16
by @kitty
A CIKIN DUHU
Kitty💕
Wattpad@ mssmeemah
16
Bayan komawarsu d'aki Abbu ya lura yanayin fatima ya sauya ya cigaba da janta da hira har lokacin tafiyarsu gida yayi, 'kanwar Mum ita ce ta maidasu gida ta kwana dasu yayin da Mum ta zauna wurin Abbu.
Kallonta yake yana jiran tayi maganar karime amma sam ta'ki ce mishi komai, bayan ta tayashi yayi shirin bacci itama ta hau shimfid'arta ta mishi sallama saidai bacci yayi 'kaura daga idanunta. Me Abbu yake nufi da karime? Ace duk cikin 'ya'yansa da iyayensa da ita matarsa bai ambaci kowa ba sai karime? Anya batayi babban ganganci ba da ta amince aka rufe case d'innan? Wane tsautsayi ne ya sanya ta bari Abbu ya janye ra'ayinta ashe mummunar nufa'ka ce a zuciyarsa? Da ya d'auki karime ina zai kaita? Lallai tayi wawan tunani da bata bari karime ta shiga kotu ba domin da 'karfin dukiya sai ta tabbatar da an gar'kame karime indai har zata shigo rayuwarta. Dabara ce tazo mata ta yanda zata tabbatar karime tayi nisa a rayuwar Abbu ko da ba'a kamata ba za'a yanka mata warning kuma yanda taga karime ta tsorata da 'yan sanda tanada tabbacin shirinta zaiyi aiki. Da wannan zuciyarta ta samu nutsuwa bacci ya d'auketa.
Shima Abbu tunanin karime ne ya mamaye mishi zuciya, ina ta shiga? Mutuwa tayi? Guduwa tayi? Asbiti daban aka kaita? Wani hali take ciki? Gaba d'aya hankalinsa ya karkata ga karime domin ihun da takeyi a lokacin da motar ke juyawa ne yake dawo mishi cikin kansa, runtse idanu yayi jin kan nasa ya fara ciwo saboda tunanin da ya fara saidai bai dena tunanin ba ya cigaba da sa'ke-sa'ken hanyar da zai nemo karime a duk inda take matu'kar tana raye. Dole yayi involving DPO a wannan yanayin shine kad'ai yake ganin zai iya gano karime tunda ba sanin gari tayi ba.
Washegari 7am Fatima da su umaima suka iso asbitin da abincin breakfast, sannu suka ma Abbu kowanne ya gaidashi abinda ya bashi mamaki domin tunda ya dawo babu wanda ya gaidashi a cikinsu, cikin murmushi zee tace "Aunty ce tace idan munzo mu dinga ce maka ina kwana".
Dafa kanta yayi yace "naji dad'i kuwa zainab Allah ya raya ku yayi muku albarka". Washe baki tayi ha'korinta da take famfara ya bayyana, matsowa umaima tayi ta d'auke hannunsa daga kan zee ta d'aura a nata wanda ya sanyashi dariya yace "to kema Allah ya rayaki". Kewar 'ya'yan nasa ta shiga zuciyarsa ya fara tunanin yanayin da zai shiga idan ya koma saudi, gaskiyar Mum ne da tace baisan komai a kansu ba amma a wad'annan kwanakin wata irin sha'kuwa ke wanzuwa tsakaninsu.
A yau ma su biyu suka bashi abinci yana cin abincin mum ta fita domin tayi waya. DPO ta kira ta sanar mishi accident d'in Abbu yace "naji labarin hajiya ai d'an sandan da ya rakashi asbiti namu ne, yanzu haka nake cewa idan na samu lokaci zan shigo na dubashi".
"Aikuwa da ka kyauta DPO, amma ba wannan ba kana da masaniyar karime ce ta haddasa wannan hatsarin?"
"Karime kuma? Yarinyar da muka sallama jiya? Ko itace wadda ya kusa kad'ewa?"
Kallon 'kofa Mum tayi tace "A'a ita tana cikin motar amma kuma ance da aka sameshi ba'a tarar da ita ba, DPO bansan me yarinyarnan take nufi da iyalina ba dukda na janye case d'in kisan Abdul amma a yanzu na fara tunanin akwai wanda ya turo ta saboda yanayin yana kamanceceniya da juna, banda Allah yayi Abbu yana da tsawon kwana da saidai muyi kuka biyu, DPO dan Allah a nemo yarinyarnan bansan gaba me zata aikata ba ko nawa ne zan biya ku kamata ta fad'a muku manufarta a kan iyalina".
Shiru yayi na d'an lokaci sannan yace "idan har tana cikin motar kuma ba mutuwa tayi ba aka nemeta aka rasa bayan wannan accident... to lallai akwai ayar tambaya akanta. Ki bari idan nazo zan yiwa shi Alhaji wasu tanbayoyi zamuji abinda ya faru".
"To DPO nagode amma banaso ya san munyi maganarnan da kai".
Dariya DPO yayi yace "karki damu hajiya zanbi komai a hankali sai nazo d'in".
Shima Abbu Mum tana fita ya kira number DPO yaji busy, ajiye wayar yayi ya cigaba da hira da yaransa suna bashi labarin school da 'kawayensu da 'yan aikinsu, sauraronsu Abbu yake a nutse yana jin dalilan da suke sanya ake koran 'yan aiki a 'kan'kanin lokaci ciki harda musanyen bedsheet da akayi tsakanin gadon zee da na Umaima har sukayi fad'a Mum ta kori 'yar aikin akan wannan dalilin.
Suna hirarsu mum ta shigo ta cigaba da harkokinta tamkar babu abinda ya faru. Bayan sun gama breakfast tace da Abbu "zanje gida nayo wanka na shiryo na dawo babu wani abu da kake bu'kata ko?"
Murmushi yayi yace "babu komai ki samu ki huta domin nasan baki samu isasshen bacci ba jiya, zuwa azahar haka sai ki dawo".
"To saina dawo". Ta 'kare maganar tana side hugging d'in Abba, zee da hammad ne suka fara tureta ganin tayi hugging d'insa ta hannun da ya karye tayi dariya ta tafi. Tana fita Abbu ya sake kiran DPO a wannan karon ya samu kiran ya shiga. Gaisawa sukayi DPO yace "labari yazo mana abinda ya sameka Allah ya 'kara kiyayewa, dama nace zan shigo na dubaka anjima".
"Alhamdulillah mun tsira da rai ai shi yafi komai, magana ce dama nakeso muyi amma tunda kace zaka shigo idan kazo sai muyi".
"To babu matsala". DPO ya fad'a yana katse kiran. Kallon Abbu Fatima tayi ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tayi shiru, gani take Abbu bazai iya auren karima ba ko dan yarintarta amma kuma ba zata tura maganganun mum gefe ba, tabbas akwai manufar da ta sanya Abbu ke shigewa karime to menene dalilinsa?
Ana sallar azahar DPO yazo duba Abbu, suna gaisawa DPO yace "abin ya bani mamaki daga fitarku kuma sai aka ce wai kunyi hatsari, ya ita kariman take? Wani d'aki aka kaita".
Mamaki ne ya kama Abbu yace "Dama karime na asbitinnan?"
"A'a ance dai kuna mota tare nayi tunanin itama tana nan".
Numfashi Abbu ya sauke yace "maganar da nakeso muyi da kai kenan DPO, bansan ina karima ta shiga ba inaso a nemo min ita ko nawa ne zan bayar".
Kallon Abbu DPO yayi yace "kana zarginta ne?" Girgiza kai Abbu yayi yace "ko kad'an babu laifin karime a accident d'innan, tafiya nake ina waya ban lura da yarinya tazo tsallaka titi ba, d'auke kan motar da nayi shine ya janyo wannan matsalar amma da na farka babu karime babu alamunta, DPO ka saka amintaccen yaronka ya nemo min karime a duk inda take a zagayen kano zan bada ko nawa ne amma banaso Amina ta san abinda ake ciki wannan magana ta zama tsakanina da kai".
Murmushi kawai DPO yayi yace "karka damu za'a nemota, yanzu ma zan kirashi". Ciro wayarsa yayi ya danna number Ahmad bugu d'aya ta shiga Ahmad yace "sir".
"Ahmad akwai aikin da nakeso na baka ne idan ka shigo anjima. It's confidential banaso wani ya sani".
"Understood sir". ahmad ya furta tareda yanke kiran.
__________________________
Shiru Taishu tayi tareda sunkuyar da kanta Modibbo yace "kiyi tunani taishu amma ina ganin ke kanki zaki fi nutsuwa idan muna zaman aurene dake kuma dabo jauro batada matsala yanda naga ala'karku inada tabbacin zakuyi zaman lafiya".
"Nagode da tayinka Modibbo amma a yanzu raywata na tsaidata har sai 'yata ta bayyana gareni sannan sai na koma ga 'yan uwana, nagode da tayinka na alkhairi idan har munada rabon zaman aure zamuyi a gaba amma ba yanzu ba".
Modibbo ya fahimceta yace "babu komai taishu na fahimceki zan kuma taimaka miki d'ari bisa d'ari har ki gano 'yarki, idan har aure ya kasance tsakanina dake nasan hankalinki zaifi kwanciyar da 'yarki a kusa dake fatana Allah ya bayyanata da gaggawa".
Amsawa tayi da Amin suka rufe maganar, ana kwana biyu dabo jauro ta tunkareta da maganar ta sanar mata abinda ta sanarwa Modibbo, mamaki tayi yanda dabo jauro bata kishin mijinta hakan yasa dabo jauro dariya tace "suma masu kishin cutarwa ce kawai ba kishi ba, akwai soyayyar da ta wuce kabi ra'ayin wanda kakeso matu'kar bazai cutu ba ko ya cutar da kai?"
A haka zama ya mi'ka taishu tana saka ranar zuwa Fasi a kowane lokaci tana canzawa har ta kwashi watanni bakwai a rugar modibbo, a lokacin har ta fara aikin fura ana fita da ita kuma Allah ya sanya mata albarka a 'yan watannin da ta ta samu alkhairi sosai domin Hauwa'u sai ta fita da bokiti guda babba a hannunta na fura da 'kwaryar nono a kanta amma furar ta 'kare wani lokacin ma nonon yayi ragowa.
Taishu ganin ta d'an tara kud'ad'enta ne ya sanya ta sanarwa Modibbo da dabo jauro zata je garin su mahaifin karime ta gani ko tana can, sun had'a mata goma ta arzi'ki nono, man shanu, cukwui, daddawa da sauransu duk tayi tsaraba sannan Modibbo da kansa ya d'auki shanu biyu da yayi mata al'kawari ya sayar dasu aka kawo mata kud'inta fal jaka.
Rabuwa sukayi da hawaye ita da dabo jauro domin a yanzu auren hauwa ne kawai ba'ayi ba danejo da baddo duk anyi aurensu, matar bamanga ta haihu tagwaye maza. har yara sunyi wayo wanda taishu ita tayi wahalarsu saboda tsananin kunya na fulani, matar bamanga ko kallon yaran batayi sannan duk kukan da zasuyi ba zata d'aukesu ba balle har ta basu nono, taishu ita tayi rainonsu take gane lokacin da ya dace suci abinci ta kaisu cinyar mahaifiyarsu, sai tayi fama tukuna zainab ke ciro nono ta shayar da yaran nata haka idan sun gama taishu ita zata d'aukesu daga cinyar zainab ta goya d'aya ta ri'ke d'aya. Sai a yanzu da suka fara wayo ne suna rarrafawa gareta take d'an sakewa har idan anyi mata magana tana iya d'aukansu da kanta ta shayar dasu, mamaki sosai hauwa tayi dabo jauro tace ai ba abin mamaki bane sun saba ganin hakan har fiye da haka ma domin akwai wad'anda saidai a matsa nono a cokali a baiwaa yaro ba dai su bayar da kansu ba ko zaka d'aga rigarsu ka aje yaron. Mamaki dabo jauro keyi akan yawan ambaton karime da Taishu keyi tace a al'adar da ta taso hakan ba laifi bane.
Tunanin wahalar da zasu sha takeyi domin yaran sun saba da ita saidai itama tana bu'katar ta nemi tata d'iyar. Sun jima suna sallama sannan suka kaita har titi ta hau mashin d'in da zai sadata da Fasi, garin su mahmudu kuma gida na farko ga taishu wanda ta taso ta tsinci kanta a ciki.
Tana isa gidan Ibrahim ta tarar baya nan yayi tafiya wani garin, cikin gidan ta shiga da sallama suka amsa saidai duk wadda ta d'ago ta kalleta sai ta koma harkokinta, jiki a sanyaye tace dasu "dan Allah karime tazo nan?"
Wani mugun kallo hadiza ta watsa mata tace "Kin aikota ne ko kuma kin bada ajiyarta? Ai nayi tunanin zata iya ri'kon talaucinta kice har ta jima da fara zubarwa, to Allah ya rabaku da d'an dakan kuka domin kurwar shege dai bata ciyuwa".
Hankalin taishu yayi matu'kar tashi tace "dan Allah na ro'keku ku fad'a min idan tazo".
Saratu ce ta kalleta tace "Hauwa 'yarki bata zo ha rabonmu da ganinku daga ke har ita tun mutuwar mahmudu, idan ba alkahiri bane ya kawoki ki fita ki bamu wuri".
Wurin da hauwa (taishu) zata tsuguna ma ta fuskanci tashin hankalinta babu, a gigice ta sake hawa mashin ta koma rugar modibbo domin anan ne kad'ai zata iya tunani tasan ta ina zata fara ta kuma samu nutsuwa a zuciyarta.
Ta 'bangaren karime kuma Inna ta takura mata da zuwa garinsu, sati d'aya da zamanta a gidan inna ciwukan jikinta suka fara warkewa ranar da ta cika sati cif Inna tace a lallai ranar zasu je garinsu iyayenta ta ganewa idanunta komai. Tun daga hanya gaban karime ke fad'uwa har suka isa 'kauyen fasi saidai bata ta'ba tunanin zata tarar da tashin hankalin da ta tarar a wannan rana ba...
*****
Jarrabawar karime na gab da zuwa qarshe, saidai kuma wani qalubale ke jiranta a gaba?
Abbu... Mum...DPO...Ahmad...
Ga kuma Taishu (hauwa) ta nufi timiya, shin zuwanta zai zamo silar yayewar duhun da suke ciki ko kuma akasinsa?
Duk zaku samu abinda kukeso a A CIKIN DUHU. tafiya ce mai cike da tausayi, al'ajabi, da kuma soyayya mai tsuma zuciya tareda tsantsar kulawa...
To anan free pages yazo 'karshe, masu bu'katar cigaba zaku biya 500 ta wannan account, VIP 700
0472624453
Musa maryam Aminu
Gtbank.
Zaku turo shaidar biya ta wannan number WhatsApp
***
Nagode da soyayyar da kuke nuna min🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰