CHAPTER TEN 10
by @misshajo
🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸
```MALLAKAR```
*HAJARA L SADEQ*
@Miss Hajo✍🏿
*END OF BOOK ONE 1* 👆🙇
🅿️..........*19 & 20*
Sosai aka Sha dagu da sabren kafin ta yarda ta shiga Mota Saida ta gaji da kukanta kafin bacci ya kwasheta a jikin maman katsina har suka isa katsina Tana bacci.
Kai tsaye masarauta suka nufa saboda motarsu daban dasu hajja Suna Isa maman katsina tahau tadata a hankali ta bude idanuwanta Tare da Karewa inda suke kallo Lokaci guda ta Had'e fuska kamar zatayi kuka ta ce .
'"mamy Ni banason masarauta ,"Cikin sigar lallashi ta ce "Kinga kwantar da hankalinki ba abunda za ayi Miki Anan din kinji y'ata"Make kafada tayi kamar wata Yar goye ganin Tana neman 'Bata Mata Lokacin NE ya sanyata nuna Mata wani dogari Daya b'ullo ta ce "Kinga Baki fito ba yanzunnan zan hadaki da dogari ya zanemunke".
Jin Haka ba shiri Sabren ta fito tare da Mak'alk'ale maman katsina ta ce "Kiyi Hakuri mama karkisa a dakeni wlh na fito"To shikenan bar kukan muje ko Yata"Kama hannunta tayi har suka isa part d'inta duk inda ta wuce ana kawo gaisuwa Sabren dai rarraba idanu kawai take har suka isa katafaren Palourn Wanda Ganinsu ya Sanya Mufida Tashi da sauri tare da rugowa ta rungume Sabren cike da zallar farinciki ta ce
"oyoyoy my sis Sannunku da zuwa kafin ta kalli mamy ta ce "Sannu da zuwa mamy"Yawwa Mufeda ya Gidan"Alhamdulilah kafin ta kalli Sabren dake kwakwabe fuska ta ce"Ga sister ki Nan baby kuje dakinta ki saki jikinki kinji nandin gidankune "Make kaf'ad'a tayi Tana Shirin Fashewa da kuka ta ce.
"Mama ni banason Nan din ki maidani wajen mom da dad "to naji za a mayar dake Amma yanzu kuje Ki huta' ko?kafin ta kalli mufeda tace "ga Yar uwarki Nan Kuma kanwarki Nasan kinganeta tunda Kuna Dan gaisawa za a shigo da kayanta ki kaisu dakinki kuje ki Bata Abinci tayi salla tayi wanka".
"tohm Mamy ?ta fada kafin ta kalli Sabren ta ce "Muje ko sis?Zata Sanya kuka mamy ta Had'e fuska ta ce "Kika sanyamun kuka Zan fasa maidake ?Cikin sauri ta hadiye kukan Tana goge hawayen ta ce .
"Na daina"Kama hannunta mufe tayi suka shiga bedroom d'inta ita ta ha'da Mata ruwan wanka da kanta bayan ta fito daga wanka kallon mufe tayi ta ce "Ina kayan nawa"Akwatinta da tun zuwan mom yola suna Asibiti ta had'o mata kayanta aka shigo dasu ta janyo tare da budewa ta ce.
"gasunan"Budewa tayi Daman duka kananan kayane cikinsu ta Sanya wasu mararsa nauyi Tana gamasa ta Haye gado Tana kallon gefe ta Lula duniyar tunani"Mufe ita ta rufe kayan kafin ta ce "Bazaki Tashi Kiyi salla ba Sabren Mamy tace a hanya la'asr tayi muku ga magrib itama har anyi"ba ayin sallar ta fada Tana rufe idonta "Dariyar mufeda tayi ta ce "sallar ce bakiyi kome?ba a saniba Yar ba'ka kawai"Dariyar mufe ta Kuma sawa ta ce "Au a kaina Zaki huce fushinki kenan to Yi Hakuri yar Farar danginmu ".
shiru Sabren tayi na Yan wasu Lokaci Jin mufe Bata Kuma magana ba ya sanyata juyowa kallonta tayi Tana salla Tashi tayi zaune Saida mufe ta Gama sallar kafin ta ce.
"waike kadai na gani a Gidan ko duk anmusu aure?a a a Yaya Maryam Taje bikin wata friends d'inta Shiyasa Baki ganta ba "To ina Aunty Farida wadda mom ta Tab'a ban muka gaisa da ita tace itace first born din Mamn katsina .
"Tana gidanta Kano take Aure kardai itama Baki Santa ba"zaro idanu tayi irin a mamakance ta ce "kaiii Wai har anmata aure"Dariyar mufe tayi ta ce "Eh Mana koni Lokacin da akayi bikinta Banda wayau ke Kuma Lokacin ko yayeki ba ayiba Yanxu Haka babban d'anta yayiki tsawo"Allah da gaske?Eh mana lokaci guda ta washe fuska ta ce.
"Kice Ina da abokin wasa"Dariya sosai mufe tayi ta ce "ke Yanzu Baki wuce wasa ba Sannan ma da d"an zumunki zakiyi wasan"Harararta Sabren tayi ta ce "Ehmana Ina ruwanki"To naji Amma yanxu Tashi Kiyi salla kinji Yar kanwata".
Tilla Mata pillow Sabren tayi ta ce "ba ayi din Tashi muyi game a wayarki Dan Allah"bazan bada ba indai bakiyi salla ba Kuma Ina dasu Amma sai kinyi sallah jin haka ya Sanya Sabren mik'ewa faka_faka tayi sallar ta salamce tahau gado suka hau buga game sosai mufe tayi mamakin kwarewar game irin na Sabren duk game din da suka shiga ta iya Shi ita kanta a Dan zaman da sukayi na yan montuna ta tabbatar da ba k'aramun Wasa bane a ranta Suna Cikin game Daya daga Cikin hadimar Mufe ta shigo ta shaida Mata Hajiya na kiransu suje suyi dinner da to mufe ta amsa Mata Sabren hankalinta Yana wajen game Dakyal mufe ta samu ta Amshi wayarta suka fito tare da Sabren d'in.
a tsararren dining area din dake shake da manyan kuloli na alfarma suka tarar da mamy da Maryam Suna dinner karasawa wajen sukayi tare da Jan chairs suka zauna "Kallon Sabren Mamy tayi da Fara a fuskarta ta ce "Kici abinci sosai kinji ".
"Dan murmushi Sabren tayi ta ce "To Mamana"Maryam ce ta dakata d'aga cin abincin da take tare da Kame Baki ta ce.
"Mamy kardai Yar aunty Amina ce ta girma Haka ,Rabona da ita fa tun Tana 8years ko 5 "ai Dole kice bakisan Yar uwarkiba mararsa zumunci Wai Kuna cousin sister's Amma bakusan juna ba ai hada laifin Aminar da Bata zuwa da ita kuma again ba zumuncin zuwa inda suke ba Kuke ".
Sosa Kai maryam tayi ta ce "Ba Haka bane Mamy Yanzu ai inshallah zamuyi zumuncin kafin ta kalli Sabren ta ce "sannu ko kanwata kinsanni Ai Ni ko?Make kaf'ad'a Sabren tayi tare da kallon mufe ta ce "Kice Bazanyi magana da ita ba yanzu".
Dariyar Maryam tayi ta ce "To menayi"Tana tuttura Baki Gaba ta ce "Bake Ce kikace Baki gane niba bayan Ni Ina zuwa Saida na tambayeku"Sorry my kanwa Nina Isa nak'i ganeki Wasa nake maki my sweet sisterta dawo nanma ayi kaunar zumunci".
ta fada Tana janyo hannunta tare da zaunar da ita kujerar gefenta "Lokaci guda Sabren ta saki fuska tare da yin Murmushi Dan a rayuwarta ba abunda takeso sama da Yan uwa idan taje gidan friends d'inta taga yayyunsu da kannansu sosai abun ke burgeta sabanin ita da take ita daya Tana kallon Maryam ta ce.
"Aunty Kema Ai yayata ce ko?eh Mana yayarkice ni Mai matukar kaunarki my sister "Cike da farinciki Sabren ta ce "yeee Nima Ashe Ina da yayyu kamar su Affan Amma meyasa bakwa zuwa Inda muke"Murmsuhi Maryam tayi Mata ta ce "muna zuwa Lokacin Baki wayau shiyasa Amma Yanzu ai kindawo Cikin mu ko ?Make kaf'ad'a tayi ta ce.
"a a a wajen dad Dina zan Koma saidai idan ku kun yarda ku bimu"Amma ai zakiyi Mana kwana biyu indai kina son muma mu bikin?shiru tayi na Yan mintuna kamar Mai tunani kafin ta ce"To na yarda Amma gidanmu zaku Koma da Zama"Mamy Ce tayi murmushi sosai take so da kaunar Sabren a Cikin ranta yarinyar nada shiga Rai over ta ce.
"Yanzu dai ki Barmun daughter taci Abinci ai kuna tare saikuje kuyi ta hirar Taku"Mufe ce ta kalli Maryam ta ce "Aunty daga zuwanki harkin kwacemun fada wajen sis"Dariya Sabren tayi tare da yi mata gwalo ta ce "Ke ai kanwata ce"Duk Dariya sukayi kafin su Fara gabatar da dinner dinsu Sabren taci wannan taci wancen Har Saida ta KoshI kafin ta mike Tana kallon mamy ta ce.
"Mamyn katsina Ki kiramun Mom d'ina"Tirkashi Mamy ta fada a ranta kafin a fili ta ce"Bata sayi layi ba Amma dazu ta kirani a wayar wani Dr sun Isa lfy Suna ma Asibitin gobe za a Fara duba lafiyar dad din naki kije ki kwanta gobe da safe kunyi wayar".
Nan fa Sabren ta ce Bata San wannaan ba kuka ta fashe dashi tare da bajewa Kasan tiles tahau diddira kafa sai an Kira Mata mom d'inta ba lallashinta da ba ayi Mata ba Amma ta tubure ta ce.
"indai ana son na hakura sai an sayamun ice cream"Dakuwa many tayi Mata ta ce "Gidanku keda ice cream din katuwar wofi kitashi kije ki kwanta ko na zaneki ".
"to ki maidani gidanmu Nidai Allah sai ansayamun ice cream"ta fada Tana cigaba da diddira Kafa Maryam da Mufe Dariya kawai suke Mata dansu Basu tab'aga Sangarta irin wannan ba katuwar budurwa na acting din Yan yaye.
"Maryam ce ta ce "chab akwai aiki Gaba Keenan to Nidai na tafi saida safenku"ta nufi sashenta Tana Dariya yayinda Mufe itama Tana dariyar ta shiga lallashin sabren Amma kamar zuga ta ake Mamy ganin ba sarki sai Allah yarinyar tayi nisa ga wani ihu da take Tana Shirin Tara Mata mutane a dauka ba lafiya ba ya sanyata lallashinta tare da aikawa a sayo mata ice cream Din.
ana kawowa ta Mike kamar ba itace ta Gama murje murje ba ana Mika Mata ta goge hawayen tare da Fara Dariya Ta kalli mamy ta ce "Thnks Mamy na"kafi ta Ruga da gudu d'akin Mufe "girgiza Kai Mamy kawai tayi tare da kallon Mufe ta Mika Mata d'ayar robar ta ce.
"Saida safe ki tabbatar Tana cika salla nauyin Dana Dora Miki kawai akanta"Dariya Mufe tayi ta ce "to Mamy inshallah Zan kokarta Naga kamarma batasonyin salla Dan dakyal tayi dazu"Haka Uwar tacemun batason yin sallah Sai taga dama Shiyasa na Dora Miki Bangaren Nan naji da sauran "Tana Gama fadar Haka ta shige sashenta yayinda Mufe ta wuce sashensu itama Tana ta Dariya ita Daya Dan ita Gaba daya maganar Sabren ma yanda take komai a sangarce Dariya yake Bata.
Cikin sati guda Sabren ta Fara sabawa da Yan uwanta soboda irin yanda suke janta a jikin da nuna Mata kulawa musamman Mufe Sannan hankalinta yadan Fara kwanciya kasancewar kullum sai sunyi waya da mom ta wayar Mamyn katsina tanajin lafiyar dad d'inta Sannan Suna video call ,dangane da shiriritarta ba abunda ya ragu Yanzu babu abunda yafi damunta Daya wuce Zama waje Daya yanda ta Saba da yawo jinta take kamar a Kaya take,.
Sanye take Cikin blue din jiens tare da farar t-shirt ta Sanya farin combost d'inta hula Ce kawai a kanta ganin ba kowa a Palour mufe da Maryam Suna school Mamy Kuma Bata fito ba ya sanyata Cikin sauri ta fita d'aga part din, wani lumshe Ido tayi Koda taji hasken Rana sosai take karewa masarautar kallo Wanda sai Yanzu take Gama ganinta,kowa harkar gabanshi yake hakan ya sanyata Fara zagayawa Yawo ta shigayi ta shiga Nan ta fita Chan .
Tana Cikin Tafiya Taji tayi Karo da mutum Kadan ya hana ta fad'i cike da tsabar masifa ta ce "uban uban wani shegen ne ya Bugeni"Haidar dagowarshi kenan cike da zafin nama niyyarshi ya wanke wacce Yar rainin wayan ce har da Zata zageshi ".
Saranda yayi ba shiri Cin Karo da kyakyawar fuskar da tunda yake tsawon rayuwarsa Bai taba cin Karo da kyakyawa ba kamar yarinyar da yake gani gabansa, sakato yayi Yana kallonta kamar wani statue,irin kallon da yake Mata Ne ya Kara kular da Sabren cike da masifa Ta fara jaraba "Kai makahone ko baka da hankali da Zaka Bugeni Sannan ma shine ka tsaya kana kallona ko?.
Murmushi Haidar ya sakar Mata tare da. Cewa "Am sorry pretty ban gani ba Kiyi Hakuri"wata harara ta Dalla Masa tare da Had'e fuska sosai ta ce "Ai bansan wani Abu Hakuri ba malam ,sai ka biyani diyyar Bugeni da kayi Kasan dai ko a kotu kudinka sun haura dubu dari biyu ko?.
Ta fada Tana tsatsareshi da manyahn Idanunta "Barema Ke kyakyawa ai sai dubu dari biyar"ya fada Yana Dariya"Harararsa tayi ta ce "ba wani dadin bakin da zakamun nayi maka ragi ka biyani diyyar da Robar ice cream guda ukku tare da gasashshiyar kaza ,da Kuma Kwallon kwakwa ukku"Dariya sosai haidar yayi kafin ya ce "Su kawai Kike bukata pretty ?Tana Harararsa ta Ce"Eh idan Kuma baka siyamun ba Kara Zan kaika wajen Sarki ".
"Ah ah yi Hakuri ba akai ga Haka ba kyakyawa tare zamuje ko Kuma jirana zakiyi na dawo"Tana Zama wani dakali ta ce "Jeka dawo Ina Nan"Haidar har ya Isa Mota yana juyowa Yana kallonta har kusan faduwa yayi sosai yarinyar ta shiga ransa lokaci guda bai taba ga yarinyar da ya kamu da tsananin sonta cikin kankani lokaci ba kamar wannan yarinyar ,ga dressing dinta ma yayi mugun Tafiya dashi".
Sabren ko Yana Barin wajen ta hau Dariya tare da cewa "Banza gara hotiho kawai har na Masa wayau"Tana Nan zaune Har Haidar ya dawo sosai tayi mamakin hada abunda Bata fada ba ma ya saya Mata "Amsa tayi Tana Shirin Tashi ya ce "Baki fad'amun ba to sunanki pretty"Tana wani yatsine fuska ta ce "Shima na kud'i ne"To nawa za a sayarmun"ban shirya saidawa Yanzu ba "binta Haidar yayi ganin Tana neman b'arin wajen tare da Cewa "kina son na dinga saya Miki wannan abubuwan kullum?.
Dan ya lura kwata kwata Bata da wayau "lokaci guda ta juyo Ta ce "Da gaske?Da gaske Mana Amma Sai kin yarda kin Zama kawata "Kare Masa Kalo tayi kafin ta ce "Amma ai Kai babba ne Ni friends Dina duk ba manya bane"To ba so kike na dinga saya Miki kayan Dadi ba ko su kananan friends din naki suna saya Miki"Shiru tayi Jim kafin ta dago ta kallesa ta ce "a a basa sayamun na yarda to "Good girl My friends wani Bangaren Kika zo Wai Dan Nasan dai ke bakuwace a Gidan Nan"
"Bangaren su Mufeda Ni diyar sister mamansu ce"Okay nagane to mu dinga haduwa a Nan ko gobe ma da la'asr mu hadu anan zanyo Miki sayayya?Sannan karkicewa Hajiyar Ni friend dinki ne"Harara ta Galla Masa tare da Cewa.
"To sannu Daddyna kake bani wani umarni kamar wani uba na"Kafin tayi Gaba "wani dogon numfashi Haidar Yana gabaki Daya kafafuwanshi gagaranshi dauka sukayi bai bar wajen ba har saida yaga bacewarta wani sanyayyen murmushi ya saki cikin kasalalliyar murya ya ce " I love you so much my pretty...
A dakinsu ta baje ta dinga ciye ciyenta Tana ci Tana dariya ta ce "Gaskiya garin Nan duk Basu da wayau,jifa garan ya zaci da gaske nake yayo mun wannan sayayyar ,Allahsarki ko Ina Yaya beauty Shima da nayi mashi wayau yayi ta sayamun abubuwa Rance "Kafin ta kwashe da dariya.
Wanda Zata iya ci taci kafin ta Sanya wasu Fridge wayarta ta janyo tare da Kiran affan sosai suka Sha hira cike da kewar juna affan ne ya ce.
"Ina wannan Babar da kika cemun ba Kakarki bace ,kusan kullum sai sunzo suyi ta buga Gidan inaji jiya Mai gadinku ya ce musu bakowa Gidan karkiga jarabar da ta dingayi Tana ta zagin mom dinki Wai Zata sayar Mata da d'a Kinga zagin da suka dingayiwa mom dinki ita da wannan lutetiyar".
"tsohuwar banza ce ai Dan Allah Affan idan ta Kara zuwa Ni na sanyaka ka harbeta da kwari da baka ko ka kad'e shaggu a kekenka Sannan karku sake ku fada musu inda su Mom da dad suke"Dariya sosai Affan yayi ya ce "Kai besty Kakartaki Nidai ba ruwana"Uwar kakata Allah kiyaye wannan munannar ta Zama kakata, banza Ni har ka batamun raima sai anjima",
Baccine ya kwasheta bayan Gama wayar.
Tunda Sabren ta Tashi taga ana ta Shirye Shirye part din na musamman tare da girki kala kala ita dai taga Shirin wannan yasha banban da Wanda ake kasa Shiru tayi hakan ya sanyata kallon Maryam dake gefenta Tana Danna Laptop ta ce .
'"Aunty Wai Shirin me ake tayi Naga tun safe gashi Yanzu har kusan la'ars ba a gamaba "Yaya Anwar ne zai shigo gari shiyasa"Waye to yaya Anwar din?.
ta tambaya "Shima yayankine daga Aunty farida saishi saini sai mufe Shima Nasan Baki sansa ba"Shima Kuma d'an mamyn katsina NE?Cike da kosawa da tambaya Maryam ta ce "Eh jekiyi salla ko azahar bakiyi ba "Make kafada tayi ta ce.
"Banyi to sai anjima"Wai meyasa Kika fiya Wasa da salla baby kefa ba Yarinya bace kin Isa ki fad'awa wasu "Turo Baki Gaba tayi ta ce "To Nidai nace Miki Yanzu bazanyiba kafin ta Haye gado ta janyo wayar Maryam tahau buga game,sanin ba yin zatayi ba ya Sanya Maryam kyaleta taci gaba da aikin da take.
Kamar ko yaushe duk zuwan da zaiyi tofa sai yasha bushe_bushe da kiraye_kiraye Wanda tun bayason abun harya hakura Dan ba yanda zaiyi Dole ,Sanye yake cikin manyan kaya irin na gidan sarauta masu tsananin masifar kyau saboda fad'an da mai martaba yake masa akan zuwa da kananun kaya ya sanya yanzu yake zuwa da manyan kaya kamshi ko duk inda ya gitta sai wajen yajima Yana kamshi Kai tsaye Bai zarce ko Ina ba Sai part din Ammynsa ,.
*Hajiya Talatu*
Ganin irin Shirin da ake a masarautar ne ya tabbatar Mata Yarima Anwar Yana tafe hakan ya sanyata fita tun safe ita da Ummul kulthum Tafiya sukayi Mai nisa Saida suka shiga har kasar Niger domin zuwa wajen sabon malamin da sukayi,.
magunguna ya Basu sosai ya ce"d'aya kina komawa Gidan ki turare d'akinki dashi Gaba Daya muddin ya shaki hayakinnan tofa aiki ya Gama sai yanda kikayi dashi ko uwarsa Bata Isa ta fad'a Abu ya tsallake ba".
"Kafin ya fiddo wani ruwa a kwalba ya mikawa Ummul khairi ya ce "Ke Kuma wanna Lokacin da zai shigo ki wanke fuskarki ki tabbatar Kunyi Ido hudu dashi tofa zance ya kare da kanshi zai dinga bibiyarki harsai kinja Masa aji ,Kafin ya dauko wata kwalbar turare ya ce "Wannan Kuma ki shafa sa Shima ki tabbatar ya shaki kamshin ba k'aramun Aiki muka Sha ba wajen hada magungunan Nan Sha Yanxu Ne magani Yanzu da kanku zakuzo Kuna mini godiya Amma akwai sharad'i guda Kar a sake maganin ya Tab'a k'asa Koda Wasa Kar ya ta'ba k'asa Dan k'asa itace makarin hadin magungunan muddin ya taba k'asa Aiki ya b'aci"bama zai Taba ba malam nagode Allah saka da alkhairi kafin ta dauko makudan kud'i ta Aje masa ta ce "tukuicinka Yana Gaba malam sai aiki yaci Yanzu muna sauri na tabbatarma da Kila ya iso saimun dawo.
____"Irin tarbar da yake samu a Koda yaushe ita ya Samu a wajen mamyn Nasa da kanta ta dinga b'ara Masa ayaba Tana basa Hira suke sosai irin ta d'a da uwa,Daga ita saishi a Palourn mamy ce ta ce "Wai ya maganar transfer taka kuwa gwarzona nifa nafison ganinka kullum kusa Dani bana son nesan Nan"Yana murmushi ya ce "Mamy keda Abba kunki Hakura da transfer Nan,Inajin Dadin aiki a chan ne shiyasa ,ya mai jikin tun Kuna abujar naso naje na duba sa Sha anin Aiki ya Hana Yanxu Suna madinar har Auntyn?
"E to da sauki za ace Amma har Yanzu dai Bai farfado ba"Cikin nuna rashin Jin dadinsa ya ce "Allahsarki Allah ya bashi lfy Ina Yartasu kuma"Amen ya Allah khadija Tana Nan na taho da ita Tana ciki Daman Ina tason kazo muga wace Makaranta yakamata a kaita saika kaita s s one tunda tayi jsce".
"inaga ammy kowace ma da an kaita da a jira zuwana ba ma "ya fada cike da ladabi"Girgiza Masa Kai tayi ta ce"a a a Kasan harkar karatu Dole saida namiji ai ba kurewa lokaci yayi ba "To shikenan mamy inaga mezai Hana a hadata da Mufeda kawai kamar zaifi"?Eh Daman Dole a hadasu Makaranta Daya da wani Dan y'artawa dai Har Yanzu akwai Saura"to shikenan' gobe Saita Shirya tare da Mufe naje na kaita din tunda Gobe Tuesday".
Tunawa da har la'asr ta wuce ya Sanya Sabren tunowa da maganarsu da Haidar ya ce zai yo Mata sayayya yau Aiko ba shiri ta Aje laptop din Daga ita sai hula ko takalmi Babu ta ruga a guje Mamy ganin fitowarta da gudu Cikin daga murya ta ce.
"Ke Khadija Ina zaku haka Cikin gudu "Ina Sabren bama ta saurareta ba tuni tayi Gaba Hankalin Anawar na kan mamy baima ganta ba yaji dai 'Karan gudu Sabren gudu ta dingayi Tana haki a zatanta mamy ta Sanya an biyota Daidai Mama Talatu ta shigo Tana niyyar nufa Bangarenta rike da kullum magungunan Data rike a hannu gudun matsala Daidai Sabren dayo wajen ji kake Gam ta tunkudeta Gabaki Daya magungunan suka baje a k'asa sabren ko bama ta tsaya tabi takantaba tasandai ta Buge mutum Amma batasan ko Meye ba.
"wani irin ihu mama talatu tayi tare da Dora hannu aka tsundumawa Sabren zagi tahau kutuntumawa Wanda babu dadin ji Takaici Daya ishi kulthum kuka ta fashe dashi ta ce shikenan duk tafiyar da wahalar da mukayi ta tafi a banza Kai Amma Allah tsinewa tsinanniyar yarinyar chan ko Yar gidan uban wacece,"Mama talatu ko Zaman Yan bori tayi .
Sabren Saida takai inda suka hadu da Haidar kafin ta tsaya Tana haki ,Haidar Daman Yana wajen Cikin sauri ya taso Yana tambayarta meyasa tayi gudu Haka Dan yasan tazarar tsakanin Part din Mamy da Nan nasu hakan yasa basama wani haduwa Dan idan ba dalili ba wani ma saisuyi wata Basu hadu ba Tana haki ta ce "Mamy Dan karta Sanya a biyoni shiyasa nayi gudun"Ohh sorry my pretty ya fada Yana son taba hannunta Yana tsoron karta masa jaraba dan ya lura jarababbiya ce.
"Saida ta Gama hak'in kafin ya Bata sayayyar da yayo Mata tun a Nan ta bude robar ice cream tare da Fara Sha har wani lumshe Ido take Dadi yakai Mata Karo da wannan abun Haidar ya samu damar kamo hannunta a hankali cike da barikanci ya ce.
"Wow pretty hannunki laushi me kike shafa Masa Nima ki sammun na dinga shafawa "kwata kwata hankalin Sabren Bai kawo Mata komai ba ta ce "Ba Komai Fa Nake shafawa wlh Haka yake "sosai Haidar ya dinga janta da hira Wanda a Haka yadinga murza hannunta ita kuwa Sakaran ko a kanta Dadi yakai Mata Karo Saida ta Gama ciye ciyenta kafin ta Mike wajen 5 tace Zata wuce.
"Saida yarakata gab da part din kafin ya juya yanajin wani Dadi a ransa ya Samu daman yanda yakeso yayi da yarinyar da tunda yaga yarinyar ya kwadaitu da ita dukda ba wata babba bace shida yake Hulda da manyan babies Amma Gaba Daya baitabajin yanayi irin Wanda yake shigaba idan gashi ga yarinyar sigarinshi ya fiddo ya kunna tare da komawa ciki,.
Dadi Sabren Taji sosai da Bata iske Mamy a Palour ba Kai tsaye dakinsu ta wuce Tana Jin Dadi ta samu Wanda zai dinga Mata sayayya,around 9pm Suna dining Suna dinner Mamy ta kalli Sabren ta ce"Gobe ki Shirya tunda safe Tare zaku tafi school da mufeda yayanku zai kaiki ayi Miki register "Batare da gardama ba Sabren ta ce"To mamy"Dan Koba komai ta samu hanyar da Zata dinga ganin gari.
Washegari tunda safe Saida ta riga ma mufe shiryawa Around 7:30 sungama shiri har break fast sunyi d'akin mamy suka biya sukayi Mata sallama kafin su fito Kai tsaye inda Yayan nasu yake Tsayawa da motarsa Mufe tajata suka nufa Lokacin Yana ciiki back seat Mufe ta shiga Sabren na niyyar shiga baya mufe ta ce "ki shiga gaba Mana ba kowa".
Daman ita sabren tafison zaman Gaba a Mota ba musu ta bude murfin motar tare da shiga ba laifi ta danyi shigar kirki tunda ta Dora hijab a jiens din dake jikinta dukda Bata Kai Mata gwuiwa ba ,"Good morning Yaya"Cewar mufe daga Baya"Morning too how was your night"Alhamdulilah"ta bashi amsa".
Jin kamar tasan Mai muryar ne ya Sanya Sabren juyawa tare da kallonshi Daidai shima ya juyo Dan ya kalli ta rufe k'ofar yaja idanunsu ya sartse Cikin na juna ,wara idanu sosai Sabren tayi Dan son tabbatar da shi dinne shima kallon mamaki yake Mata cike da tsoro Sabren ta wara manyan idanunta ta ce "Yaya Beauty Kaine da gaske..........✍️
*Alhamdulilla anan na kawo karshen free page kuma karshen book one na wannan littafin nawa Mai take khadijatul sabren kamar yanda na fad'a Wanda suka biya ne kawai suke da daman cigaba da karanta gawurtaccen Littafi da yazo daga cikin gawurtattu biyar salon wasan littafin khadijatul sabren yanzu zai fara zaku biya kudin ku ne ta hanyar da muka rubuta muku a kasa Ki saya da zuciya daya Ba dan ki fitar ba y'ar uwa shi Allah baya yafe hakki duk kankantarsa saimun hade a paid group masoyan Gaskiya da Gaskiya masu ci da guminsu domin neman Karin bayani a tuntub'eni akan number wayata kamar haka *** Miss Hajon ce dai da ta nishad'antar da ku a littafanta irinsu ,Ni da yaya Arman,Auren wata Tara da sauransu*
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
***
Masu turo kati MTN ta wannan number.
***
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
***
*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿