FreeArewaPen original
WATA SOYAYYAR
- 1views
- 37chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
FATALWA BAƘAR TAFIYA SAKACI SALMA RAZANI WANI ƘARNI RUWA BIYU ƘULLALLIYA
Sample · Page 1
🧟♀️ *WATA SOYAYYAR!* 🧟♀️ *_Labari/Rubutawa_**AMINA ABUBAKAR YANDOMA* ( _Meenat A Yandoma_ ) tare da *ZAINAB MUHAMMAD* ( _Indian Girl_ )*NOTE*_Labarin nan zamu rubuta shi ne a yadda yazo, duk abinda kuka gani mun rubuta a haka aka tsara labarin._ *GARGAƊI!*_A guji yi mana amfani da labari ta ko wace hanya sai tare da izinin mu_*PAGE 1️⃣&2️⃣* ..."Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, lahaula walaƙuwwata illa billah, Mama wayyo na shiga uku."Fatima ta ƙarasa maganar tare da fitowa daga ɗakin a guje tamkar wadda aka harbo a kibiya.Ɗago kanta tayi a gigice."Fatima lafiya ko wani ne ya rasu, sanar dani."Mahaifiyar ta dake tsugune tana gyaran wake ta faɗa."Mama na shiga Ukku na lalace, alkamis yayi mani miss call ina barci, mama yaya zanyi"?.Fatima ta ƙarasa maganar hawaye na ƙoƙarin zubo mata.Girgiza kai kawai mahaifiyar fatima tayi domin ta fahimci babu abinda ɗiyar ta ke buƙata a yanzu tamkar addu'a, taga soyayya kuma taga masoya da dama a rayuwar ta amma bata taga gamo da masoyayya irin ta fatima da alkamis ba.Ganin Fatima na ƙoƙarin fita yasa mahaifiyar ta saurin riƙo hannun ta, Umar yayan fatima shine ya fito daga cikin ɗakinsu a fusace."Mama dan Allah yau ki gyale ni inyi ma yarinyar nan dukan kawo wuƙa, ki barni in tattaka ta, Alkamis ɗin banza Alhamis ɗin wofi, dan Allah mama ki kauce ko yau ɗaya ne in koya mata hankali."Umar ya ƙarasa maganar yana huci tamkar kububuwa."Wayyo Allah na Abba na kana ina? Wayyo ya zagi Alkamis mama kina gani ba zaki ce komi ba, zuciya ta zata fashe, zata tarwatse."Fatima ke ihu tana surutai, wannan abun da da ta ke shi ya ƙara tunzura zuciyar Umar bai san lokacin daya fizgota daga bayan mahaifiyar su ba ya shiga sauke ma belt ɗin a jiki.Ihu take tana ƙoƙarin gudu amma riƙon da yayi mata ba na wasa bane, mahaifiyar Fatima akwai kara da kawai ci duk da cewa fatima ita ce auta amma alkunya tasa ta kasa kwatar ɗiyar ta a wurin Umar, inna Habiba Abokiyar zaman maman Fatima data shiga makwaftan su jin ihun yayi yawa yasa ta fitowa a gigice ta faɗo gidan."Umar baka da hankali, kashe ta zaka yi, Maman Fatima kina ganin shi ba zaki hana shi ba"?Inna Habibi ta faɗa yayin da tayi nasarar kwato fatima.Yaƙe wanda yafi kuka ciwo Mahaifiyar fatima tayi."Habiba Fatima bata ji baki san halinta bane.""Yo ko bansan halinta ba ina dalili kawai daga shiga ta makwafta zai same ta ya fara jibga kamar yana danbe da sa'ar shi, umari ka fita idona in rufe.""Wayyo baya, ya gota mani awaza, inna Habibi duba mani ki gani awazata nan"?Fatima ta ƙarasa maganar tana dire-dire tamkar ƙaramar yarinya, ganin da gaske rigar zata ɗage tasan Habiba riƙe hannu fatima."...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.