CHAPTER 3-4
by @autarmama
👑PRINCE SAPWAN👑
*STORY AND WRITTING BY SALMEERT (AUTAR MAMA , ƳAR LELEN ROYAL STAR) AND MARYAM YUSUF (OMMU JUWAIRIYYA)*
*YARDA MUKA FARA LITTAFINAN RANAR 20 MAY 2022, ALLAH KA BAMU IKON GAMASHI LAFIYA*
*WANNAN LITTAFIN ƘIƘIRAREN LABARINE BA MUYISHI DAN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA, IDAN YA YI DAI-DAI DA TSARIN GIDANKU KO MASARAUTARKU TO* *ANYI MANA AFUWA BADA SANI BANE*
*BA MU YARDA WANI KO WATA YA CHANJA MANA TSARI KO YANAYIN LITTAFINAN BA*
*WANNAN LITTAFIN NA KUƊINE #200 NE KACHAL KUƊINSHI, KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉***
nagode kwarai da gaske💃💃
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
PAGE 3&4
"""""""""""""""""""Tana nuna jikinta, "To Allah ya yi miki Albarka Insha Allah sai kin zama gatanmu baki daya", ta fada tana maida hawayen idonta.
Sapna kuwa dauke kanta tayi, bata nuna tama ganiba, a hankali ta nufi gurin wanke-wanken tana dafe ciki tare da ciza lips alamar tana jin ciwon har cikin kwakwalwar kanta, A hankali take wanke-wanke, ball taji anyo da wani kwano har saida ya bugar mata kafa wani irin azaba ce ta ratsa har cikin tsakiyar kanta.
ko dagowa batayi ba dan tasan ko waye zai iya yin haka, ba ko Sallama ta shigo gidan tana fito kamar ƴar arnaku buta ta dauko toilet ta shige da waka abakinta babu ko Addu'ah girgiza kai Sapna tayi tareda cigaba da yin wanke-wanken ta,
"Ke bakar annoba, kiyi maza ki gama wanke-wanken nan ki zo ki haza murhu don ban ga uban wanda zai dafa miki abinci ba" cewar Inna tana maka mata harara, ita dai Sapna kanzil ba ta ce ba, kawai ta cigaba da yin wanke-wanken ta, Malam kuwa abun duniya ya ishe shi,
Yana son yayi magana amma yana gudun yace wani abu Inna ta hau shi da zagi domin kuwa sarai sanin halin matar tashi da yayi zata iya zabga mishi ashar ko agaban waye, Ummi shiru tayi bata iya ce komai ba amma maganar gaskiya ba kadan take tausaya ma Sapna ba, a kullum adduar ta guda shine Allah ya kawo mata miji na gari tayi aure ta huta abun ta,
Sapna bata wani jima ba ta kammala wanke-wanke, nan take ta shiga kazantaciyar kitchen nasu ta hada wuta yanda Inna ta umurce ta, tana yi tana zubda hawayen bakin ciki, don ba kadan take jin jiki ba, ga aikin da Inna ta sake saka ta, ita sam batada mutumci a idon yan gidan ba mai kaunar ta in ka cire Ummi wani lokacin Malam na dan son ya nuna mata kula amma kuma sai ya kasa, ita dai bata san miye dalili ba, amma ai in da sab'o yaci ace ta saba,
Adduar ta a koda yaushe shine Allah ya bayyanar da mahaifiyar ta, domin kuwa Ummi tasha bata labarin cewa Umman ta bata mutu ba, kawai dai basu san in da ta nufa bane, domin kuwa Ummi bata taba gaya mata cewa Umman ta haukacwa tayi ba,
**************
"Jakadiya kiyi yanda nace ki aikata, wallahi idan kika bani kunya zaman ki ya kawo karshe a cikin fadar nan", cewar Fulani tana makawa Jakadiya harara, "Ranki ya dade duk yanda kika ce ayi hakan ma za'a yi Uwar'gida sarautar mata, Allah ya ja da zamanin ki,
"Ya isa karki cika ni da surutu" Fulani ta dakatar da ita tareda nuna mata hannu alamar ta fita, ba tareda bata lokaci ba ta fita tana mai kimtsa abubuwa da dama aran ta,
"Yau kinmanin kwana uku kenan amma har yanzu babu alamar ciwo tattare da dan iskan yaro nan hanya kuwa Jakadiya ta aiwatar da abunda na umurce ta tayi cewar Fulani ta na kallon Waziri,
A dan rude Waziri ya fara magana "Fulani me kike nufi, Jakadiya kika bawa magani ta sakawa Yarima Sapwan a abinci lalle kin yi wauta, kar ki sake ki kara bata, kuma yanzu ki san yanda kikai kika nuna mata wannan magani ba wai na cutarwa ne ko wani abu ba, saboda gudun asirin mu ya tonu,
Kii tuna, jakadiya tana tareda Gimbiya Khadija komai ma zata iya gaya mata, "A'a Waziri kwantar da hankalin ka, ai na riga da na mata kashedi in har ta yarda ta gaya ma wani toh zata ziyarce lahira ne, domin kuwa a ranar bazata kara koda minti daya bane a duniya,
"Hmmm toh shikenan naji zancen ki, amma ki kula sosai, ki bari mu bi ahankali sai mu kashe Dan banza ba tareda ya bamu ciwon kai ba, cewar Waziri, Fulani wani Irin murmurshi tayi wanda ita kadai tasan ma'anar sa, bata sake kallon Waziri ba belle yayi tunanin zata yi magana,
****************
Kwance yake saman tafkeken gadon sa, wanda gaba dai ya tafi da tunani na, da alama dai itama Yar lelen royal gadon ya tafi da tunanin ta, domin kuwa gado ne mai kyau ya hadu iya haduwa, ya salam na iya furta ba tareda nace komai ba, Prince Sapwan sai danne-danne yake a laptop dinsa da alama dai wani aiki mai muhimmanci yake, domin kuwa gaba dai ya tattara hankalinsa kan laptop din,
Gani nayi ya dafa kirjin sa, yana son yin magana amma ya kasa furta komai, daga nan kuma bai sake sanin inda hankalin sa yake ba,
Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita ta na fadin "Yarima kayiwa Allah ka mun magana, me yake damun ka ne, me kaci, ka gaya min don Allah ta fada ya yinda ta sake fashe da wani irin kuka mai cin rai, sosai jikin mai martaba yayi sanyi nan take ya shiga rarrashin ta, shi kan sa ji yake kamar ya dinga kurma ihu, domin kuwa a gaskiya ya tsorota da wannan yanayi na d'an nasa addu'o'i ya shiga tofa masa tareda karanto ayatul kursiyu,
Wayan sa ne ta shiga ruri nan take ya daga tareda cewa "Doctor ka shigo, doctor shigowa yayi tareda gaishe da Mai martaba, sarki ko amsa masa bai yi ba "don Allah ka gaya min me yake damun Yarima, Doctor ka ga ya min gaskiya idan ma matsalar babba ne kawai sai na fita dashi kasar waje, Sarki ya fada a sanyaye,
Kalo daya zakayiwa Price Sapwan ka shaida komai bazai iya yiwa kansa ba a halin yanzu domin kuwa kwance yake kamar mattace amma idon shi bude, komai baya iya wa kansa tunda safe da abun ya faru dashi, Gimbiya Khadija kuwa taci kuka har ta godewa ALLAH,
"Dube-dube likita ya shiga yi wa Prince Sap nan take ya juya ya kalle Sarki tareda cewa, "mai martaba kayi hakuri don Allah bisaga maganar da zan fada domin kuwa Yarima Sapwan yayi lossing din kwakwalwarsa a halin yanzu ba abunda zai iya tuna, kuma ba abunda zai iya yiwa kan sa,
Ai bai ida zancen sa ba Gimbiya ta fashe da kuka mai taba zuciyar mai saurare, sosai ta shiga rera kuka tana jin tausayin dan nata, nan take sauran matan gida suka fara shigowa daya bayan daya, ai kuwa nan take ko ina ya dau zancen rashin lafiyar Prince Sap, kowa ya girgiza ba kadan ba, ya yinda murna wajen Fulani da Kilishi ba'a ko magana, amma fa a boye,
Mamaki Fulani ta shiga yi ita dai bata san ta masa komai ba, amma tunda tasan daman ba ita kadai ce ke bakin cikin sa ba, shiyasa nan take ta bawa kan ta amsar cewa aikin Kilishi ne,
Magani kala-kala babu wanda Sarki baiyyi ba, kasashen waje kuwa ba inda ba'a kai Prince Sap ba, amma ko alamar chanji babu ciwo kullum sai gaba yake tayi, kusan wata biyar kenan da rashin lafiyar Sapwan, babu in da masu je, Gimbiya kuwa yanzu tama daina kuka ta barwa Allah komai,
*******************
Da sauri ta fito daga cikin rubaben dakin nata, sanadiyar wani irin aman da take ji, tuwon da taci jiya duk ya bata mata ciki, ni dai sai kallon ta nake tayi domin kuwa yarinyar kyakyawa ce ajin farko, sai da Yar lelen royal ta taboni tana cewa Oum Juju zaki chinye diyar mutane😂 ai kuwa nayi maza na kauda idona daga kallon ta,
Inna ce ta fito tana kururuwa tana cewa "Innahu min Sulaimana wa innahu Bismillahi Rahmani Raheem, me nake gani haka, Sapna ba dai ciki ne dake ba"
Sapna a rude ta d'ago tareda fashewa da kuka tana fadin "Wallahi ni ba ciki ne dani ba kar ki min sharri, Inna bude baki tayi tana mamakin Sapna, domin kuwa koda wasa Sapna bata taba gardama da ita ba, amma ga shi nan yau tayi,
Ummi ce ta fito daga cikin dakin tana fadin "Yoo kuma sharrin da zaki mata kenan, domin kuwa taji duk abunda ke wakana a tsakanin su, Inna don Allah kiyi hakuri ki shafa mata lafiya, kin dai san tun jiya bata jin dadi, Inna bata ce da Ummi komai ba fashe wani mugun harara da ta watsa mata,
"Sannu Sapna, Allah ya sawwake" cewar Ummi tana mai kara jin tausayin Sapna, "Yauwa" Sapna ta fada da kyar, Ummi wanke mata fuska tayi tareda gyara mata jikin ta, suka koma daki, ko minti biyar basu yi ba Inna ta kwala mata kira,
"Ke shegeya ki fito ki fa dora sanwa, don dai bazai yu ba na dafa abinci kuma kiyi zaune-zaune ki ci ba, uban ki ma yaci, saboda haka wlh ko mutuwa zakiyi sai kin dafa abinci, "Haba don Allah Inna ki bari ni nazo na dafa" cewar Ummi ya yinda ta yaye labulen dakin tareda cewa, "kin ga dai tun jiya bata jin dadi don Allah ki shafa mata lafiya mana,
"Kin ga Ummi ki fita a idona na rufe, ko kuma in saba miki wallahi ni ban haife yar da zata dunga mun wa'azi ba tana takura min kinyi kadan, baki isa ba wallahi, dakin Sapna ta nufa tareda cewa "ke kuma bakar munafuka ki fito nace ko kuma mahaukaciya uwar ki ce zata zo ta dafa muna abinci,
Tun daga cikin daki Ummi ta dinga jiyo sautin kukan Sapna, domin kuwa duk sanda Inna ta kira Umman ta da mahaukaciya toh fa ranar Sapna wuni take tana disgar kuka, sosai yarinyar ta dinga bata tausayi, Ummi zata shiga dakin ta kenan, budar bakin Inna sai cewa tayi,
"Wallahi ki kaje kika rarrashe ta, toh ban yafe nono na da kika sha ba, shashashar banza kawai wace bata san ciwon kan ta ba, Ummi dai shiru tayi tana kallon Inna daga bisani tace "Inna kiyi hakuri me yayi zafi haka,
**************
"Gimbiya ta abin so awaje na, kin san dai ina son ki sosai fiyeda tunanin ki, kuma nasan kina min biyyaya, bakya yin jayyaya dani, toh yau ma ina son ki min biyyaya, ki saurare ni da kyau" "Toh shikenan Mai martaba Allah ya kara sawon kwana ina sauraren ka" "Allah shi miki albarka, Khadija ina son nayi Yarima aure,
Gimbiya tsoro ne bayyane karara akan kyakyawar fuskar ta, kuka take shirin yi, mai martaba ya dakatar da ita tareda girgiza mata kai alamar a'a kar tayi kuka, "Don Allah kayi hakuri ba wai saba wa umurnin ka zan yi ba, amma don Allah ka bari har sai Yarima ya ji sauki ya kuma zaba wa kan shi matar da yake so, amma a halin yanzu babu matar da zata so zama dashi sai don kudin mu da kuma mulkin ka, "mai martaba kayi min rai ka fahimce nufi na don Allah, Gimbiya Khadija ta fada ya yinda ta fashe da kuka mai cin rai,
Sosai take bawa mai martaba tausayi, domin yasan Khadija mace ce mai ilimi da sanin yakamata sam abun wani bai dame ta ba, rarrashin ta ya shiga yi tareda nuna mata amfanin auren da zai yiwa dan nasu,
nan fa ta kara nuna masa, ai ita zata iya kula dashi, nan mai martaba ya dinga nuna mata, ai wasu abubuwan bai kamata tana masa ba, wani abu bazata iya masa ba sai dai matar shi, nan dai ya dinga bata baki har ta amince, "toh amma Mai martaba wace ce matar tashi" ,ta fada tana kallon cikin idanunshi.
"ki kwantar da hankalinki idan lokaci ya yi, zaki san ko wacece", ya fada yana dauke idanunshi daga cikin nata.
"yadai kamata da nasan ko wacece sirikar tawa ko rowarta akeyimin", ta fada da murmushi kan fuskarta.
"ki kwantar da hankalinki kinsan dai bazan taɓa zaɓawa ɗana abinda zai cutar dashiba", ya fada yana dan dafa kafadarta.
****************
Sapna ce ta fito murhu ta fada, kafin ta daura gangarememiyar tukunyarsu lamba 10 kafin ta tashi, ta dauki niƙan su ta , kai a achan ta tsaya har aka niƙo musu kafin ta dawo, rariya ta dauka ta fara tankaɗen dawar da takai niƙa, kafin ta gama har ruwan ya taso, hakan yasa ta talga.
tana cikin aikine Baba ya shigo, dafa kanta ya yi yace, "Allah ya yi, miki Albarka Allah yasa ki zama wani abu a rayuwa", ya fada yana maida hawayenshi.
"to Ahmadu , su kuma nawan da baka sa musu Albarkar sai sun zama wani abun", ta fada tana jifarsu da harara, shidai bai ce komai ba, ɗakinshi ya shige.
da sauri Inna tabishi tana cewa ", to kawo abinda ka samo ka wani wuce daki zugui-zugui sai kace wani na Allah", ta fada tana dalla mishi harara.
da sauri ya fiddo kuɗin ya miƙa mata, "Kai! Ahmadu karka rainamin wayau kace wannanne kaɗai kuɗin", ta fada tana huci kamar ita ta nemo kuɗin.
"Wallahi Tabawa iya kun kuɗin da nasamo kenan yau", ya fada da alamar tsoro cikin maganar tashi.
"ban yarda ba tashi, na cacikeka ", ta fada da tsawa, jiki na ɓari ya tashi tsaye, wanda nida Omu Juju gaba daya saida mukaji tausayinshi.
saida ta gama cacikeshi tsaf , kafin ta dunguri kanshi tana cewa ", dallah matsa chan lusarin Namiji , mutswwww"ta fada tana karasawa da tsaki.
bayan Sapna ta gama abinda takeyi ne tsaf, na aikin gida kafin ta fara kicininyar dafawa Inna Shinkafa da wanken da takeyi mata tallah.
kafin ta gama har an fara kiran magrib hakan yasa, tana gamawa ta dibo ruwa a tuƙa-tuƙan Unguwarsu tayi wanka haɗi da Alwallah tayi Sallah tana gamawa Inna ta daura mata Shinkafar fita tayi domin tafiya gurin , da take zama.
Mazane cunkus gurin masu karta nayi masu , busa sigari na.........
*muje zuwa....*
*ZAKU IYA TURO DA KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN👇*
*1499884120 UMMA SALMA SANI ACCESS BANK.*
*KO KUMA WANNAN ACCOUNT DIN👇*
*2153892190*
*U.B.A BANK*
*MARYAM YUSUF*
*IDAN KUN TURO TO KU TURO DA SHAIDAR BIYANKU TA WANNAN NUMBER👇*
*****
*KO KUMA WANNAN NUMBER DIN* 👇
*****
*ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️, TARE DA SAHIBAR ROYAL STAR*💫