CHAPTER SIX 6
by @misshajo
🧸 *KHADIJATUL SABREEN*🧸
```MALLAKAR```
*HAJARA L SADEQ*
Arewabook👉@miss Hajo✍️
🅿️............*11 & 12*
Cin Karo da kyakyawar fuskarsa mai dauke da tsantsar kwarjini da haiba Gaba Daya jikinsa a mummurde yake daka kallesa kaga kakkarfan gaske Kyakyawane ajin karshe Wanda tsayawa kwatanta Kyawunshi ma B'ata baki Ne Dan page D'aya Yayi Mana kad'an mu bayyana ainahin surar wannan bawan Allah wannan Shi ake kira da ainahin mijin novel(lol)Kyakyawane na bugawa a news Ba Fari bane irin chocolate colour dinnan ne da fatarsu har wani glowing take,gaba Daya kyakyawar fuskar tasa zagaye take da lallausan sajen da yasha g'yara kallo Daya zakayiwa sajen kasan ba k'aramun g'yara yake Sha ba duba da irin yanda ya kwamta luf bakin sajen har wani shining yake,dogon hancinshi kamar an zana idanunshi ko kallo Daya zaka yi mashi ka sadda saboda wani irin kwarjini da haiba(,Nayi sakato Ina jinjina Tsantsar kyau da Allah Yayi a wajen wannan bawan Nasa, Bansaniba Ashe har ya wuce saurin binsa Nayi hada had'awa da gudu Dan dauko muku rahoto yanda ya kamata).
Tafiya yake irin ta jinin sarauta Taku yake cike da izza har Lokacin masu kirari da bushe bushe Basu bari ba Wanda Jin hakan yake tamkar ana d'iga Masa digon darma a kansa dan a rayuwarsa inda Abunda ya tsana Bai wuce hayaniyar jama'a da irin wadannan abubuwan masu hawa ka ,
baiyi Wata Tafiya Mai tsayi ba ya Isa ga fadar Mahaifinsa Mai Martaba Alhaji Salim muhmod ko ban fad'a ba kunsan dai yanda kyau da tsaruwa yake na Gidan sarauta musamman Aje ga fadar Mai gayya Mai aiki ,gaba Daya hakimai,da Yan fadar sarki suna zazzaune.
sosai aka shiga yiwa Yarima barka da zuwa Fuskar Yarima da Annuri ya karasa ga kujerar Mai Martaba Wara Masa Hannu Yayi Inda ya shige ya lafe a jikin mahaifin nasa yanajin Wata nutsuwa Na saukar Masa sauran fadawa da Y'an zaman fada gaba Daya watsewa sukayi saboda dokar sarki ce Indai Yana magana da iyalansa Bamai Zama a wajen musamman Kuma *Yarima Anwar* da yake star a wajensa ,.
a hankali Mai Martaba Ya dago dashi daga jikinsa tare da shafa kyakyawar fuskarsa ya ce "Soja na barka da zuwa nayi farinciki matuka da Allah ya dawomun dakai lafiya da kuma nasarar da kukayi a yaki munga irin karramaka din da akayi sannan ina tayaka murnar karin girma da ka sake samu shiyasa a Koda yaushe nake matukar Alfahari dakai my son Allah dafa maka akan komai"Ameeeeen Abba na nima Ina matukar Alfahari da Kasancewarka uba a gareni fatan munsameku lafiya"gaisuwa sukayi irin ta soyayyar d'a da uba Kafin ya Tashi ya wuce Bangaren mahaifiyarsa.,
Tungada shigarka Bangaren Uwar gidan sarki Hajiya Aisha Fulanin sarki mahaifiyar Yarima Anwar zakasan ka shigo daular masarautar,Palour ne D'aya bayan Daya zakayi ta wuce su kowannensu Kuma shake yake da Abun duniya kayan alatu,da Kuma kaya irin na Gidan sarauta ko wani daki lik'e yake da kyawawan hotunanta ita da Mai martaba gaba D'aya ,Hadiman dake aiki a Bangaren Saida suka k'ame ganin shigowar, Yarima Anwar kowannensu na kawo irin tashi gaisawar tare da dukursawa kowa Yayi k'asa da kansa ba Wanda ya Amsawa tafiyarsa kawaii yake Cikin izza da takama.,
Saida ya karasa Babban palour Wanda ya take wad'ancen komai da kyau Aljannar duniya kenan Mahaifiyarshi dake sanye cikin Lafceciyar Alkebba Mai matukar Kyau da daukar hankali sanye take cikin tsatsatsadan lace Mai masifar kyau Tana ganin shigowarsa ta Mike tare fadada fara'arta ta na ware Masa Hannu ta ce.
"Oyoyo my son ur welcome ,sannu da zuwa Mazan fama namijin duniya na oyoyo "Lokaci guda ya saki wani lallausan Murmushi Tare da rungume mahaifiyar tasa yanajin guminta wata irin nutsuwa Na k'ara sauko Masa ,."cike da farinciki ya dago tare da dago da fuskar mahaifiyar tasa Yana Murmushi ya ce "miss You alot Mamy na".
yanayin yanda Yayi maganar ma kadai ya Isa ya saukarwa da Mai sauraro kasala cikin wata zazzak'ar murya Mai cike da nutsuwa.
"Murmushi Mamy tayi ta ce "Miss You too Soja na muje ka ci special girkin da na Sanya akayi domin Kai kadai" I can't eat anything now I want to rest mammy anjima idan na huta zanzo naci".
ya fad'a Yana D'an langabewa "kardai har Yanzu kana Nan da rashin son cin abincin Nan naka son "murmushin gefen Baki Yayi Wanda ba kowa zai fahimta yayishi ba ya ce"Ina ci Sosai Mamy na ko Kinga na rame Ne"Girgiza Masa Kai tayi ta ce".
"A a a a kyau ka k"ara ta fad'a Tana latsa wayarta tare da yin Kira ta ce "Ku shigo ku gaisa mun gama.gaisawar"Saboda girmamasa da ake Indai Yana magana da Mamynsa tofa ko kannansa Basa Zama wajen har sai sungama".
Tana sauke wayar Y'an Mata su Biyu suka shigo Palourn kallo D'aya zakayi Musu kasan sud'in jininsa ne D'aya Bazata wuce 22 years ba sai d'ayar bazata wuce 17 years ba "Kowaccensu da fara'arta ta shigo Palourn cikin girmamawa da nuna Farincikin dawowarsa Sukayi welcoming nasa tare da dukursawa har k'asa suka gaishe sa ,ya Amsa Musu tare da tambayar lafiyarsu Suka Amsa Masa da Alhamdulillah"Tare da Kallon Mufeeda ya ce "Ya school d'in hope kina maida hankali ko ?".
Tana fara'a ta ce "Ina mayarwa Sosai Yaya Ai munshiga s s two Yanzu"Yana latsa waya Ya ce "Karatun naku baya sauri"wara idanu tayi sai Kuma tayi Dariya ta ce "Yaya na zata haka za kace Yayi gudu fa?.
Shiru yayi mata Hakan bai dameta ba Dan tasan yayan nasu ba mutum bane Mai fiya doguwar Magana idan yaso "Maryam dake zaune gefensa ta ce "Yaya Ni baka Tambayeni ya school d'inba Ina maida hankalin?.
Ba tare da ya dago ya kalle Ta ba ya ce "a a a karki maida Tunda Position ake rubuta muku"Yar Dariya tayi ta ce"Uhm to Nima dai Ina maidawa Dan Second semester dinnan Bani da c o ko Daya" good girl"Ya Fada Yana jinjina Mata da Hannu.
"Yana mik'ewa ya kalli Mamy ya ce "Na wuce Part d'ina Zan huta'"Okay a biyoka da abincin kenan"Eh Nan da 2hours, Mufee ko Maryam su kaimun "
Murmushi Mamy tayi bayan barinshi Palourn ta Girgiza Kai ta rasa dalilin da yasa 'Dan nata bayason hada Hulda da Mata Ko gyara part dinsa za ayi Dole sai baya part din hakan yasa ko hadima bashi da ita ita gani take kamar ma tsoron matan yake gashi dai jinin sarauta tilon d'a namijin sarki Wanda ake sa ran shine magajin masautar Amma kwata_kwata Bai damu da sarautar ba kwata kwata ta lura sarautar ba itace gabansa ba yafi mahimmanta aikinsa fiye da ita.",
Kwanciya Yayi a makeken royal bed dinsa d'akin ba abunda yake Dauka sai sanyayyen kamshi har wani lumshe Ido yake saboda Shi Daman can mutum ne ma'abucin son kamshi a Rayuwar Yarima Anwar Yana Kaunar kamshi shiyasa kullum Baya rabuwa da turare motarshi, office dinsa,duk inda zaije tofa zakaji yana kamshi Bai Jima da kwanciya ba baccin gajiya ya daukesa.,
Koda ya farka Yayi mamakin jimawar da Yayi a bacci Bathroom ya fad'a Yayi wanka bayan ya fito ya shirya cikin wasu tsatsadan kananan Kaya da suka Amsa sunansa Sai Baza kamshi yake Cikin takunsa kamar Wanda baison taka k'asa Ya fito Palourn sa Wanda ni kaina Saida nayi kauyanci cin Karo da tsadaddun Furnitures din dake shake a Palour Kai tsaye dining ya nufa ganin an jera abinciccika da drinks² kala_kala yasan aikin Mamynsa Ne,Baici wani Mai yawa ba fruit salad din Ne ma yasha Mai D'an yawa masallacin cikin masarautar ya nufa Dan gudanar da Sallar la'asr Da aka Kira cikin jam'i..
*HAJIYA TALATU*
Safa da marwa kawaii take ta kasa zaune ta kasa tsaye Ga waya a hannunta Kallon matashiyar budurwar da Ta haura 24years tayi ta ce,.
"Kina Gani surayya Wai har Anwar ya shigo masarautar Nan tun 1pm Amma har Yanzu Bai Tako ya gaishe Ni ba,kina gani Da idan ya shigo masarautar Nan kafin ya je Bangaren uwarsa ma saiya Fara zuwa ya gaisheni me hakan ke nufi,kodai tsinanniyar Uwar sannan ta shiga ta fita ta rabani da d'an da na raina da hannuna ,ita harta Isa ta rabani da Anwar D'an danasa buri a kansa,fiye da yaran Dana haifa,never wlh abunda bazaiyu bane wallahi,tallahi,kinji na rantse Bata Isa ta rabani Da Anwar ba haihuwarsa kawaii tayi Amma Ni ta haifawa Bata Isa taci gajiya biyu ba ta ci gajiyar sarki yanda ta mallakesa komai sai ita,Kuma taci gajiyar Uwar sarki,Ni Nan nice Zan Zamewa Anwar uwa Ni zanyi yanda nake so dashi ,Kartayi tunanin ita kad'ai keda d'a namijin Ni da nake da Mata Zan tashi a tutar banza saidai ita ta tashi a banza ,hmmm Mai laya ya kiyayi Mai zamani muje zuwa Yanzu zamu Fara buga wasan dake Hajiya Aisha ".ta karasa fada Tana wani shu'umin murmushi.,
Surayya Dake latsa waya Bata dago ta kalleta ba bare ta sa ran amsa hakan ko Sosai ya kular da Hajiya TALATU,cikin fushi ta ce "Watau Ina magana kin mayar Dani mahaukaciya bakima da Lokaci na"Mik'ewa tayi Tana had'e fuska ta ce.
"Ba abunda ya shafeni bane "Tana Gama fad'ar haka ta Mike tabar Palourn,"Sakaran banza wacce batasan ciwon uwarta ba ".
ta karasa fad'a Tana Jan dogon tsaki tare da Kara dannawa number da take ta trying Kira ta Kara a kunne Jin Tana ringing kamar yanda tayi ta Kira daukace ba ayi ya sanyata Jan dogon tsaki cike da fushi ta ce ,"Sakaran banza ita ma ko Ina ta Sanya wayar",Bata rufe Baki ba aka Dauka "Cikin fad'a ta ce "Wai Gidan ubanwa Kika Aje wayarki tun dazu Ina kiranki Baki dagawa".
Cikin gigin bacci tace "Ina bacci ne Aunty meya faru"to saiki tashi daga baccin asarar *Yarima Anwar* ya shigo gari kome kike ki barshi ki chanchada ado sannan ki shafo turaren Nan na wajen boka Lauje ki barbade jikinki dashi sannan ki Sanya kwallin Nan da duk kayan da ya Baki ki maza ki taho kiyi shigar daukar hankali na fad'a maki' "Ina jiranki yanzu Yanzu".
"Ihun murnar da ta buga ne ya Sanya hajiya TALATU kauda wayar daga kunnanta ta ce Sakaran banza Shekara da shekaru kin kasa sace zuciyarsa kina mace Amma ki kasa.sace zuciyar d'a namiji shima sai shegen taurin kai,.Bata rufe bakinta ba Taji sallamarsa cikin Palourn"Lokaci guda ta hargitse tare da Nemo nutsuwarta Cikin fara'a ta Fara da cewa.
"Lale Mar haban d'ana na kaina D'aya tamkar da dubu Yanzu nake Shirin zuwa Wajen naka samun labarin da nayi kazo Naji ko lafiya nasan dai Kayi watanni bakanan baka ga mamanka ba Ni zaka Fara mamarin gani hankali na duk ba kwance ba Yana wajenka saida naga cin nasararku a yak'in Nan hankali na ya kwanta "D'an murmushin gefen bakin da ya Saba Yayi Mata Tare da cewa.
"Ina Yini Mama na sameki lfy "Tana zauniya gefenshi cikin kulawa ta ce "Lafiya qalau My son ya hanya Kun shawo gajiya Sannu ko ".
Sosai mama TALATU da dinga janshi da hira Wanda baya biyemata Sosai hakan Bai dametaba saboda tasan halinshi mutum Ne marar son yin maggana da rashin son hayaniya.
"Jin karar bud'e k'ofa Ne ya Sanya Hajiya Talatu Daga Kai Ta kalleta sanye take cikin wasu matsatsun Kaya Atamfa Riga Da sicket sicket din bayanshi Mai katuwar tsaga.
,Kasancewarta Mai kiba Sosai ya Sanya kayan suka Dame jikinta Sosai Bata da Wani Kyau na azo a gani haka Bata da muni tana dai da kyanta Daidai misali bak'a ce Amma ba'kin nata Mai kyau taci daurin tuge kaga tsiya gyale a kaf'ad'a Tana taunar chumgum ta karaso tsakiyar Palourn ta gefen Ido Hajiya Talatu ka kashe Mata Ido D'aya itama kashe Mata tayi tare da Gyaran murya cikin muryar daukar hankali ta ce "Assalamualaikum".
Anwar har Lokacin Kanshi sadde Yana latsa waya Bai dago ba haka bata sa ran zai dago ba saboda sanin halin izzarshi da gadara da tayi hajiya ce ta Amsa Mata da cewa "wslm Ummulkulthum yanzu Kika dawo kenan "Tana wani yauki ta ce.
"Wlhko Aunty Ina Yini"Kafin ta karasa kujerar da Anwar yake cike da pretending Ta ce "Lah Ya Anwar Yaushe ka zo Waida kaine zaune ina Yini".
Sai Sannan Ya D'ago tare dayi Mata kallo Daya ya Tabe Baki ya ce "Lafiya"Kafin ya Mike Ya kalli Hajiya ya ce "Na wuce mama".
ba zaka zauna muci gaba da hirar ba son kasan nayi kewarka fa da yawa" Zan dawo mama Yana Gama fad'ar haka Ya bar Palourn Cikin takun kasaitarshi Wanda kulthum garin kallonshi Har Faduwa Daga kan sopa taso tayi dankwashin da mama ta Kai Mata ne ya dawo da ita Daga duniyar Tunanim shaukin kaunar Yarima Anwar data Lula Firgit ta zabura ta ce.
"Me nayi Miki Aunty"Ubanki kikayimun Dan Ubanki haka Kika zauna Har yabar d'akin Sakaran banza da Kika rako Mata ko shagwabar Nan Baki iya ba ta Mata Mai makon ki bishi kina shagwaba kina rangwada Kina cewa"Haba darling ya zaka tafi Bamu ko gaisaba ,me kakeson na girka maka,ko Uhm muje to na bika nayi maka hira ,da sauran shagwabar Mata Amma banzar Kika barsa yatafi haka sakkarai Shaka tafi kawaii.....
*Adamawa Yola*
"Daga Gidan ubanwa kike Tun dazu da wannan tsinanniyar shigar Dan Ubanki "
Mom ta fad'a Tana tasowa ranta a matukar Bace ta nufota"Baya Sabren tayi da niyyar rugawa Taku Daya mom Tayi ta chafeka Tare a wanketa da Marin da Bata taba Mata irinshi ba .
"K'aran da ta fasa ta durkushe a wajen ya Sanya Dad fitowa daga bedroom da zuwanshi garin ba jimawa Kenan.
"Duka Mom ta hauta dashi cikin fushi take cewa"Dan Ubanki ban hanaki yawo ba,ban hanaki fita ba,Gidan ubanwa kike zuwa bada izinina ba,Khadija daukar magana kike son kimun Shekara Sha Biyar Tsit dake Aiko yau zanji Gidan ubanda kike zuwa".
"ta fad'a Tana niyyar Kai Mata wani dukan Dad ya riketa cikin fushi ya ce "me tayi maki Zaki hau mun Yarinya da duka meye haka Amina sau nawa Zan fada maki ki daina Dakar mun y'a matukar ba sabawa kikeson muyi ba meyasa Ina kiyaye abunda ke bata miki rai Amma Ni bakya kiyaye nau so nawa Zan fad"a maki idan kina son bacin Raina ki tab'amun y'a why Amina kike dukanmun y'a sau nawa zanyi maki kashe"Cikin fushi mom ta D'ago ta ce.
"Rabona da ita tun azahar fa bansaniba tayi sand'a tabar Gidan Nan dubamun awa nawa tayi a waje Ina taje da wannan shigar,da da Yanzu fa ba D'aya bane yanzu ba Yarinya bace kome zakace saidai kace Amma wlh bazan yarda ta lalacemun ba saboda kan a zageka sau Daya an zageni sau dubu Dan haka ba ruwanka da tsakanina da ita ka barni na Tarbiyantar da y'ata Abban Sabren Banason Abunnan Nima matukar ba so kake mu samu sabani ba wlh Ka Bari na binciki inda take zuwa Tunda tayi jsce dinnan yawonta ya Tashi daga unguwa ya koma Gari ,Gidan ubanwa take zuwa,wata sani a garin ?"
Ganin Mom tayi sama ne ya Sanya dad kwantarwa ya ce "Yi Hakuri To Naji mu bincike ta din Amma. Karki sake dakanta please"Kafin ya kalli Sabren dake kuka Tana diddira kafa ya ce ,Sorry daughter yi shiru Ina kikaje".
Saida Yayi ta lallashinta Wanda hakan k'ara kular da mom Yayi Kafin cikin kuka tace Dad Ni ba inda nake zuwa Ina Gidan su Affan tun d'azu"Taso to my daughter sorry yiwa mom Hakuri rashin sani ne Kafin ya kalli mom ya ce.
"Kinji ko ba ason Yanke hukunci cikin fushi"Ban yarda ba wlh Bari na Kira Maman Affan d'in na Tambayeta Karya take"
"Tana Gama fadar haka ta janyo wayarta daga chaji gaba D'aya Sabren ta tsure kallon dad da tayi ya Sanya hankalinta kwanciya tare da lafewa jikinshi Tana turo Baki a ranta ta ce "Ai tunda Dad na nan Baki Isa ki sake Duka na ba".
"Ringing Biyu Maman affan ta dauka ko gaisuwar kirki basuyiba Mom ta ce "Dan Allah Aunty Sabren tazo Gidan Nan yau kuwa?.
"A a a Gaskiya Tun yau ban sata a Ido na ba Yanzu ma nake yiwa Affan fad"a tun azahar rabona dashi"Okay nagode"Mom ta fad'a tare Da katse wayar Chazar wayarta ta dauka tare da nannadewa ta ce.
"Wallahi koki fad'amun inda kikaje ko Yau mu fitar da raini Ni dake a Gidan Nan ?ta fad'a Tana rib'a wayar charger Biyu"Wata irin zabura Sabren tayi tare da Mak'alk'ale dad ta fashe da kukan Tabara Ta ce "Dad Karka Bari ta dokeni wallahi Zan fad'a Mata inda bazata dokeni ba...........✍️
*Domin magana da marubuciyar kai tsaye ****
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
***
Masu turo kati MTN ta wannan number.
***
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
***
*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
_*Miss Hajo ce*_🤙