A CIKIN DUHU

12

by @kitty

A CIKIN DUHU...

Kitty💕

Wattpad @ Mssmeemah


12


Fita Mum tayi ta nufi d’akin Fatima hankali a tashi domin ta tambayeta abubuwan da ta sani tsakanin Abdul da Karime saidai ta sameta tayi bacci. Jiki na rawa ta fita ta d’auki wayarta ta kira DPO saidai ta kasa samunshi. Haka ta kwana bata runtsa ba videon da ta gani yana yawo a cikin kanta, runtse idanu takeyi saboda kawai ta kawar da hotunan saidai sun gaza fita. Hango karime take yanda ta fita hayyacinta duk a dalilin son zuciya irin. Meyasa bata fara zama ta tilastawa karime ta fad’a mata gaskiya ba? Meyasa bata bi shawarar Abbu da Fatima ba? Da irin wad’annan tambayoyin ta kwanta har bacci ‘barawo yayi awon gaba da ita.


Kiran sallar asuba ne ya tasheta tana tashi ta rarumi wayarta ta kira DPO tayi sa’a kuwa ya shiga, yana d’aga wayar ba tareda gaisuwa ba tace “Inaso na rufe case d’in da na kawo a yau d’innan”.


Mamaki DPO yayi yace “Hajiya ai ba’a rufe case hakanan sai mun duba munga babu wasu evidence a kai, kuma case ne na kisan kai kinga
” dakatar dashi tayi tace “maganar kisan kai ta ‘kare likitoci sun sanar mana mutuwa yayi from natural cause kuma babu alamun yarinyarnan ce ta kasheshi. Saboda haka a saketa kawai a rufe case d’innan ko nawa ne zan biya”.


“To Hajiya mun riga mun shigar dashi fa amma ba za’a rasa abin yi ba gobe ki kawo evidence na natural cause of death d’in mu saka a ciki sai a rufe case d’in”.


“Duk abinda kace za’ayi amma dan Allah a sallami yarinyarnan kar ta sake kwana a cikin wannan cell d’in tunda ita ba mai laifi bace”.


“Idan kikazo da safen duk abinda ya kamata za’ayi”. DPO ya fad’a tareda katse wayar, sallah mum ta tashi tayi ta d’auki lokaci mai tsayi tana ro’kawa Abdulyassar gafarar ubangijinsa har saida gari ya fara haske sannan ta tashi ta fita, bata damu da mutanen da zasu zo ba hankalinta yana kan d’auke nauyin karime daga wuyan Abdulyassar ta kuma nemi gafararta ko ya samu sassauci.


Abbu ta samu da umaima a parlor yana koya mata karatun ‘kur’ani tace “ Abbu zanje a rufe case d’innan”.


“To Allah ya taimaka, kin d’auki isassun kud’ad’e?” Amsa mishi tayi da eh ta fice cikin sauri. Binta yayi da idanu har ta fice sannan ya cigaba da biyawa umamima karatunta.

__________________________

Tashin karime daga bacci yayi daidai da shigowar Mum cikin station d’in. Wani irin tsoro ne ya ziyarci karime domin duk lokacin da Mum tazo azabar da take ciki tana sake ninkuwa. A yanzu ta sake tabbatar da d’an sanda abun tsoro ne domin basu da imani.


Jikinta duka tsami yake mata yayin da ciwukan jikinta wasu suka fara fidda ruwa, rigarta ma daud’a take sanyawa tana goge wasu ciwukan saboda yanda suke fidda ruwa marar kyau. Hannunta ta d’aga domin ta ‘kulle gashin kanta saidai azabar da taji a dantsen hannunta ya saka ta sauke.


Fitsari ta fara ji wanda ya sanya hawaye gangarowa fuskarta, ta tsani yin fitsari a wannan wurin saidai babu yanda zatayi, ko dai ta matsa ta tsuguna suna kallonta tayi ko kuma ta ha’kura tayi a jikinta wanda wannan ba mai yiwuwa bane.


Runtse idanunta tayi tareda gyaran murya saidai har yanzu muryarta bata fita. A zuciyarta tayi addu’ar neman ku’buta sannan ta koma ta takure domin a yanzu ko ruwan tsarki babu cikin cell d’in. Batul sallah kuwa saidai ta kalli gabas a yanda take tayi domin sun’ki bata hularta ta sanya.


Duk abubuwan da takeyi idanun mum na kanta har DPO yazo suka shiga office d’insa. Nan ma sun d’auki tsawon awa guda domin dagewa yayi sai an kawo evidence ‘kwa’kkwara wanda zai nuna tabbas ba karime ce ta kashe abdul ba. Abbu ta kira yaje wurin doctor da kansa ya kar’bo takardar da aka buga na possible cause of death likita yayi signing ya baiwa Abbu shi kuma kai tsaye ya mi’ka takardar station. 


Tambayoyin tuhuma DPO ke musu suna ‘ko’karin kaucewa saida ta bada kud’ad’e masu yawa sannan ta samu shawo kansa ya amince zai rufe case d’in. Saida ya amince sannan Mum ta samu nutsuwa ta fara hammar baccin da ta rasa na daren jiya. Kallonta Abbu yayi yace “ummu fad’ima ki koma gida ki samu bacci ni zan ‘karasa abubuwan da suka kamata”.


Shima DPO d’in ya amince saboda gajiyar da ya gani ‘karara a fuskarta ya bata wurin da zatayi signing ta tafi ta barshi da Abbu. 


“Anya alhaji ba kaine ka janye ra’ayinta lokaci guda ta janye caae d’innan ba?” DPO ya tambaya yana kallon Abbu, Abbu bai tanka mishi ba ya cigaba da yiwa Abbu tambayoyi a lallai sai ya ‘kureshi daga ‘karshe Abbu yace “DPO yaronnan d’ana ne, duk abinda nayi ba abinda ya shafeka bane idan ka cigaba da tuhuma ta zaka jika a gaba domin kaine abun tuhuma a yanzu. Kayi belin yarinya ka rufe case kawai idan ba zakayi ba da kaina zan d’aukaka case d’in muga ni da kai waye zai shiga problem”.


Ganin Abbu ya mishi jan ido yasa ya hanzarta yayi closing case d’in ya kira d’aya daga cikin ‘yan sandan dake wurin yace “wannan yarinyar da ke cell d’in mata ku sallameta anyi closing case d’in”.


Sara mishi dan sandan yayi ya fita ya bud’e karime. Yana bud’e ‘kofar ta razana ta ja baya tamkar zata shige bangon cell d’in, ransa a murtuke yace “fito”.


Tashi karime tayi da ‘kyar ta iya tafiya ta fito daga cell d’in tana dafa bango har ta ‘karasa wurin table d’insu. Abbu ta gani tsaye da DPO tsoronta ya ‘kara yawaita domin tana jin suna maganar kai case d’inta kotu, ko ranar shigarta kotun ne yazo?


Littafi aka bata DPO yace “sa hannu a nan”. Tareda mi’ka mata biri, kallon biron tayi ta kalli DPO ta bud’e baki domin tambayarsa ta yaya zata saka hannun saidai babu kalmar da ta fito, tsawa ya daka mata wadda ta saka ta zube a wurin tare da dafe kanta da hannayenta kuka na ‘kwace mata. Abbu har ya bud’e baki sai kuma yayi shiru. Wancan d’an sandan ne yayi mata bayani yace “biron zaki saka ki rubuta sunanki a nan ko baki iya ba?”


Gyad’a kanta tayi alamun eh yace ta mi’ka yatsanta ya goga mata biron yace ta danna hannun a wajen. Tana saka hannu yace “to shikenan dama ba wani abu kikazo dashi ba a hakanan kika zo saboda haka ga hanya nan ki tafi an sallameki”.


Cak tayi tana kallonsu domin bata aminta da zancensu ba gani take gwadata sukeyi suga ko zata gudu su kasheta saboda haka ta’ki motsawa ko kad’an. “Ko kina son zaman nan d’in ne na bud’e miki ki koma?” Cikin sauri ta girgiza kai yace “to fita mana me kike jira!!”


Da sauri ta fice tana tuntu’be, gaba d’aya ta dibirbirce ta rasa inda zatayi sai yanzu take tsananin nadamar barin ‘kauyensu da tayi. A haka take tafiya tamkar mahaukaciya duk wanda ya wuce sai ya kalleta ya sake kallo wasu cikin tausayawa wasu kallon tuhuma.


Mota ce tayi parking a gabanta taga Abbu ya fito daga ciki, da sauri ta ja baya yace “karki tsorata karima ba wani abu zan miki ba, ki shiga muje asbiti a dubaki”.


Girgiza mishi kai tayi tana sake ja baya yace “zaki fad’i, bazan cutar dake ba karima taimakonki kawai nakeso nayi a duba lafiyarki kiga ciwukan jikinki, daga nan duk inda zakije bazan hanaki ba idan garinku zaki koma ma ni mai taimaka miki ne, dan Allah ki shiga mota mu tafi”.


Bata yarda dashi ba amma ganin batada wani mafita yasa ta shiga motar domin ko gudu zatayi baifi tayi taku uku ba ya kamota. Suna fara tafiya ya d’auki wayarsa ya kira Fatima ring d’aya ta amsa tace “Abbu ya ake ciki? Mum tace an rufe case d’in Karima ko?”


“An rufe Fatima gani ma ga karima zan kaita asbiti ne a dubata inaso ki kawo mata kayan da zata sanya a jikinta ne amma banaso Momynku ta sani”.


“To Abbu zan kawo ba zata sani ba amma gidannan za’a kawota? Abba dan Allah kar ka dawo da ita gidannan ta koma gidansu kawai”.


“Fatima ko ma wacce magana zamuyi idan mun had’u asbiti ko kuma na dawo gida sai muyi for now ki kawo mata kayan da zata zaka zanje abitin doctor Yun
..” bai ‘karasa ya zare ido tareda sakin wayar ganin wata yarinya da yake shirin bugewa a titin, kaucewar da yayi ne ya sanyashi dukan gefen titi motar ta fara wani irin juyi a tsakiyar titi, salati yake yana ‘ko’karin saita motar saidai ya kasa Karime kuwa ihu take iyakar ‘karfinta tana ri’ke da gefen kujerar motar.


Allah ya taimakesu babu wanda suka buge motar ta sake dukan gefen titi sannan ta tsaya. Wani irin haya’ki ne ke fita daga motar karime ta d’ago goshinta na zubda jini ta kalli Abbu, yanayin da ta ganshi ne ya sanya ta firgita domin kansa na kan steering hannunsa d’aya yayi wani irin lan’kwasa ga jini shima dake zuba daga goshinsa. Mutane ta hango suna yowa wajen motar a gigice ta bud’e motar ta fice kafin su ‘karasa ta nufi cikin wani lungu.


Tafiya take tana kuka ‘karfinta na ‘karewa duk wanda ta gani sai ta ro’keshi taimako, bakinta ya bud’e amma lokacin mamakin ma bata da shi saboda yanayin da take ciki. Tayi tafiya mai nisa har mutane sun fara gudunta suna tunanin mahaukaciya ce. Wata dattijuwa ce ta taho karime ta nufeta tana fad’in ta taimaka mata, kallonta matar tayi tana tunanin ko mahaukaciya ce cikin sauri karime tace “wallahi ba mahaukaciya bace ni ki taimaka min dan Allah ni ba macuciya bace”.


Dattijuwar ta tsaya tana tunanin ta yanda zata taimakawa karime ta ciro 200 a ‘karamar jakar hannunta ta baiwa karime tace “ke kuwa baiwar Allah daga ina kike haka?”


“Daga ‘kauye nake banida kowa iyayena da ‘yan uwana duk sun rasu, bansan kowa a nan ba wallahi masu aikatau na biyo bansan ko ina a garinnan ba ki taimaka min”. Tausayin karime ne ya kamata tace “ba taimakonki ne banaso nayi ba baiwar Allah halin zamaninnan nake tsoro, ni kaina taimaka min akeyi muje dai na baki abinda zan iya gidana nan kusa yake sai ki tafi garinku Allah ya kawo miki mafita”.


Tare suka jera suka nufi gidan matar ta bud’e ta shiga karime na daga waje, qirjin matar wani irin bugu yakeyi domin ta tsorata ji take tamkar aljana ce shiyasa ma ta amince ta taimaka mata domin bataso ta kasance aljana kuma tazo ta nufeta da sharri. Idan ta taimaka mata tasan ba lallai ta cutar da ita ba. Kaya ta d’auko set guda da hijabi ta fito ta dan’kawa karime dake dur’kushe a ‘kofar gidan, Kar’ba karime tayi tana godiya daidai lokacin da Ahmad ya nufo gidan yana ‘kara sauri ganin innarsa da wata yarinya a waje wadda yake kyautata zaton Karima ce ta police station d’insu.


Tun kafin ya iso karime ta firgita tana shirin guduwa dukda ba uniform ne a jikinsa ba amma jikinta gaba d’aya ya d’auki rawa saboda tsananin tsoro. Ri’ke karime yayi dake shirin guduwa yace “Inna me wannan takeyi anan?”


Inna itama ta tsorata ganin yanda karime ke neman guduwa zarginta ya tabbata yarinyar macuciya ce tazo ta cutar da ita, bakinta na rawa tace “wallahi Ahmad a hanya na ganta a wannan yanayin tace na taimaka mata shine nazo na bata kaya da kud’i. Ka santa ne?”


“Inna itace fa nake gaya miki an kawo ta ta kashe d’an gidan da take aiki. Yau aka ce za’a kai case d’insu kotu inada tabbacin gudowa tayi”.


Cikin sauri karime tace “wallahi ba guduwa nayi ba ka tambayesu sakina sukayi har aka ce na dangwala hannu”. Yana ri’ke da gefen rigarta ya d’auko wayarsa ya kira abokin aikinsa domin shi bai shiga ba yana off ranar aka sanar mishi an rufe case d’inta an bada belinta. Maida wayar Aljihu yayi ya saketa yace “ ‘bacemin da gani!! Idan na sake ganin ‘kafarki a hanyarnan sai na karairaya ki”.


A razane ta matsa da shirin barin gurin Inna tace “A’a dakata guduwar tayi shine kaima zaka barta ta tafi?” Girgiza kai yayi yace “Inna rabu da ita ba guduwa tayi ba an rufe case d’in ne sun gano ba itace ta kasheshi ba aka sallameta. Mu shiga daga ciki ta tafi ko ma ina zataje ko ta koma garinsu domin mutane ba abin yarda bane, ruwa baya tsami banza”.


Free page


Littafina na kud'i ne 500 kacalđŸ„°đŸ„°ku nuna min solidarity ni kuma zanyi 'ko'kari na baku abinda zu'katanku suke so😁😁


Akwai VIP 700 ga wad’anda basu son jira😉😉 3 pages ta private a kullum insha Allah.


Account details

0472624453

Musa maryam Aminu

Gtbank


Ki a tuntu'beni ta wannan number

***