A CIKIN DUHU

14

by @kitty

A CIKIN DUHU

Kitty💕

Wattpad @mssmeemah


14


Jikin karime ya sha wankin ciwo tun tana cije baki har saida dauriyarta ta 'kare ta fara kuka, sosai nurse d'in ke bata kulawa inna na gefe na mata sannu. Anyi mata d'inki a goshi da biyu a hannu sai bayanta da akayi dressing aka ce kar ta bari ruwa ya dinga ta'bawa. Godiya sosai Inna ta musu sannan suka tafi gida Ahmad yana ajiyesu ya nufi station d'insu domin jin yanda ta kaya har aka sallami karime. Yana zuwa ne aka sanar mishi Abbu yayi accident a hanya bayan tafiyarsa. Ganin babu wanda ya tuhumeshi maganar kud'i ya sanya ya tattara 'kafafuwansa ya koma gida.


A tsakar gida ya tadda inna yana rafka sallama ta dur'kusa tana gogewa karime jikinta, d'auke kansa yayi ganin karime d'aurin 'kirji ne kawai a jikinta shima bayanta a bud'e inna na goge mata bayan. 


"Ni ko karimatu tunda zama ya kama tsakaninmu ki fad'a min ina iyayenki suke? Idan babu su ina 'yan uwanki na uwa ko na uba?"


Sunkuyar da kai karime tayi tace "Mahaifina ya rasu shekaru biyar da suka wuce mahaifiyata kuma mutuwarta ce ta fito dani garinmu na taho nan. Banida wasu 'yan uwa duk yayyena da 'kanne idan aka haifesu basa zama".


"Allahu akbar Allah ya ji'kansu baki d'aya. To 'yan uwa fa na uwa ko na uba?"


"Bansan 'yan uwa Baaba ba saboda asalinta ba 'yar garinnan bace kuma bata ta'ba fad'amin garinsu ba. Baba kuma 'yan uwansa sun hanemu zuwa garesu a lokacin da ya rasu suka yanke duk wata ala'ka damu".


"Meyasa?" Inna ta tambaya tana gyara zanin karime tareda zama a kujerar dake gaban karime ta fara goge mata 'kafafunta. Sosai karime ke jin dad'in jikinta saboda rabonta da wanka kwana biyu kenan. Dattin dake fita a jikinta kuwa har kunya take ji. Kafin ta amsawa Inna Ahmad ya fito daga d'aki yana tambayar inna abincinsa, hamdala karime tayi domin batayi shirin barin gidannan ba tana da tabbacin suka ci duhun dake lullu'be da rayuwarta tabbas sai sun koreta.


Shige da fice ya fara na d'aukan cokali da kopi da faranti wanda yasa inna ta tattara karime suka koma d'aki. Suna shiga inna ta cigaba da tambayarta tace "banaso dai nayi shisshigi amma mai ya faru tsakanin Mahaifiyarki da dangin mahaifinki da har kika za'bi ki shigo garin da baki san kowa a cikinsa ba kiyi rayuwarsa 'kas'kamci ta aikatau a kan kije ga dangin mahaifinki?"


Sunkuyar da kai karime tayi inna tace "karki damu ba sai kin fad'a min komai ba amma da ace nice zan nufesu ne domin ance naka naka ne ko d'an iska ne sannan laifin wani baya shafar wani ta yiwu da kinje garesu sanadiyyar maraicinki zasu ri'ke ki amma karime zaman wannan garin ba naki bane. Zan ri'ke ki har Allah ya baki lafiya sai muje 'kauyen naku tare na dan'ka musu ke wani 'kauye ne?"


"Tamaru". Karime ta furta tana jin ranta babu dad'i domin har ga Allah bata tunanin akwai ranar da zata koma 'kauyen mahaifinta. Ba 'karamin duka tasha a hannunsu ba lokacin da taje sanarwar mutuwarsa kuma ba wannan lokacin kawai ba indai zata je to da 'kyar take 'kwatar kanta ta dawo gida tun tana 'karama. Ko tare da baba suka je haka za'a yita zungurarta wasu a 'boye wasu ma a gaban idanunsa har ya dena zuwa da ita.


"Ni da kaina zan d'auke ki muje can naji ta bakinsi, rayuwarki zata fi inganta idan har akwai wani naki amma a nan ko aure zakiyi karime zaiyi wahala ki samu nutsuwa a cikinsa".


Karime dai bata sake cewa komai ba har aka gama gyara mata jikinta ta saka kayan inna, ba wani yawa suka mata ba domin itama inna 'karamin jiki gareta domin karime ma ta fita tsayi.

__________________________

HAUWA'U (TAISHU)


Bayan tafiyar karime kasuwa ne Baaba ta shiga gyaran gidan domin su samu wurin da zasu zauna. Kayayyakinsu ta ciro ta had'a ruwa ta fara wankewa tana tunanin rayuwar kad'aicin da zasu shiga saboda rashin Habu, da ace yana raye da yanzu yazo ya tsuguna yana damunta sai ya wanke shima tana korarsa yana 'ki har sai ta gaji ta bashi d'ankwali. Da Habu yana raye yanzu yana nan yana kukan karime bata je dashi kasuwa ba har sai baaba ta nemi abinda zata d'aura masa talla ko aiken da zata mishi tukuna ta samu sukuni, da ace yana raye...


Hawayen da taji a fuskarta ne ya katse mata tunanin da take ta goge hannunta jikin zaninta ta share hawayenta tareda fyace hancinta, sanyin da suka kwasa a jiya ya sanya zazza'bi ya rufe ta ga mura dake neman dam'karta saidai ba zatayi gangancin kwanciya a wannan yanayin ba, tasan matu'kar ta kwanta karime ma zata iya kwanciya ciwo.


Tunawa tayi da labarin da mahaifinta agalher, a lokacin cikin yarensu na buzaye ya dafa kanta cikin murmushi yace "Taishu ke d'in ta daban ce, ina ganin wani haske mai girma a tattare dake wanda ban ta'ba ganinsa a jikin wani mutumin timiya ba amma bansan dalilin da yasa mutane suke ganin duhu a zagaye dake ba, taishu da inada iko da na yaye mayafin sirrin dake lullu'be da rayuwarki amma Allah bai bani iko ba. Ina fatan na rayu naga abinda zaki zama a rayuwa taishu".


A lokacin murmushi taishu (Hauwa'u) tayi tace "na aminta da zancenka domin kai kad'ai kake sona kai kad'ai ne kake ganin haske a gareni Babana, meyasa mutanen gidannan basa sona baba? Me muka yi musu?"


Murmushi kawai yayi yace "taishu ba laifinsu bane, rubutun 'kaddararki ne a haka kuma Allah kad'ai ke da ikon sauya wannan 'kaddarar a lokacin da yaso. Kiyi ha'kuri da duk irin rayuwar da zakiyi amma inaso watarana ki nemi 'yan uwanmu, kije garesu nan ne mafarin komai insha Allahu anan ne komai zai zo 'karshe".


"Inane garinmu Baba? Me zai hana mu koma can?" Girgiza kai agalher yayi yace "Taishu idan muka taka 'kasar garinmu a yanzu daga ni har ke ba zamu rayu ba. Ina fatan zaki koma a lokacin da komai ya lafa ina miki addu'ar su kar'beki a matsayin 'ya. Sunan garinmu timiya yana cikin 'kauyen bagzane a garin agadez cikin nijar, idan kinje ki nemi tanalher ko ki nemi sune 'yan uwanmu zasu kar'beki hannu bibbiyu, karki bayyanawa kowa kanki sai kin samesu".


Watanni kad'an bayan wannan maganar tasu Allah ya d'auki ran Agalher kuma ya mutu bai bar mata komai ba sai wata sar'karsa wadda ita kad'ai ce abinda ke tuna mata da mahaifinta. Kayansa da ya bari Rabi ta 'kona su a lokacin da take ganiyar azabtar da Taishu. Rayuwar da tayi ne a bayan rasuwarsa ta fad'o mata kuka take sosai har wankin ya gagareta. Zama tayi dirshan ta ci kukanta ta gode Allah sannan ta d'auki wankin ta 'karasa tana yanke shawarar komawa timiya. 


Zama tayi tana dogon nazari akan labarin da mahaifinta ya bata na garinsu da sunayen mutanen da yace ta nema saidai banda timiya babu abinda 'kwa'kwalwarta ke tunawa. Cije baki take taka tunanin a cikin wani 'kauye timiyan take a nijar saidai Allah ya mantar da ita komai, nasan timiyan a nijar take amma a 'kar'kashin wani gari? Sunayen mutanen da zata tuntu'ba gaba d'aya ta kasa tunawa.


Wani sabon hawaye ne ya biyo mata fuska ta kalli gari a lokacin ta lura da gari ya fara duhu karime bata dawo ba. Tsoro ne ya ziyarceta tana tunanin ko wani abu ya sami karime? Mayafinta ta d'auka ta le'ko cikin gida saidai wani ihu da taji ne ya ja hankalinta.


Mahaifiyar sani ta hango ta fito ta nufo gidansu a guje tana wani irin ihu kamar mahaukaciya, kafin kace meye wannan mata sun fito daga gidajensu babu ma batun dauko mayafi wasu kuma suna le'ke da d'aurin 'kirji kansu ko d'ankwali babu. Kukan kura matar tayi ta dam'ko wuyan Taishu dake tsaye tana kallonta.


"Wallahi idan kin kashe 'ya'yanki da na wasu kin zauna lafiya ba zaki kashe nawa ki zauna lafiya ba. Tunda yaronnan ya muku magana ya shiga d'aki sai gawarsa a fiddo mini. Ki dawo min da kurwar d'ana Hauwa!!"


Idanun taishu sun kad'a sunyi jajir saboda azabar ma'kara da taji, matan wurin kuwa salati suka kwasa wasu na tafa hannu suna fad'in "sani ne ya mutu?".


Kuka uwar sani ta fashe dashi tana fad'in "kuna tsaye kuna kallonta ta kashe min sani? Idan baku d'auki mataki ba wallahi kurwar mazajenku zata fara lashewa. Sani ya mutu babansa ma yana nan a kwance magashiyyan".


"Kai amma tir da halinki".


"Wannan matar annoba ce zamanta a cikinmu bala'i ne".


"Yanda ta kasheshi a kasheta kawai".


"To kafin dai a kasheta d'in taje ta tsallake baban sanin idan har ya tashi sai mu san abinda zamu mata, idan ba haka ba zamu kasheta ne shima ya bita". Wata mata ta furta tana watsawa taishu kallon 'kas'kanci.


Dukkansu sunyi amanna haka suka ja Taishu tamkar akuya tana tafe suna tankad'a ta har gidan wawo. Suna shiga suka sameshi a tsakar gida kwance yana amai nan fa mata suka hau salati. Tunkud'a hauwa akayi har ta kusan taka shi tayi saurin tsallakeshi.


Tana tsallake mutuminnan amansa ya yawaita. Hankalin matan yayi matu'kar tashi nan fa matarsa ta sake kukan kura ta cakumo Taishu. Taishu kuwa tsananin tashin hankali yasa idanunta sun tsaya 'kyam babu ko d'igon hawaye haka bakinta ta kasa furta komai. Duka aka hau yiwa hauwa har saida suka kaita 'kasa sannan aka fita da ita daga cikin gidan.


Samarin dake kusa da gari duk sun fito ga ba'kin da suka zo jana'izar Sani, an cika ma'kil a 'kofar gidansu sani aka sanar da cewar hauwa (taishu) dai ya tabbata ita ta kashe sani saboda haka kafin a kaishi makwancinsa saidai su tafi tare. Liman da wasu daga cikin ba'kin da suka zo sunyi 'ko'karin lallashin mutanen garin amma sam sun'ki ji. Aka ce sarkin yawa yafi sarkin 'karfi. Wasu 'karfafan mazaje ne sukayi caraf da Taishu suka nufi bayan gari da ita mutane na jifanta ta baya.


Gaba d'aya tayi laushi ta gama sadda'karwa mutuwa zatayi, ri'kon da saurayin yayi mata ne ya sassauta tana yun'kurawa kuwa ta 'kwaci kanta ta kwasa a guje. Allah ya dafa mata ta tsere musu suna jifanta har tayi nisa. Cigaba sukayi da jifanta har wani dutse ya daki bayan kanta ta fad'i a wajen.


Matsawa sukayi d'aya ya kara hannunsa a hancinta yaji babu alamar numfashi ga jinin dake malala daga bayan kanta, kallon juna sukayi sukace "ku barta anan tayi mushe idan har aka binneta tashi zatayi ta dawo ta cigaba da kashe mutane".


Suna komawa gari suka sanar da taishu ta mutu, mutane basu yarda ba har saida wasu suka je suka ganota da kansu nan fa mutanen gari suka dage a lallai sai an 'kona gawar taishu idan ba haka ba zata iya tashi tunda mayya ce. Kawuna ne suka rabu wasu sukace a barta wasu suka ce a 'konata, gari aka koma aka cigaba da tattaunawa akan abinda za'ayi da gawar taishu wasu suka bada shawara a fara kai sani a dawo tukuna. Shawara suka yanke sai dare ya raba tukuna aje a 'kona gawar hauwa domin kar ba'kin dake zuwa garin suji abinda ke wakana, a lokacin da zasu tafi ne yayi daidai da dawowar karime daga kasuwa ta had'u da nata ibtila'in


Taishu tana kwance a wurin a sume har ta d'auki tsawon awanni biyu, farfad'owa tayi da azababben ciwon kai ta fara kalle kalli tana tunanin me ya kawota wannan wurin? Da 'kyar ta tuna janyota da akayi da niyyar kasheta tayi zumbur ta tashi tana tafe tana tangad'i, d'ankwalinta ta saka ta d'aure kanta dake zubda jini ta cigaba da tafiya cikin gonakin mutane tana gudu tana tafiya har Allah ya sanya tayi nesa dasu. Tayi tafiya mai nisa sosai domin har ta shiga wani 'karamin 'kauye na fulani wanda yake fili ne fetal sai bukkoki basu wuce bakwai ba, a lokacin asuba tayi har alfijir ya keto.


"Wacece ke?" Taji magana a bayanta, juyawa taishu tayi cikin dakewar zuciya domin sam bata ji tsoro ba tace "ba'kuwa ce taimako nake nema". Wani matashin saurayi ta gani tsaye da buta a hannunsa yana 'kare mata kallo. Kafin ya bud'e baki wani ya sake bayyana a gefenta yana tambayar wancan cikin harshen fulatanci wacece wannan? Mutum ko aljana? D


Dariya saurayi na farkon yayi yace "mutum ce da alamu wai taimako take nema".


Cikin harshen filatanci na biyun yace "kana da abin taimaka mata ne? Ka rabu da ita ta fita kawai kasan bamu son ba'ko".


Free page


Littafina na kud'i ne 500 kacal🥰🥰ku nuna min solidarity ni kuma zanyi 'ko'kari na baku abinda zu'katanku suke so😁😁


Akwai VIP 700 ga wad'anda ba zasu iya jira ba, 3 pages a kullum😌😌


Account details

0472624453

Musa maryam Aminu

Gtbank


Ki a tuntu'beni ta wannan number

***