Page 1
🧟♀️ *WATA SOYAYYAR!* 🧟♀️
*_Labari/Rubutawa_*
*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*
( _Meenat A Yandoma_ )
tare da
*ZAINAB MUHAMMAD*
( _Indian Girl_ )
*NOTE*
_Labarin nan zamu rubuta shi ne a yadda yazo, duk abinda kuka gani mun rubuta a haka aka tsara labarin._
*GARGAƊI!*
_A guji yi mana amfani da labari ta ko wace hanya sai tare da izinin mu_
*PAGE 1️⃣&2️⃣*
..."Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, lahaula walaƙuwwata illa billah, Mama wayyo na shiga uku."
Fatima ta ƙarasa maganar tare da fitowa daga ɗakin a guje tamkar wadda aka harbo a kibiya.
Ɗago kanta tayi a gigice.
"Fatima lafiya ko wani ne ya rasu, sanar dani."
Mahaifiyar ta dake tsugune tana gyaran wake ta faɗa.
"Mama na shiga Ukku na lalace, alkamis yayi mani miss call ina barci, mama yaya zanyi"?.
Fatima ta ƙarasa maganar hawaye na ƙoƙarin zubo mata.
Girgiza kai kawai mahaifiyar fatima tayi domin ta fahimci babu abinda ɗiyar ta ke buƙata a yanzu tamkar addu'a, taga soyayya kuma taga masoya da dama a rayuwar ta amma bata taga gamo da masoyayya irin ta fatima da alkamis ba.
Ganin Fatima na ƙoƙarin fita yasa mahaifiyar ta saurin riƙo hannun ta, Umar yayan fatima shine ya fito daga cikin ɗakinsu a fusace.
"Mama dan Allah yau ki gyale ni inyi ma yarinyar nan dukan kawo wuƙa, ki barni in tattaka ta, Alkamis ɗin banza Alhamis ɗin wofi, dan Allah mama ki kauce ko yau ɗaya ne in koya mata hankali."
Umar ya ƙarasa maganar yana huci tamkar kububuwa.
"Wayyo Allah na Abba na kana ina? Wayyo ya zagi Alkamis mama kina gani ba zaki ce komi ba, zuciya ta zata fashe, zata tarwatse."
Fatima ke ihu tana surutai, wannan abun da da ta ke shi ya ƙara tunzura zuciyar Umar bai san lokacin daya fizgota daga bayan mahaifiyar su ba ya shiga sauke ma belt ɗin a jiki.
Ihu take tana ƙoƙarin gudu amma riƙon da yayi mata ba na wasa bane, mahaifiyar Fatima akwai kara da kawai ci duk da cewa fatima ita ce auta amma alkunya tasa ta kasa kwatar ɗiyar ta a wurin Umar, inna Habiba Abokiyar zaman maman Fatima data shiga makwaftan su jin ihun yayi yawa yasa ta fitowa a gigice ta faɗo gidan.
"Umar baka da hankali, kashe ta zaka yi, Maman Fatima kina ganin shi ba zaki hana shi ba"?
Inna Habibi ta faɗa yayin da tayi nasarar kwato fatima.
Yaƙe wanda yafi kuka ciwo Mahaifiyar fatima tayi.
"Habiba Fatima bata ji baki san halinta bane."
"Yo ko bansan halinta ba ina dalili kawai daga shiga ta makwafta zai same ta ya fara jibga kamar yana danbe da sa'ar shi, umari ka fita idona in rufe."
"Wayyo baya, ya gota mani awaza, inna Habibi duba mani ki gani awazata nan"?
Fatima ta ƙarasa maganar tana dire-dire tamkar ƙaramar yarinya, ganin da gaske rigar zata ɗage tasan Habiba riƙe hannu fatima.
"Yau ni naga abinda ya fi zare tsayi, a gaban Umar zaki ɗage riga Fatima."
Inna Habibi ta faɗa.
"Wallahi duk ke kika sa yarinyar nan ta renani ki barni in koya mata hankali."
Cewar Umar.
"Kana sake buguna sai na huce akan waccan budurwar taka me kama da muciya, da wasu idanu kamar na besfa."
Fatima ta ƙarasa maganar tare da shigewa ɗaki ta banko ƙofa sakamakon biyota da Umar yayi.
Maman Fatima da abokiyar zamanta dariya abun ya basu.
"Yaya, Al'amarin Fatima da Alkamis yana bani tsoro, Tunda nike ban ta6a ganin soyayyar irin wadda fatima ke nuna ma Alkamis ba, nasan zargi haramun ne amma ina kyautata zaton anya ba asiri Alkamis yayi ma Fatima ba, ki duba ki gani rabin soyayyar da take mashi bai yi mata ita."
Inna Habiba ta faɗa.
"Habiba ya zanyi, addu'a kaɗai zamu bi fatima da ita, Fatima tayi nisa bata jin kira tsorona Allah kada Alkamis ya kashe mani yarinya ya wata rana."
Ta ƙarasa maganar da karyayyar murya.
"Subhanallah! Yaya ki daina wannan maganar insha Allah hakan ba zata faru ba, Yaya nifa ji nayi ana cewa Alkamis ɗan neman mata ne ga kuma shaye-shaye da yake yi, kada ya lalata mana rayuwar yarinya."
"Habiba nima na samu wannan labarin domin yana ɗaya daga cikin abinda yasa Umar ke tsaye kan Fatima ko kaɗan bai son alaƙar dake tsakanin su da Alkamis."
"Allah ka tsare mana Fatima domin ina da tabbacin mun ba fatima kyakkyawar tarbiyya kuma insha Allahu ba zata bamu kunya ba."
Inna Habiba ta faɗa.
Ganin rana ta fara yasa su shiga madafar abinci a tare, Fatima kuwa kwanciya tayi saman kujerar Inna habiba tare da kallon silin ɗin daƙin zuciyar ta cunkushe da tunanin hukuncin da Alkamis zai yi mata na rashin ɗaukar kiran shi da tayi.
"An jima idan kun taso makaranta ki biya ki bashi haƙuri."
Wata zucitar ta shawarce ta.
Bata fito waje ba sai da taji mahaifinta ya shigo gidan, bayan tayi ma shi sannu da zuwa take zayyane mashi abinda ya faru, murmushi yayi domin yasan laifin fatima ne, amma dan ya kwantar mata da hankali sai cewa yayi.
"Yi haƙuri mama na Asibiti zamu je ko wurin masu ɗorin gargajiya a duba awazar."
Ya ƙarasa maganar yana me danne dariyar dake son kubce ma shi.
"Abba a gyale awazar aita warke."
"Ki barni da Umar in ya shigo zai gamu dani, waya ce mashi ana bugun uwar masu gida, je kiyi shirin islamiya domin naga lokaci ya kusa."
Wani farin ciki ne ya ziyarci Fatima domin koba komi zata samu damar bawa Alkamis haƙuri, fatima ns shiryawa gidan su Farida ƙawarta ta nufa, Farida ita ce ƙawa ɗaya tilo tun tasowar su wannan ƙawance yake har kawo yanzu.
Bayan sun gaisa da mahaifiyar Farida ɗakin da zai sadata da ƙawar tata ta shige
"Wai kwance ma kike baki shirya bs, aiko tafiya ta zanyi in barki."
Fatima ta ƙarasa maganar tare da jefa ma farida Harara.
"Haba dai Babyn Alkamis ai nasan ba zaki tafi ki barni ba sallah kawai zanyi mu wuce."
Fatima kuwa jin an ambaci rabin ranta ya sanya ta washe baki.
"Kin wanke kan ki, muyi sauri kada mu makara."
"Ai ni kona makara duk bugun da za'ayi mani sam bazan ji shi ba, indai saboda Alkamis ne."
Babu jimawa suka fito tare da wucewa makarantar, duk yadda Fatima ta baza idanu ko da Allah zai sa taga Alkamis amma shuru bata ganshi ba, haka suka ƙarasa makarantar Allah ya so su malamin ƙur'ani bai kaiga shiga ba, da sauri suka shige ajin.
Koda aka tayar dasu Fatima bata 6oye ma farida inda zata je ba.
"Ni kau da zan faɗa maki kiji da nace kada kije wurin AlkamiS, Fatima ba kyau kina yawan zuwa wurin shi wannan ba al'adar mu bace."
Farida ta faɗa cikin tattausar murya domin tasan koda tsawa tati ma Fatima indai akan Alƙasim ne babu abinda zata fasa.
"Na sani Farida! Kin san fa nayi mashi laifi dole ne inje in bashi haƙuri in ba haka ba zanyi mummunan fushi dani."
"Sai me idan yayi fushin dake, wallahi Fatima kina ƙona mani rai wani lokacin, kin tsaya a kan namiji ɗaya yana baki wahala tamkar zai sabautar da rayuwar ki, ban taba ganin soyayyar da budurwa ke zuwa zance ba sai taki, ya zage ki yayi maki duka amma ba zaki rabu dashi ba, Fatima ba masoya kika, duk da kasancewar shi ɗan shaye-shaye ɗan neman mata amma kina nan maƙale dashi, baki gudun wata rana ya lalata maki rayuwa"?.
"Ya ishe ki Farida, idan ba zaki tayani son abinda nike so ba kada kice zaki kushe shi, tunda ba zaki raka ni ba kinga tafiya ta."
Tana kaiwa nan ta fizgi jikkar ta ta yi gaba.
Ganin shagon buɗe ya tabbar ma Fatima yana nan bai fita ba, dan haka gabanta ne yayi wata mummunar faɗuwa, tamkar kazar da aka jefa da gishiri haka Fatima ta fara takawa zuwa cikin ɗakin, bakin ta ɗauke da sallama ta ɗaga Labulen ɗakin, abinda ta gani ne ya sanyata sakin labulen ta fasa ƙarar data ankarar dashi cewa wani ya shigo, duk da kasancewar yana cikin maye haka ya miƙe tare da takowa gaban Fatima yana layi, wami wawan mari ya ɗauke ta dashi wanda ya haddasa mata ɗaukewar ganin ta na wucin gadi.
"Ke saboda kin rena mani wayo shine zani kiraki amma ki ƙi ɗauka, yau kwana nawa baki zo zance ba, kodan kinga na ɗaga maki da bugu kwanan nan ne"?.
Ya ƙarasa maganar cikin maye.
Kumci a dafe hawaye na zarya ta duƙa har kasa tare da rike ƙafar shi.
"Dan Allah Alkamis kayi haƙuri kwana biyu bani jin daɗi shiyasa banzo ba, danAllh wace ce waccan zaune a gefen ka"?.
Fatima ta ƙarasa maganar tana share hawaye tare da jin wani abu ya dokare mata zuciya.
"Cika ta ce, babu ruwan ki da ita, ke Beb maza ki fice ki bamu wuri zamu yi magana."
Wata muguwar harara wadda aka kira da Beb ta wurga ma Fatima tare da jan tsoki ta fice daga ɗakin.
"Oww ba zaki tashi ki gyara mana ɗakin ba haka zaki bar mana shi"?.
"Zani gyara yi haƙuri."
Fatima ta faɗa tare da ajiye jikkar islamiyyar ta tahau aikin.
Tana yi hawaye nabin fuskarta domin ansha faɗa mata Alkamis ɗan neman mata ne amma sam bata ta6a yarda ba sai yau da idanun ta suka gane mata, "na gama aikin zani wuce gida."
Ta faɗa kanta a ƙasa.
"Saura yau ma in ji shuru baki zo zancen ba tabbas jikin ki sai ya gaya maki, maza fice ma ni daga ɗaki domin yanzu Beb ɗi na zata dawo, "inshaAllah zani dawo ba zani sake 6ata maka rai ba, kaji tausayi na ina sonka ina matuƙar ƙaunar ka in babu kai mutuwa zanyi."
Kukan da yaci ƙarfin ta ne ya sanya ta yin shuru.
"Najii ki fice mani daga ɗaki."
Babu yadda zata yi haka ta fito daga ɗakin hawaye nabin fuskarta, komi Alkamis zai yi mata ba zata iya cire soyayyar shi a zuciyar ta ba, Allah ne ya ɗora mata soyayar Alkamis babu yadda ta iya, haka ta ratso hanya hawaye nabin fuskar ta, lokacin da ta isa gida har an gama sallar magriba.
Bata damu da abinda zata taras a cikin gidan ba damuwar ta ɗaya ita ce ya zata yi ta fita domin zuwa zance wurin Alkamis, bakin ta ɗauke da Sallama ta shiga gidan, idanun jama'a ne suka dawo kanta, da sauri inna Habiba ta fara tambayar ta lafita.
"Kiyi magana Fatima, sawun yatsu mike gani a fuskar ki sannan ga kuka kina yi."
"Fatima ba magana ake maki ba, daga ina kike, ina kika je"?.
Mahaifiyarta ta faɗa.
"Naje wurin Alkamis nan ta kwashe kaf abinda ya faru ta sanar dasu."
Fatima yarinya ce me faɗar gaskiya koda zata jefa ta cikin matsala domin tun farko an tarbiyance ta da faɗar gaskiya shiyasa komi zai faru bata maka ƙarya.
Salati da Sallallami suka hau yi.
"Fatima me kike so ki mayar da kanki, ɗakin saurayi, Fatima kina so ki bata mana tarbiyyar gida kina so kiyi mana baƙin fentin da bai taba goguwa har abada."
Mahaifiyar Fatima ta faɗa ranta a matuƙar 6ace.
"Kiyi haƙuri yaya, wannan al'amari sai dai addu'a, tun ina ganin wannan lamari a matsayin shirme sai gashi abu ya girmama, wuce kiyi sallah ki ɗauki abincin ki kici."
Inna Habiba ta faɗa.
Jiki ba kwari haka Fatima tayi sallah ta tasa abincin a gaba amma ta kasa koda loma ɗaya ce tunanin ta shine ya za'ayi ta fita ba tare da mahaifiyarta sun gane ba, Usman ne ya shigo gidan jin Fatima shuru yasa shi cewa "wai ina ta Alkamis ne? Tunda na shigo gidan naji shuru banyi tozali da ita ba."
Da sauri ta fito daga ɗakin domin tafi shaƙuwa da Usman duk da kasancewar shi ba uwar su ɗaya ba.
"Ta Alkamis barci kika yi na ganki sukuku"?.
Murmushi tayi domin a duniya bata 6oye ma Usman komi ta yi wata irin shaƙuwa da shi.
"Kai na ke mani ciwo ."
"Kinsha magani"?.
"A'a."
"To je ki ɗauko magani kisha."
"Ai banci abinci ba."
"Maza wanko hannunki kizo muci ga abinci nan."
Umar da shigowar shi kenan yaci karo da Usman yana cin abinci da Fatima tsoki yayi.
"Duk ku ke sake sangarta yarinyar nan, tana rena mutane."
"Bakomi a barmu muci abincin mu, in ban kula da yar ƙanwata ba waye zai kular mani da ita, maza ci abincin ki ki ƙoshi."
Ɗago kai tayi ta harari Umar ganin zai gano ta tayi saurin kauda kanta.
Suna gama cin abinci Fatima tace barci take ji kanta ke mata ciwo, ɗakin inna Habiba ta shige domin tun da ta yi wayo nan take kwana, jin tsakar gidan tayi shuru, inna Habiba kuwa tana ɗakin Maman fatima suna hira, a hankali ta lalla6a ta fice daga gidan ba tare da tsoron duhun da gari yay ba haka ta nufi wurin Alkamis....
*NASAN WASU ZASU CE SUN SAN NI DA LABARIN ALJANU YAU KUMA SAI KUKA JI NA SOYAYYA, TO KU KWANTAR DA HANKALIN KU DOMIN AINAHIN LABARIN BAI FARA BA, MUNA NAN ZUWA WURIN ALJANNUN🚶🏼♀️🚶🏼♀️*
*MEENART......✍🏼*
***