A CIKIN DUHU

13

by @kitty

A CIKIN DUHU

Kitty💕

Wattpad @mssmeemah


13


“A’a Ahmad kar kace haka, ni nayi zaton ma ba mutum bace shiyasa nake d’ari d’ari da ita amma mu taimaka mata sai muma Allah ya taimakemu ta hanyar da bamuyi zato ba. Tace bata da kowa idan ta tafi ka san ina zata nufa? Wasu irin mutane zata had’u dasu?”


“Inna ki barta itama baki san wacce irin mutum bace. Yarinyar da zargin kisa ke kanta kika san idan ta zauna dake me zata miko? Zata iya cutar dake ko ta miki sata ko makamancin haka. Inna mutum fa mugun icce ne”. Ya ‘kare maganar yana kallon karime da tayi nesa dasu tana rufa hijabin da Inna ta bata a jikinta, tabbas a baya ya tausayawa yarinyar amma a yanzu bazai bari Inna tayi gangancin da zai janyo musu matsala ba. Alamomin tambaya ne birjik a kan yarinyar bazai bari wata ala’ka ta ‘kullu tsakaninta da Innarsa ba.


“Da ba’a taimako Ahmad da yanzu nima ina garari a tituna ina yawo ko kuma na fad’a harkar banza. Fatauci muka taho da kakanka a hanya Allah ya d’auki ransa ni kad’ai na ‘karaso gari da tsohon ciki, cikin ikon Allah da taimakon mutane na samu matsuguni gidan wani bawan Allah har na haifi mahaifinka a cikon gidan aka bashi auren mahaifiyarka kana sane duk da wannan. Da ace ba’a taimako har na haifeshi? Har ya samu yayi auren mutunci? Halayenmu na wannan zamanin sune ke janyo mutanen cikinsa ke lalacewa. Idan baka taimakawa mutum ba lokacin da abu zai sameshi ba shi kad’ai zai shafa ba harda kai, maganar mutum mugun icce bata da wani tushe a nan domin daga mai taimakon har wanda za’a taimakawa ba ababen yarda bane”.


Ahmad yasan ya da kakarsa babu riba hakan yasa ya ja numfashi yana kallon hanyar da karime tayi domin har tayi kwana tayi nesa dasu kasancewar unguwar cikin gari ce, ganin baya hangota yasa yace “tunda dai ta tafi maganarnan a barta kawai”.


“Ahmad yarinyarnan fa babu inda zataje zan d’auketa na taimaka mata har Allah ya kawo lokacin da zata koma garinsu komai dad’ewar lokacin kuwa. Kwanaki nawa ne suka rage min a duniya? Sai kaga ta yiwu sanadiyyar taimakon ta na shiga aljanna”. Tana ‘kare maganar tabi bayan karime cikin sauri Ahmad kuwa dafe kansa yayi yace “idan baki shiga aljanna ba kya shiga hankalinki”.


Inna tayi sa’a karime batayi nisa ba saboda yanayin jikinta, daga nesa Inna ta kirata tace “baiwar Allah ke yarinyarnan tsaya”.


Tsayawa karime tayi Inna cikin sakin fuska tace “muje na taimaka miki domin Allah kinji yarinya? Amma kar ki cutar dani dalilin taimakonki”.


Wani dad’i ne ya mamaye zuciyar karime tace “bazan cutar dake ba insha Allahu. Ni ba macuciya bace bansan
” inna bata bari ta ‘karasa ba tace “nasani yanzu muje gidana”.


Juyawa sukayi suka fara tafiya saida suka isa gidan sannan karime ta fara wani irin haki na gajiya ga ciwukan jikinta duk sun fara tsami bansa wad’anda tuni sun fara fidda ruwa. Suna sallama Ahmad ya amsa saidai bai shigo ba goggo ta nufi d’akinsa tace “akwai kud’i ne hannunka zan kaita kemis”.


Dubu biyu ya zaro ya bata ba tareda yace komai ba ta fita tareda kiran karime suka fita suka tafi kemis. Mai kemis d’in ya shawarcesu suje asbiti saboda yanayin ciwukan karime Inna tace “kai yaro mun fa san magungunan da suka fi naku amfani rashin saiwoyi a kusa ne yasa na kawota. Kayi abinda zaka iya ragowar sai muyi a gida amma babu asbitin da zani a ‘bata min lokaci a banza”.


“Baaba ai ba wai batun ‘bata lokaci bane kinga ciwukan sun fara zama infected sannan bamu da cikakkun kayan aikin da zan iya mata abinda ya dace”. Ya ‘kare maganar yana duba ciwukan hannun karime domin shi kad’ai ne a bayyane sai fuskarta.


“Kai yaro shi imfish d’in ba zaka iya cirewa ba kenan? Banda tsurfa da zamaninnan naku a lokacinmu garin magani zan bad’eta dashi kan gari ya waye ta warke. Mukayi maganin ‘konuwa ma balle imfish? Ka mata abinda zaka iya na tafi gida”.


Bayani ya sake ma Inna a lallai fa sai sunje asbiti domin kayan aikinsa na ‘kananun ciwuka ne sannan a wannan lokacin ma ba a gashe suke ba zai iya ‘kara mata imfish (infection). Haka nan inna ta kwasheta suka koma gida tana ta mita har suka isa. Sabuwar mita ta d’ora ganin Ahmad baya nan ta had’a wuta ta d’aura ruwan zafi.


Karime na gefe a zaune tana binta da kallo lokaci-lokaci idanunta na rufewa saidai tsoron abinda zai faru idan tayi bacci ne ya hanata sakewa tayi bacci. Bin Inna takeyi da idanu tana ta kai kawo bayan ta had’a wutar ta fara shirin abinci.


Suna zaune Ahmad ya shigo ni’ki ni’ki da buhun shinkafa ya ajiye ba tareda yace komai ba ya sake fita ya shigo da cartons na taliya da macaroni da masara, gero, alkama, da garin semo. Inna tsayawa tayi da aikin da takeyi tana kallonsa yana shige da fice bayan ya dire kayan ya sake fita ya shigo da kayan miya da kifi mai yawa sosai.


Inna a tsorace take tace “kai lafiya ina ka samo wad’annan?” Karime ya kalla yace “wasu kud’ad’e na samu ne Inna. Idan akwai wani abu da babu anan sai ki fad’a min”.


Eh kaman ka manta da mai. Amma Ahmad wani irin kud’i ka samu haka a tsakiyar watannan? Ko albashi aka maka nasan bazai kai ya siya mana wannan kayan ba kaji tsoron Allah ka fad’a min ina ka samo”.


Had’e ransa yayi yace “inna ki dena tuhumata gaban yarinyarnan sai ta rainani. Ba wurin wani na ‘kwata ba bani akayi bashi zan biya a hankali”. Inna dai bata amince dashi ba ta amsa mishi da to sannan tace “yauwa zaka rakani asbiti da kayanka na ‘yan sanda zan kai yarinyarnan a dubata munje kemis yace wai bazai iya ba ta kamu da imfish. Ni bansan imfish d’in bane da na kira ‘kauye wani ya kawo min maganinsa”.


Amsawa yayi da toh sannan ya fita ya sayo sauran abubuwan da ake bu’kata zuciyarsa fes babu wani tsoro. Tunda Mum ta bashi kud’ad’ennan ya rasa sukuni a kansu amma a yau da yaga an saki karime ya yanke shawarar kashesu tas idan ma ta dawo tace ya maida mata abinta yasan yaci rabonsa kuma babu yanda ta iya dashi. Tsoronsa ta fad’a ma DPO yasan DPO ya fishi son zuciya had’esu zaiyi ya cinye ya bashi dubu goma ko ashirin. Amma a yanzu ya za’bi duk hukuncin da zai biyo baya matu’kar yaci kud’ad’en.

__________________________

“Abbu!!! Wayyo Allah mun shiga uku Abbu!!!” Fatima tayi ta maimaitawa a cikin wayar domin tana jin ‘karan da wayar keyi da salatin Abbu tareda ihun karime. Da gudu ta fita daga d’akinta tana ‘kwalawa mum kira ga gida fal mutane kowa yayi cirko cirko ana jiran me zata ce.


Mum na bacci taji kiran yayi yawa ta fito tace “Fatima lafiya”. Kuka fatima ta saki tace “Mum Abbu yayi accident”. Tana fad’a sukaji sallama cikin wayar fatima domin a hands free take. Mum ce ta Kar’bi wayar wani saurayi yace “Mai wayar ne yayi hatsari muka ga wannan lambar na kai ana kira, yanzu haka an tafi dashi asbitin murtala emergency”. Yana gama maganar ya kashe wayar gaba d’aya.


Zubewa mum tayi a wajen ta dafe ‘kirjinta tana ambaton Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Fatima kuwa kuka kawai takeyi ana rarrashinta. Zee da umaima ganin fatima na kuka ga Mum itama ta fara hawaye yasa suma suka ce bari su tayasu suka zauna gefen mum suna kuka. Hammad kuwa cinyarta ya hau ya kwanta a ‘kirjinta yayi luf yana kallonsu”.


Lumshe idanu mum tayi taja dogon numfashi sannan tace “Fatima tashi ki shirya mu tafi asbitin”. Kallon ‘kanwarta tayi tace “Aisha ki zauna da su umaima a sallami kowa zamannan baida amfani”. Amsawa Aishan tayi da to ta d’auki hammad a hannunta taje ta samu ‘yan manyan dake gidan ta sanar musu zama fa ya tashi mai gida yayi accident. Nan dai masu kukan gaske da na munafurci suka fara aiki yarda masu cewa zasu bita asbiti. Cin magani mum tayi saida ta tabbatar an fara tafiya sannan taje waje suma ta sanar musu. Dake maza ne da kansu suka watse aka cire rumfa.


Suna isa emergency mum ta fad’i sunan Abbu zuciyarta na wani irin bugu, amince mata akayi ta shiga ta sameshi kan gado an nad’e mishi kai da bandage ga hannunsa da kwali an ma’kale hannun a wuyansa. wuyansa ma a nad’e, hawaye ne suka zubo mata tace “Allah ya baka lafiya Abbu”.


Fatima na daga waje da ‘kyar suka bari ta shiga itama tana ganinsa sai kuka amma ta danne kukan ta mishi addu’a. Muryar fatima da yaji ce ta sanya ya bud’e idanunsa yana waige waige yace “karima
”. Cak mum ta tsaya ta kalli fatima da itama ta zare idanu cikin mamaki. Muryarta na rawa tace “Abba karima ta mutu ne?”


“Ban sani ba fatima ki duba min cikin wajennan kiga tana nan?” Takaici ne fal zuciyar Mum tace “buguwar kai ta saka ka ta’bu ne Abbu wacce karime kuma?” Bai amsa mata ba fatima ta fita tana ta dube-dube babu alamun karime ta dawo ta fad’a mishi, nimfashi ya sauke tareda dafe kansa dake azabar ciwo lokacin da likita ya shigo.


Gaisawa sukayi da mum yace “gaskiya ya samu buguwar kai sosai sai an mishi hoto sannan hannunsa na dama ya karye zamu maidaku theater yanzu za’a mishi aiki. Ciwon wuyansa ba mai tsanani bane alhamdulillah an auna arzi’ki”.


Hamdala Mum da Fatima sukayi kafin likitan ya fita Abbu yace “Doctor akwai wata yarinya dake cikin motar an kawota ne itama?”


“Banida masaniya gaskiya domin ba mune muke Kar’bar mutanen ba”. Yana fad’in haka ya fita. Mum bata tanka mishi ba dukda tambayoyin dake zuciyarta har aka zo aka d’aurashi kan wani gado aka nufi theater dashi. Suna zuwa Mum ta kira doctor yunusa ta sanar mishi abinda ke faruwa cikin mintina kad’an sai gashi a asbitin, shi ya shige musu gaba cikin ‘kan’kanin lokaci aka mishi hoton hannun da kuma gyaran karaya sannan suka tafi hoton kai. Hoton ya nuna babu wata matsala suka nemi amenity ward aka basu.


Suna Amenity ne jama’a ‘yan dubiya suka fara zuwa ‘yan uwan Abbu da abokanansa saidai duk wanda yazo baya samun shiga Abbu yana bacci. Abinci aka kawo musu kala daban-daban sai can dare sannan aka kawo su Umaima su ganshi a lokacin ciwon kansa ya lafa sosai.


‘Dagashi akayi ya zauna umaima da zee suka haye gadon suna cin abinci suna bashi harda fad’ansu kan wanda yafi bayarwa. Ganin suna ta raharsu hnkali kwance yasa mum ta ja Fatima waje tace “Fatima kai tsaye fad’a min me ya faru”.


“Mum muna waya da Abbu yace zai kai karime asbiti ayi treating d’inta sannan ya sakata a hanyar garinsu ta tafi. Yace na kai mishi kayan da zasu ma karime asbitin dr yunusa kawai naji motar ta fara ‘kara sai kiran da mukaji tare”.


Wani kallon Mum ke yiwa Fatima tace “kuma kina fad’a min ko a jikinki ko? Fatima what is wrong with you? Idan yarinyarnan ba ita ta kashe Abdul ba itace sanadiyyar mutuwarsa amma shine har Abbu ya d’auketa a motarsa zai kaita asbiti kuma kike ganin hakan abin cancanta ne ko? Fatima ki sani a ranar da Abbu ya kawo yarinyarnan gidana a matsayin kishiya zamana dashi daku ya ‘kare har Abada”.


“Mum Abbu ba son karime yake ba taimakonta kawai zaiyi”. Fatima ta furta kanta a ‘kasa. Murmushi Mum tayi tace “wani irin taimako ne zai saka ya sallameni daga police station saboda kawai ya d’aukota a motarsa? Taimako ne ya sanya ya ambaceta kalmarsa ta farko bayan ya farfado daga accident? Gani gaki a gabansa wa ya kira a cikinmu fatima? Ke yarinya ce Fatima ba lallai ki fahimta ba amma na lura bayansa kike goyo so ki cigaba. Idan kika rasani akan ‘kazamar ‘yar aiki zaki fahimci abinda nake fad’a miki”.


Free page


Littafina na kud'i ne 500 kacalđŸ„°đŸ„°ku nuna min solidarity ni kuma zanyi 'ko'kari na baku abinda zu'katanku suke so😁😁


Akwai VIP 700 ga wad’anda ba zasu iya jira ba, 3 pages a kullum😌😌


Account details

0472624453

Musa maryam Aminu

Gtbank


Ki a tuntu'beni ta wannan number

***