyasu har saida ta tafi sannan ya zura kud'in aljihu ya koma ciki. A ranar shine mai night duty saboda haka ya 'kudiri niyyar sai ya bud'e bakin karime tayi

magana ko ta wane hali.


Su biyu ne masu night duty d'ayan ya ro'ki alfarmar Ahmad ya ri'ke musu zaije ya dawo yaronsa babu lafiya, yana fita Ahmad ya nufi cell d'in karime ya kirata, kanta a 'kasa ko d'agowa batayi ya fara mata tambayoyi, saidai tamkar yana magana da dutse karime ko motsi batayi ba balle ta nuna ta san abinda yakeyi.


Ta 'bangaren karime kuwa 'ko'kari take ta d'ago kanta ta amsa mishi tambayoyinsa amma wuyanta da bakinta ji take sam batada iko dasu, tunda ta farka a yau bakinta ya gaza bud'ewa tayi magana tamkar an sar'ke mata harshe takeji. Wannan dalilin yasa taci d'an banzan duka da safe domin a cewarsu rashin kunya ts yi musu.


A yanzun ma Ahmad fusata yayi ya tafi d'auko abin duka, saidai shesshe'kar kukan da ya jiyo ce ta dakatar dashi. Zama yayi yana maida numfashi tare da shafa aljihunsa yaji kud'in da aka bashi suna nan sai a yanzu ya fara zargi akan 'kudirin Hajiya Amina. Idan har ta yarda kuma tana da hujjoji karime ce ta kashe d'anta meyasa take basu kud'ad'e tana kuma so a gaggauta shiga kotu? Yana da tabbacin babu wanda bata siye ba a station d'insu dalilin wannan yarinyar, meyasa suka biye mata take neman jefasu matsala? A 'ka'ida mutum baya wuce 24 hours a cell ake kaishi kotu ko yayi confessing ko baiyi ba, amma karime na shirin sake kwana a ciki idan har headquarter taji wannan dukkansu suna cikin matsala.


Zama yayi yana ta sa'ke-sa'ke da tuna wasiyyoyin iyayensa akan adalci da gaskiya da kuma nasihar da Inna ke mishi a kowacce rana wadda bata wuce akn tsoron Allah da ri'ko da gaskiya da 'ko'karin aiwatar da adalci. Anya hanyar da ya d'auko akwai adalci a cikinta?

__________________________

Abbu na zaune da laptop a kan table d'in gabansa yana jiran shigowar Mum, tun yana kallon 'kofa har ya gaji ya maida hankalinsa ga yaransa dake palon cikinsu hammad ne kawai yake walwalarsa, umaima tana takure ta zubawa bango idanu ita kuma zee ta zubawa umaima idanu. Fatima kuwa tunda ta baiwa Abba memory card d'in dake d'auke da videon Abdul da karime ta koma d'aki bata sake fitowa ba. Saida yunwa ta addabeta sannan ta kira cook d'insu a waya tace ya bada abinci a kawo mata yunwa takeji.


Mum na sallama zee da Hammad suka tafi suka rungumeta suna mata oyoyo kafin ta zauna zee tace "mum ba'a gyara mana d'aki ba yau kuma ba'a mana wanki ba Aunty Nadiya tayi mana wanka kafin ta tafi amma bata tambayeni kayan da nakeso na saka ba ta bani ba shine ta saka min wannan".


A gajiya Mum tace "zee dan Allah ki 'kyaleni na gaji wallahi".


Zee tamkar wadda aka kunnawa batir a wurin ta hau ihu da bori Mum sai Abbu ne ya rarrasheta har tayi bacci tamkar 'karamar yarinya, a hannunsa tayi bacci yace da mum "bari na kaita akwai maganar da nakeso muyi dake".


Bata amsa mishi ba ya nufi d'akin su ya kwantar da zee a gadonta da yake kaca-kaca haka ma d'akin nasu kaya ko ina. Itama umaima nata gadon ta nufa da yake gefen na zee tace "Abbu saida safe". 


Murmushi yayi yace "Allah ya tashemu lafiya Allah ya yi miki albarka". Amsawa tayi da Amin ta kwanta. Abbu duk cikin yaransa yafi ji da umaima domin ita kad'ai ce halayenta suka fita daban, addu'a yake mata Allah yasa kar ta d'auko halayen 'yan uwanta da na mahaifiyarta domin halayen Mum na cikin abubuwan da ke zaunar dashi a saudiyya, bai damu da yazo ba saboda duk zuwansa sai anyi d'auki ba dad'i kafin ya koma, har wani tsoronta yakeji a lokuta saboda bala'inta.


Yana komawa parlor yaga bata nan, d'akinshi ya nufa bai sameta ba ya tsfi d'akinta ya ganshi a rufe, baiyi gangancin bugawa ba domin yasan da niyya ta rufe. 'Dakinsa ya nufa ya bud'e wayarsa ya tura mata videon da Fatima ta bashi da wasu videos uku da ya gani a ciki wanda ita kanta Fatima bata san suna ciki ba tunaninta ta gogesu duka. 


Minti talatin da tura videon yaga kiran Mum ya shiga wayarsa, danne wayar yayi ya sakata a silent ya bud'e system d'insa yana amsa gaisuwar abokanan aikinsa. Yana jin vibration na wayarsa amma sam ya'ki kulawa ya cigaba da harkokinsa. Bugun 'kofa yaji nan ma baiyi yun'kurin amsa mata ba domin shi bai shirya bala'inta ba. Idan har zata cigaba da wannan halin tabbas zamansa ba zaiyi tsayi ba zai koma saudiyya.


Bugun da Mum keyi ne ya fara yawa Abbu a dole ya tashi ya bud'e 'kofar d'akin. Yana bud'ewa Mum ta fad'a d'akin a kife domin a jikin 'kofar take jingine. Tsugunawa yayi yace "sannu". Tareda kamo hannunta ya taimaka mata ta tashi.


Wayarta da ta fad'i a 'kasa ta d'auka hannunta na rawa tace "menene wannan ka turo Abbu? Me wannan videos d'in ke nufi?"


"Ummu fad'ima bazan iya fad'a miki komai ba domin nima banida masaniya a kansu, ki tambayi fatima".


Girgiza kai Mum tayi tace "kar ka saka 'yata a cikin wannan abin, ka fad'i inda ka samosu da dalilinka na turomin su. Abbu idan har kayi hakan ne saboda na janye wannan 'karar to ka sani kayi a banza domin iyakar na farko na bud'e. Abinda Abdul ya aikata yana raye ya riga da ya wuce meyasa zaka turo min a wannan yanayin da nake ciki tamkar ba jininka bane shi? Naima mishi gafara ya kamata kayi ba yad'a laifinsa ba wallahi ka bani kunya".


"Baki bud'e sauran videos d'in ba kenan Amina amma kikazo kina fad'a min wannan maganganun? Videon da na turo miki na 'karshe shine zai amsa tambayar da kike ta zaryar neman amsarta. Video ne da ya nuna yanda Abdul ya mutu. Ki zauna ki kalla sai kiyi tunanin hukuncin da za'a ma yarinyarnan wacce irin matsala zai haifarwa Abdul a rayuwarsa ta cikin 'kabari".


Tamkar wadda aka zarewa laka Mum ta zauna bakin gado 'kirjinta na wani irin bugu Abba ya bud'e system d'insa ya kunna mata videon ta fara gani, hawaye ke bin idanunta a lokacin da ta gama kallo kuwa kuka take sosai tana fad'in "Allah ya yafe maka Abdul, Allah ya yafe maka. Ya Allah ka yiwa Abdul rahma ka Kar'bi addu'o'inmu ka sassauta mishi ya Allah. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...".


Rarrashinta Abbu yake saidai hawaye sun kasa dena tsiyaya daga idanunta, kallon Abbu tayi da rinannun idanuwanta tace "Abbu kana nufin kasan da wannan tun jiya? Idan har kana sane da wannan ina ka sameshi? Wannan ne dalilin da yasa kace kar na d'aga case d'in?"


Ba tareda da ya kalleta ba yace "ya mutu a cikin yanayin da fad'arsa baida amfani Ummu fad'ima. Dan Allah ko dan samun nutsuwar yaronnan ki rufe wannan case d'in matu'kar kika kaishi kotu wallahi mune zamu ji kunya. The moment ta bud'e baki tace ga abubuwan dake faruwa ko da itace ta kasheshi za'ayi ruling hakan a matsayin self defence ne babu wani tsatssauran hukunci a kanta domin tanada damae kare kanta. Idan mukayi rashin sa'a ma sai mun biyata tara. Amma idan kinga zakiyi hakan kiyi kamar yanda kika fad'a banida iko akan yaranki".


Free page


Littafina na kud'i ne 500 kacal🥰🥰ku nuna min solidarity ni kuma zanyi 'ko'kari na baku abinda zu'katanku suke so😁😁


Account details

0472624453

Musa maryam Aminu

Gtbank


Ki a tuntu'beni ta wannan number

***