A CIKIN DUHU

15

by @kitty

A CIKIN DUHU

Kitty💕

Wattpad @mssmeemah


15


“Dukda bamu son ba’ko amma ka ta’ba ganin wani ya nemi taimakonmu mun hanashi? Tunda har ta ratso shingenmu tabbas batada abin cutarwa a tattare da ita abinda ke wuyanta ne ma ya d’auki hankalina”.


Zuba ma wuyanta idanu sukayi tayi saurin dam’ke sar’karta a hannu, sai a lokacin gajiya ta dirar mata jiri ya kwasheta tayi ‘kasa saidai kafin ta kai ‘kasa sukayi saurin taro ta su biyu. Kwantar da ita sukayi ganin batada wani kata’bus wanda ya fara ganinta ya d’auko wu’ka zai yanke zaren dake ri’ke da sar’kar wuyanta.


“Karku kuskura ku mata komai idan ba haka ba ranku zaiyi mummunan ‘baci”. Wani dattijo ya nufosu cikin sauri yana nunasu da sandarsa, ja baya sukayi suka d’aga hannayensu d’aya yace “Lamid’o ba wani abu zamu mata ba zaren wuyanta zamu cire, shigowa tayi tace tana neman taimako”.


Shima dattijon da aka kira da Lamid’o kallon zaren wuyan nata yayi sannan ya dur’kusa cikin harshen hausa yace “daga ina kike? Me kikeso?”


“Taimako nake nema”. Ta furta tana lumshe idanunta, tura samarin yayi su kira mata cikin ‘kan’kanin lokaci wasu ‘yanmata biyu suka iso, umarni yayi musu da su kama taishu su shiga da ita suka kamata ta tashi suka nufi cikin bukkokin da ita. A kan tabarma aka shimfid’eta, ‘kwala kira yayi yace “dabo jauro!”


Wata dattijuwa ce ta fito da bazata gaza shekaru 45 a duniya ba, cikin biyayya ta dur’kusa kad’an, magana sukayi a hankali ta tashi ta koma ta fito da ‘kwarya da ganye a ciki ta zuba ruwan d’umi ta mi’ka ma Lamid’o.


Ganyen ya cire yace ta d’aga kan Taishu ya danna ganyen a ciwon dake bayan kanta dabo jauro ta d’auko farin d’ankwai ta d’aure ganyen a jikin ciwon sannan aka shafawa taishu ruwan a jikinta, cikin ‘kan’kanin lokaci bacci ya kwasheta saida tayi bacci sannan modibbo yace “ki kula da ita zamu fita”.


Amsa mishi tayi da to ta tashi ta cigaba da aikace-aikacenta na gida har ta d’ora ma yaranta tallan nono suka fice Taishu bata farka ba, lokaci-lokaci ta kan zagayo ta dubata domin ta tabbatar tana numfashi har saida rana ta riski taishu sannan ta farka daga baccin da take. Tashi tayi ta zauna tana kallon harabar gidan. A hankali ta mi’ke tsaye wanda ya sanya dabo jauro nufota da sauri tace “ki zauna karki fad’i”.


Murmushi taishu tayi tace “bana jin komai nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairi ya biya muku bu’katunku”. Juye-juye taishu keyi tana neman lullu’binta Dabo jauro tace “ina zaki?”


“Tafiya zanyi bansan yanayin da ‘yata ke ciki ba”. 


“Na fahimta amma ki zauna ki sake hutawa tukuna. Daga wani gari kike?” 


“Daga tamaru nake, bazan iya zama ba nagode da taimakonku amma dole na koma na bar karime ita kad’ai”. Murmushi dabo jauro tayi tace “ki zauna ki bari modibbo ya dawo daga nan zuwa tamaru akwai ‘yar tafiya kuma hanya babu kyau. Idan suka dawo cikin yaran sai wani ya rakaki a yanayin da kike bazan barki ki tafi ba ko ruwa baki sha ba”.


Dagewa Taishu tayi sai ta tafi itama Dabo jauro ta dage ba zata barta ta tafi ba sai modibbo ya dawo. Tunani taishu tayi taga bai dace ta tafi ba tareda ta ma modibbo godiya ba hakan yasa ta zauna saidai gaba d’aya hankalinta na wajen karime. Meyasa ta gudu bata koma ta d’auko karime ba? Meyasa bata jira ta a hanya ba tayi gaba? Me yake faruwa da karime? Shin tana raye? Ta mutu? Ta tsira? Tana garin ko bata nan? 


Tana wannan tunanin Dabo jauro ta kawo mata tuwo da miyar kuka da man shanu. Sai ruwan d’umi saboda ta d’umama cikinta. Godiya taishu tayi taci abincin sannan ta tashi domin tayi sallah. Cire d’aurin dake kanta Dabo jauro tayi Taishu ta ta’ba inda ciwon yake taji babu alamun jini sannan zafin ciwon ma ya ragu sosai, godiya ta sake ma dabo jauro sannan ta d’aura alwala tayi sallar magrib, isha, da sallar asubahi.


Sai a lokacin ta ‘karewa rugar kallo. Bukkoki ne guda takwas a cikinta sai tsakiyar bukkokin da aka shafe da siminti. Tana bin bukkokin da kallo ne dabo jauro ta dawo ta fara mata bayanin yanda gidan nasu yake.


Bukkar da take kwance a ‘kofarta itace bukkar Dabo jauro, sai ta gefenta kuma ta lamid’o da matarsa wadda taje gida mahaifinta ya rasu, sai ta kusa da ita ta bamanga matarsa amarya ce da tsohon ciki, dukkansu ‘kannen modibbo ne sai kuma bukka d’aya ta ‘ya’yan dabo jauro mata su uku baddo, danejo da Hauwa. Sai bukkar ‘karshe kuma ta bawuro d’a d’aya namiji ga dabo jauro wanda ya rasu shekarar da ta wuce sai kuma band’akinsu dake can gefe guda. Bukkoki biyu dake gefe kuma d’aya ta iyayen modibbo ce da suka tafi ziyara d’ayar kuma ta matar da modibbo zai auro.


Tana zaune a wannan rugar har yamma ta doso, saida duhu ya fara

Shiga sannan modibbo suka dawo daga kiwo shi da yaransa da sauran ‘yan uwansa dake kewayen. Suna shigowa taishu ta tashi tace tafiya zatayi. “Ki bari idan gari ya waye sai ki tafi”. Dabo jauro ta furta ganin yamma ta shiga. Dagewa taishu tayi tace “karime ‘yata tana cikin matsala zasu iya kasheta, ku barni naje na d’aukota na gode da taimakonku da inada abinda zan biyaku dashi zan bayar amma banida komai”.


“Ki fad’a mana menene ke faruwa dake? Waye zai kashe ‘yarki? Idan kikayi mana bayani mu kuma zamu taimaka miki na had’aki da wad’anda zasu rakaki ki d’auko ‘yarki”.


Bayani tayi musu daga mutuwar sani zuwa kasheta da akayi ‘ko’karin yi Modibbo ya umurci yaransa biyu su raka Taishu ta d’auko ‘yarta. Fita sukayi saida sukayi tafiya mai d’an tsayi sannan suka fita titi. Mashina biyu sukayi suka hau d’aya Taishu ta hau d’aya suka nufi tamaru.


Suna zuwa suka ce ta tsaya su shiga su gano meke faruwa. Wurin da samari ke zaune suka nufa sukayi basaja anan sukaji anan hirar karime da ta ‘bace lokacin da akaje kamota har wani yana cewa “nifa na ri’ko hijabinta zan janyota kenan kawai naji kamar an fizgeta babu ita, ai na fad’a muku babu shiri na ja da baya na shafawa kaina lafiya. Kuna gani dai itama gawar Hauwa haka aka nemeta aka rasa. Da alamu ma dai banda maita a lamarin nasu akwai shed’anci ko babban tsafi”.


Sun jima suna jin hirar mutanen wurin sannan suka nufi inda suka bar Taishu (hauwa) suka sanar mata abinda suka jiyo. Kuka sosai tayi ta dage lallai su barta taje ta ganowa idanunta inda karime take suka hanata suka lallasheta suka koma gida.


Saida hauwa ta d’auki tsawon sati biyu a kullum zata fita neman karime ta dawo babu ko labarinta. Wasu lokutan tana sa’a ta shiga tamaru ba tareda an ganta ba har gidan da suka zauna taje ta ganshi an ‘koneshi ‘kurmus.


Wata shiga da tayi tamaru ne ta had’u da ‘yammatan ‘kauyen a hanya, suna ganinta suka tsala ihu suka watse suka koma gari suna shelar sunga kurwar Hauwa. Tun daga ranar aka sanya idanu aga shigowar itama daga lokacin bata sake zuwa tamaru ba. 


Zamanta a rugar su modibbo a d’arare take yinsa a kullum jira take wani mugun abu ya faru su d’aura mata laifi saidai babu abinda ke faruwa a rugar su modibbo sai alkhairi. Taishu ta zama ‘yar gida domin tare suke tatsar nonon shanu ita da dabo jauro har kad’i ta koya mata sannan wasu lokutan ita ke girki a gidan. ‘Dakin amaryar modibbo aka bata domin auren da sauran lokaci.


Suna zaune a bukkar dabo jauro modibbo ya kirata yace yana son magana da ita. Fitowa tayi ta tsaya ya shimfid’a tabarma yace “ ya batun ‘yarki kuwa?”


“Babu labarinta har yanzu domin na zaga sosai ban sameta ba, ina shirin dai naje garinsu mahaifinta na duba ko tana can”.


“Allah ya bayyana ta, dama tambayarki nazo yi saboda zaren dake wuyanki. Zaren ya tabbarmin da maganarki ko dai ‘karya ce ko kuma akwai abinda kike ‘boyewa”.


Kallon sar’kar tayi ta ri’ke kan kan sar’kar da hannun tana mamakin maganar modibbo. Babu wani abu a jikin sar’kar zare ne irin na sa’kin da a jikin sar’kar sai wani abu round tamkar agogo amma ruwan gwal. Cigaba da magana modibbo yayi yace “duk mutumin da zai rataya wannan a wuyansa to tabbas ba ‘karamin mutum bane domin a cikin buzaye ma d’aid’aiku ne ke iya mallakar abinda ke cikin wannan sar’kar. Ki fad’a min dalilin zuwanki garemu me kike nema?”


“Banida wata manufa ta zuwa gareku modibbo face taimakon da na nema. Wannan sar’kar itace abu na ‘karshe da mahaifina ya barmin gado ina rataye da ita ne saboda tunawa dashi”.


“Mu gani”. Modibbo ya furta yana mi’ka mata hannu, kunce zaren tayi ta dan’ka mishi ya bud’e gidan sar’kar ya ciro wani dun’kulallen abu ya mi’ka mata gidan sar’kar yace “mutum d’aya ba ta’ba gani da irin wannan abun sai ke. Mahaifina yana da irinsa wanda aka bashi kyauta a wani can ‘kauye mai nisa”.


“Menene shi?” Taishu ta tambaya, murmushi yayi yace “sanin amfaninsa da sarrafashi sai wanda ke shiga jeji. Idan har zaki bani wannan zan fansheshi da shanu biyu”.


Mamaki ne ya kama Taishu domin tasan darajar shanu a wurin fulani amma zai fanshi wannan ‘kan’kanin abun da shanu har biyu? Idan har ta saida shanu biyu tana da tabbacin zata samu kud’in da zai iya kaita cikin asalinta timiya. Har ta bud’e baki Modibbo yace “kar kiyi gaggawar amsawa kiyi tunani. Sannan wannan marufin zinaren gaske ne kar kiyi wasa dashi. Ki rage bayyana shi domin kika shiga cikin mutane zaki iya rasa ranki sanadiyyar sa”.


A ranar kwana taishu tayi tana tunani saidai tunaninta na kan abu d’aya ta baiwa modibbo abinda yakeso ta kar’bi shanu ta sayar ta tafi neman ‘yarta. Juya sar’kar wuyanta take cikin mamaki, ashe tana da dukiya a hannunta take zaune cikin talauci da wahala na tsawon lokaci?


Washegari da sassafe kafin fitar su Modibbo kiwo sukayi ba’ki daga wata rugar, tunda aka sanar ma Modibbo manga maud’o yazo yanayinsa ya sauya, dabo jauro ma saida ta sauya fuskarsu ta nuna alamun d’acin rai. Tambayarta Taishu tayi lafiya meke faruwa? Dabo jauro tace “d’ansa ya kashe yarona shekarar da ta wuce a wannan shekarar gid’ad’o yaci alwashin d’aukar mishi fansa, ina tunanin dalilin da yasa yazo kenan”.


“Allah sarki Allah yayi mishi rahma, amma dabo jauro da dai kunyi ha’kuri maha’kurci mawadaci, ta yiwu tsautsayi ne ya gifta wancan ya kashe yaronku idan gid’ad’o ya kasheshi da gayya zai iya zama fitina a nan gaba, kuma ran yaron zai rataya a wuyan gid’ad’o. Kuyi ha’kuri Allah yana tare da masu ha’kuri”.


“Abinda yasa gid’ad’o yayi haka shine tunda aka kashe bawuro babu wata magana da tazo daga garesu, da ace sun bada ha’kuri abun zai iya wucewa amma sai sukayi tamkar babu abinda ya faru”.


Suna maganar Modibbo ya shigo da sauri ya kira dabo jauro gefe yace mata cikin harshensu na fulatanci “manga maud’o yazo ya bani ha’kuri har ya taho da shanu ashirin a matsayin yarjejeniyar zaman lafiya. Dabo jauro ina ganin mu Kar’ba kawai tunda ko fitinar muka tada sun fimu mutane, banaso a sake rasa wani ran dalilin fansa”.


“Ashirin modibbo? Ban ta’ba tunanin ruga mai girman ta su manga maud’o zasu zo su bamu ha’kuri ba”.


“Ni kaina nayi mamaki, yanzu yace muyi magana dake ki fito zai baki ha’kuri kema”. 


Mayafi Dabo jauro ta yafa ta fita inda suka zauna cikin yarensu na fulani ya cika ta da kalamai masu dad’i, suna washe baki suka ha’kura aka kora musu shanunsu suka d’aure. Kwana biyu tsakani d’aya daga cikin ‘kannen manga maud’o ya nemi auren danejo, harka ta girma shima saida ya bada shanu goma a matsayin na gani inaso.


Farin ciki wurin modibbo baya misaltuwa domin shanunsa sunyi ciwuka watannin da suka wuce ya rasa wajen shanu goma dalilin wata cuta da baisan dalilinta ba, bayan ya natsa ya kira taishu yace “zuwanki kin zo min da alkhairi taishu, alkhairin da nayi shekaru ban sameshi ba. Ina neman alfarmar ki cigaba da zama damu taishu, idan har kin amince ina miki tayin aure”.


Free page

Free pages sun kusa qarewa, a hanzarta a siya 😁😁


Littafina na kud'i ne 500 kacalđŸ„°đŸ„°ku nuna min solidarity ni kuma zanyi 'ko'kari na baku abinda zu'katanku suke so😁😁


Akwai VIP 700 ga wad’anda ba zasu iya jira ba, 3 pages a kullum😌😌


Account details

0472624453

Musa maryam Aminu

Gtbank


Ki a tuntu'beni ta wannan number

***